Showing 219001 words to 222000 words out of 388021 words

Chapter 74 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8263


Yace Meenat wallahi na gajine yau sosai, yau nayi over work ne
Da kyat na lalaba Yaya Abubakar ya mike zuwa yin wanka,
Kafin yafito na koma kasa na kara gyara kwalliyana,
A haka rayuwan gidan mu yai ta gudana kowa na boye halinsa saboda azauna lafiya,

Yau ma a Zaune muke gaba dayan mu muna hira a falo duk da ba wani hira bane kawai dai kowa na nashi tsabgan ne
Wayan Yaya Abubakar tai kara ya dauka
ganin wace ta kira layin shi,
Mama Ladi ce take, kiran shi a cikin girmamawa tankar tana a kusa da shi,
Bayan sun gaisa ne take ce mai ?nty, Nafisa tana asibiti ance CS za ai mata idan bata haihu ba nan da yan awowi,
Da karfi naji yana cewa subbahanallahi ita Nafisa, tun yaushe ne tafara rashin lafiyan,
Jin su nan wace ya ambata yasani saurin dago kai na ina fuskantar shi, kallo na son karin bayani nake mai,
Ansa da Mama ta bashi ne ban ji ba don wayan ba a hands free yake ba,
A take hankalina yai mugun tashi don nasan zancen haihuwan ta ne akeyi,
Wani asibiti ne kukai kai ta mama ta bada amsa da cewa Sir Yahaya ne aka kai ta,
Yace idan bazasu iya ba ne a dauke ta a mayar da ita FMC yanzun nan mana,,
Gaba daya duk hankalina na tattara gareshi don jin abin da suke fadi,
Ya kare da cewa barin turo maku Aliyu yanzun nan yaga halinda su ke ciki,
Yana kashe wayan mama ya fara kokarin duba nomban Aliyu nake ce mai Yaya anty Samira ce , ba lafiya ?
Ya ce cikin dan yanayin damuwa wai yau, kwana biyu tana wanan abin, na haihuwa har yanzu kuma bata haihu ba,
Innalillahi wa,ina alaihim,raji,um abinda na fadi ke nan a lokacin da nake mikewa,a rude nace,
Ya Allah ka tausaya muna ka sauke muna masu cikakkan mu lafiya, Salawatu ta ansa da fadar ameen,
Amma Anty Sadiya bata ce muna uffan ba sai dai gyaran yatsunta take yi kawai,
A cikin damuwa muke zaune gaba dayan mu, sai faman waya Yaya Abubakar keyi da jama,an gidan mu,
Jikina da kayan cikina sai ka rantse cewa ba a jikina yake ba,,
Don wani irin kaduwa da nake ji saboda jin cewa yar uwata tana acikkn wani hali,
Shi kanshi Yaya Abubakar din a rude yake don ya kasa zaune ya kasa tsaye,, saboda damuwa,
Ita ko Salawatu sai faman binsa da ido takeyi duk inda yabi a lokacin,
Shiga daki nayi na dauki wayana na kira mamana don inji yaya ake ciki,
Mamana ta dauka tana cewa tun da rana nake son kiranki yae Baba ,
Na gaishe ta sai nake tambayan ta ashe Anty Nafisa ta a gurfane ne tace ai shine nake son kiranki in fada maki,
Nan mama take sheda min halinda ake ciki akan wai aiki za,ai mata don dan yayi girma da yawa bazata iya haihuwa ba
Nace mama da sauki dai ko don naji Mama Ladi ta bugowa Yaya waya tana fada mai abinda ake cikki,
Mama na dai ta kwantar min da hankali yadda taga duk nadamu sai ma take tambayana ya jikin nawa nasamu lafiya yanzu ko ?
Mun dan dauki lokaci muna hira da ita cewan ina yan kanne na su ke da kuma tambayan lafiyan su,
Jiki ba kwari muka watse ranan don bace da girki ba don haka ban wani dauki lokaci mai tsawo ba a falon,
A haka gari ya waye muna mu na cikin sauraren zancen haihuwan Anty daga birnin Kebbi,
Sai da nagama shirina tsab na fito falo don na gaida Yaya saboda bazan iya jurewa ba har ya shigo dakina,
Idan ma ai har na bari ban kyautaba don ban nuna mai damuwar yar uwar shi ba ke nan duk da dai nima yar uwatace amma ai ya fi kusa da ita shi,,,,,
Yadda na samu Yayana zaune a falo da waya a hannusa yana saye da jallabiyar sa ta zaman gida mai launin ruwan madara,,
Kallon da nai mai kawai yabani tausayi, sosai don nasan damuwan dake damun shi,
Ina kwana na fara yi mashi tare da tambayan shi ya labarin mai jiki,
Cikin dauriya ya dan gyara zaman shi yace min,
Yanzun nan mukai waya da Aliyu yake ce min an shiga da ita tiyata, kuma wai ba lalaine a samu jaririn ba nace wayyo Allah na ,,,
Allah dai yasa a samu rayayye Allah kuma yafito da su lafiya,
Ina daga tsaye a bayan kujera Salawatu ta iso gurin tana cewa Yaya Abubakar ka dawo,
Ya amsa mata a hankali da cewa eh nadawo tace to ya maijikin da sauki ko,?
Nan takai zaune tana cewa gaskiya dama asibitin garin nan aka kawo ta ma da zai fi ai ,
Nace, aiko can akwai asibiti kawai dai akasi aka samu saboda rashin kaita asibiti da wuri,
Sai lokacin Yaya na yadago ido ya dube ni yake cewa agida ke nan suka barta ko ?
Na ce ance wai a gida aka barta don akwai wata malaman asibiti a kusa da su,
Ita ce ke cewa wai da sauran time juyi ne kawai har ta kai ga galabaita,
Yaya Abubakar yai tsuki yana cewa yanzu ashe ma duk sune suka ja mata wanan problem din ashe ?
Daga gurin da nake tsaye amma duke saman makarin kujera nace haka dai Allah ya kawo al,amarin kawai,
Muna gurin Ramatu tazo tana wa Yaya Abubakar jaje da fatan Allah ya raba lafiya,
Munan dai kowa na fadin albarkacin bakin sa batare da ya tanka muna ba, shi sai can mu kaji yaja wani dan guntun tsuki,,, da karfi ya ce,
Wai Sadiya may takeyine a cikin dakin nan please,?
Gaba dayan mu mukayi tsit babu wanda ya tanka masa,
Hanyan part din ta yakai idon shi tare da yin wani iri numfashi yana cewa Allah ya shirya halin wanan matar, kawai,
Gurin da Ramatu take a tsaye ya ke kallo yace kira min Sadiya please ?
Baba Ramatu kan tunda tadawo take ce mai tana zuwa, wai, ta juya abinta zuwa kitchen don bata tsaya ba,
Can sai gata tafito da alaman barci takeyi aka tashe ta,
Juyaqa yayi yakalli yanayin ta yace may kike aciki ne ke kowa na nan,
Sai kuma ya kafeta da ido bai ce komai ba,
Zaune takai tana cewa may yafaru ne wai nagan ku nan tunda safen nan haka,?
Nace a,a muna dai zancen Anty Samira ce da ke fama da jiki can gida,,,
Tambaya tayi cikin muryan ta tsatsaye tana cewa, tahaihune to ?
Kagin wani ya bata ansa wayan Yaya yai kara ya dauka yana cewa Salamu Alaikum,
Aliyu ya dai an yi aikin ne ?
Shiru yayi yana sauraren abinda Aliyu ke fada mai ida muma duk mu kayi tsit, gaba dayan mu muna sauraren shi,
Sai da yace to ita Samira din fa anfito da ita ne ko kuwa,
Bai kuma yi magana ba sai ci gaba da sauraren bayanin Aliyu da yakeyi kawai,
Yakare da cewa duk dai abinda ya kamata anyi kayi don Allah zan shigo next tomorrow insha Allah,
Ya kashe wayan ya maida kanshi bayan makarin kujera yana mai da numfashi a hankali guda guda,
Gaba dayan mu an rasa wace zata fara tambayan shi ko may ke faruwa,
Sai Anty Sadiya ce tai karfin halin cewa may ake cikine yanzu wai,
Yace a cikin tubure fuska an mata aiki anfitar da diya mace,
Carfa na ce tana da rai baby din kuwa ?
Kai yagyada min da alama yana tare da bacin rai sai dai babu halin mu tambaya,,
Nikan jin cewa Baby din is alive yasani yin murna da farin cikin jin tana lafiya an samu rayayya,,
Daki na koma ina mai farin cikin jin cewa Anty tasamu rayayyan baby bisa ga yadda ake ganin cewa da farko zata rasa baby din

Wanka nashiga idan bayan fitowana dafa dan kwantawa barci ya kwashe mai nauyi sosai,
Yaya Abubakar yashigo daki ya samay ni ina barci na hankalina a kwance,
Hakan yasa shigane cewa daren jiya banyi barci ba ke nan, saboda tunanen halinda yar uwana ke ciki,
Sai zuwa karfe daya na farka ko shi yunwane ya ta da ni daga barcin da na keyi,,
Ina bude idona kai a agogon dakin inda yanuna min time nadan yi guntun tsuki alokacin da nake kokarin mikewa zaune,
Baba Ramatu ta shigo dakin dauke da kulan abinci abinda yasani dan murmusawa ke nan,
Tace uwar dakina kin tashi ke nan ko namurmusa na kai zaune da kyau nace na tashi Baba,
Ashe nayi barcine sosai haka dai kuma baima isheni ba fa yunwane ya tadani,
Tace Alhaji ya shigo har sau biyu kina barci zan tadake yace wai na barki kiyi barcin ki,,
Murmushi nayi daidai lokacin da nake kokarin mikewa tsaye nace, yana gida ko ya fita,?
Tace bai wani dade da fita ba ai kika farka don ina ganin tare da Baba Wadda da baba Hamz suka fita ,
Alwala na dauro na fara gabatar da sallah kafin na zauna cin abinci,
Nakai wani lokaci ina cin abinci na hankalina akwance sai dai ina ta tuna halinda A?ty Samira take cikki yanzu,
Waya na dauka na fara fadawa Fattu zancen haihuwan Anty Samira inda ta jajan ta muna akan zacen Cs din,
Ina gamawa na fito zuwa waje, don indan taka Anty Saloon ce tazo tare da wata dadtijuwa gajera mai jiki ,
Natare su haba haba a main falo muka yadda zango dasu naje na dauko masu ruwan sha tare da drink's nakawo masu, alokacin da nake aje wa agaban yar dattijiwan Anty Saloon ke cemin mamace fa tazo
Da sauri nadaga kaina ina kallon mahaifiyar nata inda nakara gaishe da Mama cikin Ladabi ta dan yi kokarin rusun na min itama,
Nace a,a a Mama anice dai zan durkusa maki bake ba,
Hira sosai mu keyi dasu takawo tsaraban da akazo muna dashi irin kayan amfani na gargajiya wanda babu shi a nan sosai,
Naji dadi wanan karamcin wanda hakan yakara sani tabbatar da zance Anty Saloon a kaina da take yawan cewa tana dauka na takar kaunata ce ta jini,
Anan take ce min ai maigidan tane ya kawo su don tun da safe su ke son zuwa amma sai yafita,
Nake tambayan ta shago tace tunda mama tazo bata faye shiga ba yara ke zama yanzu ai,
Salawatu ta fito ta gan su amma sai tai tankar bata gansu ba, zata wuce amma sai Maman tace mata,
Ina wuni ?
Sai lokacin ta juyo ta kalli Anty Saloon wace bata ko kallon gefen ta ma,
A wani iri tace wa yar tsohuwar yawa sannu ko ?
Sai banji dadi hakana din ba sai nake ganin ai babba babba ne ko ,
Amma ba laifi ai cin tuwon kishiya ranko ne don zamu hadu ai,
Don ai naji yadda su kayi da Anty Sadiya akan friends din ta da sukazo suna shaye shaye a gidan,
Da zasu tafi naba Mama turmin zani lafiyayye da turare mai kamshi, tai muna taji dadi tana samin albarka da hausa da kuma yaren nufawa,,
A kofa na raka su sai ga Yaya Abubakar ya dawo yar dadtijuwar matar tai mai gaisuwan mutunci sosai,
Daga inda nake a tsaye ta cikin get nake cewa mahaifiyar Antyn Saloon ce tazo daga Bidda,
Yace ok ya juya yana mai sa hannuwan shi a cikin aljihun shi yaciro kudi yazo gab da ni ya miko min yana cewa ga shi ki bata kice mun gode, da zuwan ta,,,
Na bata tabi bayan shi,har kasa takai tana mai godiya, ya juyo yace no ba komai mun gode,,
Sai da naga wucewan su na shigo ciki a daidai da lokacin da su Baba Wadda suke ta kokarin shivowa da ledojin da suka dawo dashi,
A falo su kai ta aje kayan shima azaune maigidan yake a falo Salawatu ta kawo mai goran ruwan sha, agaban shi,
Sannu na karayi mai ina kokarin wuce, sai naji muryan shi yana cewa, ki kiramin Sadiya kuzo please ya fada a dan gajiye,,
Gaba dayan mu ,muna zaune a falon muyi tsit kamar ruwa ya ci mu,,
Ledojin ya cewa Salawatu ta jera su a kamar yadda yake mata kwatance,
Sai yake cewa Sadiya ki dauka kamar bazata dauka ba tamike tana wani yatsune yatsune fuska ta ja kashi guda,
Ya juyo gurinda nake a zaune yace ke kuma dauki guda itama ta dauki guda,
Kowan mu ledan gaban ta taja yana mai kura muna ido har kowan mu ta koma mazaunin ta,
Dayan ledan wanda shikadai ne daga ciki kuma bai kai sauran cika ba ya dan dubi gurin da nake yace,
Dauki wance kibawa Ramatu ko,
Na dan mika na jawo shi ina cewa mun gode Allah ya kara rufa asiri
Yace zuwa banda gobe zamu tafi Birnin Kebbi, da ke Sadiya da Meenatu, don mu dubo Samira da jiki da sauran mutanen gida Saboda kunga azumi ya gabato yanzu,,
Ya juya gurin Salawatu yace zamu barki da Ramatu dan ku zauna tare har mu dawo,
Tace a sanyaye cikin nuna rashin jindadin ta amma ai da nima an tafi dani ko,
Fuska adaure yace ke yaushe kika dawo daga can da zaki ce a tafi dake kuma,
Ya cigaba dacewa duk da na duba store naga akwai koma na karo abubuwa da dama daga ciki,,,
Sai yai shiru ya koma ya kara kwantawa saman kujera yana mai lumshe idon shi a hankali yana hamma kamar mai jin barci
Muna zaune gaba dayan mu munyi shirun mu kayi don bamu da say daga gare mu
Yace yanzu abinda za,ayi duk wace ke da abin yi zuwa gobe sai ta je tayi, don tunda asuba zamu bar garin nan insha Allah,,,
Ina kokarin mikewa tsaye ne na ji muryan Anty Sadiya ta na fadin cewa, Meenatu idan zaki shiga gurin wanke kaine sai mu tafi tare,
Fuska a sake har a zuciya na ba matsala nace to Allah ya kai mu anty sai mu tafi da guri don kada layi yai yawa,
Na kwashi kayan mu nida Ramatu nabar gurin saboda nagane cewa Salawatu bata acikin good moode, zaune kawai take tana yake,
Baba Ramatu ta kasa rufe baki sai ikon Allah take fada,
Tace kai jama,a gaskiya wanan irin alherin ban san may zan fada ba,
Nace aiko sai kiyi maza kije godiya kafin ya shige don nasan da wuya ki gan shi sai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kila da safe,
Da sauri ta nufi falo don tai mai godiya daga shi sai Salawa sai dai da alaman ba a cikin dadin rai suke ba,
Ta na zuwa gab dasu taji yana cewa na fada maki cewa bazaki ba period bazan canza magana na ba don ki ji,,,
Ramatu ta karaso zuwa gurin su ta tsuguna har kasa tana cewa Alhaji nagode Allah ya kara rufa asiri,
Hannu ya daga mata yana cewa no ba wani abu ki tafi kawai ,,,
Salawa tabi bayan Ramatu da wani irin uwar harara har ta bace ma ganin su,,

****** ********** ******
Kitso kawai anty Sadiya tayi wai bazata iya zaman gyaran kafa ba dan haka akai mata kitso wanda ya fitar mata da da kkyau fuskan ta a fili,,
Nikan anyi min kitso an,wanke min kafa da yatsun hannu na an rangada min kumshi a kafa, da hannaye na, tsab kafin a gama min Anty Sadiya duk ta matsu ta koma gida dole na kira Baba Hamza yazo ya tafi da ita,

Sosai,nake shirin kayana tsab a dan karamin trolley daga gurin da nake zaune ni da Ramatu ne a dakin nawa,
Ita ce ke ta faman shirya min kayan da na harhada zan tafi da su tsaraba,
Ina kallon lokacin da mike ta nufi drower dina na mirror ta debo magani na ta cusa min a jakata ,
Dariya ta bani don ta san cewa idan don tani ce bazan sha ba kuma zan tafi za su ba,
Tace aida ina da nomban mama da sai nace ta sakaki a gaba kina sha,
Nace yanzu ai tunda kin sa aidole na sha Baba amma ni sai nake ganin cewa naji sauki ko,
Tsab komai da nake bukatar tafiya dashi ya hadu inda Ramatu ke ce min gaskiya Uwar dakina da Alhaji zai yarda in koma gida har zuwa lokacin da kuka dawo,,
Nace a cikin murmushi au, bazaki zauna da Salawatu ba ke nan kike nufi,
Sai da tayi kamar ta leka kofa don kada wani yaji may zatace sai ta juyo tana ce, min,
Ina tsoron abokan ta mashaya kada su shigo suyi min dukan tsiya a gidan nan babu kowa boni ya ci ni,
Dariya sosai ta sakani harda kwalla tace ai tun ranan da tace wa Uwargida kada takara saka mata ido ga al,amarin ta kuma ta bugawa Alhaji waya a take, take sheda mai cewa aiwa Uwargida kashedi a kan ta,
Yaya Abubakar wanda ke tsaye daga kofan dakin yai gyaran muryan alaman yana gurin a tsaye,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login