Showing 144001 words to 147000 words out of 388021 words

Chapter 49 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8297

ba sai mikewa nayi zuwa bathroom na hada mashi ruwan wanka,
Nafito ban tsaya,ba fuska a dan daure nace ga ruwan wanka can Yaya,
Gurin Wardrobe din shi na nufa ina son in dauko mai kayan da zai sa, idan ya fito,
Daga inda yake,tsaye, yake ce min, bazan samu cudawa ba ke nan,
Gurin gado na nufa na,fara gyara,gadon don duk mun chukwikuye shi kamar bashine na gyara dazun tsab ba,
Ya,shige bathroom ni kuma na fito zuwa, daki na don in kara kintsa jikina saboda Yaya ya bata min shiri,

Salawatu bayan shigan mu, takai yan mintuna zaune a falon taga ai ban sauko ba,
Don haka sai taji tankar ta kama da wuta don haushi, kishi nata azalzallar ta,
Kusan sau uku taje ta dawo, taje ta dawo don taga ko na sauko sama,
Abincin dake jere a saman dining table tariga da tun shigan mu tai masa ta,asa, ko,
Wanka na shiga na gyara jikina tsab, kamar bani bace, dogon riga na sa wanan karon,
Misscalle din Anty Samira na samu har uku, ta kirani don haka na,dauka ina ce mata, ta ai ina gurin naji yadda su kayi amma ta bari zan kirata insha Allah,,
A gurguje na fito falon fuska hade don yau kan gaskiya mun makara sosai ba mu ci abinci ba,
Anty Sadiya bata wasa da cikin ta tana falo zaune, tana jiran fitowan mu tare muka fito da maigidan don zan shiga kitchen naga saukowar shi,
Jug na,dauko wanda na hada muna zobo,drinks a cikin sa,
Salawatu ce karshen fitowa fuskan ta tamau, ba bu walwala a cikin sa,
Ni dake da girki nice zaune a kusa da Yaya Abubakar, ina zuba mai abinci a plate,
Sadiya itace tafara cin abincin tana kai cibi a baki sai tai saurin furzarwa,
Cikin wani irin murya na mamaki tace Meena, ? Tana mai min wani irin kallo,
Abincin na kalla sai kuma na,dago ido na kalleta,
Kafin in sauke idona sai naji Yaya Abubakar daga gefe na ya furzar da nashi wanda ya fara kaiwa baki,
Yaya akayi haka ne wai ?
Ya tambaya cikin bacin rai da kuma mamaki fuskan shi a daure,
Diba nayi daniyar inji may suka ji, gishiri ne kamar zai daye bakin mutun don kaifi,
A hankali nace gishiri a girki na ?
Sai kuma nai murmushi ce, to nima ban sani ba don ban girki da gishiri ni,
Sai dai ban san ya akayi kuma gishiri ya shiga ba, haka don ban ko ga roban salt din ba ma ni,
Salawatu tace bama zan ko ci ba don ban shiri da gishiri ni,
Amma dai ai ya kamata ki kula da yadda zakiyi girki kada adinga barnan abinci,
Sai da na rausaya kai kadan ina mai kokarin maida abinci a cikin kula nace,
Sai dai kuma ba yaune farkon girkina a gidan miji ba ban taba samun akasi akan girki ba,
Yau din ma dai kalau nai girki na don min ina da shedan hakan,
Enough please na fada maku cewa ba zan lamunci, cacan baki ko wani abu irin haka a gida na ba,
Gaba dayan mu shiru mukayi yayin da shi ya mike ya suri keys din motar shi yafita batare da ya ce wa kowa komai ba,,
Na kwashe kayan rai bace na mayar kitchen, ga abinci lafiyayye amma na rasa yadda zanyi da shi, don bai ciyuwa,
Daki na shiga na kira fatu ina tambayan ta ko hamza yana gida, tace yafita tun,da yagama cin abincin da na basu,
Nace don Allah Fattu ko kinji yana cewa da gishiri a ciki tace a,a don cewa ma yayi zai kara gishi don baiji mai ba,
Saida mama tai masa fadan cin gishiri shi ne ya fasa zubawa,
Ajiyan zuciya nayi don nagane cewa sheri akai min a gidan don a hadani fada da Yaya Abubakar,

****** ********* ******
Cikin, murna ta daga wayan ta tana kiran noban Lubuna ,
A a matar Oga ya akayi ne wai, ?
Hmmm bari ke dai Lubuna ai kwanan nan ina cikin yar damuwa wallahi kin san wanan shigiyar yarin matan Abubakar tazo,
Wai kin samay irin yarinyar tana son ta raina min wayyo sai don wallahi ban taba tsanmanin zan samu matsala daga gare ta ba wai sai gashi akan ta Oga yana ta wani rawan kafa,
Dariya mai sosa rai Lubuna taiwa Salawatu ta dan dakatar da dariyan tana cewa,
Kema ai kinsan dole ne sai, kin samu irin wanan challenges din daga wurin shi,
Nafarko fa yar uwar shi ce yarinyar and so what inji Salawatu,,
Murmushi Lubbuna tayi tare da cewa becareful my friend, don komai zai iya faruwa fa,
Daga haka Salawatu taci gaba da bata rabarin su irin yadda zaman su yake a yanzu da kuma sherin da fara kulla min a gidan,
Da kyau nawa inji Lubbuna kawai dai ke ma don kina son sa ne in bashi ba may zai sa ki tsaya wahal da rayuwan
Akan mutum guda har nawa zai iya baki da zaki wani tsaya har ana wullakanta ki haka ?
Ni mamaki kike ba may yafi mazan da kike hurda dasu a baya, ?
Look Lubbuna ban son yawan sa ido fa ni dai nace maki ina son abina haka na,
Sai kin ji ni again bye ba zan iya sauren kina tofa bakin ki akan abin da nake kauna ba,
Daga haka ta kashe wayan tare da jin haushin aminiyar ta wace ke kokarin zagin rabin ran ta,,
Komawa tayi saman godon,ta ta zauna tare da bushewa da wani irin dariya tana cewa,
Yarinya dani kike zance an fada maki cewa, ni din ta wasa ce,
Don dole ki bar min a binda nake kauna ko kuma ki zama yar kallo a gidan nan,

****** ********** ******
Take away ne ya shigo dasu daga waje kowa guda guda da naman rago mai zafi irin na gargajiya mai yawa a leda kowancen mu da na ta kumshi,,
Tun bayan abinda ya faru zuciya na yaki yi min dadi saboda irin yadda nake ji a raina,
Saidai ma ko waye nabar mai shi da Allah abinda kawai na ce ke nan, don idan nace zan yi bincike ta ina zan fara,
Amma dai muje zuwa da mai shi don nasan idan halin mai shine gobe ma karawa za,ayi,

Tun daga nesa nake jiyo karan cibaben spoon su suna kara,,
Kamshin naman ya doki hanci na har sai da naji shi har cikin rai na,
Maimakon in nufi dining table din inda suke sai kawai, na, nufi gurin kujera na zauna,
Fuskana babu yabo babu fallasa, acikin sa don haka bazasu iya gane halin da nake ciki ba,
Ido Yaya Abubakar yabini dashi don bai fahinci may nake nufi ba,
Anty Sadiya ce tace Meenatu zo mana ga abincin ki ki ci,
Yayan ki ya leka ya samu kina sallah yace don haka muka fara ci,
Cikin dan murmusawa nace anty bazan iya cin abinci ba yanzu,
Yaya Abubakar dake kokarin kai abinci ga baki yai saurin juyowa yana na kallo na,
Cikin daure fuska yace baza kici ba may ki ka ci da zaki ce bakya ci
Na girgiza kaina ga da cewa babu ko mai kawai dai ban jin cin abinci ne,
Ban yarda ba in ji Yaya Abubakar, don babu abinda kikaci balle ki ce bakya cin abinci,
Murmushi na dan sake na ce wallahi Yaya kawai banjin cin abinci ne,
Anty Sadiya tace ko jiyafa haka ki ka ki cin komai Meenatu,
Ki dauki ko naman ki ci inji, Yaya Abubakar yace a cikin dan yanayin damuwa,
Gaskiya inji Salawa don dai kinga, zai yi sanyu in baki ci yanzu ba,
Na mike daniyar in dauki ledan naji sallaman Hamza,
Kulan da na basu abinci shi da abokan shi ya dawo min da shi yana cewa
Ina wuni Sir sai kuma yake cewa su Anty sannu ku fa ya gajiyan gida,
Anty yake ce min duk da ya girmayni ni sa ba kusa ba amma saboda girmamawa ya ke ce min haka na
Anty munfa gode abinci ma da wasoso muka cinye kin san kuraye na awajen,
Nace, Baba Hamza da gishirin kuka ci abincin hakana ?
Da mamaki ya dan tsayar da tafiyan da ya,keyi yana cewa gishiri ?
Ai ba hishiri a ciki wallahi don har na aika mama ta bamu gishi taimin fada wai in daina vin gishiri hakana bakyau,
Wallahi ba hishiri acikin sam,
Gaba dayan su ido suka sako muna suna jin yadda muke zance da Baba Hamza, akan abincin da akace yana dagishiri aciki,
Nace to mukan namu gishiri ya hana muci shi wallahi,
Baba Hamza wanda nakewa karan suna saboda Baba Hamza kanin mahaifan mu, yace
Kai wana maganace kawai don wallahi bani kadai na ci abincin ba gaba dayan mu awaje kowa ci babu kuma wanda ya ce gishiri,
Wani irin shu umin mirmushi na sauke don ko yanzu Alhamdullahi na samu sheda
Kitchen ya nufa ya ije kulan da na basu abinci a ciki yafito yana cewa Sir a rufe get don zamu watse zamu kallon Ball ne,
Muryan yaya Abubakar ya na cewa Hamzo zoga wani abincin ka dauka ko?
Take way dina na bashi tare da diban masa naman dake gaba na mai yawa so sai,
Sai godiya yake ta zab gawa ya addu,a tare da fatan alheri ga maigidan da mu,,,
Babana Hamza na fita daga falon na sauke wani irin gwauron numfashi take, nafara dancin nama na a hankali,
Ina korawa da ruwan holandia, milk mai sanyi dake gabana,
Zuciya na tai mun tas don Allah ya wanke ni daga TARKO da aka dana min
Yaya Abubakar tunda ya duka ya fara aiki a system din shi bai dago kai ba,
Ko ba,a fada ba nasan ran yan mazan ya baci ke nan yau,
Nice ta farko mikewa daga bin dokan da akasa muna na zaman dole falon,
Zaman da kusan duk a takure muke sai dai Sallawatu wace da farko tana dan jan shi da hira,
Amma da taga tai magana daya biyu ba ansa tai shiru tama fara waya, wai tana gaisawa da mutanen gidan su,
Daki na koma inda na fara shirin zuwa turakan maigida,
Yana daga zaune ya hango ni lokacin da na shiga kitchen don in dan sa ruwan zafin Lipton a wuta,
Don yanzu shan ruwan Lipton ya zama min kaman wani kwazaba shan shi na keyi sosai,
Hakan yasa shi duba time din system din tare da dan sauke hamma,
Tun fitowa Anty Sadiya ta mike tana kokarin hada yan abubuwan ta a hankali ta dan dubi gurin da Yaya Abubakar yake tana ce masa sai da safe ni zan tafi in kwanta,
Kofan dakina na rufa ina saye cikin wani zumbulelen hijab sai kamshi ke tashi a jikina,
Hannu na yana dauke da dan flasks dina da cup dan karami,
Na tsaya inda Yaya yake zaune ina cewa zan kwanta Yaya
Na juya gurin Sallawatu wace keta wayan karya da dariya nace to sai da safe ko ?
Kai kawai ta gyada min ba tare da tace komai ba wai ita tana waya,
Ban ko kai ga karasa hawa steps din ba naji shiru banji muryan ta ba,

Ban dade da kwantawa ba naji shigowan Yaya Abubakar dakin,
Bathroom yafara shiga yadan jima ciki yafito, yana saye da wani dan wandon boxer,
Injin ya kashe fitilan dakin a lokacin har na dan fara barci,
Ta baya naji ya rungomini yana cewa yau barci kike jine haka ?
Cikin yanayin mayen barci nadan bude idanuwa na da suka fara nauyin saboda batci,
Jikina gaba daya ban jin dadin shi, don haka nake kwanakin,nan idan dare yayi, sai inji zazzabi a jikina,
Yaya Abubakar ya ce ga jikin naki da zafi mana Meena ?
Dan murmushin karfin hali na sake nace haka nake duk kwanakin nan,ai,
Cikin murya mai kama da fada yace shine baki fada min ba mu koma asibinti akara dubaki,
Yaya haka yanayin zazzabina yake sai a hankali zai dai,
Are you sure ?
Nace wallahi ko Yaya da sannu zan daina jin shi ai, ya amsa da fadin OK
Sai naji ya kara matse ni a jikin shi ya na sauke ajiyan zuciya a hankali,
Cikin wata irin siririyar murya nace,
Yaya ya amsa a hankali da fadin na,am ,
Nace dazun kaman da Anty Samira naji kana waya ko ?
Ya ce itace mana,
Nace haba Yaya yanzun fa kune iyayyen mu, don Allah ya hore maka shekaru ilimi da kuma abin duniya,
Kamar yadda kowa ke kokarin ganin cigaban gidan su,
At list ace akwai wani jigo wanda idan wani abu yw taso zai tare,,
Ya ansa ciki ciki da fadin hakane ,
Nace to yaya ai ina tsan manin ba Anty Samira ba ko mu da bamu fito ciki guda da kai ba a yanzu zamu iya neman taimakon ka ka ba mu ,
Umhmmm inajinki ya ce, nace yaya don Allah ka taimakawa yar uwanka kamar yadda Allah ya taimake ka,,
Shin kin manta da halin Mama ne Meena, yanzu ina bata Mama zata ce don may na bata,
Sai a lokacin na juyo muna fuskantar junan mu nace,
Taimakon tsakanin ka da mu yan uwa ka daban ne ba dole bane sai Mama taji
In yaso ita kuma Mama sai ka tura mata da nata kace gashi ayi sha,anin haihuwan Samira dashi kaga ai baka tauye kowa ba,
Nadan marairaice murya na nace,
Ko ya kagani yaya ?
Amsa kamar a ikin bacin rai da cewa, shike nan naji
Kice ta turo da account nomban ta zuwa Wednesday nace to Yaya mun gode,
Ban san lokacin da na kai hannuna a jikin shi ba nafara shafa,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[8/14, 10:39 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-KAREEM


Yan Uwa Massoya ZAINAB MAKAWA Da Novels, Dina Ina Kara Mika, Godiyana, A Gare Ku,
Kau,nan Da Kuke Gwada Min Banda Bakin Da Zan Gode Maku Akan Shi Sai Dai, Ince Allah Ya Kara Rufa Muna Asiri,
Don Na Samu Alheri Sosai Daga Gare Ku Massoya Na, Ubangiji Allah Ya kara Rufa Asiri Ya Sawa Sauran Dukiya Albarka,,,,,,
Nagode Nagode Abin Daga Allah ne Kawai,
Alhamdullilahi Ala Kulli, Halin=?O?=?O?=?O?=?O?
Ba sai na fadi sunayen ku ba duk inda kuke kun san kan ku nagode kwarai wlh,,,,



Abin duniya duk ya taru yai mata yawa a rayuwa don babu dama tashiga taron mutane yanzu,
Sai a fara gudu a na cewa ga manya, ga manya nan,
Saboda banda gidan malam tsoho ta kara shiga wani gidan buki kusa da gidan ta,
Iskan kusan mata biyar ya tashi a gidan ranan da kyat tasha don sun mata mugun shaka, a wuya,
Hakan ya ba mutane tabbacin cewa ita muguwa ce ta sosai,
Yanzu diyan ta da yan uwanta da ya zama ma dole sai sun shiga gurin ta ne kawai ke shiga gidan ta,
Ta zama mujiya a cikin al,umma, sai dai maza su wa yanda take sana,a da su basu tsoron ta don sun ce ai in ma maya ce bata cin mutane akwai dai irin sihirin da take yi,
Don haka su kan je neman hayan mashi ko yar vesper gurin ta don tana dasu tana bada hayansu,
Abin da tafara hankalta (kula) da shi yanzu shi bata samu kamar farko,
Yadda Dodon ta kan mata aman kudi da farko yanzu sam baya yi,
Bai wuce a sati yai mata sau guda ba ko sau biyu kuma basu yawa irin farko,
Kai ta gyada tare da kuftawa, tana cewa a ranta ba kowa ya fara jawo mata matsala ba sai wanan mugun tsohon malam Manya,
Yanzu bata da aiki sai na wahalan jan ruwa daga rijiyan gidan ta ko famfo zuwa cikin randan da ta boye dodon ta a ciki,
Matsala guda shine yanzu boka yai nisa dasu wai ya koma can dajin Bargu da zama,,
Saboda yanzu baya samun wani alheri a nan addini ya ratsa zukatan mutane, ba kamar farko ba,
Don yai wa wata mata aiki, bayan Mama Ladi itama matar ha gida ta mayar mai da kayan shi tai ta mai tujara da tonon asiri,
Yadda akayi shine, matan tazo gurin shi da kukan tana son sana,a don duk abinda ta rika baya zama kudi, sai ya lalace,
Shine yace ta kawo sabon kwarya wanda ba,a taba aiki dashi ba,
Jiki na rawa takai masahi sabon kwaryan yace ta tafi bayan kwana uku, ta dawo,
Da ta dawo ya bata kwarya da wasu duwatsu guda uku, acikin sa, yace ta boye inda babu mai gani,
Dukiya sai dai agani a wajen ta ta bashi dubu uku kamar yadda ya bukata,
Ta tafi gida tana murna da jindadi takai kwaryan ta can ta boye karkashin gadon karfen ta,
Kaman kwana biyu cikin dare sai ji tayi wasu irin manyan tsuntsaye


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login