Showing 357001 words to 360000 words out of 388021 words

Chapter 120 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8257

Ga yaran kuma suna kuka da alaman yunwa yafara sasu agaba ke nan,
A hankali idanuwan na suka dan fara budewa yayin da nake jin kukan jarirai sama,sama acikin yanayin da nake,
Cikin wani irin murya mai laushi nace ku kai su susha nono mana,.
Dasauri yakai kunnuwan shi a saitin kunnuwana yanacewa Meenat Meenatu sannu,
Na amsa a hankali da cewa yauwa, ina kokarin gyara kwanciyana,
Da sauri su kayo kaina suna kokarin gyara min kwanciya don kada na matse ciwona, gurin tiyata,
Sai faman sannu sannu suke min suna cewa Alhamdullahi
Can nawani ce wai wai dan Allah ku sakeni wallahi ciwo nake ji, cikin wani irin murya mai ban tausayi,
Da sauri Baba Wadda ya juya sai kawai ya saka kuka cikin wani irin murya mai ban tausayi,
Su Dije da Gwago Habbi dake ta waje sukayo cikin dakin da sauri hankalin su a tashe,


ZEEEEE MAKAWA YELWA
[12/7, 10:12 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 3?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MAANI

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai barkan mu da jumma, Allah ya sada mu da alherin dake cikin wanan ranan mai tarin albarka, =?O?=?O?=?O?
JUMMA,AT MUBARAK ,,,,,,,,,


Tana zaune kasan ties din dakin ta nabawa yar ta dake rugumay a hannnun ta nono,
Waya yana makale a kunen ta tana magana daga ciki inda zancen su a kan rashin lafiyan Meenat ce,
Inda take kara masu bayani, akan yadda haihuwan yazo wa Meenatu a cikin tashin hankali,
Saidai a nata irin bayanin sai take gani kamar harda samu guri, yasa meenatu take kara narkewa,
Shigowan yaranta dakin ya sata katse wayan da takeyi inda take masu magana akan su cire uniform din su a,kai,wa mai wanki,
ta basu abinci don an riga da an,dafa abinci a lokacin, duk da yaran ba,wani damuwa su kayi da abincin ba,,
A baya ta saka yarta karamar ta goya ta sai take cewa sauran yaran idan sun gama su samay ta a falo,
A zaune ta samu Salawatu wace sai waya take da alaman gulmane ita ma a lokacin takeyi tana wani shake muryan ta don kada a ji may take fada a wayan,,,,
Maimakon Fatima ta zauna sai ta dan tsaya tana jijiga yar ta dake son yin barci a baya,
A daidai lokacin da Salawatu ta kai karshen wayanta ta dago kai tana cewa,
Ina nan ina zancen wanan abin mamakin na gidan mu ne mutumi duk ya kasa sukuni akan mace daya,
Fatima wace take a tsaye tana dan jijiga yarta sai dan murmushi tayi tare da dan kada idanuwanta, tace hmmm bari kawai Allah ya kyauta,
Salawatu tace ni wallahi, abin mamaki yake bani yadda duk ya rikice ya zama wani sususace,
Murmushi Fatima takarayi don yanzu tsam take bata yarda da zancen Salawatu sosai saboda irin huduban da uwar ta tai mata akan zancen hadin kan su,
Don haka ba yarda ta furta komai ba sai cewa da tayi,
Ai kinsan akwai zumunci mai karfi a tsakanin su gata kuma matar shi ce,
Kin,ga ko ba Aure a tsakanin su akwai zumunta mai karfi da zai sashi a wani hali,
Kai kai kin bani mamaki da har kike fadan haka ki na nufin cewa, saboda tana yar uwar shi yake wanan rawan kafan akanta,
Daga inda yake tsayw yana jin zancen su yadan gyara tsayuwar shi don yaji may Fatima zatace again,
Fatima ta dan duka a saman kujeran dake daga gefen ta tana cewa, amma kuma fa kin san sha,anin haihuwa daban yake balke wace akaiwa CS,
Ga diya uku ancire mata a jikin ta koda ba CS akai mata ba aidole ne taji jiki sosai, don fa akwai wuya a haihuwa, sosai,
Kwas, kwas kwas su kaji alaman shigowan shi gidan daga waje,
Shiru su kayi babu wacce tace kallah lahu daga cikin su kuma sai faman yi mai sannu da zuwa suke
Ita salawatu harda cewa ya maijiki da sauki dai yanzu ko,
Mamaki so,sai na irin makircin Salawatu ya kama shi don ta bashi matukar mamaki,
Bai taka masu va kawai ya sa kai zuwa part din shi har ya fara tafiya sai ya juya zuwa part din Sadiya don yai magana da ita,

****** ********** ******
Yanzu Rukaiyya kina nufin haka zan zauna ina kallon irin yadda yakewa matan shi rawan kafa a gidan na
Ki duba fa tun da yarinyar nan aka ajeta asibiti wallahi in fada maki babu wani kulawa da yake muna yanzu,
Kwatakwata hankalin shi yana gurin wanan yarinyar,
Ni wallahi sai yanzu nake yarda da zancen mamashi da take cewa irin su agida halakane don, mutum ba zai gane komai ba agurin miji,
Bai san may na cikin wayan ta fada mata ba, amma sai yaji Sadiya tana cewa ni kin san ban faye yarda da irin mutanen nan ba,
Ki duba fa yadda suka mayar muna da uwa wata Dodo a cikin mutane,
Gaskiya ni zance in dai wanda zan tafi gurin boka ko malam ne gaskiya bazan tafi ba
Kafin ta ce wani abu sai ya murda kofan shiga gurin ta
Irin kallon da yai mata ya sata kaduwa amma dakiya irin nata sai kawai ta dake tana cewa a irin muryan ta,
Har ka shigone yaya mai jikin take da sauki dai zuwa yanzu ko,
Itama ba amsa don alokacin Sadiya tai matukar bashi mamaki sosai
Saboda bai taba zaton cewa kishin ta ya kai hakaba da har idon ta zai iya rufewa akan yar uwar shi,
Ashe mata basu da tausayi irin haka saboda kishi idanuwan su ya rufe har su kasa tausayin irin halin da yar uwar su take a ciki saboda kishin banza da suka saka a ran su,
She dan yana yawan samun sa,an mata ta hanyar kishin su da yai yawa, har idanuwan su ke rufewa,
Yanzu duk irin tashin hankalin da yarinyar ake ciki da ita bai sa jikin su yin sanyi ba sai ma kara taurin da sukayi,
Abin mamaki wai ma sai Fatima ne ta dan yi taushi daga cikin makircin na su,
Abinda ya kara daure mai kai shine irin yadda a gaban shi suke nuna concerns din su ga rashin lafiya wai har da tambayan yaya maijiki, ?
Shin wai duk mata haka su,ke ne ko kuwa dai shin bai yi dace da masu halin kwarai ba.
Ke nan har ita Meenatu din halin dake gareta ke nan a take wani zuciya yace mai sam ba haka bane don a tare dashi da ita sukayi jinyar Sadiya da tai ciwo,
A lokacin da Salawatu tabar gidan haka ta dinga rokon shi akan yayi hakkuri kuskure ne aka samu,
Ita,ce kuma silan zaman diyan Fatima agidan kai har ma Fatiman kan ta,
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da kaiwa Sadiya kallo yana cewa, ta dafa mai ruwan shayi yanzu, don shi kawai zai iya sha a lokacin,
Kafin ya fito daga part din Sadiya ya samu Salawatu da Fatima duk sun watse daga gurin da ya samay su, da farko,
Yana shiga dakin shi yar fada saman gado inda yaci gaba da tunanen rayuwan duniya,
Idanuwan shi suna a lumshe Sadiya ta shigo dakin hannun ta yana dauke da flask, din ruwan zafin da zai sha shayi kamar yadda yace
Daga inda yake a kwance yana jin sautin duk a binda take gudanar wa a dakin,
Batare da ya bude idanuwan shi da kuma hannun shi da ya sa ya dan kare fuskan shi, da shi,
A hankali ta dawo bakin gadon da yake a kwance ta zauna dan nisa dashi kadan
Tana mai fuskantar shi, sai da tai wani numfashi san tace Abubakar dama magana na ke son yi da kai don ina son na dan yi tafiya zuwa Birnin kebbi saboda,na dade ban zo duban su ba,
Wani huci yayi yana dafe da goshin shi, yace cikin wata irin murya,
Yanzu kuma zuwa Birnin Kebbi yazo maki a zuciya naga da can baya idan nace ki tafi sai kice min bazaki tafi ba don bank son dogon tafiya,
Abin mamaki sai gashi yau da bakin ki ke cewa kina son zuwa ki duba su ya karshe da ce good and fine,
Sai dai ki sani mutum ya debo kadan don gudun afkawa daga ciji don wallahi idan mutum yadebo da zafi bakin shi,
Tai mamaki kwara da kalaman shi don a zaton ta baiji abinda ta fada a waya ba kawai dai yana ce mata hakane don
Kawai matsalan mahaifiyar ta da aikai case din Dodo yasa yake ma ta gatse a kai,
Shiru su kayi gaba dayan su babu wanda yake iya furta wani abu kowa da abinda zuciyar shi ke sakawa ,
A hankali ta mike don barin dakin saboda zuciyar ta ya baci ga irin maganan da ya fada mata saboda yanzu bata da bakin bada amsa don mahaifiyar ta ta zubar masu da mutunci ko,
Idan kin fita ki rufo min kofana don ban son damuwa da yawa ina bukatan hutuwa,
Dan juyowa tayi ta dubi gurin da yake kwance inda har zuwa yanzu yana a yarda ta samay shi a kwance,
Tasan cewa mai iya canzawa Abubakar halin shi sai Allah da ya halicce shi
Yana jin fitan ta yasan cewa, ta fita daga dakin sai ya sauke ajiyan zuciya tare da dan mirginawa yana mai ci gaba da mamakin mata,
Yarasa gane may suke wa kishi haka a tsakanin su don shi yaga cewa duk abinda zai masu a tare yake masu
Idan ma har kwaruwa ne ai Meenatu ce a ke kwaruwa, don su yana wa iyayyen su alheri har ma da su din,
Amma ita Meenatu, sai dai yai,wa iyayyen ta tare da sauran mutanen gida kuma bata taba damu da zancen ba,

****** ********** ******
Alhamdullahi don zuwa yanzu na dan samu sauki don idan an gasheni ina gane mutum ,zan kuma iya karbawa,
Karfe bakwai na safe yana acikin asibiti, inda suke gaisawa da su Gwago habi da Mama Biu,
Yana tambayan su ya su ka kwana, ya jikin may jiki da sauki ko,
Batare da ya jira amsa daga gare su ba ya fara tafiya zuwa dakin, da nake a kwance,
Ya sa,may ni a kwance ina idanuwa a lushe takar mai barci,
Kamshin turaren jikin shi,ne ya daki hanci na ya sakani bude idanuwana hankali na sauke su acikin nashi inda na mayar a hankali na lumshe idon nawa,
A hankali na motsa bakina tare da fadan Yayana,
Sai mutum ya saurara, a hankali zai fahinci may nake nufi tare da gane abinda nakeyi,
Irin yanayin da yaga idanuwana aciki shi ne ya bashi, tsoro,
A hankali ya durkuso a gabana idon shi kyam a kaina, kaman mai son gani wani abu ajikin nawa,
A sanyayye na ji muryan shi gap da kunnuwana yana cewa, kaunata ya jikin naki, may kike ji yanzu may ke damun ki,
A cikin wata irin murya mai nuna tausayi da kuma rikicewa yai maganan, tankar zai fashe da kuka,
A cikin daurewa irin na mai jin jiki sosai na bude bakina a hankali nace mai, tare da kokarin nuna gurin da akai min aiki nace,
Ciwo, zafi a hankali tare da kara lumshe idanuwa na, a hankali,
Jiyayi tankar ya rungumay ni don wani irin tausayi na da ya tsirga mai azuciyan shi,
Kamar ace ya mayar da ciwon a kan shi wanan yarinyar dake wahala ta huta hakana
Kusan wata bakwai mutum yana ta wanan irin wahala haka, ba hutawa,
Hannun shi ya mika ya riko hannuwana yana cewa ubangiji Allah ya baki lafiya,,
Jin jikin nawa baida wani karfi ya kara, saka shi a cikin rudani, ya lumshe, idanuwan shi , tare da dan jinke hannun nawa a cikin nashi,
Ya kai wani lokaci rike da hannun nawa yayin da idanuwa na suke a lumshe sai dai zuciyata tana nuna min cewa kila mutuwace zanyi wanan irin ciwon haka,
Muryan shi naji yana cewa inane ke maki ciwo yanzu Meenat,?
Na kasa bude baki nabashi amsa saidai gurin theater da na nuna mashi,
Ya Allah ya baki lafiya yabawa duk kan kullumin musulmin Allah,
Daga bayan shi Gwagona Habbi ta amsa mashi da Ameen ya Allah, tare, karasa shigowa dakin ita da Maman Biu,
A hankali ya ke zare hannun shi daga cikin nawa yayin da ban saki hannuwan nashi ba,
Da sauri ya juyo yana mai kallona sai yaga hawaye suna zubowa daga idanuwa na,
A take tsikan jikin shi ya tashi, shima idanuwan nashi suka kawo ruwa yadan fara kwalla,
Gwago Habbi ce ke cewa haba dai mai sunan malam ai yanzu anga sauki Alhamdullahi don gashi har tana magana
Itace ma fa ta ta,damu yin sallah asuba yau din nan yanzu ai Alhamdullahi gaskiya,
Gurin aikin ne nake ganin yai mata tsami yana damun ta don haka muka kwana da ita a daren jiya tana muna korafi a kan gurin na ciwo,
Idon shi kyam a kaina yace zan ga likita in mashi complain indan ya shigo da safen nan,
Maman Biu tace sun,ce yau da safe muyi mata wanka ko jikin nata zai dan yi mata karfi ai,
Da sauri ya juya inda Maman Biu take yana cewa a haka za,ai mata wanka Mama ?
Tace insha Allahu acikin hikima da dabara ai zamuyi mata wankan,
Mama tace ni yanzu wallahi yaran ma sunfi bani tausayi saboda rashin samun kulan uwa da basu samu, ka ga har sun dan ramay wallahi,
Still hannuwan shi suna rike da nawa yake cewa, zanga likita idan akwai abinda ya dace asaya masu sai a sayo masu ,
Ya dan duko gab da fuskana yana cewa sannu kin ji bari naje naga likita na dawo yanzun nan,

Bai dade da fita daga dakin ba da taimakon wata nurse sukayi min wanka inda suka canza min zanin dake a jikina, dana saman gadon da nake a kwance,
A saman kujeran roba fara nurse din ta saka suka dora ni, a kai,
Ruwan Lipton suke bani a baki a hankali ina dan kurbawa,
Abinda basu sani ba shine dakin nake gani yana dan juya min a hankali,
Shigowan likita da Yaya Abubakar ne suka farga da irin halin da nake a ciki,
Likta dashine suka mayar dani samam gadon inda ba bata lokaci na lumshe idanuwa na, sai barci,
Dukkan su suna tsatsa a kaina inda likita ke fada masu cewa kada su damu stress ne ke damuna ba komai ba
Ai tunda har ankai warka insha Allahu komai ya wuce kenan sauki zai shiga a hankali,

****** ********** ******
A haka sauki ya dinga shigana a hankali har takai ina iya sauka da kaina daga gado zan kuma iya dan zaunawa naba yara nono su, sha,
Nice da kaina na roki Yaya Abubakar da ya koma gurin aikin shi hakana,
A lokacin Lami yar aikin mu tana gurin na kuma san cewa zata fadawa su Salawatu uwar dakin ta ,
Tashigo kawo muna abinci saboda Ramatu bazata samu zuwaba don Amir yana fama da zazzabi kwana biyu,
Don haka Lami tace zata zo don ta duba jikina dama mun san da cewa tana masu leken asiri ita,
Zuwanta yayi daidai da ahigowan Yaya Abubakar shida wani abokoin aikin shi Aliyu,
Ina zaune inabawa Amira nono wace naji ance sunan Mama, Saratu aka saka mata wai don tana da hakkuri sosai ita bata kuka sam ko nono sai an kawo ta abata,
Shine yaya yake cewa ta ci sunan Mama Saratu don ita ta biyo ke nan,
Ya shigo ya samay ni a zaune yau har da dan riga na saka a jikina na dan saka hula akaina,,
Fuskan shi dauke da murmushi tun a kofa da ya hangoni a zaune ina bawa yarinya nono,
Jikin shi saye da shadda gezenah mai ruwan light green dinkin shi iya cinya kawai, kan shi babu hula amma yayi sabon aski,
Sajen fuskan shi yadan kwanta mai lub a fuskan gwanin ban sha,awa,
Yana shigowa, muka gaisa da abokan tafiyan shi da sauran mutanen dakin da,suka sama,
Yake cewa yau kan Alhamdullahi inda wayan shi ya fara ringing acikin zancen shi nagane cewa da yan gurin aikin su yake waya,
Yana gamawa nake ce mai amma ya kamata kakoma hakana don kada a samu matsala a gurin aikin ko Yaya
Irin yadda nai magana acikin dan langabe kai yasa shi yin murmushi tana cewa ke nan har kina ganin kin samu lafiya zan iya tafiya ko,
Saida nai yar har daidanuwa,na nace ga dai jama,a ai insha Alkah ina samun kulla yadda ya kamata,
Don yanzu ina jin sauki sosai don dazun harda dan round nayi zuwa compound din asibitin,
A tare suke fadan masha Allahu aiko abu yayi kyau wallahi,
Aliyun Jos yake ce min sannu kinji madam Allah ya tsare gaba nace a hankali Ameen
Duk a lokacin Lami yar aiki tana make a gefe guda kamar wata marainiya,
Tafiyan su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login