Showing 36001 words to 39000 words out of 388021 words

Chapter 13 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8202

oyoyo Anty Meena oyoyo yaran gidan uncle ke wanan ihun lokacin da mai yar besfa ya aje Meena da kayan ta a kofan gidan su dake a cikin Sama,Road,
Ihun yaran ne yasa iyayen su gane cewa Meena tadawo Meena sarkin aiki ga tsabta da iya girki,
Haka matan gidan na uncle din ta ke ce mata, a duk lokacin da ta tsiri yin wani aiki,,,
Anty Amarya wace itace tafi bawa Meena fuska agidan ta kwaso da saurin ta daga dakin ta cikin farin cikj da ganin Meena din,
Ja tayi ta tsaya a daidai lokacin da sukai kicibis da Meenatun a kofan shigowa falon su,
Meena wace ta duka tana daukan dan karamin dan Anty amarya wanda yaga meena yake murmushin nuna yasan ta fa,
Shin Meenatu ba dai mai kin kafara shafawa ba ko ?
Meena wace ta ji maganar uwar dakin ta kamar a mafarki tai saurin dagowa cikin dariya tana cewa,
A, a,a wallah anty mikaini ?
Ke koga yadda kin ka koma Meenatu an ?
Dariya Meena tayi don jin zolayan da amaryan uncle din nata ke mata,
Sai a lokacin uwar gidan wace ke zaune tun shigowan Meena din saman dining table tana shan abu a cup tai magana,
Walleh Meeana an duk ke canza kamar ba ke ta ba, ?
Ko mummy ?
Inji Meena din wace ke ta faman murmushi saboda jin dadin ganin yan uwan ta,
Gaskiya inba, don gida gida bane da sai tace nan gidan uncle din ta yafi mata dadin zama don ba wani sa ido ko tsangwama a gidan
Ba kamar gidan su ba da duk abinda mutum keyi idon mutane na gare shi,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/7, 10:02 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AS-SALAAM,,,,,,


Baba Buhari ne zaune a gaban mahaifin shi malam tsoho, inda yake koro mai duk yadda al,amuran da suka faru, akayi,
Malam tsoho sai faman kada kai ya ke yi don mamaki koda yake bai dauki sarakuwan nashi cikin mutanen kirki ba dama,
Tun farko bai ra,ayin ta sam da dan nashi abudai ne in yaro yace yana ra,ayi sai a kyaleshi yayi,
Ina kake malami Naam Baba ya ansa wa mahaifin nashi a cikin ladabi,
Katai kayi hakkuri kajiya ?
Halin Ladi sai ita,,
To amma Baba ,
Hannu malam tsoho ya daga mai alaman ya isa haka nan,
Shiru Baba buhari yayi a vikin biyayya yan? mai dukar da kan shi a lokacin,
Magana gudane shine kayan yatinyar ga Aminatu wanda an,kan ansa,
Hakan baiyi dadi ba sam wallahi sai dai kawai ayi hakkuri abar zancen,
Shi kuma Samaila zan ganshi in mai magana don kada ya dauki abin da zafi a ran shi,
To amma yarinyar ga Aminatu yau ta koma makaranta sam banga wani bacin rai a tare da ita ba,
Baba ai kasan yarinyar yarinyar kirki ce ba zata taba nunawa ba,,
Amma zanga sauran abokan tafiyan nata don inji ko may yafaru acan gidan dan naka,
Saboda naji cewa wai matar, mai suna batada lafiya,
Baba shima cikin mamaki ya tambaya, ya ce, may ke damun ta,
Bari dai mu bincika a hankali,
Kasan matar taka bata da kwanciyar hankali balle a ce, ayi zancen kai tsaye,
Hakane Baba inji Baba buhari ya ba mahaifin shi ansa atakaice,
Cikin kwantar da harshe Baba buhari ya ce, to baba
Su wa yan nan kayan na wurin ka fada ta mamaye yaya za,ayi da su?
Cikin sauri malam tsoho ya ce, kai, kai dama ai wanan kayan yara ne kabar mata kawai Allah sa albarka kaji,
To ,Baba inji Baba buhari ya ansa acikin ladabi,

****** ****** ******
Wanan labarin da yazo ma Abubakar yai matukar bata mashi rayuwa, sosai
Ya dade yana tambayar Baba Wadda wanda ya bugo mai waya yana sheda mai abinda ke faruwa,
Sam baji dadin jin wai mama ta karbe kayan yar gurin kanin mahaifin shi,
Yariyar da duk kusan zaman su a gurin shi ya na hankalce da cewa ita ce mafi wahala agidan, nashi,
Amma sai gashi wai ita ce kuma mama ta karbewa kayan,
Ba komai kamar yadda yai wa Baba wadda alkawarin zai aikowa Baba samaila da wani abu don ya dan rage zafi,,,,
Kiran Salawatu ce ya,shigo a wayan shi abinda ya dan washe mai zuciya ke nan,
Daukar wayan yayi a cikin jin dadi yana mai cewa ya akayi ne Salawa, kamar yadda yakan kirata
Cikin lumshe ido don jin dadin sautin muryan dan matashin da tayi tace,
Babu komai Sir na dai kiraka ne kawai don inji muryan ka,
Tooooo, fa inji Abubakar din wanda ya fadi haka acikin yar dariya da nuna mamaki,
Cikin lumshe ido yace ni har na isa babban yarinya kamar ki, ki ce kina son jin murya na,
Sir ai har ka wuce hakan a gurina,
Tau na gode inji Abubakar ya fadi haka a cikin jin dadi da nuna kulawa,

****** ******* ******
Aisha wace ke zaune kusa da kakan ta wace ya turawa kwalban zuma da tazo roko gurin shi wai zataci masa dashi,
Malam tsoho yace wai ke Aisha, may matar yayan naku ta bakune haka kowan ku yai kiba da haske haka,?
Da sauri Aisha ta dago kai cikin jin mamakin maganar kakanta,
Ta ce malam muka dai bawa kan mu ko ?
Matar da bata iya ko da kula da kanta ba balle wani,
Ai in fada maka malam wanan matar sam wallahi bata dace da yaya Abubakar ba,
Malam ya dauko mata wani guntun kilishi a leda wanda yaji kuli kuli, da yaji yace karbi wanan,
Karki tashi ki zauna sai kin cinye don kar ki fita dashi wani yagani gashi iyakar shi ke nan,
Nan Aisha ta samu guri tafara yagan kilishi a hankali,
Malam tsoho yace to shi yayan na ku may yake ci da bata girki,
Samira tace wai sayowa yakeyi ko kuma ita samiran ta dafa amma yace wai ba dadi girkin Samira,
Shine da muka tafi kasan halin Meena da son aiki itace ta kirkiro muna girki da sauran aiyuka har mukeyi,
Malam yace toshi yayan naku yana ci ko ?
Ta ce malam cikindago kai tare da tsaida cin kilishin ta tace sosai ma har fa da cefanai yake yo,wa daga baya, sai mu girka,
Kai malam tsoho ya kada, don al,ajabi ace wai mace bata girki a gidan ta,
Bai kai ga karasa tunanen shi ba sai yaji muryan Aisha tana cewa,
Wallahi, malam yaya Abubakar sam bai yi sa,an mata ba,
Ga mace wata iri ba fasali ba zuben suffan mata ko kadan,,
Wai ma malam baka san wani abuba yanzun haka wata tsohuwar yar bariki tana nan ta lakewa yaya Abubakar gam, kamar chewing gun,
Gaban malam ne ya fadi don jin sabon masifan da ke shirin kara bullowa jikan nashi,
Ya na tunanen yadda zai bullowa zancen Sadiya sai kuma ga wani sabon zance anzo mai da shi,
Gaskiya dole ne yasan abin yi akai,
Bazai hana shi aure ba amma yar kirki yar asali wace ta fito daga zuria mai mutunci,
To amma shi Abubakar din yana ra,ayin ita matar da ki kace yanzu din ?
Daidai lokacin da Aisha ke kokarin tura kilishin karshe abaki tace,
Malam matar fa mai kudi ce, don ko da zamu dawo dubu ashirin taba mu sabbi fill da su,
Wani iri malam ya ji amma afili sai cewa yayi Allah ya kyauta kawai,,,

****** ****** ******
Meenat yanzu tun zuwan ta Abuja ta canza kamar da ga irin yadda take a da don yanzu komai nata na siffan manyan matane,
Amma a bangaren ta sam ita bata san da wanan girman da canza kama, da ake mata ikirarin tayi,
Hutun meet time break suka samu don haka ta dawo gidan uncle din ta don birnin kebbi yai mata nisa,
Sun samu Anty amarya suna shagalin buki a gidan su inda kaunar ta ke aure,
Hakan yasa yan gidan su uncle gaba daya banda mummy wacce ke tsayawa gida suke halarta wanan bukin,
Sosai anty Amarya taji dafin zuwan Meena a wanan lokacin don ko ba komai zata kula mata da yaran ta ai, a gurin,
Duk da ba wani sutura mai tsada ke ga Meena ba hakan bai hana ta fitowa cas a gurin bukin ba,
Ya wancin yan uwan anty amarya sun san da zaman mina agidan uncle don a tare suke da anty amaryan,
Hakan yasa a yanzu da tazo cikin su bata zama wata bakuwa ba,
Wata sister su anty amarya da tazo daga Kaduna tana kwance saman gado ta hakince,
Alokacin Meena ta shigo dakin dauke da jakar kayan da ta can,zawa salim dan wurin anty amarya,
Matar anty Zainab tace Fatima wai ina kika samu wanan yar kyakyawan buduruwar ce haka ?
Anty amarya tadan kalli gurin da Meena ta ke tana zuge zip din jakar tace wallahi diyar Nafi,u ne ,
Yarinyar senior sister di shi ce daga kebbi take tazo karatune nan sokoto,
Kai amma gaskiya akwai mace a wanan gurin wallahi,
Ke zaki auri yaro na,?
Dariya akasawa matar duk dakin don jin abinda tace,
A lokacin Meena take kokarin fita daga dakin,
Amma sai Anty Zainab din tace tsaya mana yan mata ba wasa nakeyi ba,
Wata daga cikin matan dake dakin tace wani yaro naki badai Amir ba,
Kai haba wane Amur da wana ai tai ma Amur girma sosai,
Ina da yaro faruk dan yayan Man ne yazo daga chadi,,, a gurin mu yake zaune yanzu haka yana aikin banki ne,,,
Kai kice zamuci naira ke nan inji Anty amarya, ke fatima kada kibani yar ki ki kuma koma kuna kwakwalewa dana aljihun shi,
Dariya akasa gaba daya dakin don jin abinda suke cewa,
To wanan zizarar aikema kin san zanci naira akanta dole,
Itakan Meena daga haka tabar dakin batare da ta tsaya acikin yan uwan ba tana jin barkwancin su,
Can Meena ta samu ta bayan gidan inda babu hayaniyar mutane da yawa tazauna tare da kallon duk wasu masu shige da fice,
Wata matace ta hango matar tana da irin zubin diyan gidan su anty amarya ita ma,
Sai dai da ganin matar miskilace don mutane na gaishe ta amna tana wani shan kamshi,
Ga zobba da sarka masu tsada a wuyan ta daga matar matar manya ce,
Kusan zubin su guda da matar da Meena ta baro a cikin daki watau anty Zainab,
A gurin da take tsaye tana magana da wani gurin dauko abu a handa bag din ta sai wani abu yafado daga jakar nata,
Da sauri Meena ta karasa gurin ashe wani karamin bag ne,,
Don haka Meena ta duka ta dauki jakar inda tabi bayan matar da sauri don ta kai mata,
Sai dai kuma bata san gurin da matar ta shiga ba saboda girman gidan,
Saboda haka meena ta rike yar jakar gam ga hannun ta
Sai dai hankalinta yana gurin masu shige da fice a gidan,
Ko da Allah zai sa taga wanan matar da tayar da hakar nata tun dazun,
Shigan hajiya karama, gidan direct dakin mahaifiyan su ta nufa inda tasa akira mata yan uwan ta fon suyi shawara,
Saboda su karasa sayaen abubuwan da ba,saiwa amarya ba,,
Bayan haduwar sune hjy karama, ke kokarin dauko jakar ta don ta bada kudin da akace na sayen wasu set din dining table, wanda yafi na farko da suka saye girma,
Nan jakka yace daukar ni inda kika aje mana,
Aiko wasa, wasa cikin rudewa ta fara zazage kayan baban jakar ta ko Allah zai sa tagani amna sam bataga komai ba,
Nan take jinin ta ya soma hawa,inda ta samu bakin gadon mahaifiyar su ta zauna tare da dafe kai ,
Kafin wani lokaci labari ya fara yaduwa cewa an sace wa hajiya karama jakar kudin ta har da dollar's a ciki,
Ga Meena zaune tana jin anawanan labarin amna tunda taji ance sata sai take zaton ko a cikine akai ma wata mata sata,
Don haka sai Meena bata kawo cewa jakar dake a hannun tane ake cewa wai da dollars din America a ciki ba,
Gata har cikin daki inda take jin su anty amarya ana ta kudundumin an sacewa babban yarsu jakar kudin ta gaba daya, da ta shigo dashi daga Kano,,
Ita kan ta dauki abincin da anty ta ki,rata ta dauka tabawa salim din ta,
Zancen har yakai maza daga waje sun fara shigowa nan da nan duk gidan ya hargitse da hayaniya kowa da abinda yake fadi,
A take wasu suka yanke shawaran cewa suzo atafi gurin wani malami a duba mata,
Amma ita Anty karima data kira mijinta sai cewa yayi tabarwa Allah kawai,
Amma da yake magana yai yawa sai tabi zancen mafi yawqn yan uwanta akan su tagi din,
Sunfito tare da sisters din ta da brother's din su har su hudu kowa da abinda yake fadi,
Meena wace ke gurin aamfo tana wanke hannu ta hango matar da tun safe take bida cikin wani irin yanayi, da gudu tabi matar tana cewa mama, mama,
Matan dake gefen fam fo suka hauta da fadan wai tabar famfon ruwa abude,
Ihun da suke mata ke, ke ke ke shine yadauki hankalin kowa zuwa gare ta,
Ita ko meena sai gudu takeyi tana haki zuwa gurin matar,
Tana cewa mama tun dazun nake neman ki wallahi bangan ki ba da har naji tsoron ko kin fita daga gidan ne,
Don na duba ko ina ban ganki ba, sai kokarin ciro jaka take daga hankaden n ta da taboye tana cewa
Gashi dazun da kika tsaya acan kina magana bayan kin wuce ne nagan shi nabiduk dakuna ban ganki ba,
A lokacin ne ta dauko wanan jakar tana kokarin mikawa matar wace da farko bata zaci cewa da ita Meena ke magana ba,
Lah jakatace kuwa a ina kika tsunce shi ne da sauri tana kokarin budewa don ta duba,
Idon sauran yan uwanta na akan jakar gaba dayan su,,
Allah sarki wallahi komai ba, a taba daga ciki,
Meena wace jin haka yasa ta kokarin juyawa don takoma gurin da take dauraye plate's
Yan mata tsaya mana yaya sunan ki yar albarka, ?
Ameena tace atakaice inda wata daga cikin sisters din su tace diyar mijin Fatima ce fa,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/9, 9:17 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 7?


ZAINAB IDRIS MAKAWA,


ALLAH- AL- MU,MIN


Casbi ya ke ja a zahiri amma azuciyar shi tunane acikin fam,
Daga kishingide yake kwance inda ya mimike kafan shi,
Yai makari da kafadan shi na dama hannayen nashi sai jan casbin suke yi,
Idon shi a lumshe suke bakin shine kawai ke motsi,
Hakan kawai ne mutun zai gane cewa ba barci ya keyi ba a lokacin,
Baba Wadda ne yai salma a lokacin cikin girmamawa ya kai durkushe yana gaida mahaifin na shi,
Idon shi ya bude ya na kallon dan autan nashi kamar mai nazarin wani abu,
Sai ya furta sunan shi a hankali, Wadda mun,kwan lahiya, ?
Cikin dukar da kai Wadda yace lahiya lau Baba,
A,a dare da jama,a ?
Wallahi duk lahiya lau Wadda an,
Mikewa Baba Wadda yai niyar yi don tafiya wurin tsabagar gaban shi,
Amma sai ya ji murya mahaifin nashi na cewa yaka Wadda ne mi guri kazauna dama ina son ganin ka na,
Gaban Baba Wadda ne ya fadi don shi a zaton shi yaiwa malam tsoho mahaifin shi wani laifi ne,
Amma sai yaji mahaifin nashi nacewa da ma tambayan ka na naka son yi,
Akan iyalin Abubakar can wajen su ?
Cikin mamaki Wadda ya dago kai don tunanen may tsohon ke son ji akan iyalin yaron yayan nashi ,
Tambayar da malam ya watso mai sune suka dakatar mai da tunanen nashi,
Shin Wadda wai a,a kka ga zaman mai, suna na da matar shi ne,
Yaran ga na da sun ka dawo , sun ka hwada min cewa wai,
Zaman takwarana da maidakin shi sam babu dadi, ?
Shin ,a,a, zance shike na ?
Shin gaskiya na su,kai ko ko a,a na ?
Zama Baba Wadda ya gyara da kyau inda ya fuskanci mahaifin nashi yace,
To walleh maganar gaskiya ita, ta haka zancen shike,
Don dai duk wani kulawa wanda ankasan mata da shiya,
Sam wanan macen batayi,
Kai baba ingajarce ma walleh zaune dai take dusha da ita kamar wata gwakyanya,,
Malam Manya wanda rayuwar shi ta baci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login