Showing 375001 words to 378000 words out of 388021 words

Chapter 126 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8285

ku can baya,
Amma aida kin fada min tun lokacin da kika fahince cewa ga inda suka tafi don kinga tana shanmatan shine ta hanyan cewa maganin haihuwane take nema,
Tana tapka barna ta wanan hanyan wanda har halan ya gusar mai da hankalinshi baki daya,
Wanan matar ba sai an fada ba tafi ku wayo sosai wallahi duk acikin ku babu sa,an yinta,
Na amsa da kai dakuma fadan cewa hakane malam nima na sani duk sunfi wayo da shekaru,
Sai naji yai murmushi yana cewa, amma ai Aminatu mijin ku kuma yafi kaunar ki aduk cikin ku,
Cikin kuka nace malam haka dai ake gani amma gaskiya yafi kauna ita Salawan da Fatima ai,
Malam yace ba gaskiya bane hakan Aminatu Abubakar yana kaunan ki tunfarko don da bai kaunar ki da saboda fitinan mahaifiyar shi da ya sake ki,
Amma saboda yana kaunar ki duk fitinar Ladi dole ta saka mashi ido dake, gashi auren ku ba wani dadewa yayi ba Allah ya albarkace ku da zuria masu albarka,
Murmushi nayi don jin may yace yace to ko ke fa amma zaki ce wai bai son ki yana sonki fiye da kowace mace a duniyan nan,
Na bude baki zanyi magana sai yace Aminatu watarana ko ina da rai ko banda rai zaki fada da bakin ki nace yana son ki yana kaunar ki fiye da tsan manin ki,
Nan yaci gaba da kwantar min da hankali tare da kara min karfin gwiwa akan na kara hakkuri kamar yadda nake don Allah yana tare da masu hakkuri akoda yaushe,
Daga karshe yake fada min cewa insha Allahu badadewa ba zasu yi kokatin ganin sun karya duk wani asirin da Salawatu taiwa Abubakar din ,

****** ********** ******
Sati guda bayan hiran mu da malam sai gasu sunzo muna bakin weekend shi da salawatu abinda yasa na kirashi da bakin weekend shine,
Tunda suka zo gaba dayan mu baida lokacin mu sai uguwa suke fita shida ita wai zuwa gurin tsabgogin ta da yan uwa,
Sun iso a cikin dare ne babu wanda yasan cewa zasu shigo a ranan,
Ramatu ce tazo take fada muna isowan shi sai da na dauki lokaci sannan nafita zuwa yi mashi sannu da zuwa
Na samay shi adakin shi tsaye yana waya ina saye da wani dogon riga wanda ya matse min jiki hip's dina sun fito gwanin ban sha,awa,
Daga kofan shiga dakin na tsaya ina cewa sannu da zuwa
Ya daga min hannu alaman ya karba min ban tsaya ba na juya nabar dakin abina zuciya ta tana muradin shi alokacin amma sai nadake na basar dashi kawai,
A tsakiyan falo na hadu da salawtu tafito ta rufa towel a jikin ta banga wani canji ba a gareta,
Fuskana dauke da fara, nake cewa aa mutanen kasan kudu sannu ku da zuwa tafiya babu sanarwa balle a shirya maku,
Saicewa tayi wallahi sai da rana muka shirya tafiyan batare da mun wani shirya ba,
Aisha ce ta katse mudaga sakon da take sanar damu cewa itace ta sa aitafiyan a hakan,
Aisha tana ce min mummy Amir ya fadi bakin shi yana jini,
Nace a hanzarce a ina take ce min a falon mu yataka ruwane,
Da sauri na wuce batare dana karasa saurarenta ba zuwa gur8n duba Amir din wanda ya fadi,
Sai harkokin su suke muna kallon ikon Allah ba wanda ya tanka masu,
Allah ya taimakeni da farko har na tayar da hankalina kamar yadda naga Fatima takasa zama ta kasa tsaye,
Daga baya bayan na roki Allah akan ya bani hakkuri da dauriya sai ko Allah yacire min duk wata damuwa a tare dani,
Nan na mayar da duk wani abinda sukeyi ba komai ba inda nake shigewa part dina nida yarana da duk wasu mutane na don kafin duk su fito da safe duk mungama wani abinda zamuyi mun shige ko, abin mu,
Ashe wanan abin yana bata mashi rai don dama tun can farko shi mutum ne mai son gani iyalin gidan sun hadu a falo ko guri guda ana cuwaniya a tare amma sai gashi ba kowa daga part dina duk muna daga cikin sashen nawa,gaba dayan mu,
Ina zaune a tsakiya falo ina bawa yarana nono ga plate din abinci daga gefena kaina babu dan kwali, sai gashina da yasha gyara yana dukule yana sheki,
Dariya na keyi alokacin saboda yadda yaran ke ta kokarin kama nono a tsakanin su,
Bamuyi aune ba sai ganin shi mukayi yadaga labulen falon fuskan shi a daure yana bin mu da kallo daya bayan daya,
Tankar ban gashi ba sai kokarin gyara kwancin hassan da na keyi asaman ciyana sai ya dago kafa guda yatokarawa dan uwan shi take abin ya bamu dariya na cire kafan yaron cikin cewa ji babban kawai kana jan dan uwan ka fada,
Daga can kusurwan dakin Asmau ke cewa sannu Yaya,
Ya amsa a dakile, dacewa yauwa sannun ku dai,
Ban kula shi ba naci gaba da wasa da yarana nafita batun shi kamar zaiyi magana sai kuma naga ya juya yafita,
Nabi bayan shi da kallo har yakulewa ganina, na sauke ajiyan zuciya tare da dan lumshe idanuwana,
Fitan shi yai daidai da fitowan Salawatu daga part din ta sai wani kallon tuhuma take mai na may yakaishi part dina,
Nan yadan fara kamay kamay yana cewa tun safe banga kowa a waje ba daga cikin yaran nan shine ashe suna daga ciki,
Duk ya rude saboda wani irin abu da yake ji lokacin da ta watso mai harara akan may yasa ya shiga gurin mu,,
Allah ya kyauta Sadiya tace daga gurin da take zaune a cikin tagumi,
Duk hiran da yake mata fuskanta a murde yake bata saje mai ba duk ya shiga rudani ya susuce saboda rashin gani sakin fuskan ta,
Itako sai cika take tana batsewa wai ya kula wata ba ita ba,
Fitina irin na Salawatu duk da tana can tare da maigidan bai hanata da tazo ba wai ta karbi girki,,
Inda yadan turza shine da yake cewa may zai sa ta karbi girki a ranan bayan mu ukune anan din,
Sai take ka manta cewa Meenatu bata girkine ita yace saboda may fa sai take cewa wai aikin da akai min mana,
Yace har yanzu bata karbi girki bane may taje jirane wai ?
Bata saurare shi ba ta shige bedroom din shi ta kwanta abinta ba yadda ya iya dole ya shige gurin ta,
Da safe washe gari ina kwance ban tashi ba daga barcin safen dana koma yi,naji ya shigo dakin nawa a cikin barci naji muryan shi yana magana yana cewa Asmau baya tashi bane,
Sai Asmau take ce mai tana ciki ta kara kwantawa ne ya shigo dakin yana saye da rigar barci a jikin shi,
Ance jiya Amir bakin shi ya kunbura wai ya fadi ya akayi yafadi yake tambayana, a lokacin da nabude ido mukayi arba dashi,
Yana tsaye ya harde hannayen shi a saman kirjin shi yana mai kura muna ido nida Amira kwance a saman gado,
Sai da na dan gyara kwanci ya tare da kokarin bude idanuwana da sukai min nauyi nace,
Faduwa yayi a saman ties shine bakin yadan hau,
Ba,a goge gurin ne da har akabar ruwa ya fadi har baki ya fashe, yana inane yaron ?
Nace a cikin daure fuska yana gurin Ramatu ta goya shi don gurin yana mai ciwo baiyi barci ba da dare,
Shima fuska a daure ya saki ajiyan zuciya yana dubana a cikin wani irin yanayi maradadi yace ya akayi baki karbi girkiba har yanzu,
Mamaki da takaici ne suka rufeni sai kawai na kallr shi na kawar da kai,
Tuni haushi ya rufe shi sai naji yace ba ke nake tambaya ne kin kyaleni,
Nace saboda lafiyata shi yafi min komai a rayuwa har yaushe na tashi daga jinya dazan je karban wani girki can,
Haushi da bakin cikin maganata suka rufe shi sai yake cewa ni kike raina wa wayyo haka meenatu ?
Nace a takaice bazan karbi girki ba sai naji karfin jikina sosai saboda idan wani abu ya samay ni hasaran iyayyena ne da yan uwana, kawai,
Ido ya kura min acikin takaici don danne zuciyar shi kawai yake don wani irin haushi da takaicina yake ji a zuciyan shi amma dai ya daure yana kokarin ganin yafitar da hakin shi gareni,
Banza nayi dashi tankar ban sanda yana gurin ba don nima zuwa lokacin haushin, shi nake ji,
Kawai don ya mayar dani ban san ciwon kaina ba zai shigo min da wani zancen wai karban girki,
Bai kara cewa uffan ba ya juya yafita daga dakin rai a bace nima jin yafita na kuta tare da kokarin mikewa ina cewa don ina Aminan mahaukata kawai don ka bukaceni sai na samay ka a haka babu wani kulawa ko dubaiyya,
Tun wanan lokacin nakara kama kaina ga harkan su har suka karashe abinda ya kawo su suka kwasa suka koma,
Koda zasu tafi har sun shirya tafiya ne na samu labari a gurin Baba Wadda yake ce min wai ranan zasu koma da dare,
Daya shigo bani kudin amfanina ne yakecewa wai sun fito ke nan su zasu koma
Batare dana kalle shi ba fuskana a daure nace Allah ya sauke ku lafiya, yasa kai yafita don kada taga ya dade a gurina,
Fadan su biyu da fatima wanan zuwan don ita sam bata da hakkuri ko kadan, da sun mata data maganta kuma ba magani sai makara kiyayyan dake shiga tsakanin su
Inda na koma asibiti don likita ya kara duba lafiyata tare dana yara kamar yadda suka umurce ni danayi duk karshen wata saboda jikin danaji da yawa,
A gidan bayan tafiyan su a haka muka kasance acikin damuwa saboda wanan zuwan ya tabbatar muna cewa da control din Salawatu yanzu yake komai, saidai yana iya kokarin ganin ya dan boye amma abin bai boyuwa,
Saboda sunan sunyi girkine kawai amma yana manne da Salawatu duk yini ba sauki ga al,amarin sai na Allah,
Bayan komawan su acan sukai ta fada a tsakanin su wai may zai sa yazo yana kula sauran matan shi,
Yazo yana mata wullakanci agaban mutane duk ta saka shi ya shiga cikin wani yanayi gashi ta karbo sabon kulli agurin bokayen ta duk ta rikitashi sosai,
Wani irin shaukin ta yakeyi don sam bai kaunan yaga bacin ranta ko kadan,
Ga kudin da take karba agurin shi kamar an aiko ta ba tausayawa sam,

ZEEE MAKAWA YELWA
SEENABU
[12/26, 9:28 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL BADEE'U
Yan uwa musulumi ina muna fatan alheri acikin wanan lokaci da muke a cikin sa na shiga sabuwar shekaran nasara,


Yau kimanin sati uku da tafiyan su inda muna nan muna ta rokon Allah akan irin halin rayuwan da muke a ciki,
Sannu a hankali nake shirin tafiyan da naiwa yaya Abubakar nason zuwa ganin yan uwan mu a gida Birnin Kebbi,
Mun shirya tsab inda zan yi tafiyan ne da duk wani wanda ke tare dani don har da Ramatu da ita zamu tafi saboda diyanta babu kowa a garin duk sun tafi makaran ta a lokacin,
Nan muka rufe part dina inda zamuyu tafiyan ne da motoci guda biyu Lawal mijin Fattu wanda ke gudanar da komai na gidan a halin yanzu shine, yai muna shirin tafiyan,,
Abin idan ka gan mu gwanin ban sha,awa inda mota guda nice da yarana sai su Asmau na da Ramatu Antyn Nani, da suke cewa Antyn raino, atare dani, Baba Hamza' yana jan mu,
Sai dayan motan da ke dauke da kaya Baba Wadda da abokan su yusuf, da Aminu su ka biyo mu ,
Mun iso da yamma lis, lokacin marance yayi akwai mutane a kofan gidan mu masu daukan karatu,
Isowan mu yai daidai da akwai wasu daga cikin iyayyen mu a gurin karatun,
Tsayuwar motocin mu a kofa yajawo hankalin mutanen kowa idon shi a kan mu,
Kafana dake saye a cikkin takalman kasan indiya na kamfanin Bella, bakake, na fara sakowa daga waje inda ya fara daukan idon jama,an gurin,
Nan, muka fara fito gwanin ban sha,awa inda akayo kan mu ana muna sannu da zuwa acikin so da kauna,
Sai murna da jin dadin munga yan uwa mu keyi a lokacin inda yarana ake ta karban su a cikin mutunci, ga kuma so da kauna,
A part din mahaifana muka yadda zango inda jama,an gidan mu da yara ke tururuwan zuwa muna sannu da zuwa, acikin murna,
Ga ruwa da fura mai sanyi yaji nonon shanu a aje muna a gaban mu ga kunun aya sai kamshi ke tashi,
Murna da dokin ganin mahaifiyana ya hanani shan komai daga cikin abinda aka gabatar muna,
Dije tashigo inda na mayar da hankalina a garesu muna yaushe rabo suna min yaya jiki da sauran jama,a,
Dije tace Meenatu wa zai Hank a haka yace kece kikayi irin wanan jiya wata bakwai a renon ciki asibiti har kika kai kusan wata daya acan,
Dan gajeren murmushi nayi, nace alamarin Allah ke nan Dije,
Tace wallahi baki ga yadda kikayi wani kyau bane kin dan yi kiba ga haske,
Naji dadi sosai da,ba,ace na ramay ba sai gashi duk da halin rayuwan da nake ciki ana cewa wai nayi kiba,
Hakan ba karamin dadi yai min ba araina so sai don ko ba komai ai zan ji dadin kara boye sirina sosai,
Sai kuma Dijen ke cewa ga abin sha annaje maku banga kinci komai ba kin san fa cikin ki har yanzu akwai jego a tare da ke, balle wanda ke shayar da har diya uku, alokaci guda,
A cikin yar sakin fuska nake cewa sun min sanyi ne kin san ina shayarwa shiyasa ban son shan abu mai sanyi ,
Saboda yaran musan Amira wace bata da wuyan kamuwa da sanyi da zaran ta dan sha sanyi yanzu kiji ta fara atishawa,
Dije tace, ashe yaran kulawa suke samu sosai shi yasa sukai wani irin kiba tankar inji na hura su, mursmushi kawai nai mata muryan mahaifiyata ce naji tana cewa,
Tau a kawo maki abincine inji Mamana Saratu,
Nadan girgiza kaina nace wallahi a koshe nake naciyo abinci a mota da mukazo da shi,
Sallah zan tashi na dauro alwala kafin aikira don ko la,asar bamuyi ba,
Dije ta bude baki za tai magana mukaji muryan daga waje ana fada wai don may za,a kawo kayan da mu kazo da su a part din iyayyena ,
Dole akaisu part din ta har da mu din mu koma acan tunda aure nake ba wai a karkashin su muke ba,
Ikon Allah nace alokacin da na ke aduke daniyar daukan buta don zuwa yin alwala,,
Mamaki ya cika min zuciya nace a cikin dakiyar zuciya akawo min kayana nan do bana wanda ake tsan mani bane,
Wanan kalamin da yafito min abaki ya farune a sakamakon jin haushi abinda mama takeyi haka,
Gashi dan nata da take kuri dashi ba ma wani kulawa muke samu daga gareshi ba da har zata fadi hakan,
Don haka kamar yadda na bada umurnihakan yaran gidan mu yan kan,ne na suka dinga jido min kayana zuwa part dina tare da taimakon baba Wadda,
Yau na bawa Mama Ladi mamaki kwarai inda ta taso wai da zuman yi min masifa akai,
Amma abin mamaki tana shigowa alokacin na idar da alwala ina dan diga ruwa a bakina, ina karanta lailahaillah wa,adahulashari,kallahu har zuwa karshe shi,
Ta shigo part din namu babu ko sallama tana cewa ina Meenatun din take ne,
Na amsa da cewa gani Mama, sai kuma naga tayi dan dabur dabur duk sai tai tankar ta dan rude tana cewa,
Au to kunzo lafiya ?
A cikin mamaki nima na karba mata gaisuwan dace wa Lafiya Kalau,
Yanzu idan nai sallah zan shigo ai, mu gaisa,
Sai take cewa nazo ne akan naga ana son nuna min iko nida jikokina nace azo dasu inda nake akece min wai kin ce komai a nan za, a kawo maku shi,,
Nace eh duk wani, kayan danazo cewa nayi akawo min su nan inda nake, ne, nace mata hakan ba a cikin rashin kunya ba,
Ido ta dan kura min kamar wace zatai wani magana amma kuma sai naga taja ta juya zuwa inda ta fito, rai a bace,
Na rasa dalilin da yasakata kariya da ga masifan da tazo muna dashi, a part din mu,
Abinda ban sani ba shine ashe wanan hailalar da tasamu ina yi dana idar da Alwala shine ya sakata yin taushi saboda karfin shi,
Tana daidai fita daga part din namu sukayi kicibis da mahaifina wanda dawowan shi ke nan daga gurin sana,ar shi,
Kallon kallo suka sakar wa junan su kowa yana tuhumar dan uwa,
Saboda shi Baba yana mamaki don ganin ta a part din shi don yasan ba banza ba tazo sashen nashi,
Yayin da itama take wa Baba kallon macuci yana son su mallake ma ta danta su kadai,

****** **********


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login