Showing 246001 words to 249000 words out of 388021 words

Chapter 83 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8219

yai mai nasihan kula da zumunci,
Da zamu tafi na bude yar post dina na ciro dubu biyu na basu sai fatan alheri suke min,
Daga gidan kawu Manu muka wuce gidan, yayar Anty Sadiya,
Tun shigan mu gidan matan gidan ke muna sannu da zuwa sama sama mu ka gaida su mu ka fito na basu kyautan kudi, suma nace su sai wa yara Sweet,
Gidan wani yayan Baba na da suka hada zumunci ta gurin uwayen su wanda ke zumunci sosai da mahaifina duk cikin yan uwa nasu yafi zuwa daya,
Shima mun mai kyauta muka fito zuwa gidan gwagwanin mu su biyu duk mun gaida su,
Gidan karshe ne ban san ko gidan waye zamu tafi ba saidai da muka tsaya, a bayan gidan sarki gidan yake,
Sadiya ce naga ta f?ra hade fuskan ta tamau tana magana ciki ciki a lokacin da zamu fita daga motan,
Mun shiga duk da ba musan kowa ba antare mu dai ba laifi zamu ce,
Wata bakar matashiya mace yar gaye na gani ta fito daga daki, tana rike da hannun yarinyar yar kimanin shekara, uku,
Ta zauna gab da kujeran da dattijuwar gidan ke zaune tana cewa sannuku da zuwa cikin dan wani yauki da yanga takira wata mace mai masu aiki tace akawo muna ruwan sha,
Ganin yadda take yasa ban ko dauki ruwa guda nasha ba,
Duk da ko ina jin kishin ruwa a lokacin, ba wai ban ji ba,
Shigowan su Yaya Abubakar ne gidan yasa naga abin mamaki don a take a gaban mu naga wani irin sallo da yanga agaban su,
Sun gaisa ana wani haba haba dashi kamar wani sarki a gaban su lokacin,
Sai dattijuwar matar ke cewa matan ka ke nan a she ?
Murmushi kawai yayi ba tare da yai wani magana ba,
Haka kawai irin yadda na lura da mutanen gidan sai na ji ba su kwanta min a raiba,
Sai daga baya,ne na fahinci ashe gidan su Aliyu abokin shi mu ke,
A take na tuna cewa ai mijin Fatima wace Yaya Abubakar yai nema da farko yarasu kuma a tare muka tafi gaisuwa da yaya wanda a lokacin duk ta sake,
Shin ko dai ita ce ma wanan din a zaune gaban mu yanzu ,
Sai a lokacin ne nai saurin dago kaina na dubu gurin da da take zaune a gefen idona,
Ai,kuwa abinda na gani yasa gabana faduwa saboda irin manyataccen kallon da takewa Yaya Abubakar a lokacin,
A take naji wani irin kishi wanda ban taba sanin cewa ina dashi ba ya turnike ni, a lokaci guda,
Anty Sadiya wace duk ta kasa sukuni a zaune kawai take a gurin duk dan tsawon lokacin,da muka dauka azaune,
Tsam ta mike daga tsaye ta kokarin gyara gyalen da ta yafa a jikita,
A hankali su ka bi ta da idanuwan su falon suna kallon ta,
Ina daga waje tace idan kun gama ganin ta fitane yasani nima mikewa tare da cewa sai anjiman ku,
Yaya Abubakar daga gurin da yake zaune yaji wani irin nauyi da kunya sun lulube shi a lokaci guda,
Murmushi ya dan sake tare da dan lumshe idanuwan shi,
Abakin mota suka samay mu tsaye bayan sun dan dauki lokaci kafin su fito,
Motan tayi tsit baka jin komai sai FM radio da ke aiki suna wani talla akan zazzabin cizon sauro,
Daga gurin da nake zaune a bayan mota na jiyo muryan Aliyu a hankali ya na tambayan ina muka nufa kuma sai Yaya Abubakar ya bashi ansa a hankali da cewa Asibiti,
Asibiti mun samu yan gidan, mijin Anty Samira da yawa sun,zo gaida su don haka ba muyi wani dadewa ba a ciki,
Yaya Abubakar ya cewa Aliyu ya,wuce da mu masaukin shi direct gaba dayan mu,,
Muna shiga na wuce don in gabatar da Awala kayan Anty sadiya naganiba dakin wanda hakan yasa ni sanin cewa a nan sadiya take zaune yanzu,
Nafito na tada sallah na kawai ba tare da na tsaya jiran wani abuba,,
Bayan na idar na dade a gurin zaune ba tare da na mike ko naiwa wata magana ba ,
Shiru shiru yaya Abubakar bai shigo dakin ba ya sani daukan waya na buga mai wayan tana ringing bai dauka ba,
Mamakin hakan naji sosai don nasan cewa idan na kirashi wani lokaci ma shi ke kashe wayan sai ya kirani ta layinsa,
Daga gurin da Anty Sadiya take zaune tana dan,ne danen wayan ta,
Ji nayi tsuki sai ce min tayi yau ai bazai jiki ba Meenatu tunda yana kallon ana mai wanan kissan,
Murmushin jin abinda ta fadi na yi nace, kai haba Anty wani kalar murmushi ne bai gani ba a duniyan nan,
Text nai mai ina sheda mai cewa lokacin shan magani na ya dan wuce,
Baidade ba sai gashi fuskan shi still a daure nasan cewa hakan nada nasaba da fitowan da mukayi daga gidan su Fatima,
Ki tashi a mai dake yace min don haka ban tsaya jiran komai ba na mike tsaye inawa Anty saida safe cikin murmushi nabar dakin hotel din,
A mota dagani sai shine zaune sai a lokacin naga ledan masarana da gyada wanda suka saya muna dazun,
Tun shiga na ba wanda yai magana daga cikiin mu nidashi,
Mun danyi nisa kadan a hankali cikin natsuwa ba tare da ya juyo gurin da nake zaune ba ya kalle ni ba, yace,
Don kuyi min wullakanci ne yasa dazun kuka tashi, daga gidan su Aliyu ba tare da umurni na ba, ?
Saida na gyara zamana batare da juya ba nima cikin rashin sake fuska don ko banza a gajiye nake lokacin guri kawai nake son samu in kwanta,
Nace aa yar siririyar murya da cewa, ni ban bar gidan ko falon ba sai dai kawai na fitane, saboda na gaji sosai, aikawa ne,
Murmushi naji ya sake tare da cewa amma dai ai kinsan ko wacece Fatima ko ?
Sai a lokacin na juyo gare shi nace Fatiman diyar Gwago?
Dariya na dan bashi sai cewa yayi bai ma san wace nake zance ba shi
Daga haka na daure fuskana batare da,nakara cewa komai ba kuma, daga lokacin,
Na juya fuska na ina fuskantar window din motan
Yar boyayyan dariya na bashi saboda ya fahinci ban son jin zancen ke nan,
Mun isa gida ya tsayarda mota ina kokarin bude kofan motan ina cewa saida safe ,
Yace ki shirya don zuwa sundaya zamu bar garin nan insha Allah,
Tau kawai na ce tare Allah ya kai mu lafiya nasa kai na bar motan,
Ban,jira tashin sa ba na shige gida abina batare da na tsaya jiran wani abuba,
Zuciyata sai harbawa take a kan abinda nake hasashe daga gare shi shida Fatima,
Mamana na samu a tsakar gidan mu tana yan aikace, aikacen ta take ce min mundawo, na amsa mata da tare da mata sannu da gida,
Daga haka na shige daki jikina duk ba kwari a lokacin,
Tufafin jikina na fara sauyawa tukun tare da son in watsa ruwa a jikina,
Ina kokarin mikewa ne wani irin yunwa ya ziyarce ban jira komai ba na fara cusa abinci a cikina ,
Saidai badon dadi nake cin sa ba cusawa kawai nake yin don ceton kaina, daga yuwan da nake ji a lokacin,,

****** ********** ******
Yana shirin kwanciya ne yaji wayan shi ta dauki ringing alamar kira ya shigo mai,
Sadiya wace ke kwance a gefen shi tankar ta na barci ta kara lafewa,
Da,farko wani irin shu,umin murmushi taji ya sauke murya kasa, kasa yake cewa
Aiko min dadewa bazan manta da muryan da ya fara yawo a kwakwalwana da farko,
Sai ake tambayan shi ya muka dawo daga ziyaran da muka kai dazun,
Kafin ya bada ansa saida ya dan juya, gurin da take a kwance yaga still tana nan yadda take da farko,
Sai yaci gaba da,wayan shi yana cewa, lafiya kalau muka dawo,
Tambaya ta jefo mai da cewa tana fatan har yanzu akwai kaunar ta a zuciyar shi kamar farko don taga yanzu ya zama dan madubin mata,
Dariya sosai zancen ta ya bata tare da cewa a cikin dariyar shi wanda yasa shi mikewa zuwa dan wani wajen shan iska dake adakin ta gefe, guda,
Yace mata aikema kin san cewa har in na zama dan madubin mata tokece ai ta farkon dauka ki duba ko ?
Taji dadin wanan zancen don hakan ya tabbatar mata da cewa ta samu karbuwa sosai daga gare shi,
Tace amma ai kasan yanzu da can baya ba daya bane akwai yan banbanci sosai,
Murmushi yayi tare da cewa ke ce ke wanan tunanen don ni a gareni duk daya ne babu wani canji a hakan ma,
Allah ne ya kyauta don Sadiya ji tayi tankar ta kuwata saboda abinda kunnuwanta ya jiyo mata,
Sun dauki lokaci suna wayan sannan su kayi sallama tare yi ma juna kalaman soyayyan sai da safe,
Bathroom ya shiga yadan kara kimtsa jikin shi kafin ya kwanta,
Ya dan dauki hannuwan shi ya dora a jikin Sadiya wace tai saurin kauda jikin ta daga gare shi,
Yai mamaki kwarai da ganin ashe ba barci takeyi ba don alama bai nuna cewa idon ta biyu ba,
Duk da baiji dadin yadda taji shi yana soyewa awaya ba gaban ta,
Amma da yake na mijin duniya ne sai kawai ya dake kamar babu komai yana kokarin cin ma burin shi gare ta,
Malam da kayi hakkuri har ka jira wace tafi kowa tazo ma tukun ina ga zaifi ma sauki,
Murmushin kasaita ya sake tare da cewa ai ba wani dadewa zatayi ba tashigo kawai da abinda nake jira ne,
Daga haka ya gyara kwanciyar shi ya juya mata baya batare da ya nemi wani abu daga gare ta ba don yasan cewa ya riga ya bata wanan daren nashi ko yau,
Ita ko Sadiya kamar ta hade zuciyar ta take ji a lokacin don barci ma gaba daya yaki zuwa mata ranan,
Sai zuwa dare sosai bayan zuciyar ta yai ta mata sake ,sake kala kala akan zaman gidan Abubakar,,

****** ********** ******
Waya muke da Anty Amarya tana sheda min cewa, an na neman mu a school muyi summiting din evaluation form din mu,
Nan muka fara hiran rayuwa da ita kamar kullun take tambayana yaushe ne zamu koma, nace ban san time ba amna dai ina ganin kamar nan da weekend ne don wai hutu ya dauka yace,
Amna kuma ni ina son a barni don ayi sunan Anty Samira dani kafin na wuce,
Tace ke ma kin san da wuya ya barki nan din don ba zai yarda ba,
Nace ai yanzu ina da excuse don zan tsaya batun summiting din form dina,
Sai kuma nace ai ni Anty bama zan bishi ba saboda idan son samune in zauna abina a gida,
Cikin garaje tace min ke kada ki fara shi idan bai bari ba kawai ki bishi ku tafi don auren ki yafi maki wanan karatun,
Shiru nayi ina sauraren ta har ta kare min fada da fadakarwa akan muhinmancin rayuwar aure,
Nace cikin sanyin murya Anty Yaya Abubakar fa da alaman wani auren ne zai jajibo kuma again,
Da karfi tace what ?
Wai wasa ko da gaske Meenatu ?
Nace wallahi ko Anty ina matar da mijin ta ya rasu wace ya kaini mukai gaisuwa a sokoto lokacin da muka dawo daga Niger,
Tace kwarai kuwa anyi haka Meenatu, don Allah bari zancen nan Meenat,
Nace to ni dai abinda nake ji a jikina ke nan Anty don dai ma naga alama,
Nake fada mata yadda akayi ya kaimu gidan su Fatima din da action din da suke yiwa junan su,
Abin mamako sai naji anty ta kwashe da wani irin mahaukacin dariya a cikin waya, tace,
Na Mijin Duniya ke nan shi watau ma ba cikin mazan zamanin nan yake ba ke nan ?
Dan tsuki nayi nace wallahi Anty wata yar duniyace fa haka da ita sai wasu matsatsun kaya take sakawa ajikin ta,
Dariya anty tayi min tace wata sabuwar zance ke nan kuma amma dai bawai dagaske ba dai ko ?
Kune dai ke ganin hakan ko ?
Nace anty ni dai haka zuciya take nunamin, tace to ina ruwanki tunda ba akanki zata zauna ba,
Ai kowa da halinta take zama da miji sannan hakan kuma ba haramun bane ai,
Don haka koma da zaiyi ne yaje yai tayi shiyasani don babu abinda ya damay ki,
Kawai tunda kinga shi mutum ne mai son raya sunna to ki dai yi kokarin gyara fannin ki kawai,
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Sai ki kara kwantar da hankalin ki kiga may ya fi bukata ga mace a rayuwan shi,
Daga fannin abinci, tsabta, kwalliya, kwanciya da sauran su,
Daga gurin da nake kwance a saman gadon Mamana, nadan lumshe idona don jin bayanan da Anty tai min,
Sai naga cewa wani ne daga ciki ban
yiwa Yayana Abubakar da har zai sashi ganin wata ta waje can,
Gwargwdo gaba dayan mu kowacen mu tana kyautata mai sosai ta ko wani fanni,
Muryan Anty ne yakatseni da take cewa su maza da kike ganin su Meenatu idan suyi niyar yin abu babu fashi sai suncin ma gurin su,
Don haka bawai zaki ce zaki ci gaba da yadda kike da farko bane yanzu kuma sai mu canza mai wani salon idan mun fahinci ko yaya dabi,un ta yake,
Don fa kin san cewa kowa da kalar ta, ta makircin balle ita wanan da ta taba zaman gidan miji tun farko kinga zata fiku iya badakala, ga maza,
Don kin ga ai yanzu mun fahinci ko wacece Salawatu ko ?
Na ce hmmm kawai don ko ita aiban gama fahintar taba ai, don kishiyace fa, yau dadi gobe daci,,,
Bawai anty ta kare zancen ta bane wayan ya katse a lokacin,
Don haka sai na fahinci cewa kudin wayantane ya kare kila,
Nisawa nayi tare da kokarin gyara kwanciya na, don inji dadin tunane,
Mahaifiyatace na gani a tsaye tana gyara kayan dake saman kujera,,
Sai a lokacin nasan da cewa tana dakin don ganin yawan kayan da ta nade a gefen ta,
Kafin inyi wani tunane ta jefo min tabaya da cewa,
Wacece yake nema ?
A hankali na furta mata da cewa wanan Fatiman ce kaunan Aliyu da yaso aure da farko
Tace ta gidan zabarmawa hayi na ce ita ce Mama ,
Tace to sai may yar Baba idan zai aure ta aiba akanki zata zauna ba ko kuma ba ke ce zai kawo wa kishiya ba ai,
Azuciya ta nace Mama ke nan ai kowan mu ya shafa wanan zancen mutanen da ne ke cewa hakan ,
Yanzu ai kishiya kowa take kaiwa hari ba wai sai wace take biwa ba,
Mama tace kibi a hankali kamar yadda Anty n ki ta fada maki don kinga kina a cikin lalura yanzu kada kijawa kanki wani wahala ,
Shi namiji babu ruwan shi tunda har kikaji ya furta to yi zai yi balle yana jin aljihun shi da yan canji,
Kuma ma don mai sunan malam ya ce zai kara aure aiba abin mamaki bane idan kikayi la,akari da kalaman iyayyen shi a gare shi,
Don komai girman ka bakin iyayye zai iya kama ka don dai tun lokacin auren ku da mama taita masifan cewa,
Malam yayiwa Sadiyar yar ta kishiya to kema sai mai sunan malam yai maki kinji yadda Sadiyan taji zafi,
Idona na rutse don takaicin mama Ladi ina maiyin tir da wanan kalamin nata da ta lakakawa Dan ta,
Mamana tace yanzun dai ki kwantar da hankaliki duk abunda zai yi kada ki fara inji sunan ki acikin wani zance mara dadi,
Ki sawa kanki hakkuri tunda ba,a kanki zata zauna ba kuma ma wai zaki iya jayayya da hukuncin Allah ne shim,?
Don haka ko kadan kada ki sawa kanki wani fitina mai wahal da ke daga baya,
Kai na gyada tare da amsawa da bakina nace to mama insha Allahu zan tsare,
Ta juya tafita ban san lokacin da wasu hawayen takaici su ka biyu idona ba tare da malolon bakin ciki,
Mutum yai ta cika gida da kulakan mata kaman wanda zai kai su kurmi, sayar wa,
Idan kaga yaya Abubakar sai kace idan an saka mai yatsa a baki bazai ciza ba, ma,
Duk da nasan cewa shi gwarzo ne sosai ga matan shi yana da kokarin biya masu bukatun su ta ko wani fanni,
Amma da wuya ace ansamu mutum a wanan zamanin yana koyi da sunnan irin haka,

****** ********** ******
Yau har kusan karfe dayan rana wayana yana a kashe ban kunna ba don gaba daya nakashe wayan saboda ban son surutu,
Wayan malam tsoho ne yabayar wai a kawo min ana magana dani ta layin shi,
Tun ban karba ba nasan cewa Yaya Abubakar ne a layin don haka na karbi wayan ban tsan mani a kunne take ba sai muryan shi naji yana cewa,
Ya akayi tun safe yau wayanki yake a kashe ba,a samun ki,
Nace ba komai just dai akashe take tun safe,
Yace saboda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login