Showing 204001 words to 207000 words out of 388021 words

Chapter 69 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8264

idona nace O Allah na ,cikin wani irin murya mai ban tausayi,
Naji yaya ya kashe minfitilar dakin tare da rufo min kofan dakin dake a bude,
Azato na ya wuce ne amma sai naji shi yana hawowa saman gadon inda naji ya rungumoni ta bayan shi cikin sauke ajiyan zuciya,
Meenat jikin ki da zafi sosai mana nace cikin dan lumshe Ido,
Ban jin dadin jikin nawane yaya duk wani iri nake ji,,
Ina rugumay a jikin shi ina mai da numfashi guda guda har barci ya kwashe ni,
A cikin barci naji wasu abubuwa da Yaya Abubakar ke min wanda ya haddasa min bude ido na,
Jin da yayi cewa na farka daga barcin da nakeyi yasa shi rada min a kunne na da cewa relax, Meenat ba komai zan maki ba,
Dole na lafe kamar yadda yace din ina sauraren shi, har wani barcin ya kara kwasa na,
Barci shima ya dauke shi can cikin barcin yaji ina ta sheka amai a bayi inda ya tashi da sauri zuwa gurin da nake
Mun dawo saman gado naji duk banjin dadin kwanci ? saman gadon kasa nake son kwanciya,
Gashi kuma na kasa tashi ga wani itin barci da nake ji,
Na dora kai na saman jikin Yaya Abubakar yaji jikina duk dumine ya ce subbahanallah sannu Meenat,
Na mike da ket don zuwa kasan tie's in kwanta amma na kasa Yaya ne yake tambayana ina zan tafine na nu mai kasa yace ok yadan kamani na sauka kasan yasamin filo nace ya barshi ,
Ina ta nushi guda guda har barci ya dauke msi karfi wanda shima hakan ya samu ya dan kwanta a bakin gado tun yana kallo na har barcin ya dauke shi,

****** ********** ******
Washegari cikin ikon Allah na tashi babu wanan amman sai dai yawan barci da nake yawan yi,
Da kyat na tashi, nai wanka na dan kara jin dadin jikina nafito, zuwa kitchen don in samu dan abinda zanci,
Mu kayi kicibis da Ramatu wace, take dauke da ledan kayanta
Cikin kokarin kakaro murmushin karfin hali, take cewa Hajiya barka da safiya,
Na amsa mata da kyat cikin dan sakin fuska nace barka dai Ramatu anfito tace eh,
Idona ya kai ga yar kar kayan ta dake rike a hanuwan ta,
Nace sai ina zuwa kuma haka da safe Ramatu ?
Ta dan gyara rike jakar hannuwan ta tace Hajiya Meena gida zan koma wanan aikin ya ishe ni gaskiya,.
Subbahanallahi may ya sa Ramatu may yafaru ne haka har zaki bar mu,?
Bayan kuma ba haka mukayi alkawari da ke ba da farko,
Kafintace wani abu Yaya Abubakar yasauko daga saman dakin shi da alama fita zauyi,
Hankalin shi bawai a gurin mu yake ba don hannun shi gudayana saye a aljihun wandon shi guda kuma yana waya dashi,
Ina kwana mukai mashi abinda yasa shi jiyuwa gare mu ke nan ya dakata daga tafiyan da yakeyi,
Mu naji yai sallama da wanda yake wayan sai ya juyo gare mu gaisuwan Ramatu ya fara karbawa ,
Sannan ya kalle ni cikin wani dan yanayi yace ya jin yai sauki ko kai na daga mashi kawai alaman eh da sauki,
Kinci abinci kisha maganin ki na ce yanzu dai zan dafa don yau Ramatu bata samu yi ba
Inda Ramatu take tsaye rike da jakar kayan ta ya duba,
Sai ga hawaye sharr a idon Ramatu tana kokarin taresu da hannun ta na hagu,
May ke faruwa ne Ramatu ?
Tambayan da Yaya Abubakar ya mata ke nan acikin muryan shi mai kama da ta rowa,
Tace cikin hade yawun takaici, Alhaji tun zancen shafa maganin da kukayi da ita jiya shine har gari ya waye take cewa nabar mata gida
Wai kilama har dani aka hada baki don aciwa mahaifiyar ta mutunci,
Tsuki naji yayi tare da juyawa da karfi zuwa dakin Anty Sadiya,
Ina a tsaye nace mata ta kawo jakan don babu inda zata tafi in ma har tace hakane ai a gurina aka kawo ki ba gurin ta ba ko ?

****** ********** ******
Magana yake mata amma sai take tankar bata ji may yake tambayar ta ba a lokacin,
Wani tsawa ya daka mata wanda ya nuna mata cewa ba wasa, azancen sa,
Ta san halin shi sarai don takan dade tana bata mai rai yai ta hakkuri
Amma duk ranan da taga cewa yana mata tsawa to dole ne ta shiga taitayin ta,
Don idan har bata natsuba zata gane kuren ta sosai daga gare shi,
Shi mutum ne mai hakkuri sosai a yadda ta san shi,
Yanzu ne ma da su kayi yawa har take jin zancen shi akai akai,
Saboda can jin yanayi da gidan nasu ya samu na kowace da irin nata halin,
Don haka tun wanan tsawan da ya daka mata yasa ta juyowa don tasan cewa ta kai karshen shi,
Yace, tambayan ki nake yi mai wanan matar mai tai maka maki tayi maki da har zaki koreta,
Cikin dakiya badon taso ba ta bude baki tace haka kawai naga bana bukatan ta atare da ni,
Ya ce good amma wallahi ki sani babu wace zata kara wani wahala dake a gidan nan ke har kina ganin cewa kin samu lafiya ke nan da zakiwa wanan matar irin wanan wulakancin haka,
To bara ki ji ni bani wulakanta dan adam a rayuwa na ,
Sanan ban a,zawa mutum laifin da ba nashi ba don haka bazata bar gida ba don ke,
Asalima ai ba gurin ki aka kawota ba ko don haka zata zaunada wace tazo gidan domin ta,
Tace kana nufin zata zauna da Meenatu wani kallon banza ya watsa mata, tare da juyawa ya bar dakin
Sai kuma ya dakata ya juyo a fusace yana cewa zancen kuma da har kike kokarin yadawa ma duniya da kan ki, ke ki sani don idai ni ne bamu maijin wanan zancen a bakina,
Don in mahar da gaske ne wallahi nabar mutum da Allah don ni Allah yana tare da ni ,
Daga haka ya sa kai ya bar dakin a cikin fushi batare da ya juyo ba
Muna kitchen yasamay mu tare da Ramatu yace ke daga yau wanan zata dinga zama a gidan nan a matsayin mai gyara ko ina da kuma kula da wasu abubuwa,
Don haka sai kisa a kwashe kayan dake wancan dakin na kusa dake, ta zauna tare dake,
Godiya Ramatu tafara mashi, tare da kwararo mashi addu,a,
Yafara tafiya yake cewa ki tabbatar da cewa kin sha maganin ki a lokaci idan har jikin bai bari ba ki kirani mu koma wani asibiti,
Na amsa da cewa to Yaya Allah ya bada sa,a Allah ya tsare ya kare yace amin ciki,ciki,
Na juya gurin da Ramatu take tsaye tana share hawaye nace dan Allah dai kiyi hakkuri ko ita ma Anty Sadiya din zata zo ta huce ai,
Ramatu tace wallahi hajiya badon ke da maigidan ku da kuke min mutunci ba haka da babu abinda zai sani, tsayawa akan wanan matar,
Jiya fa kwana tayi tana surfa min bala,i a kai,,
Wai ance, kawai a shafa mata maganin da bata son ashafa mata ajikin ta,
Cikin murmushi nace mata yi hakkuri Ramatu bacin rai ne yasa tai maki hakan,
Baba Hamza nasa su gyara mata dakin tare da kara tsabtace shi tsab,
Tare mukayi girki da ita inda na dauki na Anty Sadiya na kai mata nata daki,
Nasan cewa idon ta biyu amma sai ta, lafe tankar mai barci don kada ta amsa min ,
Nasamu guri na aje mata nafito abina batare da na tsaya wani rigima ba,
Ina fita ta bude idon tare da saukowa daga kan gadon ta don ta yi break fast saboda yunwa take ji bata karya ba ita ma,
Tun a lokacin tafara data sanin rashin Ramatu a kusa da ita don gashi tana son a daurayo mata cup amma ba halin hakan,
Ramatu ce na samu tagyara min ko ina nagida tare da yi muna girki, dare da rana,

****** ********** ******
Da safiya suka tashi da shirin son kama hanya don dawo wa Abuja,
Duk yadda suka so su gane mahaifana acikin gidan mu basu gane ba saboda yawa,
Amma sai Salawatu tace wa Anty Mariya akai su su gaida Mama na don basu ganta ba,
Anty Mariya tace ai itace wace ta kawo maku abincin da kukaci jiya da dare,
Saurin kallon junan su suka yi suna cewa da turo ranci wai kada fa ayi charming din su ?
Sai kuma suka murmusa a tsakanin su, sun samu mamana tana gyara ko ina sai kamshin mangyadan da soya wanda zata zubawa shinkafa da waken da ta dafa masu nagida don a karya dashi,
Saboda Baba na shi tun da,safe ake mai abinci da zaici kafin ya fita zuwa gurin neman kudin shi,
Idan dan abin kwadaine kuma sai a saka mashia kula,yatafi dashi,
Cikin mutunci da sakin fuska mama saratu take masu sannu da zuwa,
Sai wani yatsune yatsunen fuska su keyi kaman masu jin wari,
Babana ya fito daga daki yana masu sannu da zuwa tare da tambaya sauran abokan zama,
Basu wani dadewa ba suka fito don dama gulmane ya kai su,
Mama Ladi daga gurin da take a zaune take cewa wai shin ku gidan ku har yanzu shiru babu wanda ta motsa
Sai dai aita kawo maku kuna ci kuna zubawa a masai,
In ta tagidan nan da ake ta faman karerayin wai tayi bari tayi bari,
Suka hada ido acikin murmushi Lubuna tace Mama babu fa wani bari da tayi wanan wani salon kissane irin na wanan Yarinya,
Mama Ladi mai nema a duhu tace ai ni dama nasani sun daiyi plan ne kawai don ace hakana din,
Nan suka shiga,kushe ni da,suka agurin Mama Ladi suna cewa wai duk Yaya Abubakar hankalin shi na gurin na,
Ta fara fada tana cewa ai dama nasani wanan mugun irin da aka hada shi da ita bazai gane komai ba balle ku na tare dashi,
Maganganu dai suka dauki lokaci suna yi akaina tare da su,
Suka bata kudi ita da Baba Buhari amma sai Baba yace su bar shi kawai ya gode,
Sunyi wa malam tsoho sallama wanda yakeyi tankar bai fahince su ba,
Bayan tafiyan sune gida ya dauki zance cewa aiko Meenatu tashiga uku don wanan matar ai kilama ta girmi Mamana nisa ba kusa ba,
Wasu suce ai wanan badai ta haihu ba sai dai don kawai a zauna kawai,
Irin wanan zancen ne har yai ta yawo a kwakwalwan Mama Ladi duk hankalin ta ya tashi jin da ta yi ,
Hankalin ta duk ya daga tana ta tunane kala,kala don fa agaskiya ya kamata ace yanzu anfara haihuwa agidan maisunan malam mata har uku amma shiru haka,
Don haka ta dauki waya takira Yaya Abubakar Mariya sarkin fadan ta tana zaune daga gefe guda tana sauraren su,
Bayan su gaisa take cewa ta bugo mai don taji ko may ke faruwa agidan shi haka shiru,
Cikin rashin fahinta yace ban fahinta ba fa Mama ?
Tace ina nufin har yanzu ace matan ka babu wace ko tai batan wata, ne wai daga cikin su, ya yi dan murmushi yace
Mama ba Meenatu ta yi wanan ba yan kwanakin da suka wuce,
Rufe min bakin ka kajiya narasa ko may kake tsinta gurin wanan yar karamar Yarinya haka,
Wai ace yarinya kamar Meenatu tana juya ka kaman dan karamin yaro
Murmushi yayi don ya san ina zancen ya fito har Mama ke mai wanan korafin, murmushi kawai yakeyi na takaici tare da girgiza kan shi,
Suna gama waya da Mama yace Salawatu hmmm bazai ki canza ba ke nan,
Sai kuma tunanen zancen cikin da Salawatu tace mai tanaa shi ya fado mai a rai,
To Mama ba,taga Salawat da ciki bane da har ta fada mai haka ?
Lalai akwai magana don bai taba jin zancen ba kuma tun ranan da take ce mai tana ganin kaman tana da ciki ajikin ta,,
Meenatu ce ta fado mai a rai sai ya tuna irin yadda ta kwana adaren jiya,,
Don haka ya kira layin waya na yana tambayana ko nasha magani na,
Nake ce mai nasha saura na dare in Allah ya kai mu zan sha,
Ya tambaya babu wani matsala ko wani wuri dake min ciwo,
Na bashi amsa da a,a babu komai naji sauki sosai yanzu yace alright,,,
Mu kayi sallama ya kashe wayan ita ma Sadiya ya kirata yana tambayan ta na ta jikin yadda yake , a cikin muryan ta mara marmari take cewa da sauki,

****** ********** ******
Washegari bayan fitan Yaya Abubakar gurin aiki ba ai wani dadewa ba sai ga Salawatu da su Lubuna sun shigo gidan ,
Batare da sun yiwa kowa magana ba, suka shige dakin ta, kida suka kunna suk kure karan shi kamar gidan disco,,,
Barci na keyi saboda rashin barcin da ban samun yi dadare yanzu sai nake ji kamar mafarkin kida, har dai nakai ga bude idona,
Kida ne sosai kamar gidan zai tsage ina son yun kurawa in tashi ne sai ga Ramatu ta shigo dakin dauke da kayan da ta wanke min,
Tace Hajiya kin tashi ba ai dole don wanan haukan ai yai yawa, matar wacan dakin ne ta dawo shinesuka saka wanan irin kidan haka,
Cikin murmushi nace au Salawatu ta dawo tace eh dazun nan bayan futan Alhaji,
Nace barin tafi in gaida ita da dawo wa, Ramatu tace min haba Uwar dakina ai ba,ayin haka,
Ko kin manta da cewa da sunan ki tabargidan nan ne wai,
Yanzu abinda za,ayi shine kawai duk wani addu,an neman tsari da kika iya sai ki hau fadan shi ga bakin ki kafinkuyi arba da ita,
Saboda duk wani sheri da ta kullo tazo dashi ya koma mata,
Ramatu tace furzawa yar banza tabbatiyada ta bayan hannuwa ta bare da ita daduk sherin ta,
Dariya Ramatu tabani don ganin yadda ta hakikan ce da zance,
Takai zaune saman center carpet dina tana cewa wallahi uwar dakina yanzu zama da mutane ya koma sai da dubaru,
Kada ki raina zance na juya bayan hannuwani ki tofe yar banza sai ki fure duk wani bakar aniyarta y koma mata,
Kin ga kin mata kai kayi koma kan mashekiya ke nan,
Baki ta Ramatu ba tunda su manyan matane nayi kamar yadda tace min din tace to madallah yanzu ko zaku hadu duk wani mugun nufinta bazai yi tasiri a kan ki ba,
Nace nagode sai ma naji fitan ya fita fin arai kawai nagyara kwanciya na tare da taimakon Ramatu ban fita yin komai a wajen falon gidan ba inda zan iya haduwa dasu,
Har suka gama ihuce ihuce su sukabar gidan suna wani irin shewa da tafawa irin na goggagun matan bariki,
Muna daki da Ramatu ina shan Faten waken da nace tai min ,
Ramatu tace yan iska ta Allah ba taku ba tsofin banza kawai wai su yanbariki,
Nace kai Ramatu don Allah ki daina kulasu don ba su ko a gabana ni,
Tace amma ke kina agaban su ai har ita wacan din mara marmarin,
Murmushi nakarayi batare da na tanka mata ba don na fahinci tana masifan jin haushin su,
Kada na biye mu shagala shedan ya rude mu muma akan su,


ZEEE MAKAWA YELWA,,
[9/7, 8:29 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 8?
ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH - AL -HAMEED

Barkan mu da ganin wanan ranan mai albarka ranan da ta kasance Jumma,an karshe acikin wanan shekaran ta kalandar musulunci,
Ya Alkah ka sadamu tarin alherorin dake acikin wanan shekaran,
Ya Allah ka kare mu ka yafe muna dukkan kura,kuren da muka tabka wanda muka sani da wanda bamu sani acikin wanan shekaran,
Allah kasa muna daga cikin yantattun bayin ka Allahuma Ameen,

Kira gareku yan uwana musulmai abokan zaman median na zauren beibei isah kamar yadda muka sahircewa junan mu
Ina maikara baku hakkuri da mudinga hakuri da junan mu akan rashin fahintar juna dafatan zamu kara yafe wa junan mu,
Nagode kwarai sa fahintar junan da mukayi saboda gaba dayan mu ba laifin mubane,,,
Nagode nagode nagode kwarai,,,,

Yinin Ranan barci nai tayi abina batare da na fito wajen gidan ba,
Ganin Salawatu zatai girki a kitchen din yasa Ramatu tatara duk wasu abubuwan da tasan ina bukatan su ta adana,
Ta dawo dakina ta zauna tankar wace take gadi na,
Bayan sallah la,asar kadan na farka a firgice tunanen banyi sallah ba fa ya fara zo min, a rai,
Idona ya kai ga agogon bangon dake manne a dakin naga hudu da sha tara,
Zubur na mike da,salati a bakina ban san cewa Ramatu tana dakin ba sai ji nayi tana cewa,
Yi a hankali uwar daki na kin san fa bake kadai bace don haka ki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login