Showing 243001 words to 246000 words out of 388021 words

Chapter 82 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8309

sa,
Ya girgiza kai tare da lumshe idanun shi yace ita Ladi da kuke gani bata da tunane ne ko kadan ,
Idan ba haka da bazatayi irin wanan haukan da takeyi wa mutane ba agida,
Abin alfahari ne agareta ace ta samu suruka irin Meenatu daga tsatson ta gashi har Allah ya kawo rabo a cikin al,amarin,
Ina yaushe, yaushe ne aka kashe wutan an mata gorin cewa takwara na wai bai haihuwa,
Allah da ba azzalumin kowa bane ba gashi yanzu yabada rabo ba ta gurin da ma ba,a zata ba,
Don haka daga yau irin wanan rigingimun ban son in kara jin shi a gidan nan
Ai wanan abin kunyane kuke jawo min ace a gidana ake fadan hada zuria, aure,
Yace akwai abinda yafi haka alfahari ace daga garesu ma,auratan babu wani matsalan komai a wajen su sun dace kuma da auren junan su
wai sai a wurin ku, ku,
Ita fa Ladi bawai Meenatu ba ko ma diyar waye daga cikin ku haka zatayi da mai shi,
Don kunga ita fa ko diyan ta bata bari ba balle na wasu don haka sai kuyi hakkuri don kowa ma da halinsa ake zama dashi,
Malam, Ya dan kada kai tare da lumshe idon shi yace Allah ya kyauta Allah ya tsare gaba wanan ya zama farko ya zama karshe ita ma Ladin zan zauna da ita ai mu tattauna akai,
Gaba daya gurin shiru su kayi suna mai nazarin maganan dan tsohon cikin rayukan su,
Baba Musa ne daga cikin su ya fara magana da cewa,
A gaskiya malam zancen ka ni kan ba yau ba na riga da na san da kasan cewan yaran nan a tare wani babban alheri gare mu,
Don idan anyi la,akari da irin yadda a yanzu muke samun kulawa daga maisunaka wanda mu yanzu bamu da abin cewa sai dai mu, yi maka fatan alheri a rayuwanka irin yadda kake muna Allah ya baka zuria masu albarka suyi maku fiye da wanda kai muna,
Gaba daya gurin suka karba da Ameen ya Allah kowa ya shiga fadar albarkacin bakin sa, kuma,
Yaya na yana daga gefe yana sauraren su, yana mai lumshe ido daga zancen su
Yasan cewa yayi babban kuskure abaya so sai duk da dai a lokacin ba wai yana da wadata, (hali ) irin yanzu bane,,,
Shirun da wurin yayine yasa shi dan dagowa ya dube gurin da malam din yake zaune ya ce,
Ina son,wanan shekaran ta bana Baba da Mama su sauke farali a tare dani,
Da naso in tafi da matana dukka amma sai gashi ita Meenatu tana da lalura don haka tagiyanta atare da mu bazai yi ba shiyasa na yanke shawa cewa a tsakanin shi Baba Samaila da Mama Saratu sai guda ya tafi, a madadin ta,,
Ai,ko take guri ya dauki kabbara da murnan jindadi,
Duk yan uwan Baba suka ce sai dai shi ya tafi don bai yiyu mama ta tafi shi baije ba,
Yaya Abubakar ya dago kai ya dubi malam tsoho wanda,duk murna da farincikki ya kashe shi, ya ce,,,
Sai kuma kai malam don naga cewa barinka gurin nan ba karamin matsala bane don haka ta International zaku tafi kai da Baba Wadda,,
Yace ina son kafin mu tafi sai a dauke ku photo saidai kuma bansan ko zaku so zuwa ta Abuja ko tanan Kebbi,,,
Baba musa yai saurin cewa ta nan Kebbi dai zai fi nake gani,
Yace ba matsala zanga Aliyu sai a san yadda za, ayi aksi yace zai fita saboda zancen tafiyan su,
Baba musa yace maisunan malam ina malam ya kashe wan nan zancen tafiyan ko,
Tsayawa zakayi atare damu har zuwa lokacin da ka debona komawan ka daga hutunka,
Murmushi yayi tare da cewa tau Baba ba matsala nagode da fatan zaku taya ni ba Baba Samaila hakkuri ya barni da matata please ,,,
Dariya aka kwashe dashi tare da dan kara tatauna wasu al,amurorin akan harkan gidan,,
Kafin wani lokaci zancen tafiyan su Mama Ladi makka ya kewaye ko ina cewa an biya masu makka hadda Baba na Samaila, za,a tafi,,
Wanan zancen duk sai ya gushe da batun maganganun da ajetayi na fitina agidan mu,
Sabon zance kuma ya shigowa mutanen gida da na waje,


****** ********** ******
Wanan zuwan da mukayi ya kara sawa sunan Yaya ya dan yi fice kamar yadda da zaran mutum yana gurin samu atake da tayi wani abin bajinta zakaji gari ya dauki ciri,
To shima wanan karon hakane abin ya kasance , agare shi on mutane sai zance su ke yi a, gari cewa ai dan gidan malam tsoho yana nan ya,samu babban guri a Abuja,,
Abubuwan business sosai su,ke kafawa a gari shi da Aliyu wanan zuwan,
Yau daga wani unguwa sukd sai Aliyu ke cewa yana son zuwa ya duba mahaifiyar su a gidan su don haka Yaya Samaila yace su tagi tare don ya gaisa da ita shima,
Kai tsaye suka shiga gidan yana nan kamar yadda ya san shi da farko a baya, ,
Hajiya tayi murna kwarai da ganin Abubakar a gidan su don tadade bata ganshi a idon taba., sai dai yakan aiko mata da sako wasu lokuta can ba,a rasa ba,
Yar dattijuwan mai zubin kamala zaune a saman daya daga cikin kujerun da ke dakin nata,
Take cewa Abubakar ka yanke zumunci ko ko sau daya baka taba kawo min iyalinka nagansu ba,
Aliyu daga gefe yace gashi wanan zuwa dukkan su yan Birnin Kebbi sukazo yar Abuja ce kai suka bari tsaron gida,
Murmushi Yaya Abubakar yayi kasa kasa yace anyi kuskure mama za a gyara insha Allah,
Sai kuma tace yaran shi nawa yanzu sai kuma ta runa tace aff iji ance har yanzu babu rabo a gidan ka,
Gashi ko kaga ikon Allah ita Fatima yaran ta uku fa inda badon ma maigidan nata yarasu ba aida kila yanzu takai hudu ko,
Aliyu daga gefe ke cewa ai ya,zo hargidan lokacin rasuwan yai mata gaisuwa, ta ce Allah sarki aiko kaga banji ba fa,
Aliyu yace a,a mama kindai manta don tun bai tafi ba ma na fada maki, cewa gashi yazo da matar shi gaisuwa,
Tace Allah sarki gaskiya na manta da hakan wallahi,
Wai ma ina Fatiman take tazo su gaisa mana ina tashiga ne wai,
Sai ta fara kiran sunan Fatima, Fatima can kuma tace ke yar ma,aiki ina kikashige,
Fatima wace ke daga dayan dakin dake hade da falon ta amsa tafito
Tana saye da wani dinkin buje da riga na atamfa, sun dan matse mata jiki, sun sa bazaka iya gane cewa tayi haihuwa har uku ba,
A hankali ta karaso cikin falon bakin ta dauke da sallama,
Tana wani rausaya don ita mace ce mai son jan aji da yanga,
Suna hada ido dashi sai yaji wani irin yarr a zuciyar shi,
A bayan kushin din da mahaifiyarta take akai ta dan zauna a hannun kujeran tana cewa sannu da zuwa ,
Yace Fatima kina lafiya yaya yaran da karin hakkuri ta dan lumshe ido tace Alhamdullahi na godewa Allah,
Sai akai dan shiru falon kowa na nazarin abubuwa a cikin zuciyar shi,
Aliyu ne ke tambayan ta ina yaran ta su ke tace a yangace wai yanzun nan suka tafi gidan sister din ta maimuna,
Yace ok ok Yayana yana daga gefe duk yana sauraren su wayar shi da tai kara yadauka yadan fara magana da mai kiran wani abokin aikin shine ya kirashi sun dan kai yan mintina suna waya da mutumin ya kashe baka jin komai sai kiran miliyoyi da sukeyi ga turancin shi gwanin sha,awa sai kace ai a turai aka haife shi ma,
Yana kashe wanan kiran kuma sai ga wani kiran yashigo mai kiran Salawatu ce tana mai tambayan shi acikin shagwaba yaushe ne za su dawo ,
Ya mike a hankali daga gurin da yake zaune zuwa waje,
Fatima wace tabishi da ido daga gurin da take zaune ta dan lumshe idon ta tare da shakan kamshin turaren shi,
Wanda tun shigowan shi falon nasu ya gaurareye da kamshin sa ta ko ina,
Itama mahaifiyan su Aliyu daga gurin da take a zaune zuciyar ta ya kiyasta mata wani abin daban
Shikan Aliyu bin bayan abokin nashi kuma boss dinshi a yanzu yayi zuwa waje,
Yana fita mahaifiyan su Aliyu tace ikon Allah yaron nan ya samu lafiya sosai ke nan, Allah mai iko, ke nan dubi yadda su ka tashi da Aliyu,,
Muryan Fatima ce daga bayan ta take cewa mama ance matan shi biyu ko,
Mahaifiyan nasuu tace anya kuwa basu fi biyu ba bakiji abinda yayanki ya fada ba yanzu,
Tace wai har mata uku amna kuwa ni da can ce min ya keyi shi mace guda ta ishe shi a rayuwan shi,,,
Tace abinda Allah ya rubuto mai ai sai yayi su don abin daga Allah ne fa,
Tana son mi kewa zuwa cikin sai gasu sun dawo ciki shida Aliyu ya koma saman carpet inda ya zauna da farko,
Yasa hannu a aljihun shi yaciro kudi ya aje su agaban mama ya mike tsaye, tare da mikawa Fatima wasu kudin yana cewa, ta sai wa yara alawa su sha yana gaishe su,
Maman su Aliyu sai gidiya takeyi da fatan alheri akai,
(Jama,a mudinga aikata alheri muna samun addu,an yan uwa musulmai a rayuwar mu don Allah kadai yasan wanda zai ma addu,aya kama ka a rayuwa)
Ya dade da fita daga gidan amma kamar yana a zaune a gurin saboda fitinanen kamshin sa da ke ta shia falon gaba daya ma gidan kamshi ya keyi,,
Suna fitane Aliyu shike tuki wanan karon da kanshi don Bado driver ya koma ko,,
Sai za,a koma maigidan zai kirashi yazo su tafi tare dashi,
Ban fito ba sai zuwa yamma nafito zuwa part din Mama babu kowa daga ?ikin yaranta yan jikokin ta kuma suna kofan gida gurin karatu ,
Da sallama na shiga part din nata tana zaune tana yanka ganyen miya da alaman itace da girki,
Na gaida ita acikin girmamawa ba yabo ba fallasa ta amsa min da alaman cewa malam yai mata nasiha, akai,
Nace ta kawo yankan ganyen in kama mata amma sai ta kiya na dauki tsintsiya na share mata ko ina a part din tare da kwashewa nasa yara suka zubar,
Nadauko muciya na zauna saman dan kujeran ta na mata yar (tsugono) na tuka tuwon ya tuku sosai, gwanin ban sha,awa kafin tafito har na hada, mata miya, sai dai tana fitowa naga ranta baiso hakan ba amma sai na dake kawai,,
Tambaya dai nasha shi gurin mama cewa kesa abu kaza kesa abu kaza, nabata amsa da cewa nasa komai duk abinda ta ke tambaya din daga dangin maggi daddawa kayan yaji,,
Nikan ina gamawa nabar part din nata batare da na tsaya komai ba zuwa namu part din,
Nan ma ban zauna ba aiki mukayi tare da mama na, kafin dare mun gama komai nai wanka ina zaune a gurin da nayi sallah kira yashigo a wayana
Yaya Abubakar a layin yake cemin in zauna da,shiri zamu tafi asibiti guri Anty Samira tare ,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
[9/21, 8:07 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH -AL-WA,AJID,,,

FATAN ALHERI GAREKU YAR UWA RABIN JIKI ABIN ALFAHARI NA A,KO,DA YAUSHE
ANTYNA NAFISAT HARZAMI TARE DA DUK SAURAN MEMBERS NA FAMILY DIN HARZAMI GABA DAYAN SU MAZA DA MATA,,,

Lokacin da naji abinda Yaya Abubakar ya fada sai nagane nufin,
Shiru nayi ina tunanen yau may ya faru da bai tafi da Anty Sadiya ba, ne,
Don tare su na zuwa tare don ni banda lafiya tun zuwan mu,
Amma kuma don may kuma yau zai tsiro cewa wai tare zamu tafi da shi,
Abinda ban sani ba shine har Anty Sadiya ne zamuyi tafiyan tare don zamu wasu gurare gaida mutane,
Sai da na fito ne gane cewa tafiyan harda ita,ne za, ayi shi a lokacin,,
Saboda na samay su a mota gaba dayan su, su uku azaune, suna jirana,
Yaya Abubakar da Aliyu zaune a gaba sai Anty Sadiya zaune a baya ita kadai,
Na bude bayan motan na zauna tare da yi masu sallama,
Na gaishe su a cikin ladabi cikin girmamawa da ladabi,
Kowa ya amsa min ba laifi don haka Aliyu ya ja motan shi muka fara tafiya, saida tun a lokocin da na shiga motan na gan su zaune a cikin motan
Rayuwana ya bani cewa da akwai gurin da zamu tafi kila,,
Ni dai azaune nake batare da na cewa kowa komai ba, sai kallon motocin da ke ta moving a saman titin ,
Muryan Aliyu ne naji yana cewa, ya dai tsohuwa asai maki gyada dafafa ne ko masara mai zafi,?
Murmushi naji Yaya Abubakar yayi daga gaban motan da yake a zaune ya dan gyara zaman shi ka dan yace,
Ai kawai kasaya mata don ba ita ba har muma din nan ci zamuyi ai,
A gaban wasu mata masu gasa masara a saman hanya ya tsayar da motar shi yana cewa, yanzu dai bari mu saya mugani,
Zace suke tayi sai dai ni hankalina baya a tare da ni lokacin ina can ina tunanen duniya,,
Sai ledan abu mai zafi naji Yaya Abubakar yana miko min yana cewa karbi nan.
Kamshi gasassan masara ne ya daki hanci na tare gyada, dafafa ,
Ban san lokacin da na lumshe idona ba a hankali don dadin da naji,
A zatona mu biyu ne dashi shi sai naga Anty Sadiya da nata a gaban ta, ita ma,
Gidan wani mutum wanda na sani da dadewa tun ina yarinya muke zuwa da kafa daga gidan mu a lokacin bukin sallah ,,ana cewa wai wan Mama Ladi ne can mu ka fara zuwa,,
Mun samu dadtijon a kofan gidan sa zaune saman kujerar katako yana kallon titi,
Bai gane cewa mune ba sai da yaga Abubakar ya fito daga cikin motan ya nufo shi a cikin girmamawa ya gaishe shi, a ladabce sunan da diyan Mama Ladi ke kiran shi, dashi kawu,Manu,,
Sai lokacin dattijon ke fadin a,a Sadauki ne, yau a gidan nan
Sunan da na tuna cewa mafi yawan yan uwan Mama a da haka suke kiran Yaya Abubakar da shi,
Mun, gaishe, shi a cikin mutunci da girmamawa inda yake muna iso cewa mu shiga cikin gida gurin iyalin shi,
Gidan gina ne irin na mutanen garin birnin kebbi na da can,
Ginan dakin laka wanda za a yabe ko ina har saman ginan da laka, yai kyau baka jin sanyi a cikin sa kusan muma agidan mu tsofin gina a haka suke sai dai ire,iren part din mu ne da ba,a dade da yin su sosai ba ake da dan bugun kwano,
Matan duk da ba su san mu ba sun tare mu a cikin mutunci inda na gane su ,
Sune dai tun nada can baya da muke zuwa tun muna yara kanana, ita ta karshe da idan mun tafi muke yawan zama a dakin ta muna kwalliya don tana yawan shafa janbaki da powder, don shi kawai ranan da babu islamiya sai mu ce Anty Samira tace zamu tafi gaida kawu manu,
Shikuma sai ya bamu naira,naira idan zamu dawo gida munyi kwalliya,
Kallo guda nai mata sai naga matar ta girma sosai don kanta har ya fara furfura,
Sun shimfida mina tabar man kaba sabuwa yasha turi mai kyau a jikin shi ,
Sai ruwan randar kasa mai sanyi da aka tsiyayo muna a cikin wani kwanon silver mai marfi,
Anty Sadiya aka,fara bawa sai tace a,a a barshi ta gode na mika hannuwa na nakarba don wani irin kwadayin shi naji a lokacin,
Don haka na kafa kai na na kwankwadi ruwan sosai na rufe kwano nace na gode,
Daga gurin da Uwargidan take zaune take cewa gashi ko basu gane mu ba ,
Murmushi nayi nace masu matan Sadauki ne saudaukin Ladin shiyan sarakuna,,,
A tare suke cewa a,a a shin kuna ?
Sannun ku da zuwa an taho lafiya yaya yara ya jama nice dai mai ansawa don Anty Sadiya sai wani ya mutse fuska take yi,
Shatu, ce tace shin ko keta wadda anka ba shi gidan su,
Nai murmushi na ce ni ta ke dai, mun samay ku lafiya, ko ta amsa da fadin walle lafiya lau
A,a kaji arziki ba aiko mungode da zumunci wallahi ina sadauki din,
Ya na a kofan gidan tare da kawu ,
Nace ina su yar Asama, sai da suka danyi dariya su kace ashe baki manta da su ba ke nan ko,?
A lokacin ne su Yaya Abubakar su ka shigo gidan tare da mai gidan a lokaci guda,
Shima wani tarbama aka dauko mai kyau aka shimfida mai ya zauna
Muna daga gefe suna hira da kawu Manu, na abubuwan dake faruwa acikin,dangi da kuma wurin Mama,,
Da zamu tafine ya ba kawu kudi tare da mai alkawarin cewa zai dawo insha Allah kamar yadda kawu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login