Showing 189001 words to 192000 words out of 388021 words

Chapter 64 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8291

ko. ?
Cikin mamaki take kallon shi tace Oh, haka kace ko ,?
To, Babu inda zan tafi tunda ai bani kadace da wahalan cikin ba harda kai ma,
Ya ce a yar hasale to ban siyo ba saiki kyaleni hakana please,

Fanin fruit din sunada yawa sai na raba biyu na nufi dakin Anty Sadiya dashi don in basu su sha, in suna da bukata,
Na samu Ramatu a zaune tana jan tasbaha anty tana daga kwance tana kallon TV,
Nai masu Sallama ina mai mika ma Ramatu ledan Fruit din ,
Nace ga Fresh Fruit da aka siyo yanzu nace barin debo maku ko ?
Daga gurin da Anty Sadiya take tace da watermelons a ciki ?
Nace eh da akwai shi ta mike zaune Ramatu tajawo plate tafara zubawa a ciki,
Nai masu sai da safe nadawo dakina, nai addua na rufe kofana,
Ban wani dade a farke, bayan na gama yin addu,oi na da na saba yi kafin in kwanta barci,
Duk da ina yi amma kuma tun ranan da matsala ya faru da anty Anty Sadiya ban yarda in yi barci banyi addu,oi na ba

****** ********** ******
Washe gari ban fito ba sai da nai wanka na gyara jikina tsaba acikin wani purple material, mai adon flowers ash,
A Niger na sayo su da muka tafi shida kan shi Yaya Abubakar ya zaban min shi,
Nasa su ne don nasan yana sha,awansu tunda har ya zaban min su,
Ashe kenan zai ji dadin ganin nasaka su ajiki na da ina boyon su ne saboda banda kaya da yawa amma yanzu da naji cewa zai sayo min sutiru sai kawai nace barin saka abina ajiki inja aji,
Suna zaune a dining don cin breakfast, din su wanda yanzu da karfi da yaji Salawatu ta hana aci a tare,
Daidai lokacin da nake kokarin fitowa cikin tako irin nawa ,
Salawa ta zubu min ido, tana mai min wani irin kallon kamar manya,
Nasan ba komai take kare min kallo akai ba sai wanan tufafin da na saka ajikina, masu daukan ido,
Kamar yadda na hango ta ta ashe ni da ido nima din haka nai mata don wani irin kallo na watsa mata tare da harara,
Daga gurin da Yaya Abubakar yake zaune ya tsuro min ido tare da sake min wani mayaudarin murmushi,
Ya tataro dukkan hankalin sa gareni, yana ma sakemurmushin gani na,
Nima dai muna hada ido murmushin nasakar mashi, mai narka zuciya don nima kaina ban san da cewa na iya irn sa ba,
Tuni Salawatu ta tsura mashi ido acikin mamaki tana mamakin yadda yanzu bai ko iya boye feeling din shi kan wanan yarinyar,
Wani harara ta wurga mashi tare da jan tsuki, batare da tace uffan ba taci gaba da kokarinkai cibi a bakin ta,
Na karaso har gaban table din yayin da kamshin jikina dana tufafina ya daki hancin salawatu,
Wani mugun haushi da takaicin wanan yariyanr ya ziyarci zuviyar ta
Yaya ina kwana nace mashi yayin da nakai gwiwowi na kasa gab da kujeran da yake a zaune,
Sai da ya dan hade abincin da ya deba ya kai a bakin shi,
Yace lafiya kalau Meenat yaya dare ya karfin jikin ?
Da sauri ta dago kai tana kallon inda nake a tsugune cikin harara,
Sai kuma taci gaba da cin abincin ta tana wani murde fuska
Yace kizo ki zauna muci abinci ko ko kuwa kin karyane ko ?
Nadan dubi abinci nagan shi wani fari fate da shi da gani baiji wani ingredients ba,
Sai naji kamar amai zai kamani a lokacin da sauri na kauda kaina daga kallon abincin ina cewa ba yanzu zan karya ba yaya,
Ya ce O right amma dakin karya ki karasa shan maganin ki please ?
Nace insha Allah a lokacin da nake mikewa tsayd da ga tsugunen da nake,
Na wurga mata harara kamar yadda take wurgo min daga inda take zaune,
Kitchen na shiga don hada abinda zanci don gaskiya bazan iya cin wanan abinda nagani ba wai jeloup din taliya,
Ina kokarin Fere Irish yaya yaleko daga kofan kitchen din yana mi sai yadawo inajin wucewar shi dakin Sadiya,,
Naci gaba da aiyukana kawai ban tsaya wani rakiyar shi ba don ina sauri in fara aikin na saboda yunwan da cikina yafara yi,
Banyi aune ba sai muryan mutum kawai naji abayana cikin fada tana cewa,
Ke Meenat gurinki nazo wallahi barin fada maki gaskiya ki fita a idona wallahi,
Idan ba haka ba har kika bari muka sa kafan wado guda dake, agidanan wallahi zaki gane kuren ki sosai,
Ke in ma badon hadin iyayye ba ma may zai yi dake yar kauye kawai kamar ki,
Murmushi nayi kawai don sanin halinda nake ciki don ba zan bari ta kara cutana ba,
Taji haushin murmushin da na keyi batare da na kula ta ba,
Tace a hasale ai dole ki mayar dani mahaukaciya yar iska kawai macuciya azzauluma waike kina takama ke tar uwar shi ce, dake da munafukin tsohon kakan ku kukayi kutun kutun kuka aure shi don kada ya aureni,
Cikin wani iriin tsawa nace mata ke yar iskan tsohuwa gantalala,
Duk kika sake zagan min iyaye wallahi sai yau kingane koni wacece,
Tana kokarin ta yo cikina Ramatu tazo da sauri ta shiga tsakanin mu,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[8/28, 9:53 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL -QAWI,,,,


Ganin irin yadda yanayi Salawatu ya nuna min nasan cewa zata iya yin duk wani abinda ta furta a kai na alokacin
Shigowan Ramatu a gare mu yasa Salawatu ta juya da fadan a gurin ta,.
Ban san may Yaya Abubakar ya manta yadawo dauka ba don tun daga kofa yake jiyo muryan Salawatu tana cewa,
Munafukin tsohon da ya hana aure ne don a aure ki wai ya yi maku hadin gida,
In har shi yace ki takamu yadda ranki ke so to ki fada mashi aikin shi bai ci ba don ni Salawatu naci dubu sai ceto,
Bata karasa abinda ta bude baki tafadi ba kamshi da takon Yaya Abubakar ya baiyyana a kitchen din namu,
Maganan da ya makale a bakin Salawatu ke nan bata karasa ba,
Ramatu ce tace to Alhamdullahi tunda Allah yadawo dakai Alhaji,
Wallahi fitina baida kyau baida faida maida gida baya yake yi,
Idan badon nima Allah ya kawoni ba aida ba asan yadda abin zai tsaya ba irin yadda ta taso ma,
Ga kuma zagin iyayye wanda bai dace tunda iyayyen yarinyar nan ai sai nake gani kamar duk naku ne da dake tunda dan su kike aure ko ?
Fuskan Yaya Abubakar wanda zakace bai ta yin dariya ba dashi ya hade guri guda,
Salawata matso kusa dashi tana ceea yawa Oga gara da Allah ya dawo da kai,
Kafadawa wanan fitsararan yarinyar tafita hatka wallahi don ni ba sa,ar ta bace,
A zuciye ya juyo gare ta ya daka mata wani irin tsawa yana cewa,
Shut up my friend I don't want to hear from you,
Maza zoki fice min daga gida please,?
Salawa ta juyo tana duban shi a cikin mamaki tace Oga ni kake kora daga cikin gidan ka don muna fada da wanan yarinyar,
May wanan yarinyar zata gwada min ne wai da har kake kokarin ko yaushe kare ta,
Ran Yaya Abubakar ya kara baci yace, a fusace tare da mata wani kallon rainin hankali,
Wanan yarinyar ai kema kin san cewa tafi ki komai ko,
Tunda har kika tsaya duk yawan shekarun ki a kanta wai kina fitina da ita,
Tunda idon ka a rufe yake a kanta ai bazaka ga lafin ta ba ita,
Yaya Abubakar ya watsa mata harara yace ni mata na sun fiki komai Salawatu tundaga mutunci, dakuma kamun kai, don babu wace ke jamin fitina da bacin rai a gida da waje sai ke,
Wani irin mugun bacin rsi Salawatu taji a wanan kalaman nashi ,
Take taji gidan tankar yana juya mata, yau ita Salawatu ce ake fadawa haka cewa,
Muryan shi taji yana ceea Get,out in my house please ,
Fuskan shi ta duba wanda babu alamar wasa a zancen shi dole fita zatayi
Lailai ma watau namiji baida tabbas yau ita da tske ganin cewa duk ta dara sauran matan Abubakar a komai ,
Wai ta ce akewa wanan cin fuska a gaban kishiya da ar aiki,
Hawaye ne na takaici ya zubo mata a fuska yanzu bata da wata magana tunda har ya kwnce mata zanin a gaban kowa don har Sadiya dake daki saida wanan hayaniyar ya fito da ita,
Takasa koda motsawa agurin muryan shi stil yana cewa kuma ina mai tabbatar maki wanan tsohon da kika zaga har sai kin nemi gafaran shi ke da gidan nan,
Don shine sillar zuwa na duniya har kika gani kika lake min,
Da sauri ta daga kai ta kalli Abubakar wanda yau ya koma mata tankar zaki agabanta,
Yace idan na kyale ki agidan nan wata rana zan dawo na samu kin min kissan kai a gidan nan tunda ke dabi,un ki na yan jagaliya ne ,
A hankali naga Salawatu ta juyo ta kali gurin da nake tsaye da yukan da nake fere dan kali,
Sai kuma ta juya ranta abace tafice da ga kofan kitchen din hawaye na zuba mata a idon ta,
Bayan ta Yaya Abubakar yabi a fusace ya cewa Iam tied with dis in my house please live us alone,
Daga dakin ta yana tsaye daga kofa ya ke fadar hakan ta girgiza kai azuciyar ta tace tab dijam yau kan angama sance mata a kasuwa daga wani irin kallo za,a dinga yi mata agidan kuma,

****** ********** ******
Tafiyan salawatu bai min dadi ba a rai don ba dadi irin haka , duk da dai mahaifana ta zaga da kakana,
Amma bai,kamata ace har ta bar gida akan hakan ba don saboda yaya Abubakar tsaye yai mata har sai da ta gita gidan,
Shima ya fita, duk Anty Sadiya ta nuna cewa hakan shine daidai ni dai a gaskiya har cikin raina banji dadi ba,
Maganar Ramatu ne ya dan hankaltan da ni inda take cewa to ke uwar daki na. Idan har Alhaji bai dauki mataki a kanta ba watarana babban magana zata jawo mai a gida,
Sai a lokacin nagane cewa warning din ta yake son yayi don haka nace Allah ya kyauta kawai,
Ganin da nayi cewa yanzu Anty Sadiya taji sauki sosai yasani cewa ta karbi girkin ta a ranan idan don cooking ne ni zan dinga yi gaba daya,
Batayi musu ba ta karbi girkin ta tare da yi min godiya gurin Yaya Abubakar ne dai muka samu matsala,
Don daya dawo yagane cewa Sadiya zata koma girki yai ta masifa yana cewa kamar abin gudu bazata bari taji sauki ba sossi , zata soma girki a yanzu,
Amna sai na bashi hakkuri ina sheda mashi cewa nice zan diga cooking din gidan gaba day,
. kuma indai yai haka Sadiya zata zaci ko wani abu yake nufi na daban,
Dole ba don yaso ba ya hakkura ya barta taci gaba da yi duty din ta,,
Bayan na kare aikin komai dake gabana sai na shige dakina don in huta,
Ban kai minti biyu da kwantawa ba Anty Amarya tabugo min waya ,
Na dauka da sallama abakina ina mata gaisuwa tare da tambayan ta kan,nena,
Nakuma tambaye ta lafiyan uncle dina tare da na su mummy,
Anty ke ce min kwana biyu banji ta ba tana can gidan hajiya suna jin yarta kamfanta ke ciwo har sai da ta kwanta asibiti,
Na tausayawa tsohuwan tare da yi mata sheri irin na jika da kaka,
Nan Anty take ce min ai Abokin Uncle dina Nasir ya samu matsala da matar shi, don tana ganin kamar har sun rabo
Nai Innalillahi tare da tambayan yaushe ?
Anty Amarya take cewa ai ankwana biyu da yin case din yanzu haka tana gidan su kano,
Yara kuma suna nan an dawo dasu sokoto gidan iyayyen shi,
Allah sarki amma gaskiya banji dadin wanan labarin ba anty
Tace ai kowa ma meenatu don kin san halin mu mata bamu tsaya muyi bincike ko muyi tunanen mafita ga al,amari.
Sai dai kawai mu kama hauka akan dan abinda baikai ya kawo ba,
Waifa wayan mijin ta ne taga photo wata mace a ciki ga kuma kafan wani namiji kwance, sai dai ba a dauki photo namijin full ba half body ne kawai, ya fito,
Shine ta ce duk yadda akayi mijin tane a kwance ba kowa bane wai Nasir ne,,
A take zuviyan ta ya hau ya na shigowa take tambayar shi ko wacece a picture yace mata ina ruwan ta da tambaya,
Kinji abinda ya hada su fada ke nan Meenat, niko anty amma dai mata Uncle Nasir tai sakaci sosai wallahi ,
Mumata idan abu yazo sai bamu kwantar da hankali mu yi nazari sai kawai muce zamu yanke danyen hukunci,
Yanzu Anty musalima ace full picture din shi ta gane ai sai tayi kokari na farko ta rufa mai asiri,
Na biyu ta zauna tayi nazari may yakai shi gurin waccan matar da har ya ita tsalake ta,
Kyawo ko dressing ko marking love, da sauran su,
Amma wai sai ki ga mace tana ta hauka kamar ba diyar musulmai ba wace tun tana karama tana jin yadda, akecewa mata hudu Allah ya umarci maza da yi,
Matsala dai da abin tsoro shine baka san ko wace ce za,a kawo maka ba,
Wanan kuma ai sai naga mutun ya dukufa ga rokon Allah kawai don samun mafita,,
Hakane inji Anty Amarya tace ai idan ido ya rufe komai, mace mai kishi tana iyayi,
Yanzu da tai hakkuri ta tsaya tayi na zarin wa yan nan abubuwan da kika lissafa ai da baikaisu ga haka ba,
Ni wallahi Meena da ni ita ce zan fara yiwa Uncle din ki duk wani abinda nasan najan ra,ayin maza ne,
Don yanzu idan kin bibiya ma bata ko kama kafan matar Nasir din ba ita ta cikin photo,
Nace ni yanzu anty bagashi ba kaman kin sani kikace in fita zancen Salawatu ,
Ba sai gashi ba kawai ta tunkare ni jiya, wai zata dake ni kuma again,
Ina kitchen ina aiki sai da mai aikin mu ta ta shiga tsakanin mu da ita ,
Ta dinga surfa min zagi ta uwa ta uba har da dan bawan Allah tsohon mu malam tsoho jiya yasha surfa,
Wanan mata dai anyi yar iskan banza wallahi mace kamar iblishiya haka,
Nace Allah yasa ashe mai gidan da take tunanen ko ya fita bai kai ga wucewa ba yai mantuwa ya dawo, duk abinda takeyi a kan idon shi ne,
Masha Allah inji Anty takara da cewa da kya wallahi ai gwamma da yaji ta da kunnuwan shi,
To yaya akayi nan na kwashe duk yadda akayi na fada mata da cewan da yayi sai ta ta roki malam tsoho gafara sanan zata dawo gidan shi
Kai amma ko dai Abubakar ya burgeni sosai wallahi yana son ya gwada mata cewa yasan darajan iyayyen shi sosai,
Anty ta ce to in dai har haka gaskiya Meenatu aiki ja yasamay ki sosai wallahi,
Don yanzu tunda ba imani ne da ita ba zata ce duk yadda zatayi taga cewa yai maki wulakanci zata yi,
Don haka sai ki kara dagewa gurin addu,oin dakuma sadaka akan duk abinda ta dauko ya koma mata,
Yanzu dai kinga kina da ciki babu zance amfani da kayan mata,
Musaman na cusawa duk da nasan baki yin amfani dana cushe cushe dama,
To amma shi wanan hayakin kanunfari ki dakartar da yin shi don Wallahi idan har mace nada ciki tai hayaki a gaban ta zubewa yakeyi tayi bari,
Don haka kada ki fara kice zakiyi yi shi yanzu babban abinda zakiyi tunda kina a haka shine ki yawaita shan kayan sa ni ima, kawai,
Da kuma dabarun gado sai ki sanyadda zaki kama mijin ko a wanan fannin,
Don zata tafi ta kara jin huduban shedan gurin aminan ta na banza fiye da da,
Don haka wallahi duk mace keda kishiya irin haka ko da tafiya tayi sai kiyi kokari kafin ta dawo kema ki kara naki fannin,
Nace Anty aikuwa na gode wallahi tace maza ki maida kaimi gurin kara jawo mijinki a jikin ki,
Nace insha Allahu Anty zan gyara don a gaskiya banyi dabaran yin haka ban sam,
Tace aiko zaki kirani da kanki kisheda min idan har ta dawo, din,
Tace na fada maki harda kwalliya yana sa namiji kara susucewa don wallahi mazan wanan zamanin sun banbanta da mazan da can
Don mazan yanzu zakiga ko mata biyu gare su idan guda bata da karfin yar uwa sai kiga hankalin su ya koma ga wace keda shi,
Mai kaya tab ga daki da kuma kayan sawa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login