Showing 312001 words to 315000 words out of 388021 words

Chapter 105 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8233

Sadiya wace bata ko fitowa balle ta nuna kulawanta ga aminiyar uwar ta tana dakin ta akoda yaushe,
Azaton su maigidan bai fahinci irin zaman da sukeyi da mahaifiyar tashi ba, tunda baya zama gida,
Ranan da yake gida weekend suka so su gwada makircin cewa ai suna kula da ita,,
Ba wani boyo Mama tai masu tas a gaban shi abinda ya bakan ta wa Yaya Abubakar rai gaba dayan su ranan sai da rayukan su ya baci da shi,
Don jajirce masu yayi akan cewa sai sunbar maigidan shi don baiga amfanin zama dasu da yakeyi ba,
Tunda mahaifiyar shi bara da daraja a idon su da zaisa ta samu daran a kula mai da ita,
Sai da kyat su Lawal da Anty Mariya suka samu ya hakkura amma gaba dayan su ya daure masu babu wace ke ganin fuskan shi,
Ganin cewa Mama taki kwantar da hankalinta yasa shi ba shiri maida ita gida, don ta samu lafiya yanzu sosai,,
Wanan tafiyan sunyi shine tare da Fatima kamar yadda yai mata alkawari cewa zai zo da ita idan ya dawo, din,
A Motan shida Fatima ne zaune a gaba sai Mama da mariya a baya a hankali yajawo su har suka uso gida Birnin kebbi,
A wanan lokacin ina da sauran two weeks nagama exam dina don haka muna sokoto ,
Kwanan su biyu ya shirya yadawo Abuja saboda aiyukan da sukai mai yawa a office tun dawowan shi saudiya din,

****** ********** ******
Muna gama exam da kwana kamar uku mahaifina ya bugo min waya yana tayani murna da fatan alheri,
Inda bayan mun gama waya yake ce min Aminatu yaushe zaki dawo don ku shirya komawa, dakin ki,
Wani irin dam naji gabana yaba da don in akwai abinda ke sakani faduwan gaba a yanzu shine zacen komawa na da zama Abuja,,
A dan daddare na amsa mashi da cewa tau baba zan dawo zuwa wani sati insha Allah,
Allah yai maki albarka naji yace tare da tambayana Amir da sauran yaran uncle,
Mungama waya da mahaifina sai nakejin wani irin zufa yana keto min daga cikin jikina,
Gashi a lokacin Anty Amarya bata gida don duk kwanakin nan bata zama sai sintiri takeyi wanda a tunane na hankan yana nuna tana wani abune na muhinmin wanda bai barin ta zauna gida,,

Jikina duka a mace har zuwa lokacin da, Anty ta dawo gida ta samay ni a hakana ban cikin dadin rai,
Tana kokarin cire hijab daga wuyanta yayin da idon take gareni a inda nake a tsaye daga gefen gado ina dan jijiga yaron da nake goye dashi a bayana,
Halan mi ankayi tamabayan da ta, jefo min ke nan tana jefa hijab din ta a saman kujeran dake dan falon part din ta,
Sauke ajiyan zuciya nayi ina cewa cikin dan washe baki babu komai anty,
Saida takai zaune saman kujera hannun ta yana a cikin jakan ta take cewa,
Lafiya kalau fa nafita na barki amma yanzu na dawo nasamay ki fuska babu annuri,,
Nadan yi dariyan yake again nace ba komai bane dama Baba ya bugo min waya yana ce min na shirya na dawo zan koma Abuja,
Tace cikin dan daure fuska aini na sani tunda na taho naga fuskan ki haka babu annuri a tare da ke,
Tace shin wai ke Meenatu in tambaye ki, mana don Allah,
Wai matan, ga da kike fargaban zama da su ba mata bane yan uwan ki,
Komai naku dayane, halinku guda dabiar ku duk guda ne, gurin kokarin kyautatawa miji,
To may zai baki tsoro yanzu kamar wata bakuwar harka can,
Shi kodai ira wagga amaryan taku kika tsoro,ne wai,
Da sauri, na dago kai na dube ta tare da girgiza kaina cikin murya mai kama da ta mai son kuka nace,
Anty ni wallahi duk ba wanan ba ni dai yadda zan zauna da wanan karamin yaron kuma tare da miji,
Shiru naji anty tayi tare da kura min ido can tace yau ko Allah ya gwada min Meenatu,
Shin komai bana Allah bane kin taba ganin mutum ya wuce kaddaran shi ne a rayuwa,
Shiru nayi ina kallon ta inda naga tadan kwantar da murya kasa kasa tana cewa babu abinda zai samay ki da yardan Allah Meena ki kwantar da hankalin ki dan Allah,
Abubakar yana kaunar ki bazai bari su cuta maki ba ko kadan don haka duk wani abinda nai maki, nasiha akan shi don Allah kiyi kokarin kiyayewa,
A take idona suka ciko da hawaye ida taci gaba da cewa, ki gyara zaman ki tsakanin, ki da ko wacen su,
Namiji shi baruwan shi idan ya ajeku shike nan shi , bazai damu da yasan may ke gudana a tsakanin ku ba,
Don haka nake son ki kara kwantan da hankalinki da su kiyi nazarin irin rayuwan kowacen su,
Nace cikin muryan kuka ina mai goge kwalla da cewa tau Anty,
Tace daga kan yaron ki zaki zaki fara fahintar so na tsakani da Allah,
Duk wanda ke son dan ka yana kaunar ka kaima don da bai kaunarka bazai kalli inda kake ba balle danka,
Don haka sai kiyi taka tsantsan don , yanzu dakin koma idon su gaba daya akan ki zai koma don su samu wani abinda zasu camfa a kan ki don kawai suyi black mail din ki,
Musalai masu yawa anty ta dinga kawo min don nayi taka tsantsan da mutanen da zan koma na zauna da su a can,
Nan dai na samu hanyoyin da zankare kaina daga duk wani, sherin da za,a iya kullamin,
Naiwa Anty godiya sosai tare da mata fatan alheri a rayuwan ta,,
Tun daga lokacin na fara shirin komawa gida BK kamar yadda Mahaifina, ya umurce nida nadawo gida,
Sai da zan dawo ne nafahinci ashe ba karamin shirine, Anty tai min ba, don duk wani abn da akewa mace idan zata koma dakin ta,
Duk wani abinda zan bukata na rayuwana acan saida aka hada min shi tsab,
Har wanda zan iya sharin da sauran matan gidan duk an hada min su, abin mamaki hardasu, dubbula da alkaki, da cake,
A sokoto anty ta saka akai min kitso da su lalai mai kyauda daukan ido,
Dan jariri nama an mai aski an saya mai man gargajiya masu gyara fatan jikin yaro irin su alaidi mankade, man albasa da sauran su,
Tunda safe mu kayi sallama da mutanen gida inda uncle dina yai min yan nasihohi, masu kashe jiki, anty na take ce min zata zo, BK kafin na wuce ai,

****** ********** ******
Agidan mu ma naga irin shirin da akaimin irin na yar gata don komai ansiyamin,
Wanan ya kara tabbatar min da cewa tafyata yazo ke nan,
Nazo BK washegari da yamma sai kawai ga anty Amarya ta iso itama ta samay mu,
Ashe waida safe zamu bar gari zuwa Abuja, saidai wanan karon mun canza hanya ta garin Minna na Niger state zamu bi,
Nasamu nasihohi agurin kakana da iyayyena tafiyan mu ya samu yan rakiya Dije da mama sa,a sai Anty Amarya,
Na shiga part din Mama Ladi don muyi mata bankwana,,
Tana daga zaune gurin da ta idar da sallah muka shiga part din nata, na durkusa har kasa ina mata, sallama,,
Bata samu abinda ta ce min ba sai ido da ta dan tsura min kamar, mai tunanen abinda zata ce ,
Ina kokarin mikewa don a tsanmani na ba tada abinda zata ce, min, muryan ta naji tana cewa Allah ya tsare, min Dana daga duk wani kulle kullen da a kai mai,,
Murmushi na sake inda na,amsa da karfi dacewa Ameen ya Allah Mama nagode, sai anjima
Ban karasa fita daga part din taba naji muryan ta tana cewa, ai zaki je ki samu yan iskan matan gidan nan naku kukwama dasu,
Kaina girgiza tare da sake yar fara,a a fuska na azuciyata ina cewa duk yadda akayi Mama bata sha da dadi ba ke nan zaman ta da su can,

Mama ladice ta saka c cewa bazamu tafi da jikan,taba Aisha wace ta ke lake dani
Nayi sallama da kowa agidan mu ida yan uwa suka gwada min soda kauna kamar kada na barsu,
Har mun shiga mota ana batu tashi Aisha tana ta kuka harda birgima akasa ,
Cak Baba musa ya dauko yarinyar ya sakata a cikin mota mu ka wuce da ita zuwa Abuja,,,
A take Mama Ladi tashiga surfa masifa da jidali, babu wanda ya tanka mata daga mazan gidan har matan gidan babu wanda ya tanka mata,
Har tagaji ta kyake don kanta tana cewa sai ta shiga mota har Abuja, ta dauko jikin ta,

Babu wani wahalan da mu kasha a wanan hanya sai hiran mu muke a tsakanin mu,
Mama Dije sai mamakin irin yadda garuwan da muke, wuce irin girman su yake,,
Musalin karfe, hudun na yamma muka isa gidan mu inda gida duk ya canza muna a fuska,
An,kashe,naira na gugan naira a wanan guri gaba daya duk gidan ya sake ni kaina ban gane gidan ba,
Mun samu su Baba Wadda da Baba Hamza a kofan gidan suna jiran isowar mu, a lokacin,
Sun yi farin ciki sosai daganin mu inda suka kasa boye farin cikin su a fili,,
Da taimakon su muka isa part dina inda muka yada zango a falon dake cikin part dina dake dauke da dakuna uku a cikin shi,
Mun zauna bamu dade ba saiga Fattu da Baba Ramatu dauke da kulolin abincin da su ka girka muna, kafin mu zo,
Duk hayaniyar da, muke agidan babu matan gidan ko guda da ta leko mu daga part din ta,
Ga su Baba Wadda da Hamza' suna magana a cikin daga murya,
Mun ci abinci munyi sallah, muna zaune anty Amarya,suka mike ita da Fattu suka fara zagaya part din,
Salawatu ce tashigo tana rike da dankwalinta a hannu tana kokarin daurawa a kanta,,
A,a bakin KB ne mukayi haka babu ko labarin zuwan ku yau din,
Fusakana dauke da murmushi nake cewa a,a Amaryan Yayana ne mun samay ku lafiya,
Ta wani dan tabe baki tana kokarin zuwa gurin da Amir yake tana kwance a saman kafan Dije fuskan shi a sama yana kallon ruping din dakin,
Tabani ansa da cewa aikunsan inda Amaryan ku take don yanzu ni ban yarda da dadin bakin ku,
Bayan ta dauki yaron ne take cewa a,a Baba may kake ci haka ka girma hakan ga ka yi wani irin nauyi,
Da ga gurin da take tsaye take wani kare min kallo, cikin mamaki, nafahinci may takeyi don haka, nakara gyara zamana don ra kalleni da kyau,
Taima yaron dan wasa sanan tai muna a huta gajiya mu kai mata godiya,
Sadiya da Fatima basu shigo ba har mukai sallah magrib muna zaune sai hira muke acikin raha da dariya,
Baba Ramatu da Fattu sunata aikin saka kowani kumshin kayan da mukazo da shi,
Sadiyace tashi tana wani daure fuska tana dan dube dube kamar yaune farkon shigowan ta part din,
Taimuna sannu da zuwa tare da cewa ashe kuna hanya ne yau din nan,
Daga haka batace uffan ba tajuta tabar dakin cikin kokarin dan danna wayan ta,
Gabadaya aka bi bayan ta da kallon mamaki don sam ba,a zaci hakan ba daga gare ta,
Shigowan yaya Abubakar a gidan direct part dina ya nufo don yai muna sannu da zuwa
Fuskan shi yana dauke da annuri, yake masu sannu da zuwa,
Nan suka shiga wasan barkwanci da mama Dije tana ta mai ba,a na jika da kaka,
Ban san da shi ba afolo nafito daga cikin uwar dakin ina dariyan zancen Anty Amarya,
Ganin shi yadan sani jin wani shock har saida na nuna re,action a fili,
Cikin dan rudewa nake ce mai sannu da dawowa cikin murmushi tare da lumshe idon shi yake cewa Maman big man, ke nan,
Acan cikin kwanyan idon shi na hango wani irin sakon da yake sanar min,
Na dan dukarda kaina saboda jin nauyin irin kallon da yake min a lokacin,
Salama Fatima ne wace ta caba kwaliya cikin wani material sai shining yakeyi an mata dinkin skirt da riga sunyi tie din ta sosai,
Sannu ku da zuwa take cewa cikin sakin fuska take wani yin far da ido tana kada jikin ta ,
Gaba daya idanuwan mu suna a gareta muna mata kallon mamaki,
Bata ko juya gurin da yaron yake ba a kusa da mahaifin shi sai kokarin son ta hada ido da maigidan takeyi amma shi hankalin shi baya gareta, lokacin,
Cikin wani murya take cewa Sweet Bukar ka dawo ashe sannu da dawowa,
Sai lokacin yadan dago kan shi yadan dubeta yana cewa yagidan ya kuke,
Abincin kafa is read kada yai sanyi a dining tundazu yake sama,
Murmushi yai kawai wanda al,adanshi ne hakan sai ka fahince shi zaka gane may yake nufi,
Kaman zata jirashi su fita atare amma da taga ba daman hakan sai kawai ta sa kai tafita daga dakin ,
Yadauki lokaci ana hira dashi dasu Anty Amarya inda suke yaba irin yadda gidan ya canza a lokaci guda,
A nan yake fada masu cewa da safe idan Allah ya kaimu zaiyi tafiya zuwa kasan Chaina saboda wasu kaya da za, shigo masu dashi,
Yace don Allah su mama Dije su dan dakata, kada su wuce har ya dawo yace zai yi magana da malam da Baba Buhari ya sanar dasu,,
Amma ita anty Amarya sai tace inda ta dan kara kwana biyu zata koma ita,don tabar yara a gida,
Yai mana saida safe yabar dakin zuwa nashi part din ,cikin jin shi a wani yanayi na daban
Fitan shi yasa anty Amarya cewa Meenatu sai kin yi da gaske akan wanan yar iskan
matar ta gidan nan,
Wai fa gaba taso ta saka shi har sai ya fita part din nan,
Anan aka shiga kullamin wani sabon bom da zan hada nima wanda zai sa ta shiga hankalin ta dani,


ZEEE. MAKAWA YELWA
[11/10, 11:04 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH AL BAR

Tsab Anty Amarya ta shirya Amir a cikin wasu kaya masu laushi, ta shafa mai oil akai sai kyali suman kan shi keyi,
Wani dogon riga na saka baki, Arabians, gown mai adon duwatsu, agaban shi jikina na murza oud collection, sai wani masifafen kamshi ke tashi,
Kyana yasha rolling da gyalen kayan wanda shima duk duwatsune jikin shi,
Takalma mai dan duduke da tsawo na saka wanda ke ba da sauti,
A kafada na sagalo yarona wanda ke barci cikin jin dadin jin dumin. Mahaifiyar shi,
Fatima ce na samu a dining space tana har hada kayan da su kaci abinci,
Hakan ya nuna min alaman cewa maigidan yana daga ciki ke nan,
Takon tafiyana gami da kamshin collection din da ke a jikina suka dira mata a lokaci guda inda ba lokaci ta juyo da sauri don taga ko wacece ke da wanan hadin a lokaci daya haka,
A cikin muryan nan nawa na baiwar Allah kama da ta rowa nake ce mata a lokacin da ta dago don ganin ko wacece,
Ok , har Yaya ya shige ciki ne ?
Ban ji may tace min ba amma da alaman Ummmh tace sai kawai na fara tafiya ina cewa, ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ri, naje mu gaida shi,
Ko da ban juya ba nasan cewa bayana tabi da kallon don na bar jin motsin hada kayan da takeyi,
A hankali nake taka step's din cikin tako da rangwada, ina mai rike yarona da kyau don gudun sabulewa,
Na kutsa kai a dakin baki na dauke da sallama, wani irin sanyi da kamshi ne suka ziyarci hancina alokaci guda,
A hankali na fara kewaye dakin da kallo ina duban irin yadda dakin ya tsaru tsab kamar wani daulan duniya,
Da murmushi a fuska, shi cikin wata irin nishadadiyar murya ya ke karba min sallama, na, fuskan shi a sake,
Yana daure da towel a jikin shi da alaman daga wanka ya fito don yana da taje suman kanshi, a hankali,
A hankali ya tako yakaraso inda muke tsaye yana cewa ku shigo mana kun tsaya a kofa,
Na tako zuwa inda yaje ya sa hannun shi ya karbi yaron daga kafada na ,
Wani irin sanyayan ajiyan zuciya na ji ya sauke tare da lumshe idanuwan shi,
Bakin gado yai min nuni da na zauna nace cikin dan daga kafada da hannaye na Nop dama kawai munzo ne mu gasheka dama,
Yace to shine ba zaku zauna ba acikin wani irin lumshe ido yake magana tare da dan shakan kamshin yaron dake a hannun shi,
Turo kofan dakin akayi batare da sallama ba inda naga ya daga kai da sauri yana kallon kofan,
Fatima ce ba sai na tsaya fadan yadda yanayinta ya ke ba don tankar an aiko mata da sakon mutuwa,
Sai wani raraba idanuwa takeyi ta tako zuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login