Showing 291001 words to 294000 words out of 388021 words

Chapter 98 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8249

da kafa,
Tun zaman shi a gaban mu nake kallon irin yadda yake wani kashe Idon shi a gabana,
Ya mike fuskan shi dauke da murmushi, tare da cewa OK kukula da kan ku saboda taron mutane,,
Har ya fara tafiya sai kuma yaja ya tsaya ba tare da ya juyo ba naji ya sauke wani sanyayan ajiyan zuciya tare da cewa,
Ban son naji matsalan komai daga ko wani bangare duk abinda za,ayi kuyi hakkuri akai,
A hankali na gyada kaina alaman to tare da cewa insha Allah,,
A hankali yadan rakwafo ya mika hannuwan shi a kumatun dan jaririn wanda ke rugumay a jikina yana shan nono a hankali,
Yakara mika hannayen shi ya shafo gashin kan yaron mai laushi a hankali tare da sauke a jiyan zuciya mai dan sauti,
Allah ya raya muna kai ya furta a hankali tare da sauke dan ajiyan zuciya daga gurin da nake na amsa a hankali da cewa Ameen summa ameen,
Daga haka ya sa kai yabar dakin yayin da nabi bayan shi da kallo irin na so da kauna, wanda iyanzu so biyu ke tsakanin mu ?ida shi,
Gana zumuncin da muke da shi gana aurataiyan da yanzu ya shiga tsakani na dashi,,
A hankali na dan rutse idona tare da rugumay dan jaririn dake makale a hannuwa na yana ahan nono,
Wani irin son yaron ne naji yana shiga kowani sassan jikina a hankali yana ratsani a hankali,
Tun haihuwan yaron ban samu lokacin da nai mai irin wanan rikon ba saboda a koda yaushe akwai jama,a a tare da mu a dakin,
Nakara kai idona a hankali ina mai kara mashi kallon tsab nake ganin kamar shi da mahaifin shi tankar kaki,
Wani dadi naji ya kumay min zuciya, na a hankali nake jin son mijina da dana yana shigana,,,
Shiko yaron sai shan nonon shi yake ta sha batare da ya nuna koshi ba, a hankali na aza hannuna a kan shi ina dan sauke ajiyan zuciya,
Jin a shigo dakin yasani saurin bude idona da suke a lumshe ina kallon mai shigowan,
Anty Sadiya ce da Salawatu idon ko wacen su ya na a kan dan jaririn dake rungumay a jikina,
Sannu ku da zuwa nake masu tare da kokarin nuna masu gurin zama,don su zauna,
A,a, dadi ga hannu ana shan nono ne haka, inji anty Sadiya tana kokarin zaunawa, a bank n gadon dakin Dije,
Salawatu sai bin dakin take da kallo kamar wace ke son ta kwankwance komai na dakin a lokaci guda,
Cikin hausan nan nata take cewa ashe, a nan kuke zaune, ai ina ce ko a can part din su parents dinki kike zaune,
Duk da banji dadin zancen ta ba sai nadake ina dan yake fuska kamae da gaske,
Ina cewa, ai muna nan gurin malam tsoho muna shan dadin mu abin mu,
Tace cikin hausan ta da ba pure ba, ai sai ku mu kan idan mune ai baza mu sha wanan dadin ba gurin wanan tsohon mai nuna wariya,
Abinda bazan yarda ba dashi ke nan na juyo ina ce mata, amma wanan ki dai fadi ne don ko muna fuki bazaice hakan ba a kan malam,
Kafin tai magana Anty Sadiya wace ke kokarin gyara dan jaririn a hannu ta, tace wai Meenatu wanan katon baby haka,
Gaskiya kinyi kokari sosai, kuma ance ba,a asibiti kika haihu, ba, murmushi kawai nai mara sai muka ci gaba da dan hiran mu sama sama,
Salawatu tana daga gefe sai wani basarwa takeyi kamar zata fashe, ban san may ta gani ba take hakan,
Muryan ta mu kaji tana cewa kina nan ne zan tafi in dan huta, don dama nayi zaton cewa, wanan mai masifan yana nan ne,
Ganin ta mike zata tafi ba tare da ta dauki yaron ba nace mata, baki dauki dan nakiba zaki tafi,,,
Ta wani dan yatsune fuska tana cewa ai muna gari idan na dawo zan dauke shi,
Nace, haba, Maman boy kada yai fushi dake fa yai maki kuka, kin ki daukan shi,
Dije ce ta shigo dakin tana cewa Meenatu baki fa aha ruwan zafi ba tun dazu,ina lura da ke,
Dukawa tayi tana kokarin zuba ruwan zafin da kunun kawa a cup din,
Gaba dayan su hankalin su yana gurin ta daga gurin da Anty Sadiya take zaune take cewa aikina fama da shan ruwan zafi haka,
Fitan Salawatu Anty Sadiya tace, rabu da ita bazata dauki yaron ba, don tana da wani manufa a ranta
Yanzu haka kafin shigo nan ina jin suna waya kin san mun samu wata sabuwar yar iya a gidan,,
Mama Dije ta dago da roban ruwan zafinda zan sha a hannun ta tana cewa ,
Sai dai su mutu amma basu iya komai da jinin malam,
Dama nasan ita yar gidan zabarmawa ba son Allah da Annabi takewa maisunan malam ba,
Anty Sadiya tace ina ma kika sani Dije ai sai kin zayna da ita zaki fahintan ta sosai,
Nan Dije ta shiga zage zage nidai ina kurban ruwan zafina zafi yakai min ko ina kuma dan sauraren firan su a hankali,
Nan na fahince wasu halaiyan Fatima daga gurin anty don haka nasha alwashin yadda zan zauna da ita, idan na koma,,
Aiko Dije tana fita tafara aibanta Salawatu ce wa tana kishi har taki daukan jariri,
Abinkada yan uwa sai ran yan gidan mu ya baci suka shiga sakewa Salawatu habaici da bakar magana,
Nan da nan ta tsargu ta daina wani iskanci da tai niyar yi akan mu,

Su Baba Wadda da Baba Hamza motar suce shigowar karshe don haka suna shigowa suka wuce gidan Anty Safiya suka sauke kayayyanki da aka umurce su, sukai gidan ta,
Sun iso gidan mu da dare sosai amma duk da haka sai da suka shigo cikin gida don suga Baby,
Murna gurin mahaufiyar Baba Wadda ba,a magana ganin irun yadda dan ta ya sake a lokaci guda,
Sunyi murna sosai da ganin mu kamar yadda nima nai farin ciki sosai da ganin su,
Suna cin abinci suna min hiran irin abinda ke wakana agidan mu yanzu,,
Suna sheda min yadda ake kwasa tsakanin Salawatu da Fatima amarya, Hamza yace,
Wallahi Amarya duk na matsu ki dawo gidan duk ya koma ba dadin shiga, yanzu,
Murmushi nayi ina cewa gaskiya ba yanzu ba saboda, sai munyi wata uku a gida muna shan ruwan zafi,
Duk basu ji dadin abinda nace masu ba saboda su a zaton su da anyi suna tare zamu koma dasu,
A dakin Baba Ramatu ta samay su tana masu sannu da zuwa, nan ta zauna muka dan taba hira dasu sukai min sai da safe,
Baba Ramatu tace a dakin da nake zata kwana saboda haka ta gyara kasa wai a nan zata kwanta,
Ranan zuwanta dakin yai muna dadi don mun samu barci sosai itako tana ta fama da dan jaririn mai kukan dare,

****** ********** ******
Dakin Mama Ladi yau tab yake da jama,a sai kace ranan ne suna, saboda irin yadda gidan ya cika,
A gurin da suke zaune sai ga dan sakon Hajja ya shigo dauke da gallon din manshanu da shinkafa a cikin kwanon kaya,
Dakin shiru yayi saboda jin wace ta aiko da sakon don haka sai Anty mai mumunace tai karfin halin karban kayan tana cewa
Kai du dukka inji Inna Hajja tace a kawo a Kara a sha,anin buki aiko walle angode,
Yaune rana na farko da Mama Ladi taji wani irin tsarguwa akan wanan sakon da, Hajja tai ma,
Duk wanan irin abubuwan bata yarda cewa Hajja zata iya cutar da ita,
Sai gashi yau zuciyar ta ya nasa mata zargi akan kayan sakon da Hajja ta aiko mata da suwa,
Amba yaro naira dari tukwici, ya wuce yana murna, tare da godiya,
Dakin da take tara shirgin kayan aikin ta wanda ba,a kwana acikin shi tace a kai a aje,
Abin gidan waya labari kus,kus har ya fada kunnwn malam tsoho hakali a tashe ya shigo har part din Mama Ladi da kan shi,
A lokacin bayan sallah la,asar ne, ganin shi yasa kowa maida hankalin shi gare shi,
Yace Ladi ina kayan da Hajja ta aiko dashi gidan nan suke samm Mama ta manta da zancen kayan sai yanzu da malam ya tambaya,
Dark n aka shiga don a dauko kayan aiko sai ga Anty Mariya da gudu ta baya tafuto waje daga dakin tana cewa Innalillahi Innalillahi,
Innar mu ba man shanu bane cikin gallon jine ne da tsutsoci ba shimLkafa bane tsutsoci ne,
Daga gurin da malam yake a tsaye yai murmushi yace kun kuru da kunci shi da kunci bala,i sosai,
Da kan shi ya shiga dakin ya fiddo da kayan waje kafin ace haka jama,a sun cika guri aciki harda Sadiya wace ta fashe da kuka a lokaci guda,
Mutane kowa yagani sai hankalin shi ya tashi don tsoro take masu iska suka fara hawan iska gida ya rude a lokacin muna daki ni da baki, na
Wanan labarin ya samay mu aiko duk suka tsorace, suna, ta addu,an neman tsari,
Mama Dije ta shigo dakin a rude tana cewa kada kifita ko nan da kofa Meenatu yau gidan ba lafiya, nan ta kwashe duk yadda akayi ta fada muna,
Tace aiga malam can da tawagan shi har da mai uguwar shiyan mu sun tafi gidan nata da kayan,
Anty Sadiya tashigo gidan gurin yae uwarta da kuka nan suka labe a dakin sadiya can sabon part din mu da yaya yagina wanda a nan suka sauka, gaba dayan su suna dan tataunawa, yadda za,su yi,
Nan akaci gaba da shagulgulan buki kowa ya fita batun zancen don dama ai kowa yasan cewa muguwa ce,
Sosai maigari yai mata kashedi da gidan mu ida akace idan aka kara jin wani abu ya shiga tsakanin ta da mu sai andaureta,
Shiko yaya Abubakar cewa yayi duk wani abu ya samu iyalin shi wallahi itama sai ya kashe ta
Wai ita wace irin muguwae mace ce haka da nacin tsiya ro wallahi sai asirin ta ya tonu tunda tashiga gonan shi haka,
Andai, tatausa maganan akace abar zancen tunda yarta tana a cikin gidan don haka abar maganar har a gama zancen suna tukun,
Kunya da tsarguwa duk suka taru suka rufe Sadiya saboda irin abin kunyan da mahaifiyan ta taja mata a gidan auren ta,,
Kamar yadda malam ya umurci kowa akan a share zancen aci gaba da sha,anin bukin suna hakan ne ya faru kowa na harkan gaban shi,,
Mama Ladi wace taga har dare Anty Amarya bata zo garin ba yasa ta yin magana,
Tana zaune gurin da ta idar da sallah magaribba take cewa karyan banza aidama nasan cewa baza,a iya fida sufe wuta ba ,
Ita wanan macen mai gwada min wai ita wata tsiya ta gashi shiru bata ko zo sunan ba,
Mariya tace ina ko zata yarda tazo, ta kashe kuddin ta ga banza tunda wa yanda ma sunka haifita banga sunyi komai da za,aci a bangaren su ba,
Koda yake haka sunkayi na kunun kauri gani shi dasu dai munkayi, miyan kan kauri na dai sunka dafa cikin gidan ga,
Hira sukai tayi suna aibanta min iyayyena wai sai munyi kunya don komai bamu aje ba na fita kunya, a mahaifina kullun sai fita da gwangwaraman motar shi wai bidan kudi amma komai ba aje ba,
Wasu suce wai don sunga anyi aure na basu kashe kudi ba shiyasa yanzuma suka sake jikin su ai masu,

****** ********** ******
Zanen suna akayi, irin na mutanen da abisa umurnin malam tsoho, antaru kamar yadda ba taruwa bukin yan dangi
Yaro yaci sunan Shi Mohammad Buhari, inda mutane suka ji dadin wanan sunan da akasakawa yaron,
Anfito da abincin liyafa jama,a sunci sun sha sun koshi Masa dafa duk kowani da nama a cikin shi, ga abinsha hade da ruwan gora,
Mutane sai ci da sha sukeyi suna jin dadin su yan uwan mahaifiya na suyi kokari maza don da su aka zana suna tunda safe suna garin,
Hakan yasa aka ware masu nasu acan cikin wani rufa daga gefe guda na kofan gidan mu,
Sosai a ka karrama su da nau,in nau,in abinci tare da abin sha masu tsada, sunji dadin hakan da akai masu, sosai,
Shanu da raguna biyu aka yanke wanda hakan ba wani bakon al,amari bane don haka al,adan yan kasan birnin kebbi da kewaye yake,
Amma duk da haka al,adan yake saida Mama Ladi tai fadan cewa don zai yanka harda shanu, ai raguna biyu kawai sun isa basai ya hada da shanu ba,
Tai ta mita wai yanzu duk mutanen gida kwashewa za suyi a cinye
Da ta kirashi tana mai fada cewa don mai zaiyi hakan a cinye naman a banza ,
Sai cewa yayi haba mama dama ai don aci na yanka don kowa ya samu in ma bai isaba sai akara wani mana kowa ya samu,,
Wanan maganan yasa ran Mama ya kara baci sosai, don haka a hasale tace wai ko mai sunan malam kana tanadi kuwa, ?
Dariya sosai da mamaki Mama ta bashi don har yanzu dauka yaro karami take mai,,
Bai iya cewa komai, ba yasa kai kawai yafita, abinshi yana mamakin irin rayuwan mahaifiyar shi,

Wani dogon rigan nasaka a jikina din half atamfa half material yaji stones agaban shi,
Tsayawa bada labari irin yadda nai kyau, bata bakine, saboda duk wanda yaganin sai ya ce tirkasa,
Labari ya kai ga yan uwan Yaya na cewa nasa wasu irin hadadun kaya a jikina,
Daya bayan daya suke shigowa part din malam tsoho don ganewa idon su irin shigar tawa
Jeloup din shikafa sukayi da kuma masa da miya, suna ba mutane da makwabta da yara,
Anty Samira ce tace, wa yan uwan ta a samu abu a dan diba akai muna ni da iyayye na,
Aiko sauran sukayo cikin ta tankar za su cinye ta danya a lokacin Anty Safiya bata dakin dole taja bakinta tai shiru,
Bini, bini Mama Ladi tana turawa wai a je part din mu a duba mata ko may muke ciki,
Zuwa karfe goman Safe motocin yan uwan mu suka iso unguwar motace bus har guda biyar sai kananin motoci, guda hudu take gida ya rude da ihun murna,,,
Nan aka shiga fito da kulolin abinci kala kala da aka dafo daga sokoto gidan uncle dina,
Tuwon semo tuwon Amala, tuwon shimkafa, masa fara kal, sai shimkafa da miya yaji corsole iri iri, nama kaman ba,a san zafin kudi ba don shanu dan madaidaici ne aka yanka akai hidima dashi,
Mata yan uwan Anty Amarya da kuma kawayen ta da makwabta duk sun biyo ta acewan ta wai bukin First Born din tane ni,
Gida yakara rudewa inda Yaya Abubakar da Aliyu tare da Lawal mijin Fattu suka nufi Bindawa plaza suka kwaso masu kayan sanyi masu tsada,
Katon Katon aka jibge su a part din mahaifana sai a lokacin Anty Amarya wace ta tsaya saida taga duk bakin su sun samu gurin zama sannan tasa matan togo da tazo dasu su shiga raba abinci,
Wasu manya kuloli da ta tana tare da mukarraban ta suka nufi part din Mama Ladi da su sukace ga abincin Daki na na yar kuryan daki da suka dafa aka debo mata nata share din,
Duk wace ta bude kulla taga irin abinda ke ciki sai kaga an rufe a na kada kai don mamaki,
Suna fita Anty mariya tace tirka sa ba,ayi ba yanzu za,a yi innan mu kin koga wa nan garalin haka,
Vikin muryan nata mai kamar i,iniya tace duk burgan banzata anyi ne dai don mugani yanzu haka kila nasu wanda zasu cci babu komai ciki duk lami na,
Sai wata mata saga cikin yan uwan Mama tace walle ko na yaran da aka zuba kamar duk namana zallah,
Mutanen kebbi kowa ya san su da son nama kaman kuraye saboda zama da mutanen zuru,
Don haka kowa zancen nama kawai yakeyi irin yadda aka gwada shi kamar banza,
Duk part din gidan mu saida aka kai masu abincin da akazo dasu kala kala kowa ya lasa,
Munkai wani lokaci da Anty na muna dan tataunawa kan al,amura ida na rasa irin godiyan da zan masu ita da Uncle dina da mahaifa ,
Bakina yan Abuja sunci sun sha sun kula na zuwa gida har sun gaji,
Haka masoya Meenatu da Abubakar suka dinga shigowa gidan ban ko san su ba suna min barka da ma bani gift,
Nayi shiga ta alfarma har saida hankalin Salawatu da ?nty Sadiya ya tashi tun suna gulma a waya da Fatima har tagaji ta shige dakin ta ta ki fitowa don ta kaici,
Taiturawa akira mata Yaya Abubakar amma bai samu zuwa ba don haka tai mashi text da cewa,
Macuci dancin amana wanda ranan lahira zai tashi da part guda,
Wanan sakon yashi shivo cikin gida da idonshi da suka kada sukayi jajir,
Yasamay ta kwance dakinta tana kuka yana shiga yace wani irin text ne kika turo min dashi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login