Showing 15001 words to 18000 words out of 388021 words

Chapter 6 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8188

dan kalli Baba Samaila wanda ya ramay ya wani zabge a lokaci guda,
Nan da nan hankali mama Ladi yai matukar tashi ,,
Tai matukar kidimewa don ganin irin yadda Baba Samaila ya koma a lokaci guda,
Sai kawai ta shiga rusa kuka wi,wi tana cewa malam don Allah a yafe mata tayi kuskure, bazata sake ba insha Allah,
Malam ya ce, yanzu da zaran zancen ga yai girma duk gari ji zasuyi a dauka cewa tana MAITA,
Don ke ga Allah ya taimake ki da ace kin fara da bashi kazan da yaka so da shikenan ke bi hanya,
Don wata,rana har mutun zaicewa ki bashi jinin shi yasha, ke ko idon ki ya rufe kin iya sihiri
Baba Samaila dake zaune jingine da bango yace ai,duk zafin neman bai kawo samu,
Kawai mutum ya hakkura ga duk yanayin da ya tsunci kan, shi, don yanzu badon Allah ya gyara ba da, ba,a san iya inda wanan abin zai tsaya ba,,
Cikin muryan kuka mama Ladi kewa ku ya fe min don Allah
Malam yace Allah dai ya yafe muna baki dayan mu,,
Kuma wanan zancen ina son ya tsaya dai dai iya mu kada inji shi ga wani nan gaba,
Hakan yaiwa mama dadi so,sai don malam ya kashe wutan zancen,,,
Haka rayuwa ta kasance da ci gaba a gidan malam ,
Yanzu tsakanin mama Ladi da Hajja sai yar nisa da nisa don babu irin mugun shakuwar nan ta da,
Ita ko Hajja ko a jikin ta don arzikin ta,sai gaba gaba ya ke yi a koda yaushe,,,,

Rashin zuwan Abubakar gida akai akai ya fara da mun malam, Manya yanzu,
Don a iya ka sanin tun lokacin da mai,sunan nashi yai aure har izuwa yanzu baizo gida ya kai sau uku ba,
Gashi yanzu tasan ma,shekara, biyu da rabi da auren shi,
Abu guda ne shine duk wani dan uwa ya je zai aiko masu da sako mai yawa a kawo masu,
Ita ma fanin Sadiya matar shi haka ne,ko da yake mahaifiyar ta ba wai ta wani damuwa tayi da rashin zuwan yar nata gida ta yi ba,,,,
Kuma yadda yan gidan su, Abubakar suka damu da rashin samun karuwan ma,auratan,
Ita Hajja a nata bangare hakan bai wai damay ta ba sam,,
Idan anyi magana cewa har yanzu dai sadiya bata haihu ba sai tace lokacine bai yi ba,
Ita ko, bangaren mama Ladi ko in ce gidan su Abubakar rashin samun haihuwan shi na da mun su,
Tun dai malam Manya wanda kance abokina dai har yanzu shiru ba labari,
Bukin Sallah babba na bana Allah ya nufi Abubakar zuwa gida tare da mai,dakin shi watau sadiya,
Daga shi har ita kallo guda za kai masu kasan cewa akwai kwanciyan hankali da wadata atare da su,
Don hasken shi ya fito sosai gashi ya dan kara jiki da girma, gwanin ban sha,awa,
Wanan zuwan da Abubakar yayi ya kara tayar wa malam manya hankali irin yadda yake jin labarin, jikan nashi abin yafi da nan so sai,,
Gashi harda motar kanshi yazo lafiyya ga kuma tsaraba mai yawa,
Sai,dai duk yawan wanan tsaraban da yazo da su a kofan dakin mahaifiyar shi, mama ladi a ka labta su,,
Wanda shi Abubakar sam bai so haka ba yaso ne ace akai su can kofan dakin malam,
Tun da malam ne wanda ya tashe shi tun yana yaro sai ko sauran iyayyen su maza musan,man Baba Samaila,,,
Wanda tun baiyi aure ba duk abinda ya samo sai yace na Abubakar din shine ,

Mutanen gidane ke ta turuwan zuwa sashen Baba Buhari gurin gaida bakin Lagos da sukai saukan dare,,
Don ba,a samu ganin su da dare ba sai yau da safe don haka ake ta zuwa, ganin su,,,
Girman da yaran gidan nasu yayi yasa shi mamaki matuka don bai yi tsanmanin cewa sun,kai haka ba,
Kusan duk wanda ya shigo indai dan gidane da tsaraban shi,
Amma kuma sai wanda mama taso aba ma abin kwarai,
Duk wanan rabon da akeyi babu dan shiyan Baba Samaila ko mutum guda da ya shigo sashen, har zuwa yanzu,
Daidai shigowan ,Saratu matar Baba Samaila da iyalinta
Abubakar wanda ba ma,abuci magana bane tun farko, daga shi har matar shi,,,
Yana zaune, gefe guda yana wasa da wayan da ke a hannun shi,
Wanda alokacin kusan a hannun shi yan gidan suka fara ganin wayan Mobile,
A cikin natsuwa suka gaishe shi kamar kowa tare da masu yaya hanya,
Ya amsa cikin dan sake fuska kadan, da cewa mama, mun samay ku lafiya,?
Da ga haka bai kara cewa komai ba ita ma dai mama saratu juyawa tayi zuwa kofan waje da yaran ta,
Shiko Abubakar sai kokarin duba kaya yake yi wanda zai basu,
A daidai kofa duk wanda ke gurin a lokacin zai iyajin abinda uwa da Dan takeyi a dakin,
Haba mama inji Abubakar ya ce yan uwanane fa na ji ko duka tsaraban zan basu ai sunci shi a guri,na,
Kai ne dai ka dauke su a haka ni ko diyan shaibu, ban yarda da wanan ba balle diyan, Samaila masu daukan kai kaman wata tsiya,
Murmushi kawai mama Saratu tayi a lokacin don jin abinda mama ladi ke fadawa dan ta, akan su,
Haba mama kibar fadin haka don ni baba Samaila baida maraina a gurina,
Kaine kasan may yai maka ni dai ban yarda ka dauki cikin wa yan nan leshin kaba su sai dai wancan na gefe da na cire ma,
Suna hada ido da kishiyan mama Ladi sai wa mama saratu signal da ido ta wuce kawai,
Isan su sashen su yayi daidai da lokacin da sakon Abubakar ya iso gare su,
A lokaci guda mama saratu da yaranta Meenat da Awal su ke cewa amayar mashi ace abawa wasu yan uwa sun gode, su,
Wanan sakon yasa Abubakar fitowa dauke da kayan a hannun shi, cikin bacin rai,
Direct gurin mama Saratu ya nufa duk da yasan cewa bawai ta girmay shi bane amma a matsayinta na matar kanin mahaifin shi yana ba su ladabi,,
A daidai lokacin Baba Samaila yashigo gida daga waje sai kuma ya samu Abubakar din da kan shi a sashen shi,
Bakin Baba Samaila har kune don jin dadin ganin Abubakar da yayi yau,
Sun kara gaisaw cikin nuna farin ciki inda Baba yasa akawo mai ,shimfida,
Nan suka zauna da Abubakar kafin su fara magana Abubakar ke cewa mama don Allah kiyi hakkuri
Kada zancen mama yasa ki yi fushi har kuki ansar kayan
Sai a lokacin Baba Samaila yagane may ke faruwa,
Murmushi yadan sake mai laushi sanan ya ce, haba dai Saratu, may zai sa har ki biye wa halin Ladi,
Awal ne yace baba munji abida mama Ladi ke cewa da zamu fito shiyasa maman mu tace, abar kayan,
Batare da,Baba Samaila ya,bukaci jin Komai daga bakin iyalin nashi ba ya karbi kayan a hannun Abubakar tare da yi mashi godiya,,
Yana cewa Ladi ai mahaikaciyace wa ke bin ta nata balle yai fushi,
Murmushi Abubakar yayi don tunawa da waban sunan da Baba samaila yakira maman shi dashi,
Don tun yana karami idan sunyi fada abinda Baba samaila ke ce mata ke nan mahaukaciya,,,
Murmishi yakarayi don tuna yadda suke kwasan riki abaya,,
Gashi kuma idan harkan ta yazo shine a tsaye amma san ita mama bata ganin hakan,,,
Sai kuma daga baya ya fara yi mai nasiha akan rashin kula da gida da bai yi
Inda suka dauki tsawon lokaci yana mai nuni da rashin alherin da hakan ke da shi,,
Abubakar yabar sashen Baba samaila cikin rashin jin dadin yadda mahaifiyar shi ta nuna masu tsana,
Alhalin suna zaman yan uwan shine suma matsala kawai don wai ba ciki daya suka fito da mahaifin shi ba,
Wanan wani abu wanda tun yana karami yake sane da wanan akidar na irin yadda ake gwadawa Baba Samaila yan ubanci a gidan,
Amma da yake shi na mijin duniya ne duk yadda za a gwada mai zai iya shanyewa a ran shi,
Abinda yake ji shi ga ahi yau har iyalin shi sun fara sanin wanan bakar tsanar da ake gwada ma su agidan,,,


ZEE MAKAWA YELWA
[6/24, 10:04 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


I,HIDDINAS SSIRATAL MUSTAQU,IN,,,,,,,,,,,




A lokacin da Abubakar zai koma Lagos sai malam ya kafe akan cewa dole ya tafi da mutum guda daga cikin yan uwan shi,,,
Don haka Abubakar bai ja ba don yasan cewa tun da tsohon ya ce haka yana da,wata manufane,
Maganar farko sai malam yace a dauki daya daga cikin "yayan Baba Samaila,
Aiko mama Ladi ta tuma ta kafe sam ita bata yarda ba ,
Ga Abubakar da kan,ne a dakin su shine za,a ce a tsallaka aje har sashen Baba samaila,
Baba Buhari zai yi magana malam yace a,a ya bar,ta ta ba da yaro guda daga fan,ninta,,
Ba kunya ba tsoro mama Ladi ta shirya Samira tace a tafi da ita,,,

Jama,an gidan malam manya da yaran, su, su,ka taru kofan gidan malam don yiwa mutanen Lagos rakiya,
Abubakar ya na zaune kafa tankwashe, saman tabarma a gefen malam.
Inda malam din ke kara ja mai kune akan al,amarin duniya,,
Ita kuma Sadiya tana tsaye jingine a gaban mota tana wani yatsunar fuska,
Su,ko mutanen gidan sun daga gefe sai kallonta, su keyi suna yatsunar fuska su ma,
Wasu kuma daga cikin su haushin yadda take masu kallon bazan suke ji,
A can kuma gefe Samira ce da yara yan uwan ta suna ta yi mata suraita irin na ke kan Samira kinji dandin ki za,a dake har Lagos,,,
Ita ko samira sai washe baki takeyi don jin dadi za tai wa yan uwan ta tazara,,

Tun fara hanyar su Samira ta fara rena kan ta don
Tambayar ta Abubakar ya fara yi da cewa, wani makaranta kike zuwa,
Cikin dan nuna tsoro da kuma nauyi Samira tace, salamatu Husaini,government girls secondary school,
A jinki nawa a can ?tace, aji uku zan je hudu,
Sai kuma yai shiru ya ci gaba da tukin da ya,keyi,
Da har Samira na murnan tamabayar ya kare,
Sai taji an jefo mata wani tambaya again,
Shekarun ki nawa yanzu, ?
Cikin rawan murya tace mama tace wai goma sha, hudu nake yanzu,
Suka yi ido biyu dashi tai saurin dukar da kai da sauri don tsoron fuskan shi take ji,,
Izunki nawa yanzu,?
Goma sha, takwass,,,
Bata karasa fadi ba taji ya ce takkwala kawai,
May kike jira har, yanzu baki sauka ba ?
Haba ai tai kokari inji Sadiya wace, ke tauna chewingun,
Common shut, up my friend ke nawa kike balle har ki sa min baki,
Cikin sauri tai wani cewa Allah ya baka hakkuri ni dai,
Allamun tsoro su ka kara baiyyana a fuskan samira wace tai da ta sani bata biyo yayan nata ba,
Tun yanzu wanan tambayar haka kamar dan jarida
Can kuma ya kara tambayar ta yaran baba wani nawa ne sai ta fada mai,
Ita kuma gwago wance fa diyan ta nawa yanzu, shima sai ta fada mai,
Har dai zuwa lokacin da tafiya yai nisa duk kan su su,kayi shiru don gajiya,

A cikin dare suka isa garin Lagos wanda yawan cunkoson shi, Samira ba zata iya gane komai ba, a cikin ida suka dosa,,,
A kofar wani gida mai hawa kusan uku suka tsaya,
Gaskiya gidan ba laifi don ba yabo ba fallasa a cikin shi,
Gaba dayan su har yayan nata suka fara kwasan kayan su zuwa cikin gidan, sashen da taga Abubakar ya sa dan makulli ya bude kofan,
A hawa na biyu suke da zama su, don haka ba suyi wani shan wahalan hawa ba,
A tsakiyan falon gidan sukai ta jibge kayan da sukayo tsaraba da ga gida da kuma nasu na sawan su,
Duk da dai shi Abubakar ya ce wa mahaifiyar shi basai Samira tazo da kaya masu yawa ba, acan,
Amma duk da haka tadan zo da yan gwargwado daga abinda take so,
Wani daki yayan nata ya nuna mata ya ce ta kwashi kayan ta zuwa ciki a nan zata zauna,,,
Dakin yana dauke da dan gado guda daya sai mirrow, a gefe,
Samira na kallo Sadiya ta dauki dan trolley din ta ta nufi dakin kwanan su,
Inda tabar sauran kayan nan gurin da aka zube su da farko,,,
Baki bude Samira ke kallon yadda yayanta ke ta faman kwasan su zuwa ciki inda ya kamata ya kai komai,
Ita ko Sadiya tun shigewar ta dakin bata kara fitowa waje ba,
Take away din da ya saya masu tun a hanya shine ya bawa Samira, guda daga ciki tare da nuna mata kitchen din su,
Shigan samira kitchen din sai da gaban ta ya fadi don shirgin da ta gani kamar ba,a ciki ake girki ba,,,,

Zaune suke a saman tabarman roba wanda aka shimfida a rufar dake tsakiyan filin sashen nasu,,,
Kasan cewa yau Jumma,a , ne duk kan su sunyi kwaliya, fes da su,,
Ga kuma shiyan nasu fes da shi kamar babu yara aciki har biyar,
Sallaya ne a hannun mama Sadiya tana kokarin nikewa da ga gurin da tai sallah,
A daidai lokacin Baba Samaila ya shigo gida da yaran shi su uku, maza, da ke, biye da shi a baya acikin shigar su ta sallah Jumma,a,ga kuma shiga na fararen shadda sun yi don, Jumma,a,,,,
Da sallamar su suka karaso cikin gidan, sannu da zuwa mama ke ma su inda su Meenat da ke daga ciki suka gane cewa mahainfin su ya dawo,
Nan su ka yo, waje gaba dayan su suna masu barka da Jumma,a
Bayan sun zauna a saman katon tabarman dake shimfede mama ta gabatar masu da abincin rana,
Kowa anzuba mai a nashi, plate, tare da abokin cin shi,
Tuwo ne na far shinkafa da miyar taushe, anzuba wa miyar kabewa bussashe, da kuma kulikuli,
Sai manshanu da aka lema a saman miyan kamshin shi yana tashi sama,
Mamace ta fara gane cewa yau Baba bai cikin farin rai,
Da alamar zuciyar shi ba ta da dadi sam don tun safe haka take gani tare da shi,,,
Loman da ya diba zai kai abakin shi ya tsaya a lokacin da ya ji muryan mama tana cewa,
Ai da ka daure ka ci abinci ko bakajin dadin shi,
A hankali Baba ya dago kai ya dube ta cikin dan sakin fuska mara walwala,
Fuskan matar nashi ya tsurawa ido don ganin cewa, ta fahinci halin da yake ciki,
Inda yaran su, suke zaune yadan kai kallon shi, gare su,
Hakan yasa mama gane cewa bai son yin magana a,gaban su a lokacin,,
Don haka sai mama tai shiru taci gaba da zubawa yaran maza miyan da suka shan ye,
Amma azuciyan Baba sai ya kasa daurewa don yasan cewa matar ta shi don, ta damu da damuwar shi,
Baba yai dan murmushi tare da yanko lomar tuwon ya ce,
Saratu ke nan ai dole ki ganni haka don al,amarin kiyayyan da Ladi ke gwada min yai yawa,
A lokacin ne ya jaye kulan abincin daga gaban shi ya jawo roban ruwan wanke hannu a,gaban shi,,
Mama tace ko ma may take nufi ai Allah ya fita Baban Meenat,
Na san da haka saratu to amma abin ne da daure kai don dai ni da da farko abin bai damu na sam,
Amma yanzu wanan abun da tai muna yasa na fara jin tsoron ta akan yaran nan,
Caraf Aliyu yaron su na uku ya sa masu baki azancen su da cewa,
Wai ce muna takeyi irin fulani irin tsiya,,,,
Murmushi Baba yayi a lokacin da Aliyu ya fadi haka nan,
Baba ya ce kada wanda yadamu da duk wani abin da Ladi zatai maku,
Nasiha Baba yaiwa ran sosai don irin yadda zasu zauna da mutane lafiya,,
Jin Meenat tai shiru a lokacin kamar bata a gurin yasa mama dan juyawa gurin da take zaune,
Ke lafiya kike kuwa kin yi shiru haka, kuma ko abincin ba,kya ci,,
Ba komai mama Meenat tace cikin muryan tausayi,
Muryan Baba ne ke cewa, Amina ina gani karama da ke kina aon sawa kan ki maganar manya ko ?
Murmushi Meenat har dan sautin ya fita sanan tace,
Baba ai ni nasaba da halin mama ba yau ba duk wani abinda zatayi nasan dashi ko ,
Takai hannun ta cikin plate din


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login