Showing 198001 words to 201000 words out of 388021 words

Chapter 67 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8255

yaya za a kwashe da mijin ki yanzu,
Nace nima anty shi nake ji wa tsoro yanzu wallahi duk na rasa may zanyi, akai,
Na ji ta nisa tana cewa sai ki fada mai kawai don baki da zabi, akai,
Nace amma anty ni naso, sai zuwa gaba ya sani ,
Kina da wani dabarane ? nace mata Allah zai kawo min mafita,insha Allah,
Tace to shikenan yanzu sai na jiki ke nan amma dai da kin fada mai gaskiya zaifi,
Nace ai zan fada mai amma sai nan gaba kadan insha Allah
Anty tace to shike nan sai dai na kira ki don inji yaya kukayi,,,
Kiyi kokari duk abinda likita yace kiyi ki tsare yin su dan Allah
Mu kai sallama da ita tana mai ce min in bi sannu kada, nayi laifi, a gurin shi nace insha Allah

****** ********** ******
Tun zaman su malamin ya fara masu bayanin akan dalilim da yasa su zo gaba dayan su, gurin shi
Dalla,dalla ya fara masu bayani abinda ke faruwa da su a tare da su dama duk wani wanda ke a tare dasu abin zai iya shafa,
Kuma akwai rabo mai karfi wanda in har akwai zuwan shi a duniya sai yazo,
Saboda irin taimakon da wanan abin ke samu daga bakuna daban daban,
Duk wanan bayanin a dunkule malam a cikin harshen shi na yaren gwarawan garin Suleja, yake masu,
Sai daga baya ne Yaya Abubakar ya fara fahintar manufa wanan mutumin , don bayani yake masau tankar yana masu hira ne,
Sai ya dan kalli Anty Sadiya ya jijiga kan shi yace,
Hajiya, sai fa kin yi hakkuri idan har kina son samun mafita akan al,amarin ku domin maganan zai girgiza ki,
Anan ya fara mata baya ni batare da boye mata komai, ba dallah dallah ta yadda zata fahinta,
Aiko Sadiya tana gane nufin shi tai sauri kura mai ido, cikin bacin rai tace ,
A cikin irin muryan tana na rashin mutunci da takan yi a hankali tankar tana jin wari ko takaicin mutum,
Kai kuma a haka zaka bulo muna da sallon cin kudin ka ,
Don kawai ka samu abin duniya zaka zaunar da mu kana zuba muna wanan sheri,
Ashe yadda nake daukan ka da zaton kai na Allah ne a cikin malamai,
Gaba dayan su tsayawa su kayi suna kallon ta acikin mamaki ta mike fuuu zuwa waje batare da ta tsaya karasa sauraren mutumin ba,,
Bayan fitan tane malamin ya kalli Yaya Abubakar a yayin da yake kokarin tatara kayan da yai masu amfani da shi,
Yace Alhaji idan har kuna ganin kazafi ne nayi maku kuna iya zuwa gurin wani inda ku ji karin bayani,
Godiya su kai mai tare da mikewa tsaye su na wa mutumin godiya,
Tare da bashi alheri tare da karban maganin da za,ai mata amfani dashi,
Suna fitowa suka hango Sadiya a bakin mota tayi murtun da fuskan ta
Daganin ta cike take da masifa a zuciyan ta kamar tana jirane kawai a tabata ta fashe,

Tafe su ke a mota babu mai magana daga cikin su kowa da abin da yake sakawa cikin zuciya shi,
Yaya Abubakar wanda saboda shiga cikin tashin hankali sai faman share zufa ya ke yi, da hankici,,
Sadiya ke a bayan mota zaune tace shiyasa sam bana son zuwa gurin irin wa yan nan mutanen ,
Masu kokarin hada fada da gaba acikin al,umma don ba su taba shuka alheri su,
Yanzu da kika samu lafiyane kike kokarin cewa, bai da mutunci ko ?
Maganar da Yaya Abubakar ya jefo mata, ke nan daga inda take zaune,
Tace wan,nan ai ba mutumin arziki bane mutumin da zai dubi idon ka yai maka irin wanan cin fuska haka,
Babu wanda ya tanka mata don kowa da abinda yake nazari,
Shidai Yaya Abubakar labarin abinda ya faru a gidan mu hiran da Baba Wadda yai muna da yazo shine ya ke mai yawo a kai,
A haka suka shigo gari cikin wani irin yanayi kowan su yake har mijin Fattu dake a tare dasu wanda bai san may ya haddasa fitina haka ba a tsakanin su don gaba dayan su ransu a bace ya ke
****** ********* ******
Sallaman da Ramatu tayi ne yasani dan daga dakina ina mai murmushi nace a Ramatu har kin dawo ,?
Sannu da zuwa ko ?
Tace Hajiya ke kadai ce agidan ashe ?
Na bata ansa acikin dan sake fuska nace, ai ban wani dade ba acan ,
Don Anty zasu fita da maigidan zuwa unguwa shiyasa na dawo, da wuri ban ko tsaya ba,
Har zata fara tafiya hanyan dakin anty nace mata gashi ko ta rufe kofan dakin ta wallahi,
Sai dai idan zaki zauna a falo harta ta dawo,,
Ba tai min wani musu ba naga takoma daga can gefe ba saman kujera ba ta zauna,
Cikin daurewa na fito don dan dora muna girki dan abinda zamuci,
Ramatu ce, na ji ta shigo kitchen din tana cewa,
Hajiya barin dan kama maki ko wanke wanke ne, da shara, na juyo cikin dan ya mutse fuska, alaman rashin jin walwala a tare da ni,
Nace a cikin bata fuska wallahi Ramatu ban jin karfin jikina sam duk wani iri nake ji a tare da ni,
Tace ai na ga alama don fuskan ki ya nuna rashin jin dadin a tare da ke,
Ita ce tai min girkin tuwon farar shinkafa da miyar kuka sai kamshin kayan yaji da daddawa ke tashi a cikin sa,,
Ta gyara mn kitchen din tsab tare da gyaro falon da sauran guraren gurin da ya kamata,,
Nafito acikin wani farin material da na saye a shago Antyn Saloon,
Ita da kanta ta bayar aja dinka min shi dogon riga ce mai, bin jiki, akai min dashi,
Ban dade da gama shiri ba naji, dawowan su a lokacin don haka ban dauki wani tsowon wani lokaci ba ,
Na fito don in masu sannu da zuwa, a irin yadda na gan su sai na fahinci akwai matsala,
Don Anty Sadiya fuskan ta a murtuke yake babu annuri a tare da ita,,
Duk sannu da dawowan da muke mata lokacin sai nake ganin kamar bata ansa mu na ba ma,
Yaya Abubakar wanda ya shigo gida bakin shi dauke da Sallama ya sauke idon a gare ni tun daga samana har kasa na, ya kalli dressing din dake a jikina,
A kusan tare mu ke mai sannu da zuwa ni da Ramatu wace ke kokarin zuwa gurin uwar dakin ta wace, ta shigo muna acikin fushi,
Yadan an,sa min a cikin sakin fuska kadan yana cewa yawa sannun ku da gida,
Fridge na nufa don in dauko mai ruwan sha kamar yadda na saba yi idan ua dawo in har nice da girki,
Ina tsaye a gurin Fridge din ne nake jiyo muryan Anty Sadiya kamar a fada ta na fada da Ramatu,
Wai, taki ciro mata key daga jakar ta da sauri tana bata mata lokacin ta a tsaye ,
Goran ruwa biyu na fito dashi daga kitchen din a saman dan ture nafara kai wa Yaya na nashi wanda yana a tsaye yana jirana,
Ina ganin ya balke marfin ya kafa kai kamar yadda ya saba yi don shi bai damu da tsiyaya ruwa a cup ba,
Na wuce zuwa gurin anty sadiya don in bata, ruwan amma tana ganin na nufo ta da ruwan sai cewa tayi,
Umm,ummm ummm ki barshi kawai Meena bazan sha ba,
Tsayawa nayi sororo ina kallon ta acikin mamaki irin yadda tai min magana yaban mamaki tankar wace aka kawo wa mugun abu,
Adaidai lokacin kofan dakin na ta ya bude tai kokarin shigewa ciki da sauri rai a bace,
Bansan cewa Yaya Abubakar ya iso gurin da na ke a tsaye ba ,a cikin mamaki,
Yadan rankwafo daidai wuya na yana cewa idan bazata sha ba ki mayar a fridge din kawai,
Na dan lumshe ido na tare dawuyana don jin sanyin maganar shi da naji a lokacin,
Yace, Meena jikin ki da zafi mana a lokacin da yakai hannuwan shi a wuya na,
Sai da na lumshe idona nace Yaya kain ke ciwo tun dazun wallahi banjin dadi,
Da sauri na ji ya juyo dani, yana cewa shine baki magana ba ,
Nace mai mai ai na sha magani don da na tafi gurin Anty Sallon ne sai take cewa wai yakamata fa in samu bed rest don jikina yana son hutu,
Zai yi magana Ramatu ta fito daga dakin tana kokarin juyawa don ganin mu tsaye a gurin da suka bar mu,
Yaya Abubakar yace No zo ki tafi abinki don dakin zan shiga nima,
Sai ya sakeni ya sa kai zuwa dakin anty Sadiya nikuma nadan gyara rigana na koma kitchen dona je ture,
A yadda na ga Ramatu a cikin kitchen din sai naji banji dadi ba ,
Don share hawaye takeyi a cikin dubara tana cewa Hajiya don Allah wai gishiri zan deboma ?nty,
Nace Ramatu don Allah kiyi hakkuri don al,amarin Anty sai hakkuri don haka take ita,
Ramatu tace gaskiya Hajiya ni bazan iya ba aiki kamata harda zagi aciki
Nace Subbahanallahi aiko abin baiyi kyau ba in harda zagi amma don Allah dai kiyi hakkuri pls,
Sai nake ganin kaman da bacin rai ta dawo gidan yau ?
Ramatu a cikin muryan kuka take cewa ai ba yau ba a kullun haka mu ke da ita,
Nace subbanallahi, gaskiya baiyi dadi ba amma zan mata magana,
Ramatu tace kibarta hajiya tunda har taji sauki ai sai in tafi gaba in nemi wani aikin kuma,
Nace a,a Ramatu bazaki ko ina ba nan dai zaki tsaya da mu kiyi hakkuri dan Allah,
Na bata gishirin nafito na hau sama na hadawa Yaya ruwan zafi,don yai wanka,
Har zuwa dakina Yaya Abubakar bai fitoba daga gurin Sadiya,
Alawala na yi tare da shirin jiran kiran salla don lokaci ya gabato,,
Daga gurin da nake a zaune ina tunanen abubuwan rayuwa inda zancen Ramatu ya fado min a rai don a gaskiya matar tana da kirki da tausayi sosai,
Idan ba ita bace ai,ban tsan mani cewa akwai wace zata zauna da Sadiya irin haka ba,
Amma ita kula da ita takeyi tsakani da Allah babu nuna kyama ko gajiya a ciki,
Duk da nasan cewa Sadiya bata da dadi don bazan ji ansan kwarai amma dai zan mata magana a kai,

****** ********** ******
Zaune yake a bakin gadon shi yana goge kan da wani dan karamin towel a hankali bayan ya fito daga wanka,
Waya na rike a hannun shi guda suna magana da kakan shi malam tsoho,
Wanda Yaya Abubakar din ya dakatar wa abinda yakeyi na, shirin shiga gida saboda da zaran su idar, da Sallah Isha i, bai tsaya jiran komai sai ya shige gida gurin iyali ya gama da majalissan sa sai kuma gobe,
Yadda mutumin Suleja yai masu baya dazun da yamma yake mayar wa kakan nashi,
Murmushin malam tsoho ne ya daki kunnuwan yaya Abubakar a cikin gwanin ta,
Wannan murmushin yasa Yaya Abubakar gane cewa da akwai kamshin gaskiya ga zan cen mutumin Suleja,
Innalillahi Wa,ina,alahim,raj,um, Yaya Abubakar ya fara nanatawa a zuciyar shi,
Wanka ya fito a lokacin amma sai wani irin zufa ya ji yana karyo mai a goshi, da duk wani kafa dake fitar da gashi a jikin dan Adam,
Murya malam tsoho ya dawp dashi a hankalin shi inda yaji malam din na cewa,
Idan har zata tsaya iya diyar ta to da sauki don in har sihirin ta ys ce zo zo ga jikokina ta kashin ta ya bushe wallahi,
A hankali Yaya Abubakar yadan daga towel din dake a hannun shi ya goge fuskan shi a hankali, tare da sauke wani itin gwauron ajiyan zuciya,
Murya irin ta wanda jikin shi ya mutu akan wani zancen mara dadi yace wa kakan nashi,
Malam kana ganin cewa wanan abin bai shafe ni ba kuwa ga irin yadda malamin ke bayani,
Malam tsoho ya bashi ansa da cewa aiko da da farko ya shafe ka yanzu insha Allah babu yadda zatayi da ku,
Saboda ai kaga kenan Kai da Meenatu kunfi karfin ta tunda har Meenatu ta gwada samun ciki ai,
Yace wa kakan na shi gaskiya ne malam amma in har wanan zance ya tabbata ba kazafi akai mata ba wanan matar zata gane kuren ta wallahi,,
Sun dauki dan lokaci suna ta hira mai tsawo a tsakani kamar ba,a waya suke zancen ba,
Da mamaki fal a zuciyan Yaya Abubakar wanda ke jin alamarin kamar ta almara,
Dunyi sallama da kakan shi acikin jin dadi tare da bashi yan shawarwari akan al,amura,
Bayan gama wayan su da malam sai kuma ya shiga wasiwasi a zuciyan shi,
Da sauri ya fara yin istigifari saboda tunanen da yayi a zuciyar shi,
Saboda duk zato da zargi sukeyiwa boyae Allah bawai zance ya tabbata bane, da gaskiya ko akwai wani evidence a kai, kawai dai zargi ne,
Kfan shiga dakin shi ya kalla tare da duban time a lokacin har tara da rabi na dare goma saura,
Yai mamakin rashin ganin Meenatu tazo dakin kuma ya tuna cewa bai ci abincin shi na dare ba,
Abinda ya sashi mikewa ke nan zuwa wardrobe din shi ya dauko wata jallabiya mai yar hannuwa kara mi, yasa ya nufi kasa,
Dining table din su ya fara kai idon shi a gurin yaga abincin shi na gurin aje,
Sai kuma ya dubi kofan shigowa falon gidan yaga ai ba,a rufe ba a bude yake har zuwa wanan lokacin,
Ga sanin shi kuwa tun zuwa na gidan ni kan rufe kofa karfe takwas na dare,
Kofa ya fara rufewa sai ya nufi sashe na kofan a rufe yake amma ban kulle ba da ya tura yaji ta abude,
Idon shi ne ya hangone kwance can saman gadona na dunkule guri guda kamar jaririya,
Ya tako, a hankali zuwa gurin da na ke kwance na fara barci, a lokacin,
Hannun da yake a wuyana yasa ni dan bude idona da sauri ina kallon shi,
Gyara kwanciya nayi ina facing din shi abin da har ya baiyanar da nightgown dina a fili ke nan nace acikin idon barci,
Yaya kaci abinci ko ? Tare da kara lumshe idona a hankali,
Tambayan da ya jefo min shi yadan sani kara bude idona,
May yasa kika kwanta anan kuma ?
Nasan cewa dama wanan tambayan yana tafe gare ni don haka na kara dunkule wa guri guda nace,
Wallahi Yaya ban jin dadin jikina ne ko kadan don wani irin jiwa nake ji da ciwon kai,
Kara kai hannuwan shi yayi saman, wuyana yana cewa ni fa Meenatu wanan ciwon naki ban fahince shi ba har yanzu,
Kusan wata da kwanaki ace har yanzu lafiya yaki a jikin mutum,
Cikin wani irin make, murya nace yaya aina fada maka abinda wanan doctor da na hadu da ita a shagon Antyn Saloon tace min dole sai na samu wadatacen hutu zuwa wani dan lokaci,
Ido ya tsura min yayin da nake kokarin gyara kwanciya na,
A wani asibiti take aiki ita, matar, da ta fada maki hakan,
Sunan asibitin da mu ka tafi da Fattu ne yazo min arai sai nai saurin cewa, maitama Clinic,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[9/5, 9:19 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 7?


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH- AL- WALI,,,,


Ni kai na wanan bed rest din da na samu ba karamin dadin jikina naji ba saboda a koda yaushe ina a daki na kwance ban, komai,
Ramatu ce na samu take tai maka min da komai, na fannin aiyukan gida, da na keyi,
Matsalata guda yanzu shine Yayana Abubakar wanda na ke ganin ya kusa gaza hakkurin shi gare ni,
Duk da ina ta kokarin ganin bai shiga bacin rai da ni ba, saboda hakan,
Sai ma period din karya da na shiga yi nakan ta cewa ai yazo yadawo,
Har nace zan tafi asibiti inga wanan matar inda Yaya ya nuna bai yarda ba sai dai mu tafi tare,
Banyi musu ba sai kuma ko may yagani sai cewa yayi mu fara zuwa da Fattu muji may za, ace muna don shi yana da meeting din safe,
Wanan daman na samu na tafi, awo saboda lokacin da doctor yace in zo awo yayi,
Likita ya tabbatar min da cewa normal abin cikin cikin nawa yake yabani magani da zan dinga sha, tare da kara jaddada min in dan kara samun bed rest din wasu yan kwana ki agai har zuwa lokacin da zan kai four months,
Takardan asibiti da maganin da akabani su na yi dubaran gwadawa Yayana Abubakar don ya gani,
Abinka da wanda bai saba ba bai san kai ba sai bai gane cewa ai magani karin kuzari ne na masu ciki akabani ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login