Showing 24001 words to 27000 words out of 388021 words

Chapter 9 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8189

tace gaskiya yamma tayi ya kamata ace mun shiga kitchen fa,
Ganin ba su da niyar tashi yasa Meenat shiga kitchen din don dora masu abincin dare,
Ga garin sai lema ruwan sama akeyi wanan ya,nayin ya,sa mutane jin sanyi,,
Tuwon semovita, ta tuka masu da miyar egusi, wanda ya sha, nama da tagani a cikin fridge duk ya kankare,
Sai kusan gaba aikin tane Samira ta shigo kitchen din don taya Meenat din aiki,
Amma kuma sai ta samu ta kusan gamawa don saura kadan,
Don haka ta dan taimaka mata da dan abu kalilan,
Suna kitchen a lokacin da sukaji sallaman yayan su Abubakar,
Meenat wace, sai,mamakin yadda mutum ya iya tukin mota cikin wanan ruwan da ake tsulawa,
Daga kofan kitchen din suka dan hango bayan shi yana shigewa a lokacin bedroom din su hannu shi dauke da yar briefcase, din shi,,,,
Mamaki ne ya kama Meenat ganin irin yadda yayan nasu ya shigo cikin gidan ba tare da nuna wani damuwa akan su bakin shi ba,
Kuma, ma ga Sadiya a falon zaune tana kallon season's film, amma sai ta ga bai tsaya ba,
Mugun hali ta furta a zuciyan ta tare da cewa wanan ai, ba halin sunna bane,
A take uncle din ta na soko, ya fado mata a rai irin yadda yakeyi masu idan yadawo daga gurin aiki,
Amma kuma ai har da laifin ita Sadiyan don dai tun jiya take ganin ta a cikin wanan dogon rigar ai ,
Ita abinda, ta gani tun a gidan su har izuwa gidan uncle din ta shine,
Da zaran yamma ta yi dai dai lokacin da mazaje ke dawo wa gida daga gurin neman kudi, ko aiki,
A lokacin ne zaki ga mace tai wanka ta chaba ado tankar wace zata anguwa ko, gurin wani gagarumin buki,
Shima kuma Uncle idsn zai dawo zai sayo dan tsara ko da bana ci ba ko dangin kayan miya ne,
Da kuma duk wani abu wanda ake yayinsa a lokacin,
Kamar rake, yalo agwalama, lemo kankana, gyada,dafafa, masara gasassa, caras, da,sauran su,,,
Wani lokaci ma ganye zai kwaso masu dafaffa irin su zogala da kuli ganayen rama, dinki, tafasa, da,sauran su dai,,,
Duk da ba wani tsada garesu ba zaki ga mata da yara suna murnan cewa baba ya dawo sai a shiga rabo,
A lokacin kuma za a fara kaeo mai gaisuwa dagida dagu da ana mai sannu da dawowa,
Wani lokaci kuma shi da kan shi yake leka ko, wani daki don jin damuwar iyanlishi idan yadawo daga aikin,
Kusan kuma hakane ai ta gani a gidan iyayyen su duk da gidane na talkawa,
Amma suna kokarin kula da iyalin su sosai kamar yadda sharia, yace,
Wani lokaci kuma malam tsoho shi da kanshi zai saye kwaryan nono da fura akai cikin gida a raba ko wani sashe na gidan,
Amma ga wanan shi ko halin kowa bai kwasa ba shi wani irin mugune haka,
Kwana biyar a gidan ka amma ace ba kasan wanda yazo gurin ka ba ma ba ma balle karramawa,
Tsuki ta sake wanda har ya baiyyana a fili ba tare da ta sani ba,
Sai jin muryan Samira tayi tana fadin may ya faru Meenan su,Baba,,
Ajinyan zuciya ta sauke tare da cewa ke dai bari sister,

***** ***** *****
Zaune yake bayan ya dawo daga gurin sallah yana cin abincin da Samira ta gabatar mai da sunan abincin shi,,
Tun a lomar farko ya san cewa ba daga hannun sadiya ko Samira kaunar shi wanan abincin ya fito ba,
To idan ma ba su bane kar dai ya ce wanan abincin daga cikin yan bakin yaran nan da malam ya turo suka cika mai gida wata tayi,,,
Sosai ya cin ye abincin nashi wanda rabon da ya zauna agida ya, ci abincin gida haka har ya manta da lokacin,
Ya godewa Allah da ruwan sama ya hana shi tsaya wa baici abincin restaurant ba,
Tun daga wanan ranan ya fara dawo wa gida don cin abinci,

***** ***** *****
Zaune take a gaban mirror tana gyaran jikin ta,
Kayan jikin ta suna da shiny,shiny wanda duk ta juya suna walkiya,sosai, turare ta fesa kusan kala biyar a jikin ta alokaci guda,
Jan baki ta dauko ta dan zizirawa bakinta sai kuma tadan kara gyara fuskan duk da kwaliyan shi yayi kyau tun farko amma sai da ta sake yin wani,
Wasu takalminta masu tudu dake gefe guda ta jawa su ta dan shiga goge su don su, dan kara haske,
Gyalenta da ke saman gadon ta, ta, dauko ta sagala, a saman wuyan ta,
Yar jakar ta ta dauko, tare da keys din dakin ta dake a saman mirror ta,
Tun shigan ta ma,aikatan tai arba da motan shi daidai, gurin da ya saba parking din
motan, a kullun,,,
Kallon motar tayi tankar shi take kallo a fili, ba wai motar ba,
A cikin dan damuwa ta karasa har office din su, cikin dan nuna yanayin damuwa,
Zaune take amma tana yi tana duban time din wayan ta dake a gaban ta,
Lubuna ce ta zo har inda take ta zauna a saman tebur din da ke gaban Salawatun,
Cikin wani irin murya irin ta goggagun mata tana kashe ido guda,
Salawa, yau ya akayi ne wai ?
Nasan dai, zancen ba zai wuce na mutumin naki ba ko,
Mr No Name,
Ki bari kawai Lubuna, yau ban samu barci ba saboda tunanen shi,

A tafe yake kamar kullun baida abokin hurda, dabian,sa ne daga gurin sallah azahar sai ya wuce gurin cin lunch din shi wanda kuma muna iya cewa breakfast,
Da dan saurin ta ta karasa inda yake gab da ya shiga, restaurant din,
Salamu Alaikum, Sir ko ba komai wanan muryan yanzu ya dan saba da jin sa ako da yaushe,
Cak ya tsaya don ya kula tafe take gare shi da dan saurin ta,
Fuskan shi cike da mamakin ganin gurin shi ta nufo direct,
Cikin dan rusunawa ta gaishe shi tare da cewa cikin dakewa,
Sir nobar ka nake so pls, ?
Cikin mamaki yake mata wani irin kallo na bai fahince ta ba,
Cikin wata irin murya tace ba wani abu ba ne kawai ina son indinga kiranka muna gaisawa ne,
Shiru yayi da farko kamar ya wuce yabar ta amma yana daga kai suna ido biyu,
Sai yaji bakin shi kawai yana karanto mata noban wayar nashi,,,
Daga haka ya juya da sauri kamar wanda aka kora,kawai, sai ya,shige gurin da ya nufa,,,,
Salawatu wace ke tsaye tabi bayan Abubakar da kallo tare da sauke wani irin ajiyan zuciya,

***** ***** *****
Abincin ne aka jera a cikin tiren silver round, daga dangin jug na ruwa, kulan tuwo da miya, sai gishiri a gefe,
Tabar da, ke a shimfede a cikin yar rumfar sashen ta tanufa da kayan abincin,
Baba Buhari yana zaune daga gefe guda, yana kokarin cire hular da ke a kan shi,
Isowan ta gurin yasa shi da furzar da iska daga bakin shi yana cewa sannu da aiki,
Yawwa malam inji mama Ladi wace takai gurfane a lokacin don aje abincin,,
Gefe guda mama Ladi ce, wace duk da ta manyanta hakan bai hanata tarairaiyan mijin nata ba,
Shinkafa da wake ne dafafa, a,cikin kulan sai mai da yaji,
Cibi biyu gana uku mama Ladi tace wa Baba Buhari,
Shin malam yaushe yaran nan da malam ya turawa mai sunan malam zasu dawo,?
Cak Baba ya tsaida cibin da ya debo shinkafa da niyar kaiwa bakin shi ,
Ladi wani irin tambayane wanan haka,?
Malam gani nayi sun yi yawa mana duk kan su ace a gidan shi zasu tare,
Innalillahi inji Baba Buhari cikin mamaki Ladi waye bare acikin wa "yan nan yaran ?,,,,
To malam ai gani nayi kamar sunyiwa matar nashi yawa ace har da su murja da Meena, da,,,
Ke dakata yace wa mama ladi cikin daga hannu da daga murya,,
Tunda sun,yi yawa sai ki shiga mota ki je ki kwaso su ko ?
Abincin da Baba Buhari bai tsaya ciba ke nan don rayuwan shi ya baci,
Ya mike tsaye yana sa taklmi yana fada da ita yace Mai sunan malam dai dan uwan su ne ko kina so ko baki so ?
Ya nufi hanyar fita waje yana mai bambami shi kadai,,

***** ***** *****
Sun zage iya karfin su sai faman goge , goge da share share sukeyi duk inda ya kamata a gyara agidan sun gyaro shi gaba daya,
Kasan cewa yau weekend ne sun san cewa yayan nazu yana gida don bai faye fita ba irin wanan ranan,
Ko zai fita sai zuwa yamma lokacin rana yai sanyi,
Suna cikin gyara, suka jiwo, Sallamar yayan nasu su,kaji wanda ya su gaba daya waigowa amma banda Meenat wace ke kitchen tana gyara,
Daya daga cikin kujerun falon ya nufa ya zauna, inda ya dan daura kafan shi guda sama dan stoll din dake gaban shi,
A daidai lokacin ne Meenat ta fito daga kitchen dauke da bukitin da tai moping,
Ganin shi ta yi azaue girshi agaban ta, batare da tasan da shi a falon ba,
Tun zuwan su yaune farkon ganin shi da ta yi a baya sai dai taji muryan shi kawai,
Ji tayi kamar ta juya baya batare da ta gaisheshi ba
Amma sai yai mata wani irin kwarji a fuska taji kawai ta gaida yayan nasu,
Tankar a cikin mafarki Abubakar ya tsinkayi zazzakan muryan Meenat tana gaishe shi,
Kallon mamaki ya ware idon shi yana mata don sam tunzuwan su yau kwana goma sha takwas bai san da ita ake ba,
Da kyar ya iya bude bakin shi ya ansa mata cikin mamaki,
Ita kan Meenat tasa kai abinta da niyar wucewa inda zata,
Yau,she kikazo ke ?
Ya tambaya cikin mamaki,
Samirace daga bayan shi taba shi ansa da cewa ai tare mukazo da ita yaya,
Amma shine ban sani ba ya tambaya cikin mamaki
Ita bata fitowa waje ne idan ba aiki zatayi ba sai kuma kitchen da take shiga,
Zai yi magana sai wayar shi tai kara a gefen da ya ajeta saman kujeran da yake akai,,





ZEEE MAKAWA YELWA
[6/30, 10:05 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- ARRAHAMAN

Layin MTN, ne ya,gani bakuwar noba wanda bai san mai ita, ba,
Da sallama abakin shi ya dauki wayar dake mai tsuwan,
Muryan wata mace ce ya daki kunnuwar shi a lokacin da take ansa mai sallaman shi,
Hausan ta yasa ya gane cewa bada ga cikin yan uwan shi bane ke kiran shi,,,
Cikin wani irin kashe murya ta fara gaishe shi inda ya ansa mata adan daburce,
Cikin mamaki ya ce don
Allah ko da wa nake magana pls ,?
Sai da ta dan sake wani sautin yar dariya irin na gwanaye sanan tace cikin wata irin murya,
Sir kana magana ne da Salawatu daga ma,aikatan ku,
Nice wace ta karbi nobar ka two days ago,
Ajiyan zuciya ya sauke a lokacin tare da dan dago kai ya kallo gurin da sisters din shi suke kamar mara gaskiya,
Ok, Ok yace sai ya dan mike tsaye daga haka yabar falon zuwa bayan back yard din gidan,
Meenat ce da Murja agurin suna kokarin shanya wasu kyalayen kujeru da suka wanke,
Nesa da su yadan taka inda ya zuba hannun shi guda, a cikin aljihun wandon shi ya na sauraren may salawatu ke cewa,
Sam yaran basu damu da may yayan su ke yi ba alokacin don su har kan gaban su kawai suke yi,
Maganar na Salawatu ne yadan sashi jin yar kunya sai yake ganin ai yaran suna sauraren zancen shi,
Duk da yasan cewa baza su taba jiwo shi ba daga inda suke tsaye,
Matsan na karshe Meenat ke yi a lokacin ne kuma ta,dago daga duken da ta ke, tun farko,
Caraf idon ta acikin nashi wanda hakan yasa tai saurin kau da nata idon,
Tare da daukan bukitin da su kai amfani da shi agurin shanyan,
Ido yabi su da shi tare da ci gaba da wayan shi da Salawatu wace ke ta kokarin tsara shi,,,

***** ***** *****
Malam mudi wanda yanzu aikin shi ya, dawo Abuja shima
A,sanadin Abubakar wanda yai mai hanyar hakan,
Don haka malam mudi tare da Abdullahi sabon masinjan shi Abubakar din su ka zama kamar abokai da junan su yanzu,
Duk wani abin,da ya dace daga aiki ko wani hidima duk su keyi wa Abubakar,
Abu gudane shi ne rashin samun fuska a gurin matar gidan da basu yi ba,,
Shiyasa ko iyalen su basu iya kawo wa gidan maigidan nasu,,
Su biyu ne yau,ma azaune a karkashin icen dogon yaron dake mai,aikatar don sauda yawa sukan zauna atare idan har babu aiki sosai,,,
Salawatu ce tare da Lubuna ke wuce,wa cikin tako irin ta yan gayu,
Hmmm inji malam Abdullahi tare da dan tabe bakin shi yana jijiga kan shi,
Hmm,ummm ya,kara cewa tare da dan rage sautin uryan shi,,,
Malam Mudi wai,ko ka kula da wani abin kaiyya dake shirin faruwa,?
Malam Mudi wanda ya wugat da ledan pure,water da ya gama zuka,
Yace kamar may fa,?
Mlm Abdullahi ya kara tausa muryan shi yace ,
Waccen yar iskan ce na ga duk kwanakin nan tana shigewa ubangidan mu,
Jiya ma a office din shi na gan,ta tana wani magana tana har da idanuwar ta mai kama dana kwankwanbishi,,,
Hmmm,ummm,inji malam Mudi yace cikin kada kai,
Yo ai wanan ba yarinya bace, kwaskwari,ma ce kawai irin na matan zamani ya boye mata shekaru,
Amma Allah na tuba aikila zasu yi yan sa,a guda da mai gidan,
Dariyan kyata malam Abdullahi ya sa har da buga kafa ,
Yace ashe kaima kagane abinda na gano ke nan dan uwa ?
Yo wlh Allah wanan da wuya maigida ya girmay mata,
Wayo kawai zatai masu shi da wanan gidahumar matar tashi mara dariya,
To, to to ashe kaima har ka gano halinta ke nan don dai ni shiru nayi da bakina don kar ace nafaye sa ido,
Haba dai aiko ita sam bata dace dashi ba don bata da marmari sam wanan matar,
Malam Abdullahi yakara nuna Salawatu da hannun shi daidai lokacin da zata shiga cikin wani office,

***** ****** *****
Malam tsoho ne zaune a majalisar kofan gidan shi,
Yara da kuma manya masu zuwa gurin shi daukan karatu lokaci, lokaci, suna zaune suna ta bibiyawa,
Baba Samaila ne ya fito daga cikin yar akwalar akuri,kurar shi, jikin shi duk butu,butu, da kura da ganin shi kasan daga gurin aikin wahala ya fito a lokacin,
Tun daga nesa mahaifin nasu, ya tsura mai ido cikin ban tausayi,
Dan nashi shida yar uwan shi suna bashi tausayi harkullun in ya tuna da watsin da yan uwan mahaifiyar su sukayi dasu sai su bashi tausayi,
Anan gida kuma bawai wani dadin yan uwa, haihuwan su, suke jiba, don ssun ware su a gefe guda,
Don ma dai shi Baba samaila ya zama na mijin duniya ne don a tsaye yake kem da kafan shi gurin neman abin rufawa, kan shi da iyalin shi asiri,
Direct inda malam tsiho yake Baba Samaila yanufa,
Tun daga nesa sosai ya cire silifas din dake akafan shi duk sun goge akasa saboda tsufa,
Gwiwa bibiyu a kasa ya tsugun na yana gaida mahaifin nashi,
Daga bisani kuma yadaga yadawo gefen tabarman da dake gefe guda yadan zauna,
Cikin dukan da kai da ladabi Baba Samaila ya dukar da kan shi a kasa,
Wanda hakan yasa malam tsoho fahitar dan nashi nada magana a lokacin,
Samaila, ya, ya akayi ne ?
Cikin dan sosa kai, Baba Samaila yace, malam dama zancen su yar Baba, da ke can gurin yayan su ?
Dazun ina daji shi kawun nata ya bugo min waya yana min tuni, kan hutun su ya kare, wai, wani sati zasu koma,,,
Murmushi malam tsoho yayi tare da dan gyara zaman shi
Baba Buhari wanda ke gefe yace a,a,a hutu ya kare aiko gara su dawo don kada su, makara,
Aikaga waccan mahaukacin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login