Showing 213001 words to 216000 words out of 388021 words

Chapter 72 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8298

Hamza da yake cewa,
Mijin ku ba karamin mai kudi bane baidai son nunawa mutane cewa shi mai haline sosai,
Don Hamza ke ce min wanan gidan ma da kuke a ciki waiya saye shi a she ?
Da sauri nadago ina mamaki wanan tangamemen gida Yaya zai saye, haba dai,
Tace yanxu ma wai masu wancan gidan dake daga gefen ku zasu sayar suma shine ake kokarin ya saya, again,
Sai a lokacin na dago kai ina mata kallon mamaki don jin may take fada, nace yanzu ke Fattu shine har kika yarda da zancen an,ce,ance haka, don dai ta yaya mutane zasu dinga sai da gida haka,
Dariya tayi tace min, ke Meenatu aisu masu irin wanan gidajen haka su keyi sai su bada haya na wasu shekaru idan gidajen sun fara tsufa sai a sayar a gina wasu new modern, masu kyau kuma,
Na ce ikon Allah amma wasu Allah ya basu arziki gaskiya mutum yai irin wanan gidan haka yabada hayan shi,
Tace ai abin daga Allah ne kawai Meenat Allah shi ke halitta bawan shi yadda yaso,
Shiru nayi ina nazarin yanzu ace Yaya yana da kudin da zai sayi wanan gidan haka amma ya kasa gyarawa mahaifan shi part din su,
Ga rufan zaman malam tsoho wanda tun ina yarinya har zuwa yau, nake fatan Allah yai min budi da falala in gyara mai shi ya koma kamar na malam Alkali, Haruna,,,
Idan da nice Yaya Abubakar ba zan sai gidan nan ba,wallahi sai dai in je makka ko in kai su Mama da su, Baba ,
Don ni ma ina son inji ana cewa gidan mu akwao Alhaji wani da Hajiya wance,
Muryan Fattu ne ya katseni daga shiga tashan dajin da na keyi ,
Tace amma Meenatu sai nake ga kamar har zuwa yanzu Anty Sadiya bata ji sauki ba sosai irin haka,
Nace amma kuma da sauki don kin ga yanzu tun lokacin da tace bata son aikin Baba Ramatu, da kn ta take dan daurewa tai wasu abubuwan,
Aiko kinga da sauki ke nan ko,
Fattu tace aini wanan matan sai nake ganin rayuwan ta kamar irin na mutane masu nakkasa na tare da su,
Irin wa yanda ba su ci gaba kuma basu son wani yaci gaba,
Murmushi nayi nace kece dai ke ganin haka Fattu amna ai tana da saukin kai,
Don kin ga da ta korin Baba Ramatu, daga baya da naba ita Ramatun hakkuri ai bata hanata tai maka mata ba da kamar su wanki yin girki da yan sauran su,
Na Salawatu ne kawai bata yarda tayi ba kuma bata yarda ko wani irin hurda ma ya da ta da ita,
Fattu tace ai ni matar tana bani sha,awa gashi ta zama maki kamar wata yar uwa wallahi,
Ko Maman Bi,u saida tai magan ta ranan da tace kince tazo ta dan mike kafan ta,
Mun kai wani lokaci zaune tare muna magana amma ni zuciya ta sai faman sake saken iska take yi,
Bayan azahar mukayi sallama da fatu inda na bata kyautan abubuwa kamar su sabulu, da wasu daga cikin tufafina tunda ina dasu yanzu Alhamdu,Lillah,,
Nake ce mata idan tana da dama gobe insha Allah nake son zuwa a wanke min kai, na,
Tace ba matsala zata fadawa maigidan ta sai ta rakani nace mata nagode, nai mata rakiya har bakin get din mu
Zan shigo gidan ne na daga kai na kalli tangamaymay gidan da fatu take cewa wai na Yaya Abubakar ne yanzu,
A falo da Baba Ramatu ta gyara shi tsab sai kamshi ke tashi tako ina na zauna don in da sake jiki daga yawan zaman dakin da na keyi,
Salawatu wace izuwa yanzu naga ta koma wata cool da ita bata son yawan rigima irin da,
Ta fito daga kitchen tazo wuce wa, gani a zaune falon ina ko,karin kunna tv sai da remote din yaki dauka yadda na ke so,
Muryan Salawatu naji daga bayana tana cewa wanan remote din yana bukatan wani battery ne
Don jiya na so a nayi amfani dashi amma sai yaki yi,,
Murmushi mai kama da ya ke nayi mata don dai ina tsoron tuban mazuru,,
Daga gefena ta zauna takarbi remote din daga hannina ta dan bubuga sai ya tashi ya fara aiki,
Sai ta miko min na karba tare da cewa nagode matan Yayana,
Murmushi tayi min tare da cewa au tanan kuma kika bullo min ko,?
Ta gyara zaman ta tana cewa kaman ko kin san irin yadda naga gidan ku ban tsanmani haka kuke so,close dashi ba,
Ina ce ko irin relative's dinan ne fa kawai a tsakanin ki dashi,
Kafin in bata ansa Ramatu takawo min jug din zobon da take jikamin ina sha, don samun lafiya cikina,
Na karba tare da godiya ina cewa nagide Salawatu ta kalli cup din dake a hannu cike da ruwan sobo tace ,
Wanan sai nake ganin ai zai iya ta da Ulcers don tsamin shi ko, ?
Ban ce kalaba sai kurban abina nake a hankali ina lumshe idona, saboda dadin shi da nake ji,
Can na ce kila wanda kike shane ke da tsami amma ni kinga wanan yanada dadi wallahi,
Yaya Abubakar ne ya shigo gida a lokacin don yanzu baida wani time da ya tsayar da zamu ganshi a gida,
Tun shigowan shi idon shi ke a kan mu yana mamakin gani mu a falo zaure tare yau,
Abinda yadade rabon da yaga wanan a gidan shi tun bayan da Salawata fara tada fitina,
Muryan shi ne ya ratso a kunnuwan mu yana cewa may kuke sha hakane a cup,
Salawatu wace iyanzu bata ganin fara,an mijin nata tai tsagal tace wanan kaunar nakace mai sha ni ban son shi don ban kanji dadin shi,
Hannu ya mika alaman in miko mai cup din dake a hannu na ,
Nace bari a dauko ma wani cup Yaya a zuba maka yace cikin girgiza kai No bani wanan din inji,
Namika mai a hankali ya fara kurba bai ce kalaba illa yana kurba yana wani lumshe idon shi har ya shanye tare da miko min cup din,
Yana aje cup din a gaba yake cewa wanan abin yayi dadi sosai wallahi waya hada shine wai ?
A hankali nace, Baba Ramatu ce,
Yace ok ina son shi wallahi kice ta dan dinga hada min shi please duk dare nasha kafin na kwanta,
Kaina na gyada tare da murmushi ina cewa ai a kullun yanzu sai tai ke min shi cewa tayi ya taimakon mutum sosai a lafiyan shi,,
Salawatu wace tunda Yaya ya fara kurban zobon naga yanayin ta canza tai shiru ta maida hankalin ta a gurin tv,
Nadan kara tsiyayawa da niyar in sha sai naji muryan ta tana cewa bani insha inji wanan yabon dadin sa da kuke yi haka,
Ta karba ta kuba a hankali tana lushe idon ta itama tace gaskiya yayi dadi sosai wallahi,
Na tsiyaya a wani cup namike tsaye don in kai wa Anty Sadiya tasha,
Ina zaki dashi kuma nace a takauce zan kaiwa Anty ne ko zata sha,
Wani irin ajiyan zuciya naji Yaya ya sauke gami da fesar da wata iska irin ta relief din nan daga bakin shi,
Na shiga gurin Anty Sadiya na samay ta a tsaye tana daura zani nai sallama ta karba min nace,
Zobone da Ramatu ta hada muna nace barin debo maki ko zaki sha,
Wani irin kallo na tayi tare da cewa tau, aje min daga can gurin mirrio,
A dadare tai maganan cikin nuna rashin godiya daganin shi,
Wani murmushi nayi iya baki don nagane nufinta gareni amma kuma nasan cewa zata shanye nei,
Har na kai kofan fita nace mata amma dakin dan fito don muna falo gaba dayan mu har ma maigidan,
Allah baku sa,an zama don ni ina da abinyi agabana yanxu zaman ku bai gabana,
Tsigar maganan ta yasa nasan cewa tana da wata manufa azuciyar ta kai na girgiza kawai don nasan halin Anty Sadiya sai ita,
Banyi aune ba gurin daga labulen dakin na hado da hannuwan Yaya Abubakar wanda a zatona nake tsanmanin bai ji may mu kace ba alokacin,
A hankali ya tako zuwa cikin dakin bayan nadan kauce mai daga hanya,
Daga gurin da Anty Sadiya take a tsaye tana rakani da hararan jin haushi, shima kallon wawiya ya sake mata,
Nidai na sa kaina nafita daga dakin don in har da sabo yanzu nasaba da halin anty sadiya,
Ina fita gurin da nabar Salawatu a gurin nasamay ta zaune, ta kurawa tv ido sai dai daganin zaman ta,na ciki na ciki,

Shiko Yaya Abubakar yana karasa shiga dakin idon shi ya hango mai cup din xobon dana aje saman mirror ta,
Direct gurin mirror ya nufa inda ya dauki cup din zobon ya fara dan kubawa a hankali tare da lumshe idon shi,
Sannu da zuwa Anty Sadiya taje mai cikin wani irin murya ciki ciki,
Sai da ya kara kurbawa yake cewa ya kuka wuni ya kuma jikin ?
Naji sauki tace a darare batare da sakin fuska ba yasan halin matar shi don haka sai bai damu da daure fuskan ta ba,
A je cup din yayi gurin da ya dauka saboda kallon da Sadiya ke mai don ganin zai shanye mata abinta,
A hankali ya tako zuwa gaban ta suka danyi gab da gab da ita,
Yace bazan samu hadin kai agidana ba sai ke da akasamu kin sauke komai da kikeji azuciyar ki kin ja kowa ajikin ki,
Yanzu irin yadda yarinyan ga ta kawo maki wanan abin bayan acan taga cewa kowan mu yasha, shine ta ga ke baki kusa ta dauko maki,
Amma sai kike mata irin wanan acting din takar baki farinciki da kawo makin da tayi ba,
O dama ai ta yine don ganin idon ka ba don Allah tayi ba,,
Ya jijiga kan shi tare da yin murmushin takaici yace ita Meenatu?
To ashe tayi kokari don ke ko naganin idon ma baki iyayi ai,
Harara ta sakar masa ta gefen idon ta tace ai ba sai ka nuna min cewa yar uwarka bace,
Har ya fara tafiya sai ya juyo ya dakata ya na fuskantar ta,
Ya daure fuskan shi tamau ya ce baki san kunya ba wallahi da bakiyi wanan zancen ba,
Daga haka yabar dakin zuciyar sa na masa kuna sosai,
Mun dan kai wani lokaci zaune a falon ni da Salawatu tana min bayanin wani film da take kallo na India a wani tasha mai suna marriage again,
Ganin da nayi almuru ya gabato ya sani saurin mikewa ina ce mata ashe lokaci yaja haka ne, kada in makara banyi alwala ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?,
Nace mata Allah ya bamu alheri ta ansa da fafin ameen ,
Ina bada baya ta saki tsaki tare da kokarin mikewa tsaye,
Ta kashe kayan kallon tare da daukan dankwalin ta tana daurawa,

****** ********* ******
Bayan mun idar da sallah ishai, ne Baba Ramatu ta shigo dakina tana cewa bara ta zuba min abinci ko zan ci ko,
Nace ai ruwan zobon da sha duk ya hake min ciki sosai yanzu banki ba dai zuwa dan anjima kadan ko
Tace ta bara dai na zubo maki naki a kula duk lokacin da kika tashi ci yana a kusa da ke,
Nace babu damu Baba na gode, tace kai uwar dakina tundai da kikaji yaron nan na kirana da Baba Ramatu kika rike ,
Nace to ai don nace ba laifi bane hakan tunda kinci haka gareni,
Saida ta dawo dauke da abincin take cemin dama ina son mu kebe in maki magana nece taufa may ya faru kuma,
Tace wanan matar da kike gani wallahi ki yi nisa da harkan ta don wanan abin da kikaga tanayi kamar gaske duk karyane,
Ladabi ne kawai irin na shegu ko munafukai don su cuta maka don haka ki yi hankali da shigo, shigo ba zurfi da take maki,,
Nace nagode Ramatu insha Allahu zan ki yaye ga duk wani sherin da take daniyar yi min,
Ta fita bada,wani dadewa ba sai gata ta dawo tanace min wai Yaya Abubakar yana ne man mu a falo,
A take gabana ya tsinke don jin may tace don nasan cewa wata sabuwar magana ce kuma kila ya faru,
Don haka na mike a hankali zuwa falon don karba kiran da ake min,
Gaba dayan su suna zaune a lokacin ni kadai ce da alamun ake jira tazo,
A hankali na karasa tare da masu sallama na samu gefen kujeran dake kusa da wanda Yaya Abubakar ya ke a sama na zau,na,
Ina jin nishin ummm din Anty dake zaune tayi tagumi da hannun ta guda ta tokare habanta da shi,
Bance kala dakowan su ba bayan na zauna na mimike kafana don inji dadin zama,
Illa dan daga kan da nayi na kalli Yaya Abubakar wanda ke ta faman aikin shi a cikin system din shi tankar bai san da zaman mu ba a gurin,
Gurin yai wani tsit sai karan tv kawai dake ta yi a falon bakajin komai bayan hakan,
Gyaran muryan da Yaya Abubakar yayi shi ya dawo da hankalin kowacen mu gare shi,
Ya fara da sallama sai kuma yai shiru yadauki remote ya, na rage karan tv da yai yawa don muji shi,
Yace abin da yasa nakiraku nan don in kara fadakar daku abinda baku sani ba ko kuma kuka sani kuka manta,
Tsit mukayi muna sauraren shi don a gaskiya fuskan shi babu zancen wasa acikin sa,
Ya dago kai ya kalli kowacen mu ya ga dukkan mu, mun natsu shi ka dai mu ke sauraro,
Ya ce ina son da farko in fara tambayan ku, may ya hadamu a wanan gidan gaba dayan mu,
Shiru mu kayi gaba dayan mu babu wacce tace kala daga cikin mu,
Yace tambayan ku nakeyi mai ya hadamu zama a wanan gidan gaba dayan mu,
Cikin mu Salawatu ce tai karfin halin cewa zaman aure ne nake ganin ya hada mu aiko,?
Ya juya gurin Sadiya yace Sadiya zance Salaqa gaskiyane ko a,a a zanen ta ?
Ta ce haka din ne abinda tace kowacen mu auren ka take yi
Ya juyo gurin da nake zaune kasan ties yace Meenat kin ji may sukace haka din ne ko a,a ?
Na dago kai a hankali na dubeshi tare da duban su nadukar da kai nace cikin sanyi murya hakane Yaya,
Yace good ,
To daga yau ina son kowacen ku tarike aziciyar ta cewa abuguda akawo ku gurina,
Don haka babu wace tafi yar uwar ta a gareni don duk guda kuke a gareni,
Saboda haka bana son daya daga cikin ta kara cewa wai don guda tana yar uwata bana son a yi zancen ta,
Ko ace wai na shigar ma daya magana sam ban son in kara jin irin zancen nan,
Yace wanan ke nan zance na biyu kuma kamar yadda nasha fada maku cewa zaman lafiya nake bukata daga gare ku ko yau she,
Don haka bazan yarda wata daga cikin ku ta dinga kawo min fitina ba agida idan har hakan ya kara faruwa to ko wacece daga cikin ku ranta zai baci sosai da ni,
Saboda haka kamar yadda na fada maku tun farko hakane ko yanzu don ban son kowacen ku ta din samin bacin rai da saura,
Kuma ina son kowa ta koma normal duty din ta kamar farko,
Tsit mukayi kowa na sauraren shi saboda ba fuskan yin wani zance gare shi,
Haka yaita kidaya muna dokoki muna sauraren shi duk da bai fito fili yai muna bayani ba musan cewa dayan mu ta bata mai rai ne,,

****** ********** ******
Washegari kamar yadda muka shiyar da Fattu zuwa gurin gyaran jiki haka muka fita tunda safe don kada mu samu layin mutane da yawa,
Fitar mu gidan Baba Ramatu wace ke ta aiyukan ta batare da ta kulawa kowa ba a gidan,
Su Lubuna ne suka shigo cikin wani matsasen kaya da ya manne mata a jiki
Sai shan taba su keyi warin taban duk ya gauraye gidan,,
Ga kida sun sa yana tashi wanda mutum tun yana daga bakin get din gidan zai ji tashin sauti,kidan na tashi,
Anty Sadiya da abin ya ishe ta tafito daga dakin ta ta nufi gurin da Ramatu ke goge gogen ta tana cewa wanan haukan yau har ina haka ?
Ramatu bata ce komai ba sai dan murmusawan da tayi kadan,
Abin ya ishi Sadiya sai tace Ramatu ta kira mata, Salawatu ba a dauki lokaci ba,
Salawatu tafito daga dakin tana wani taunan chewing gun kass kass tazo har gaban Sadiya tace lafiya dai ko ance kina kirana,
Sadiya cikin nuna gajiya da bacin rai tace haba Salawatu yanzu, wanan kidan haka kamar gidan yan rawa, haba dai,
Cikin wani irin kallo Salawake kallon Sadiya tace ban fahince ki ba har yanzu,
Sadiya tace, gaskiya bai dace ba ku saka muna kida haka ?
Tau fa wani sabon neman fitina ne kuma har da baki idan mutum yayi sai an saka mai ido,
To bara kiji


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login