Showing 240001 words to 243000 words out of 388021 words

Chapter 81 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8310

shigowan mu,
Gaba,dayan mu muka hau saman tabarman saboda babbane sosai,
Nan suka shiga gaisawa dashi acikin girmamawa sai kallon gidan yakeyi yana girgiza kai kawai,
Bayan sun gaisa da shi Gwago tajuyo gurin da nake zaune kafa a tankwashe tana cewa,
Tubarkallah Meenatu karuwa na munka samu haka shin ?
To Allah shi jissuwa lafiya yan kuda na kwana, Car sai yar kaunata (sister) karama ta karba da cewa Ameen ,,
Abin dariya yaba Yaya Abubakar don sai naga ya dan jawota zuwa jikin shi ya lakuta mata kumatu acikin wasa yake cewa, ashe kin san addua ko ?
Can Yaya ya mike tsaye yafita yana waya hakan ne ya bamu daman kara gaisawa da gwago na mu kai mata yay jikin ta,
Mikewa nayi na cire Hijab dina muka fara gyarawa gwago gidan ta da yai kaca kaca,
Na bude jakata na ciro kudi nace su fita bakin hanya su sayo muna abubuwan abinci saboda mu dafa don naji Yaya ya tada motar shi hakan ya tabbatar min da cewa yatafi,
Tsab har ban daki muka gyara wa gwago na mun sha albarka yafi dubu a ranan,
Mun yi girki mun zuba a katon ture muna ci nida yan uwa sai dadin kasancewa a haka mu keyi,
Muna tsakiya da cin abinci mukaji dirar mota a kofan gidan wanda kuma yai daidai da dawo wan maigidan Gwago daga kasuwa gurin sai da kayan miya,
Katuwar katiface mukaji sallaman wasu matasa mutum biyu suna shigowa gidan dashi,
Yaya Abubakar daga bayan su shida Baba Wadda da bakon mu Baba Hamza,,
Suna dauke da buhun shikafa da su mai da sauran su,
Yai mamakin ganin mun gyara ko ina mun share mun tara karare guri guda mun cin na musu wuta suna konewa ,.
Ga kuma abinci da muke ci nida yan uwa a cikin katon ture a gaban mu,,
Sai sannun ku da zuwa muke ta masu suna karbawa Baba Wadda ne ya jagoran kutsawa da katifan dakin Gwago bayan an kara rage kayan da muka gyara dazun,
Daga girin da nake zaune muka dan hada ido da Yaya Abubakar ya sakar min wani lalausar murmushi tare da min signal wai na faye ci
Murmushi nayi tare da dan dukar da kai acikin kunya ina cewa su Baba Hamza' a debo masu abinci ne, ?
Baba Wadda yace kamar kin san muna jin shi kuwa don muna gurin gantali aka kira mu,
Kaunata Zinatu ce ta mike tazubo musu abinci a wani kwanon silver mai fadi,
Sai kuma ta dauko wa mijin Gwago nashi da muka saka mai tun gamawan mu,
Makwabtan gidan gwago da yan garin sai zuwa gaida mu sukeyi suna cewa masha Allah Habbi ashe kina da iyali haka,
Sai kuma ashiga dakin a leka ana kallon katifan da a,kasayo wa gwago,
A can gefe guda kuma mijin Gwago ne da Yaya Abubakar, zaune suna tataunawa,
Zamu iya gane zancen su kamar suna magana ne akan zagaye gidan su,
Gwago da jama,an ta sai murna da fatan alheri suke muna,
Zuwa dan wani lokaci Yaya yamike yana cewa mu shirya mu tafi gida,
Ba don munso ba muka fara shirin tafiya gida sai godiya,gwagona keyi har da hawayen ta,,
Muka fito gaba dayan mu idon mutane akan mu caaa suna fadar albarkacin bakinsu karya da gaskiya,
Muka kama hanya misalin karfe hudu da wani abu na yamma zuwa gida,
Saida muka yada zango gurin Anty Samira asibiti muka gaida ita tana tajin dadin ganin mu,
Tana min korafin wai naki zuwa in, zauna muyi hira tunda nazo nake ce mata wallahi banjin dadin warin asibitin ne shi yasa,,,
Dariya ta saka min tana cewa ai nikan nasan cewa za,a rina wallahi tun ranan da nagan ki,
Haba Anty Samira yanzu wani canzawa nayi da zaki ce min wai wani abu zamuyi magana yaya yashigo shida su Baba Wadda da Hamza,
Muna daga gefe su ka isa gurin ta suna gaishe ta tare da tambayan ta karfin jikin ta,
Mun dan jima har gab da sallah magrib sannan muka nufi gida acikin jin dadi duk da agajiye muke amma bamu jin komai saboda mun tafi gurin yan uwa,
Muryan yan rakiya da suke shewan jin dadi mun tafi kalgo tare yasa mutanen gida gane cewa mundawo a lokacin ,
Ina shiga part din mune mama take muna sannu da zuwa nace wanka zanyi ko zanji dadin jiki na,
Mama tace min inyi maza kafin almuru ya sauka don koda ba cikki gareni ba ba,a son yin wanka a wanan lokacin,
Dasauri don dai ina son yin wanka na nufi bathroom na watsa ruwan kawai ban tsaya sa sabulu ba,
Nafito nai alawala nashiga daki sai naji wayana yana ruri cewa, kira ya shigo tsuki naja ina cewa waye mai kirana, a wanan lokacin,
Sunan Baba Ramatu ne nagani rubuce, da sauri na dauka ina cewa ai nayi fushi Baba, Ramatu,
Amma sai naji muryan ta tana cewa uwar dakina yanzu, nan matar gidan nan tazo wai na bata key din dakin ki zata dauki wani abu acikki,
Da sauri nace innalillahi kin batane Ramatu, ?
Ramatu tace haba dai uwar dakina ai nasan halin ta don haka nace mata ai da shi kika tafi,
Don dama ban taba bude kofan ba bayan tafiyan ku,
Wani irin mamakine naji nake cewa Ramatu wani sheri zatai min a dakin kuma ,
Tace nima tunanen da nake tayi ke nan tun dazun nima,
Nace cabdi ashe akwai magana don duk tai gigi bude min daki wallahi bazan kyale taba niko
Ramaru take ce min yanzu an samu mai gadi kullun sai ta fita tai masifa dashi wai yaki bari abokan ta su shigo gurin ta,,
Murmushi nayi ina cewa kyale ta kawai ba zai yarda ba ai don maigidan ya kafa mai doka, sosai,
Ramatu tace wallahi baki ga yadda tadinga min masifa ba don nace key bai hannu na ,
Dama tunda naga tana son jana ajiki nafara shan jini na da ita ina kaucewa,
Don nasan cewa ba alheri zata shuka ba, sheri take son kullamin,
Da zaran na gama aiyukana sai kawai na shige ciki abina batare da na tsaya jiran ta ba,
Allah ya kyautana ce tare da ce mata sai anjima zanyi sallah saboda an fara kiran sallah ko,
Ina idar da sallah nake jin muryan Anty mariya a part din mu tashigo tana cewa waiko Meenatu na gidan nan,
Nafito daga ciki ina cewa ina nan anty ina wuni ta amsa min wani iri, ciki ciki
Wai tambayana take yi dana tafi da su zinatu anguwa may yasa nabar yaran ta ban dauke su ba naje dasu,
Nace anty koda muka shirya tafiyan mu basu kusa lokacin yaran Baba MUSA ne kawai a guri kuma tare muka tafi da su
Meenatu kada kijawo raba daya biyu fa ki ce zaki nuna muna banbanci,
Ai suma wa yannan yaran da kike gani ai yaranki ko banza
Don na dauka cewa diyanki ne suma tunda kaunata kike,
Amna wai kina ganin su kikasa yan uwanki a gaba kuka wuce kuka bar min su,
Amma kuyi abinku don wuri kuka samu shiya don dama hakan ne akeso ayi ai
Ta juya fuuu suka hadu da Baba mu a hanya yana shigowa gida don dawowan shi ke nan,
Irin yanayin da ya ga tafita dashi yasa shi gane cewa ba lafiya ba, ke nan,
Tun daga nesa yake tambayan Mama Saratu lafiya ta tsaya mai wani inda inda yadaka mata tsawa bashiri ta shiga fada mai abinda ya faru,
Baba bai tsaya ba sai sashen Mama Ladi ya samay su suna raba abinci zasu ci Anty Sadiya tana daga gefe tana kallon yanayin su,
Babu sallama ba yashigo yana cewa wai ina Ladi ne,
Yau abinku ya isheni agidan nan wallahi ke da kin san ku ya xa ya kamata to da ko ance ki shuka min nida zuria ta rashi mutunci da bazakiyi ba,
Amma da yake ke butuluce shiyasa al,amarin ki bai bani mamaki kwata kwata,
Yau hatta takai iya iskancin ku ya kai mariya sashena don cin mutunci,
Auren daki dai ne aka yata ko ?
Tau yau zai kare yadda kike so sai ki zauna da wa yanda kike son ya zauna dasu ko,
Ai,ko Baba ya haukace yai ta masifa yace sai Yaya Abubakar ya sake don shi agaji da wanan masifan,
Kafin ace may maza suka shigo ta ko ina gidan ya cika fan da jama,a
Amma ina sam.Baba sai cewa yakeyi sai fa Yaya Abubakar yasakeni kowa ya huta, zaifi,,,,
Aiko hida ya rikice da jidali wanda hankane yasa Baba Buhari cikiin hasala ya tako har kofan Mama ya daga ashabarin da aka rufe part din da su
Ya ce to Ladi sai ki tashi ki fito daga ke har wanan yar taki ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da diyan ta wallahi baku kwana min agida yau,
Hakan ya isheni ya isheni sosai daga yau ya kare don ya ta zata dawo gida ke kuma sai ki koma naku gidan,


ZEEE MAKAWA YELWA
[9/16, 11:15 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- QAYYUM,,,,


Gida gaba daya ya rikice da fitina wasu na ganin laifin Mama Ladi wasu kuma suna jin takaici na da iyayyena,
Sai dai masu jin takaicin mu basu da yawa sosai don kowa ya san su ,,,
Irin yadda Baba ya nuna rashin mutunci ranan hankalin kowa ya tashi a gidan,
Tsaye yayi yana cewa sai an kashe auren yau kowa ya huta,
Dole Mama Ladi da taga cewa wanan fitinan yafi karfin ta tashiga hankalin ta,
Ga Baba Buhari shikuma yayi rantsuwa cewa yau Mama bazata kwana mai gida ba,
Dakin mu na,shige csn kuryan gadon Mama na ina wani irin kuka mai tsuma rai,
Haka ita ma mahaifiyata tana zaune waje daga kofan ta idon ta sai tsiyayan hawaye yakeyi,
Baba Wadda ne ya daga waya yana kiran Yaya Abubakar wanda ke can gidan su Aliyu Abokin shi,,,
A,gagauce ya iso gidan inda ya samu fitinar bai kare ba alokacin, don ga,Baba tsaye a kofan part din Mama yana jiran tabar maigidan shi,
Wani irin bacin rai ne ya ziyarci zuciyar shi a lokacin don yasan cewa yau ran Baba ya,baci ne sosai, don a gaskiya Baba Buhari mutum ne mai hakkuri sosai,,,
Juyawa yayi zuwa part din mu inda yake jin muryan Baba Samaila daga can baya gurin Baba Musa,
Gaida Mama yayi a mutunce saiyake tambayan Meenatu fa,
Murya irin ta,wanda yai kuka sosai take ce mai tana ciki,
Tausayin mama yaji don dai yasan cewa idan ta ita ce baza,a taba fada ba agidan mu,
Kamshin turaren shi yasani gane cewa ya shigo dakin namu a lokacin,,
Wai may, ki kewa kukane haka ?
Kada fa kijawa kanki ciwon kai a kan wanan zancen don babu abinda ya shafe ki a cikin sa magana ce ta manya ba tamu ba,
Abinda ya fada naji wanda hakan yai saurin sani duban shi,
Don mamaki sosai ya bani don a kan mu ne fa ake wanan zancen amma sai ya cewai, akan may nake kuka,
Na ce a hankali cikin muryan kuka Yaya baka ji may ake yi a gidan nan ba duk akan zancen mu,
Yai murmushi mai daci tare da kara harde hannayen shi guri guda,
Ya na kallo na tare da sake min murmushi ya jefo min tambayan cewa,
Bakya son araba auren na mu ne ke ?
Da sauri na dukar da kaina ina mai cigaba da zubar da hawaye,ina dan goge hawayena da bayan hannuwa, na ,,,
A hankali ya kai zaune daga tsayen da yake ya kai zaune gefena kadan,
Ya kira su nana a hankali yace ki fara shiri mu koma don bazan iya tsaya cikin wanan tashin hankalin haka ba,
Na dan dago na kalle shi fuska da fuska na ce baza mu tsaya ayi suna damu ba ke nan,
Ya mike don dama ba zama sosai yayi ba yafara tafiya yana cewa gaskiya bazan iya kai wani lokaci a nan ba haka ?
Don haka idan zaki koma ki shirya idan kuma baki tashi ba sai ki tsaya har ki gama abinda kikeyi,,,
Ya sa kai ya fita daga dakin yayin da nabi bayansa da kallon mamaki
Na tambayi kaina da kaina nace wai kodai ma baiji abinda Baba ya ce bane,

******* ********** ******
Daga dark n gurin malam tsoho ya nufa idan ya samu tsohon a cikin bacin rai sai dai babu wanda zai iya fadawa,
Zuwan yaya Abubakar gurin shi ne yasa shi dan jin dama, dama, abinda yake ji, a zuciyar shi,
Zama yaya Abubakar din yayi tare sa ba malam baya kadan ya dukar da kan shi a tsakan kanin kafafuwan shi,
Malam ne ya jefe shi da tambayan yaushe ne zaku koma,
Ya Abubakar wanda ya dago kai da idon shi da sukayi jawur ya bude bakin shi da kyat yace,
Ina ganin gobe zamu bar nan don bazanci gaba da zam irin wanan matsalalolin suna bulowa ba saboda mu,
Dama wanan ra,ayin Meenatu ce don ita a zaton ta ban son yawan kula yan uwa,
Yace malam tun farko, idan naima wani alheri abin yana zama fitina be sosai irin haka,
Shiyasa nasawa kaina massalaha kan ban damu da kowa ba kuma ban shiga harkan kowa,
Malam tsoho yace na fi kowa sanin wanan ba yau ba shi yasa ma nai kokarin yin wanan hadin a tsakanin ku,,,
Yaya Abubakar yace Meenatu yarinya ce mai hankali malam,
Abubuwa da dama da na manta dasu da farko itace a yanzu take yawan tunatar da ni, akan su,
Munyi magana da ita a kwanan baya wanda taban shawaran da ya kamata,
Tun wanan lokacin ne abubuwa da dama da su ka tsaya min arai,,
Wannan daman ne nai amfani dashi a wanan haihuwan na Samira na dauki hutu don inzo in duba wasu abubuwa,,
Malam yace jeka masaukin ka ka huta gobe karfe takwas na samu mu hadu a nan sashen nawa,

****** ********** ******
Washegari gaba dayan su diyan malam tsoho, duk kan su suna har Baba Wadda suna zaune a gaban mahaifin su,
Wanda yake saye da farar tabarau a idon shi yana daga kwance kishingide yana karatun a cikin muwadda,malik,
Hankalin shi naga karatun da yake yi tankar bai san da su ba agurin,
Shigowan Yaya Abubakar a cikin sune yasa gaba daya hankalinsu na gurin shi,,
Nan Yaya Abubakar ya tsugunna ya fara gaida su daya bayan daya a cikin girmamawa,
Sai a lokacin ne dan tsoho ya dakatar da karatun shi ya rufe da shafawa,
Sallama yai masu yayin da suke ta mika gaisuwan su gareshi ta ina kwana,
Malam wanda yai gyaran murya don yaga cewa sun natsu don suyi abinda ya kawo su gurin kowa,ya tafi neman na abincin sa,
Baba Buhari ne ya fara kallo yana cewa da fatan mai dakin naka ta dawo gida iyanzu ko ?
Baba Buhari wanda yaji nauyin magananya dan yi kokarin gyara, zaman shi da kyau yana mai dukar da kan shi kasa,
Sai kuma ya juya gurin mahaifina wanda tun malam din baiyi magana ba yai saurin dukar da kan sa kasa,,
Yace mai 'ya ga mijin nata a gaban ka sai ka karbi takardan nata ko?
Babana ya kara dukar da kanshi kasa cikin jin nauyi da ka sa daga fuskan, shi,
Gurin Baba Musa ya juya yana cewa Musa may yasa har zuwa yanzu ka kasa gane halaiyar Ladi a gidan nan,
Yanzu da ace kun kyale ta kamar yadda shi dan da ta haifa ya sa mata ido yana bida ita acikin dubara ai sai na ga zaifi ko ?
Yanzu gashi diyan naku da,suka zo maku hutu sun yanke shawara komawa indal,su ka fito yau din nan,
Gaba daya duk wanda ke wurin sai ya dago kai yana kallon gurin da Yaya Abubakar yake zaune,
Malam ya,ce wanan ke nan, yanzu abinda nake son ku sani shine ni a gida na ba saki,
Don haka daga yau ban son in kara jin zance kalman saki a cikin gida koda kuwa a bayan raina ne,
A hankali suke furta cewa insha Allahu malam baza ayi haka ba,
Malam yai murmushin takaici yace gaba dayan ku na zata zuwa yanzu zaku gane manufan hada auren nan da nayi,
Iyanzu zaku gane cewa auren nan na yaran nan wani babban TARKO ne a gare mu baki dayan mu, har su,
Yanzu wanan abubuwan da suke yi wa yan uwa musali watace can bare ya aura kuna ganin cewa zaku samu wanan alherin haka daga gare shi a koda yaushe,
Yaya Abubakar wanda ke daga gefe yadago kai yana kallon malam malam yace kwarai da gaske hakane, mana,
Ada can baya kafin ka auri yar uwar ka, matar ka da yan uwanta kawai ka,sani,
Cikin jin nauyi Yaya ya dukar da kanshi kasa malam yace amma yanzu duk abinda zai yi a na gida ne zai fi yin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login