Showing 27001 words to 30000 words out of 388021 words

Chapter 10 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8190

tun kwanan baya ta damay ni akan zancen dawowan su,
Wai an,kaiwa yaran dawainiya da yawa, don zaman bariki ba zaman nan bane,
Ko wa zata gwada ma zaman bariki,?
Mata babu tunane sam a kwakwalwan ta, ita yanzu inda tana da wayo hakan ba abin alfahari bane gare ta,
Yau ace an, wayi gari har yan gidan nan sun je gun dan da ta haifa da cikin ta sada zumun ta,
Murmushi Baba Samaila yayi tare da kada kan shi, cikin takaici,
Yace ai nasan dama, Ladi sai tayi wanan korafin akan wanan tafiyan,
Don dai kawai malam ne yace ai,ni da babu inda zasu gaba dayan su,,,
Malam tsoho dai bai tankawa diyan nashi ba duk zancen da sukeyi sai murmushi yakeyi ya na girgiza kai, har zuwa lokacin da duk kan su su kai shiru,
Cikin murya irin na tsufa yake cewa, zan yi magana dashi Abubakar din insha Allah,
Daga haka Baba Samaila yai wa mahaifin nashi sallama ya tashi ya bar gurin,

***** ****** *****
Abin da tasaba yi duk lokacin da kwanan wata yakai irin wanan lokacin yau ma shine take ko,karin yi, din kamar kullun,
Kamar yadda tasaba, bawa yaran shiya da sadakan naman kaji, da kuma na Naman rago,
Yau ma wani irin murdaden ragone kato, aka shigo dashi daga mahauta inda aka yanka aka kuma gyara, shi,,
Ba, bata lokaci aka shiga yan kawa ana kaiwa makwabta sadakan naman ,,
Masu karba su karba wa, yan da suka camfa wanan sadakar na Hajja kuma suki karba,,
Su kuma har neman kari sukeyi don wanda aka kai masu bai ishesu ba,
Duk a,kai wanan yan kan abuguda Hajja ke dauka daga cikin tunkiyan ko rago,,,
Daga shi bata daukan komai daga ciki kuma ita bata cin naman,
Duk abinda take ciki tana ganin cewa mutane basu hankalta da abinda takeyi,
Batasan cewa labari iri iri akan ta yabi gari ba kowa da irin abinda yake cewa,

***** ****** *****
Zaune take a falon da daya daga cikin takardun ta na karatu da tazo dashi,
Tana dan dubawa don gudun mantuwa, kada ya shige mata, wanan dabiar Meenat ce yawan bitan littatafan ta, akai akai,
Samira ce ta sa ma ta kira daga dakin su don haka ta mike tabar takardun nata a guri,
Shigan,ta dakin da kamar minti uku Abubakar ya shigo gidan agajiye, daga gurin mai gyaran mota yake,
Don haka saman kujeran tree sitters din da Meenat ta tashi ya hau, don yadan sha iska ya huta,
Takardun da yagani akaine ya dauka yana dubawa inda ya fahinci cewa takardan daya daga cikin sisters din nashine,
Wace ce wanan mai wanan rubuta mai kyau haka gashi kuma ta iya bayanin kowani sashe da kan ta,
Tambayar da yaiwa kan shi ke nan a cikin zuciyar shi,
Don haka ya aje takardun a saman tabur din dake a gaban shi,
Kwantawa yayi ya mike tare da dagwara hannayen shi akan shi , idon shi a lumshe suke tankar mai barci,,
Meenat tafito daga dakin don taci gaba da karatun ta inda ta tsaya,
Sai ta ja ta tsaya guri guda don ganin yayan nasu da tayi a kwance gurin da ta tashi yanzu, yanzu,
Komawa baya tai niyar yi don ganin shi da tayi a gurin ,
Amma sai idon ta ya hango mata takardun ta a saman dan tebur din dake gaban shi,
Sadaf, sadaf ta nufi gurin don azaton ta irin yadda ta ganshi ta dauka barci yake yi,
Daukan takardun nata yai daid???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai da bude idon shi inda ya sauke su a cikin nata,
Fuskan shi a murtuke kamar kullun yadda take ganin shi,
Wani iri taji kamar ta koma baya tabar takardun don tsoron shi da taji,
Kawai sai tai nufin juyawa, amma kuma muryan shi da taji yana cewa ke dauki mana ki tafi,
Yasa ta saurin dauka cikin makyarkyatan hannu kama za a rike ta,
Da sauri tabar guri inda shikuma ya maida idon shi ya lumshe kamar yadda ta samay shi da farko,
Ita ko Meenat cikin zuciyan ta sai cewa tayi mugu kawai wanda yai gadon mugun hali gurin mama,Ladi,,
Kai tsaye, dakin su ta nufa, Ganin irin yanayi da ta shigo da shi a dakin ne yasa Aisha tambayar ta ko lafiya,
Batare da taba ta ansa ba ta samu gyafen gadon da suke zaune itama ta zauna tare da yin tagumi,
Tunane barkatai ta dinga yi a kwakwalwanta tana cewa,
Watan da gaske ne da ake cewa mutum na gadon abubuwa daga mahaifan shi,
Inko haka lalai wanan yayan nasu ya gado mahaifiyar shi da tsanani sosai,
Mutum haka da girman kai, ga ahare mutane kamar mai jin warin su,
Ga isa da izza kamar wani dan gidan sarkin gwandu,
Sjigowan Samira dakin tare da kiran sunan ta shi, ya tsayar mata da zancen zucin da takeyi,
Meena wai yayan mu ne ke tambaya na wai waya hada mai zobo ranan nan,
Anty samira ke baki hada mai da kan ki aiduk dayane ko,?
Tafadi haka cikin yanayin damuwa,
To Meena ai tambayana yayi shine na fada mashi cewa kece, kike hada muna kullun,,
Don haka sai kizo muje ki hada mai kafin ya kara tambaya,
Barin je in fara jika maki k?fin ki taso ko don in rage maki aiki,
Ganin Samira ta juya ta nufi hanyar fita daga dakin,
Meenat, ta mike tsaye tai saurin da sauri ta sha gaban Samira tace,
Pls anty Samira ki taimaka ki hada masa don ban son fita idan yaya na falo,
Dariya ne ya kama Samira tace, kamar wace zai daka ko yai mata fada,?
Zo muje tare ke babu komai dan Allah
Badon taso ba tabi bayan Samira simi simi da ita kamar wace za,a kama,

Yana cikin falon still saidai wanan karon a tsaye yake yana waya, ba kamar yadda ta barshi dazun ba,
Daga kuma wanda yake wayan dashi yana da mutunci matuka agare shi,
Saboda irin yadda yake magana cikin girmamawa tankar a gaban mai shi yake,
Ta gefen shi sukabi suka wuce batare da sun gaishe shi ba,

Ba,a dauki wasu lokutaba suka hado mai zobon mai sanyi yaji kayan hadi kamar yadda tasaba yi a gida don sana,ar mama Saratu ne kayan sanyi,,,
Sunan Samira yakira inda ya dakatar da ita, sai dai ita Meenat kan har ta shige abinta,
Tambayar ta yayi da cewa,
Wai cikin yaran nan wace ce diyar Baba Samaila,?
Tace yaya Meenat ce ai diyar shi,
Wacece Meenat din daga cikin su,?
Itace mana wqnan da muka hadama zobon da ita ai,
Cikin mamaki ya ce itace wana yarinyar dake bin babban dan shi ko, ?
Ita ce kuwa inji Samira ta bashi ansa,
Wani irin faduwar gabane ya ji tamkar zuciyan shi zai yi rawa,
Yace yanzu dama da diyar Baba na Samaila a cikin ku shine ban sani ba,
Samira ta dan mai,da hankalin ta gare shi da kyau tace eh yaya,
Subbahanallah inji yayan nasu ya fadi cikin kidimaywa,
Ita kan Samira tai shigewanta tabar shi nan gurin da yake zaune,
Kusa da Meenat ta zauna tana cewa ke Meenat wai fa tayan mu bai san dake acikin mu ba,
Sai yanzu yake tambayana wai wacece diyar Baba samaila daga cikin mu,
Meenat cikin zuciyan ta, ta ce mugu kawai ai,gara da bai,sani ba tun da farko,,
Washe garine suna falo sai gashi ya fito acikin shigar shi ta zuwa office,
Gaba dayan su su ke rige rigen ce masa ina kwana yaya,
Cikin daga hannu ya ansa masu gaisuwa tare da cewa a takaice, lafiya,
A gurguje ya dan kurba tea din da ya hada wanda ga mamakin shi ya sha kayan kamshi kamar yadda iyayyen su ke yi,
Har ya fara tafiya sai yake cewa batare da ya kalle su ba,
Malam tsoho ya bugo waya jiya yace a tura ku ku koma gida don hutun wasun ku ya kare wai,
Daga haka kawai yasa kai ya wuce inda suke ta ce mai adawo lafiya yaya,
Fitan shi yai daidai da juyowan Samira gurin Meenat tace inaga saboda kene aka bugo mai waya,,,,,

***** ****** *****

Zaune take tana kokarin jawo wani file dake karkashin takardun dake saman tebur din ta,,
Wayan tane yai kara alamar kira ya shigo mata alokacin
Kamar kada ta duba amma sai wata zuciya tace mata ta duba mana taga ko waye ke damun ta haka,
Da yar tsukin ta ta jawo wayan don ganin ko waye ke damunta tana tsakan aikin ta haka,
Cikin wani irin mamaki takai zaune saman kujeranta don ganin noban dake kiran ta,
Cikin rawan hannu ta dauki wayan don karba kiran na bazata da yai mata a yau,,
Wani irin kashe murya tai sallama dashi tare da kara gigita mashi zuciya,
Salawatu indan antashi daga aiki zakki rakani wurin shopping akwai wasu yaran da sukazo hutu gurina ina son in masu sayayan komawa gida,
Cikin sauri sauri tace ok sir insha Allah zan shirya da wuri mutafi,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[7/1, 9:42 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 3?

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,


ALLAH_ AR-RAHEEM,,,,


Wani irin uban tsale Salawatu, ta daka tare da mikewa da sauri ta suri jakar ta,
Gida ta koma inda ta kara yin shiga ta alfarma ta gyara duk sassan jikin ta tsab,
Ta dawo, office duk wanda yaga ta canza shiga daga cikin abokan ta sai sun tsaya mamakin ya haka kuma ?
Sai tai masu far da ido tace abin ai sirine kawai basu gane ba yanzu,,
Har kusan zuwa tashi office, sanan ta dauko jakar hannunta takara dauko madubi ta gyara duk inda ya dace,
Wani turare ta shafa a jikin ta mai wani irin mugun kamshi,
Sai kuma daurin dan kwalin ta da ta gyara da kyau, tare da sabale gyalen nata,
Wayan ta ta aje gefe guda tana jiran kiran shi kawai,
Shiko dama dan over time ne yana can yana over din shi,
Har ya manta da zancen zasu fita da ita, sai aikin gaban shi ne yake kokarin yi kawai,
Malam Abdullahi masinja ne ya hango ta a tsaye bakin motar shi tana ta kallon agogon wayan ta cikin bacin rai,,,
Shigan malam Abdullahi office din yasa shi dago kan shi a cikin sauri
Da mamaki ya ce malam baka tafi gida bane har yanzu,
A haba dai yallabai ai jira nake har ka rarage sai in kulle ko ina ,
Allah sarki hakene fa malam Abdu don Allah kayi hakkuri, dani shap na manta da ka na jirana ne, wallahi,
Ba matsala ai,na san baka gama bane yanzun ma nazo ne in sheda maka cewa kamar naga ana jiran ka a waje ko ?
Cikin mamaki Abubakar ya ce ni ta alamar nuna hannun shi a jikin shi,
Saida Abdullahi yadan yi shiru tukun sai yace kuma yarinyar nan mai yawan tsayawa dajai nan ma,aikatar,
Cikin wani iri Abubakar ya ce Subbahanallah wallahi ni nace ta tsaya min zata rakani in saiwa yaran nan da su kazo hutu wurina tsaraba,
Daga haka ya mike tsaye yabar gurin cikin daukan yar briefcase din shi,

***** ****** *****
Daga gurin da take kwance tai mafarki kamar yadda ta saba yi a,duk tsakiyan wata,,
Ciwon maran da tasaba yi shine har zuwa yau ma ya tayar da ita daga barcin da takeyi, a dakin ta,
Nishi takeyi sama, sama ta murdewa guri guda kamar macijiya ,,
Sai kuma wani irin kugi da takeyi ga jikin ta na wani irin rawa,
A daidai bayan dakin da suke suna hiran su da kuma wanki, murja ta fara jiwo wanan kugin har sai,da tace wa yan uwa suyi shiru su saurara,
Daga dakin kwanan Sadiya ne wanan sautin ke fitowa,
Kallon juna sukayi a lokaci guda inda kuma suka kwasa gaba dayan su zuwa cikin gida,
Samira ce suka kai karo da ita zata fito gurin da da suke hannun ta dauke da sabulun wanki,
Murja ke sheda mata abinda suka ji daga dakin Sadiya,
Tsuki tayi cikin rashin nuna tausayi tace ai aikin ta ke nan duk lokacin da zatai period ko ta kare,
Acikin mamaki duk suke kallon ta inda take kokarin wucewa abinta zuwa waje batare da ta damu ba,
Meenat ce ta sa kai zuwa cikin gidan inda sauran suka mara mata baya,
Irin yanayin da take ciki yasa su gaba dayan su rudewa sai kiran sunan ta suke,yi,,,
Da sauri Aisha ta koma falo inda ta dauko goran ruwa da cup ta dawo dakin ,
Tsugunnawa tayi tafara karanto addu,oin da kakan su malam Manya ya koya masu,
Ganin haka yasa ita ma Meenat zuwa daidai inda Sadiyan take kwance cure guri guda, kamar wace zata mutu,
Addu,oi suka fara mata suna tofawa duk da dai a tsorace suke,
Aisha tace su taimaka su daga mata ita, su bata ruwan da tai addua,n aciki,
Komawa sukayi tsatsaye suna kallon ikon Allah kawai,
Can sai sukaji tayi wani irin getsawa da karfi sai ga zufa ya keto mata a goshin ta,
Daga haka tafara sakewa tankar mai shirin yin barci ko somaywa,
Sai faman sannu, Anty sannu Anty suke mata,
Ita ko kai, kawai take iya kada masu saboda azaba,

***** ****** *****
I am sorry pls abinda ya furta ke nan da isowar shi gurin da take a tsaye,
Batare da ya tsaya wani magana ba kawai ya bude motar nashi, suka shiga,
Tuki Abubakar keyi a hankali kamar wanda ke tausayin sitiyarin motar,
Wanan yanayin tukin nashi yasa Salawatu jin dadin yanayin da ta tsinci kan ta yau tare da Abubakar din,
A hankali ya mika hannun shi inda ya kara volume din redio motar kira,ar shuriem ne ke tashi a cikin suratul AN-NISAN,
A hankali Abubakar yake bin kira,an malamin cikin wata irin murya,
Salawatu wace batasan may zatayi ba awanan lokacin sai gyara zaman ta tayi a hankali tare da bin lafiyan kujeran mota,
Tafiya sukeyi batare da wani yaiwa dan uwa magana ba,
Shi Abubakar din ne yadan kau,da shirun ta hanyar juyowa gurin da take zaune yace,
Wani shagone zamu tafi, ?
Hakan yaiwa Salawatu dadi don haka bata lokaci tace mai mutafi sahad, aiko,
Tace hakane don tasan matatara ne wanan shago dole ne ma wani yaganta tare da Abubakar kafin su fito,
Daga haka bai kara magana ba inda ya juya kan motan shi zuwa sahad store din,
Shigan su shagon ne sai taga Abubakar yace mata bissimillah ko sai ki zaba masu,
Da farko English wear ta fara dauko masu, masu kyau, don taji yace kada ta damu da kudin kayan ta dai zaba masu,
Tambayar shi tayi da cewa ko su nawane yaran inda ya sheda mata cewa su biyar ne,
Kai ta kada cikin mamaki tace wani abu sai malam bahaushe,
Har mutum biyar za,a turo hutu a garin Abuja haka ?
Ganin bata zabi kayan da yasan yaran hausawa suna sawa ba yasa shi kiran sunan ta
Karo na farko kega tun lokacin da tafada mai sunan ta,,
Wani irin dadi salawa taji don aganin ta ko mahaifanta da suka rada mata suna basu kai shi iya kiran sunan ta, ba,,
Wasu dinkakkun kaya readymade, ya nuna mata dinkin shadda ne masu kyau zani da riga da dan kwali akwai kuma masu siket, da riga,
Sai kuma gurin turamayn zannuwa inda ya ce mata tazaba mashi masu kyau da kuma tsada,
Ganin tana ta dauka baice komai ba yasa ta dan juya tare da daga kai ta kalle shi,
Tambayan ta yayi da cewa sun ishe,su ko ?
Mamaki taji a zuciyan ta tace shi wanan wani irin so yakewa yan uwan shi haka,?
Da,bai jin zafin kashe masu kudi, ?
Lailai za,a rina awanan gurin, don haka dole ne tayi kokari ta kutsa kanta gareshi,
Daga karshe itama yace ta dauki duk abinda take so,
Ba karamin mamaki salawatu tayi ba don jin irin kudin da aka caje shi,
Amma ba bata rai yasa hannu ga Aljihu ya biya su atake,
Masu kwasan kayan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login