Showing 324001 words to 327000 words out of 388021 words

Chapter 109 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8304

balle dauka,
Cikin dan jin kuya da nauyi tace don may zan dauke shi wani abu ya samay shi ace nice sanadi,
Subbahanallahi mukace yayin da naji maigidan yaja tsuki yana cewa Allah ya kyauta rayuwan ki sai Allah,
Wanan ai rashin tauhidine ya kawo shi ke da ake taba naki diyan ashe baki so ake taba su,
Tace cikin mikewa tau ni yanzu naga zaka tuma ka dafe min akan wanan maganan kuma bani daya bace da zancen,
Salawatu tace ai, amma dai mu bamu nuna hassada irin haka ai don banga abinda yaron ya tare min ba da zan sashi a gaba,
Fatima wace ta fara tafiya don barin falon wanda dama kusan duk haduwa barambaram ake tashi gurin hiran,
Tace, wai munafuci ai sai a fadawa su kaji don mu nan duk zabbine,
Tasa kai tare da daukan yaranta tabar falon inda Salawatu ke mita,
Aisha wace ta fara barci na tayar zuwa ciki don ta kwanta sai a lokacin naji muryan shi yana cewa ke dan Allah ya isa haka don ban son mita,
Na karbi Amir na shiga dashi na gyara mai shirin shi tsab,
Ramatu ce na bari a part dina tare da su Mama Dije, nafito sabe da yaro na hannu guda dauke da Baby bag din mu,
Fatima ce na fara karo da ita tafito daga kicin dauke da goran ruwan sha da alama zata saka su a fridge din dakin ta ne,
Wani irin kallo ko harara ne ta bini dashi tankar ban gan taba inda na wuce, su gaba dayan su zaune a falo,
Kamshi na bar musu suna shaka yayin da nai gaba abina, sai kallon mamaki suke min wai Yarinya da fitsara haka,
Ina shiga dakin da sallamana na tsaya daga kofan dakin nafara jero addu,oin tsari kamar yadda ya dace duk wata kishiya dake shearing din dakin miji da yar uwar ta tayi,indan zata shiga dakin, kwana,
Bayan na shimfide Amir aca karshen gadon na dan dur kusa ina mai kamo hannayen shi na fara karanto mai addu,a kul,a,uzai na tsari ina tofa mai,
Naji an turo kofan dakin a hankali, ko ban juya ba nasan mutum gudane ke da ikon ya shigo dakin a wanan lokacin,
A bakin kofa ya tsaya yana kallon mu a cikin sha,awa, hannayen shi harde da juna kafan shi, sagale a cikin dan uwa ya harde su,
Na tofawa yaron addu,a na lullube shi a hankali namike zuwa inda Yayana yake tsaye jingine da bango a kofan dakin,
Na matsa zuwa gare shi inda naiwa kaina ma sauki ga kirjin shi, ba bata lokaci yakai hannayen shi ya zagayo bayana dasu,
A hankali na dago kai ina mai fuskantar fuskan shi inda na tsinkayo bacin rai a tare dashi,
Kwanta da kaina nayi a saman kirjin nashi nayi akaro na biyu, sai nadan jiya sauke ajiyan zuciya,
Cikin wata yar dasassan murya nace Yayana bacin rai ba naka bane domin mai mata fiye da daya, sai yai hakkuri a rayuwa,
Jinayi ya dago min kaina dake kwance asaman kirjin shi ya zubo idanuwan shi akan fuskata cikin murya mai sanyi da dadin saurare, yace min,
Nasan cewa aurena da yawa wani abune daga Allah wanda duk mahuluki baya wuce kaddaransa mai kyau in mara kyau,
Amma ni tawa kaddaran shine tarin mata a matsayin abokan zama rayuwata,,
A rayuwata ban taba tsanmanin cewa zan auri mace fiye da daya ba to amma sai gashi Allah ya sako mun mugun sha,awan kara aure a lokaci guda,
Ajiyan zuciya da tazama mai al,ada naji ya sake, yana maiyin shiru,
Ko ban daga kai ba nasan ranshi a bace yake don irin yadda nake jin yanayin shi,
A hankali nake dan kokarin zare jikina daga jikin shi, inda na dan riko mai hannu kamar yar jagora zuwa bakin gado,,
Muka zana a hankali na juyo na kalle shi a cikin natsuwa sannu a hankali na sakar mai lalausar murmushi don in samu, damar isar da nufina gare shi,
Badon komai ba sai don na kara jawo hankalin mijina dan uwana a guri daya, tare da duban yan uwan mu,
Nace cikin dan sauke numfashi haba yayana kaifa namijine wanda ke nuna ya isa ga iyaln shi ahalin dukkan mu a karkashinka mu ke,
Don mutum gudan mu tai maka wani abu da ba daidai ba bai,kamata ka tsaya bata ranka irin haka ba,,
Don lafin mutm guda idan kasaka aranka zai iya rushema farincikin ka a rana har yakai ya shafi sauran da ba su ji ba su gani ba,,
Don haka laifin wata ba, zai shafi wasun mu, ba a,garemu kaine mutum mafi daraja a rayuwan mu,
A hankali naga ya sadda kan shi, kasa, hakan yasani gane cewa magana ta ta fara shigan shi da kyau, don haka naci gaba da fadin malam fa yakan fadawa iyayyen mu muna ji yaya yace kowa da halinsa ake zama dashi,
Kai ya gyada alaman cewa hakana ne gaskiya na ce don haka yanzu ka mike don ga ruwan wankan ka can don har na kashe heater ko,
Kan shi a duke still naji yana cewa, Meenat, yakira sunan a cikin wani yanayi mai, mai nuna kasala,
Sai kuma naji yai shiru bai sake cewa uffan ba yayin da na tsura mai ido, don sauraren abinda zai fada a lokacin,
A hankali na mika hannu na nafara balle mai bottom din farar jallabiyar dake saye a jikin shi,
Ido ya zuba min ba tare da ya hanani ba har na gama cire mai gaba daya,
Na mike zuwa inda bathrobe din shi yake sagale na dauko mai farar kala,
Daga haka ya shiga wanka, jikinbshi duk ba kwari,
Kafin ya fito daga wankan nadan kara gyara jikina tsab ta yadda ba zaiga wani makusa a gare ni ba,
Yana zaune saman dan stol agaban mirror dakin shi yayin da na karaso a hankali na fara mulke mai jiki da man shafi da turare ta ko ina yada ya dace,
Ni kaina yau naga karfin halina da rashin kunya yadda na rufe idona nake mai abu tankar wata gogagiya can,
A daidai tsakiyan kan shi nadan tsayar da hannuna ina mashi massage din kan shi a hankali,
Yayin da yadan fara lumshe idanuwan shi da suka riga suka rikide ko, suka ja jajir da su,
A take naga jikin shi ya dan fara rawa takar wanda yasha wani irin tsimi
Sannu a hankali na fara ai,watar mai, da,wasu abubuwa a sassan jikin shi, cikin amfani da iya sabon sallon da na koya gurin Anty,
Hakan ya saka shi mikamin wuka da nama na, in mallake abinda tunfarko ya ke mallaki na,
Cak ya dora ni saman cinyan shi inda shima yafara aiwatar min da nashi sabon sallon da a da can baya baya tsayawa gwada min ya iya,
Daga haka naji ya dauke ni zuwa saman gadon ya dire ni a tsakiyar gadon dan nusa kadan da Amir,
Lokaci mai tsawo muka dauka ni da shi a cikin wani irin yanayi daban zan ma iya kwatan shi a halin yanzu ba,
Sosai ya samu natsuwan da ya dade rabonshi da samun irin shi daga gareni,
Inda ya dan kyaleni badon yasabo sai don ganin yaron dake barci daga gefe na ya dan motsa,
Wuf na tashi na fada bathroom badon komai ba sai don gudun kada yaron ya farka na bashi nono da najasa a jikina abinda akace yana kawo hinjirewan yaro idan ya girma,
Na ko samay shi rungumay, a hannun Yayana yana dan lalashin shi a hankali,
Nakarbi yaron shima ya shiga don ya gyara nashi jikin kafin ya kwanta,

****** ********** ******
A haka rayuwa ta ke ci gaba a gidan mu yau dadi gobe wuya har zuwa lokacin da ya shirya sallaman Su Dije da Mama Sa,a wa yanda ya barsu don su dan huta duk da yawan aiken da malam ke yi mashi,
Amma yace ba zata dawo ba sai yaro yai kwari sosai,
Duk abubuwan da Yaya ya sayo muna a tafiyan da yayi sun iso lafiya, har ya tafi Lagos yai clearing an sako a mota zuwa gida,
Sam dukkan mu ba mu da labarin hakan saboda, sai da kayan suka iso gare mu,
Ina wankin kayan yarana a laundry tare da dan gyara gura rai da safe lokacin ne kiran wayan shi ya shigo min,
Nai mamaki da wanan kiran don nasan cewa yana a cikin gida a lokacin ga kuma kiran wayan shi yashigo min,
Ina goye da Amir a baya na na bar Aisha a gurin Baba Ramatu suna hira tana aiki,
A falon mu na samay shi shida Anty sadiya sai Fatima wace a kusan tare muka shigo da ita,
Salawatu ce tai karshen fitowa da alaman daga barci take a lokacin,,
Gaba dayan mu mun samu guri kamar yadda ya umurce da yi saidai nice dake da goyo nake daga tsaye ta bayan kushin ina dan jijiga yaron a hankali,
Yai dan gyaran muryan shi a hankali abinda ya kara samu natsuwa ke nan don jin may zaice,
Daya bayan daya yakalle mu yafara da Sadiya yace,
Da mukai waya dake ina kasar Hong Kong watackalar mota kikace na zaba,
Sai a lokacin ne zancen ya fara dawo muna a zuciyar mu cewa mun taba irin wana zancen ai,
A hankali Sadiya tace mai fara nace maka kazabo, yace good,
Ya juyo gurin da nake tsaye yace wace kalla kikace na zaba nace a takaice baka,
Inda Salawatu take zaune ya duba ta dan bata rai yace wani kala tace Assh, sai ya juya gurin Fatima yace, kefa fuskan ta tankar zatai kuka saboda bacin rai don tana ganin ai tozarci ne ace har da Meenatu tana gaban ta ga komai yanzu a gidan nan, saida yakara tambayan ta da cewa Ehhey ?
Saida ta hade wasu yawu tace, da kyat, Ja nace ma yace good masha Allahu
Yace anjima zuwa rana zaku ga motocin ku sun iso kowa kalan nata zata dauka, don ita ta zabi abinta da kanta,,
A take fuskan kowar mu ya washe don murna, sai muka fara godiya muna cewa mun, gode mai cewa Allah ya saka da alheri Allah ya kara sabon budi,ta hanyar alheri,,
Nan aka shiga buga waya ana fadawa yan uwa da abokan arziki abin arziki ya samay mu,
Mutum na farko da na fara kira shine mahaifina tare da mahaifiya na,
Sai uncle dina da ?nty Amarya, tunda nasan cewa yau weekend ne kowan su na gida, lokacin,
Murna nake tasha inda na kira Yayana Ibrahim na sheda mai ya taya ni murna tare da godewa Allah ubangiji wata,ala,
Motaci sun iso lafiya inda kowacen mu tafita waje don taga zabinta,
Motace ta gani tafada, ta yayin irin ta zamani na mata aka sayo muna
Duk wanda yaga wanan motocin sai yai mamaki yadda akayi ya iya saya muna mu dukka,,
Sai ranan ya bawa kowa, sarkan gold daya saya muna, haba wata sabuwar murna takara tashi, ga kuma wasu kayan amfani foreign once da ya sayo muna, masu kyau,
Kowa sai mamakin irin yadda Allah ya daukaka Yaya Abubakar a lokaci guda saboda kwazon shi,
A folona mun saka kayan a gaba muna kallo nida Ramatu da Aisha su Baba Wadda suka shigo folon sundawo daga gurin dana motoci,
Baba Hamza wanda ya zube a saman kujera a folo na yana cewa wallahi Diyata kin iya zabe duk wanda yazo yaga motocin nan naki kwai ake zance,
Ina kokarin aje kayan da na kwaso agurin shanya nake cewa kai Baba na kodai kana yabon na diyar kane,,
Yace No wallahi ba hakana bane duk wanda yazo sai kiji yana yaba kyaun motar taki wallahi,
Nace to Allah ya sa mu more ma abin mu shi kuma Allah ya kara mai budi ta hanyotin Alheri suka karba min da cewa Ameen,
Nan mu ka zauna da su suna cin abinci muna hira dasu acikin farin ciki,
Baba Wadda yake kara, fada min irin na,sarorin da wannan tafiyan ya jawo wa Yayan Abubakar,
Shiru nayi a zahiri ina sauraren shi amma a can cikin zuciya na sai tunane nakeyi yadda zan shawo kan Yaya Abubakar ya taimakawa yan uwan mu a gida,
Dabara tafado min don haka sai na bar zance har in ina da duty sai na gabatar mai da ita,
Sai har koki aketayi acikin gidan kowana abinda ke a gaban sa duk kwanakin nan,

****** ********** ******
Bayan nagama aiyukana na kammala komai na koma part dina nakara gyarawa,
Don ni abadan bana son ganin kazata a gidan mace ko kadan saboda na tashi ina ganin irin yadda, mamana take da mugun tsabta duk da ban kaita ba,,
Kamar kullun suna folo zaune ana zaman saka ido da kyashin juna wai zaman hada kai,
Salawatu wace dawowanta kenan daga yawon zuwa gwada wa yan uwa mota tana bashi labarin abinda aka fada, agurin nuna motan,,
Na fito dauke da, kayan da zan tafi da su danki Yayana inda na gan su zaune a falo nai tankar bangan su ba,
Don ni izuwa yanzu ban son wanan zaman saboda na fahinci zamane na sake magana,
Idan ance ba,a ganni ba nakan ce saboda Amir baya son sanyi da yawa yana mura, yasa na daina fitowa akai,akai,
Ina tako guda guda inda duk idanuwan su yadawo zuwa gareni ina saye da dogon rigan larabawan Egypt,
Daga gurin da suke ina iya gane irin kallon da Yayana yai min,
Ashe idon Fatima wace tankar tana magana da diyarta idon ta na akan mu, kishi sosai ya baiyyana saidai a zaton ta ba,a fahince ta ba,
Murmushi mai alamar signal na sake mai tare da ci gaba da tafiyana,
Na dauko Amir na kwanta ban wani dade ba sosai sai gashi ya shigi dakin,
Ya samay ni ina waya da wata course mate dina tana fada min cewa, result ya fito,
Har ya shiga wanka ban gama wayan ba saidai kafin yafito mun kashe wayan,
Tea na dan hada mai duk da tea din ba wani mai yawa bane acan kasan cup ne sai dai yana kara mai lafiya irin ta maza,
Ta bayana najishi ya rungumoni sanyi da jikin shi ke dashi gami da reaction din da naji yasani sauke ajiyan zuciya,, a hankali,
Nace mai kafito yace eh Sweet sister may ki ke yine nace a hankali, shayin ka nake hada ma,,
Ok kawai yace
Yasakeni ya nufi gaban mirror din shi yana goga roll,on a jikin shi,
Yace ban san ya zamuyi ba zancen tafiyanki saudiya ga Amir bai kai lokacin yayye ba
Najuyo nai har da idona cikin sigar jan hankali, nace ai idan Allah ya bashi kafa zuwa lokacin sai kawai in yayye shi in tafi,,
Yadan yi jim kamar yana tunane sai can yake cewa amma kina ganin hakan bazai zama mai matsala ba ko ?
Na ce insha Allahu babu abinda zai samay shi a lokacin ai mutane da yawa suna barin yara su tafi, su sauke farali,
Yace Good Allah ya gwada muna lokaci dake da Fatima zaku tafi.
Allah ya kaimu kawai na iya furtawa,
Sai da na kai bakin gado na juyo ina cewa amma akwai masu zuwa acan gida ko ?
Ya zubo min ido kamar mai nazari can yace dafa cikin su Baba musa nake son wasu su tafi harda, Mama Sa,a saboda Baba ya rokeni hakan,
Saidai ban son Mama ta san zanen don gudun fitina,
Nace Yaya dama ina son in maka tuni akan zancen su babadin nace amma yakama su a aika masu da wani abin alheri don su shedacewa kasamu wanan cigaban haka,
Murmushi yasake min yana cewa dama nasan da wanan zancen ban tsan manin har akai war haka baki min zancen ba,
Yace na san cewa duk zancen ki ke akan mutanen gidane yake,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[11/18, 9:19 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL A'FUW


Zaune yarinyar take tayi tagumi da hannu biyun ta, ita ka dai a makaranta babu kowa sai maigadin makaran ta
Tayi kuka har tagaji dan abincin ta ya kare, ba ruwa, a goran ruwan ta, saima maigadine ya dan saya mata ruwan leda, tasha,
Daga gurin kitso duk da nasan cewa Aisha ta dawo amma hankalina yana gurinta don ban taba fita nabar ta ba ita kadai duk inda zamu tafi tare muke, da ita,
Duk da na dawo ina jin yunwa amma da ihun kiran sunan Aisha nakeyi,
Yaya Abubakar yana zaune yana waya nai sallama na wuce part dina cikin kiran yarinyar,
Ramatu tafito hankali a tashe tana cewa Hajiya ai Aisha, bata dawo ina ce ko, kuna tare ne,
Gabana ya ba da dam dam yar mutane tun safe bata dawo ba har zuwa yanzu karfe shidda da rabi na yamma,
Yaron na mika mata da sauri na juya ina cewa na shiga uku ni Meenatu, ina yar mutane ta shiga yau,
A folo na samu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login