Showing 279001 words to 282000 words out of 388021 words

Chapter 94 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8281

tokan da farko zaki ji test din bakin ki yadawo normal,
Sai kuma kiga duk wani dan ciwon mara da sayran jinin da zai tsaya yana dan wahal dake ya fita a lokaci guda,
Kafin wani lokaci jini ya dauke har kin fara sallah abinki, don wata sai kiga ta dade tana fitar da jini batare da ya dauke ba,

Wayana dake saman wani tsohon carvert din dake dakin Mama Dije yai kara na ce a miko min don Allah,
Yaya Abubakar ne saura kiris kiran ya katse na dauka ina cewa salamu alaikum,
A dan hasale naji ya karba min yana cewa ina kika tafi waya yana ta ringin,
Murmushi nayi kawai nace ina dan nesa kadan da wayan ne shi yasa,
Yace Ok to ya kuke ya mutane gida nace mai Alhamdullahi duk lafiya muke
Yace ya Bab, na ina fatan yana lafiya dai ko ba matsala,
Azatona yasan da zancen haihuwan ban san cewa anyi ta kiranshi ba,a samu layin shi ba switch off, suna meeting da bakin su lokacin,
Budewan shi ke nan ya kira layi na don yaji lafiyan mu saboda ya gaza hakkuri yau sai yaji muryana,
Azatona yasan da zancen haihuwan don haka nace maiGashi kwance ya sha ruwan zafi yana barci,
Tambayana yayi da mamaki cewa shi wa yasha ruwan zafi yake barci ?
Nace ba Baby kake tambaya ba gashi mama Abu tai masa wanka yanzu,
A hankali cikin wani irin murya ya ce kin haihune Meenatu ?
Nace na haihu mana dazun yaya ba a fada maka bane ?
Please Meenat ban son jork fa don kin rainani da yawa na mikawa Mama Sa,a waya ina cewa ga Yaya Abubakar ku gaisai Mama,
Mama ta karbi wayan da farin cikin ta tana cewa mai sunan malam barkan mu da arziki fa,
Ga maigida nan kwance yana gaisheka tare da yi maka bangajiya,
Tace ya sauran iyalinka duk suna lafiya ko muna gaida su don Allah idan suna kusa, duk a cikin murna da jin dadi take magana da,shi sai kuma hayaniyar mutane da yake iya jiyowa a wayan,
Mamaki ne ko murna suka rufe Yaya Abubakar alokaci guda ya kasa furta komai,
Dif ya kashe wayan donji yake tankar kunnuwar shi ba daidai suke ba ,
Hamdallah ya farayi ga Ubangijin talikai wanda ya azurta shi da wanan kyautan ta girma a duniya da lahira,
Duk wanda aka azurta da zuri,a ya godewa Allah ubangijin talikai, don ba karamin arziki bane Allah ya azurtaka da samun zuria,
Idan Alkah ya baka mai albarka yafi abarka da duk dukiyan duniyan nan,
Kashe wayan shi da tunanen shi yai daidai da bugo wayan malam tsoho a lokacin

****** ********** ******
Sungaisai da malam acikin girmamawa kamar kullun, ida malam din ke tambayan shi lafiya wayan shi a kashe haka yau, ?
Murmushi yayi duk da yana kokarin tausa zuciyar shi a lokacin,
Malam, ya ci gaba da cewa na bugo wayane in maka albishir din mun samu karuwa yau din nan da marancen nan mun samu Da namiji lafiyayye dashi kyakkyawa kamar uban sa,
Ma,ana dai matarka Meenatu Allah ya sauketa yai din nan ta haihu lafiya, yaron ma lafiya yake,
Alhamdullahi ya furta a fili, tare da cewa malam cikin da kidimay wa Meenatun dai tana lafiya ko ita da baby ?
Malam yace lafiya kalau suke don har sun huta yanzu nabar su a kwance dakin, Dije,
Wani irin nauyayyen ajiyan zuciya, Yaya Abubakar ya sauke yayin da yaji abinda malam tsoho yace mai,
Yace malam Allah ya raya muna Mohammed Buhari,
Malam yace Ameen ya Allah, takwarana sunan da kake son saka mashi ke nan yace eh malam domin nima na rama irin karan da akai min a baya aka saka min sunan ka,
Murmushi malam tsoho yayi don jin dadin abinda jikan nashi ya aiwatar akan mahaifin shi,
Amna don Alkah malam gobe idan Allah ya kai mu ayi kokari akai su asibiti don a duba lafiyan su,
Cikin wasan jika da kaka malam ke cewa kai bature bayan an haihu a gida lafiya may zai sa kuma ace za,a tafi asibiti a yanzun, ?
Malam tsoho yai gyaran murya don jin Yaya Abubakar yai shiru alaman yaji kunya zancen
Malam tsoho, Ya ce ai ina da niyan hakan mai suna, na dama dole ne mu kaisu don ai masu yan rigakafi insha Allah,
Yaya Abubakar ne ya katse zancen da cewa malam zan kiraka anjima domin an fara kiran sallah magrib anan yanzu haka
Ikon Allah inji malam yace muko kaga anan akwai sauran lokaci sosai kafin sallah,
Yaya Abubakar yace malam idan na koma gida zan kiraka anjima insha Allah
Sun rabu a cikin jin dadi da annashuwa saboda ko wanin su a cike yake fam da farinciki,
Suna gama sallama da malam tsoho dan tsohon yai farin ciki sosai da jikan shi ya kasance daga cikin irin diyan da ko wani gida a ke alfaharin samun irin, su,a duniya,
Don haka a take malam ya fara aiwatar da matsayin shi na kaka a gare mu, don nuna farin cikin shi a gare mu baki daya,
A lokaci guda, yasa aka tsiyo min naman yar dakwalwar kaza gassassa mai zafi ga,, yaji sai kamshi ya keyi,
Ina barcin gajiya a lokacin don haka Mama Dije tace abar ni har na tashi sai naci,
Jama,a sai barka su ke ta faman shigowa cikin gidan malam yi don farin ciki,,

****** ********** ******
Kowacen su ta caba kwaliya kamar masu zuwa gurin gasar fitar da gwanan kyau,
Yanzu abinda suka gane shine kafin duk ace Yaya Abubakar ya fito duk kan su suna zaune kowace
sai ta shiga yin nata irin iyayin, don burgewa,
?nty Sadiya ce, wace bata damu da irin wanan abubuwan da sukeyi ba tankar za su maida mijin a ciki don so,
Yau ma kamar kullun Fatima ce tai nasara samun fitowa da wuri yau tana saye cikin wani Swiss lace mai shining, an,mai, wrapper mai kyau, dinkin shi half gown,
Don haka ta na fitowa ta samu, guri daidai gurin da maigidan zai zauna ta zauna kasancewan ita,ce da girki, a ranan,
Ba tafi ko da minti biyar ba da zama sai ga salawatu tafito cikin wasu material sky colour masu flowers farare, dinkin skirt da riga, kan,ta ya sha kitsoh attache, sai sheki ya keyi,,,
A hankali yake takowa daga matakalar benen wanda ya sha ties sai sheki yakeyi don goguwa,da yasha daga sabuwar yar aikin su, da take masu gyaran gida, ita da Ramatu,
Ganin shi tafe yasa ko wacen su ta fara dan kimkimtsawa cikin style, batare da yar uwa ta sani ba,,
Sannu da fitowa su,ke mai yayin da yake zama akan kujeran three seaters dake falon,
Sai amsa gaisuwan su yakeyi tare da dan yiwa kowacen su na ta jinjinan a cikin style irin na maza,
Fatima mai girki a ranan tafara gabatar mai da abinci tare da dan kashe murya tana cewa yallabai abinci fa yana jiranka, a dinning,
Bai tanka mata ba sai kokarin neman layin waya na ya keyi a lokacin sai dai wayan is switch off a lokacin
Dan guntun tsuki yasake tare da fara neman layin malam tsoho a lokacin,
Abinci fa yana dining nace maka Yallabai kada dare yayi, baka ci ba,
Ina zuwa mana yace ba tare da ya dago kanshi daga abinda ya keyi ba, a lokacin,
Sai ji su kayi ya fara cewa Hello malam barka da wuni yaya kuke, yakuma kaji da bakon ka, ?
Jin sunan wanda ya ambata a wayan yasa ko wanin su kiran malam tsoho da sunan da suke kiran shi dashi wai ya ishe su,
Anty Sadiya tafito jikinta saye da atamfan super wax mai ruwan brown colour yasha dinki mai aikin design din wuta a gaban rigan,,
Ta zauna tare da yar makalalan sallama dauke a bakinta tana cewa ka dawo,
Bai tankaba don waya ya keyi a lokacin saboda haka yake cewa a cikin waya,
Nakiran nombanta ban samay taba yanzun nan ko watan baya kusa da itane
Jin abinda yace yasa su gaba daya maida hankalin su gareshi saboda sun fahinci cewa akan mace yake zance,
Malam tsoho ya ce mai na shiga gurin su yanzun nan da na shigo na samu sunyi barci ko tun dazun,
Shidai, jaririn ne na samu idon shi biyu yana kallon kwan fitilla a sama,,
Hmm kawai Yaya Abubakar ya iya cewa don jin may malam tsoho yace mai a lokacin,
Ya tambaya da cewa, ita Meenatu babu abinda ke damun ta dai ko ?
Don kasab anan kafinta tafi tana da likitan da ke dubata duk da dai acan ma sokoton sunce tana zuwa asibiti check up,
Hakan yasa yazun ma da ta haihu nake son a duba lafiyan ta a gani idan babu matsala,
Malam ya ce insha Allah gobe da safe za,a kai su a duba lafiyan su din kamar yadda ya dace,
Gaba daya fuskokin su ya sauya izuwa mamaki don sambabu wace tai zaton cewa cikin jikin Meenatu ya isa haihuwa a lokacin
Yayin da zukatan su ya shiga wani rudani a lokaci guda kowace da irin abinda take kiyastawa a cikin rayuwan ta,
Yayin da hankali kwance maigidan yaci gaba da wayan shi batare da duban yanayin su ba,
Jin call na shigo mashine a lokacin yasa shi yin sallama da malam tsoho wanda, ke ta bashi labari a qaya,
Sai a lokacin da yake kokarin daukan kiran yaya Mustapha ne yake dan duban su yana cewa daidai face din Sadiya,
Meenatu ta haihu yau dazun nan da marance aka bugo min, waya ana fada min,
Bakin a tare Salawatu da Fatima gurin tambayan shi cewa mai ta haifa,
Tankar baiji su ba yaci gaba da wayan shi da dan uwan shi inda a cikin wayan ne suka fahinci cewa Meenatu fa Da namiji ta haifa,
Don sunji yana cewa dan uwa kagane Mustapha don Allah gobe a kaisu asibiti a tabbatar da cewa lafiyan ta da na yaron is normal,
Sai kuma cewan da yayi zankiraka Mustapha zuwa anjima akwai abinda nake son yau din nan kai min insha Allah,
Suna sallama da Yaya, Mustapha kiran yan uwa da abokan arziki ya fara shigowa daga wayan shi,
Wanda haka yasa shi daukan lokaci mai tsawo yana waya da jama,a a lokacin,
Sai da ya dan rarage Sadiya tana batun mikewa don ita har yanzu al,amarinta sai a hankali,
Yake cewa, idan Ramatu ta fito sai ki fada mata cewa, an haifu don taji, tafadawa matar Lawal, da sauran mutane,
Daga gurin da Fatima take zaune wani irin haushi da takaicin masoyin nata take ji yau watau saboda ya samu haihuwa shine zai mata haka
Duk lokacin ta data bata a gurin girka mashi abinci sai ya share ta haka sai faman waya ya keyi abin sa, yana annashuwar an mashi haihuwa abin shi,
Aikuwa yau zasu hadu don za ta gwada mai cewa ita fa mace ce maijan aji don bata daukan raini agaban kishiya ita
Muryan shi taji ya na cewa tea nake son sha yau kawai bazan iya cin abinci ba,
Da sauri a cikin mamaki Salawatu da tun dazun tai zaman suma a zaune ta dago kai ta dube shi a cikin mamakin jin yau ko abinci bazai iya ciba ,,
Tirkashi, ashe a kwai magana ke nan a gidan nan don, dole ta mike tsaye tasan abinyi kafin taga takaici,
Jaririn da aka haifa yau, yau shine har ya shiga ran maigidan haka tun ba akai ko ina ba baiga yaron ba, amma yake irin wanan dokin haka
Wata kilama baby ba wani kyau gani gare shi ba yake irin wanan haukan haka,
Kai amma dai abin da da mahaifi duk yadda yake zakaga ai baidamu ba aran shi,yana son abinshi hakana best solution shine, ita ma kawai ta turza ta samu ciki a gidan nan,
Zaune take sai tunane take tayi kala kala a gurin don abin ya bala,in girgiza mata zuciya ace wai har Meenatu tai ciki ta haihu haka, ?

****** ********** ******
Acikin barci wanda ban san lokacin da ya kwashe ni ba nake jin muryan Yaya Mustapha sama,sama suna magana da Mama Dije,
A hankali na bude idona sai nake jin muryan shi yana cewa ita Meenatu barci takeyi ne ?
Tace ai dole tayi barcin gajiya yau Allah ya sauketa lafiya, zama da ciki ba wasa bane,
Yace gashi ko Abubakar ya turo ni naiwa wanan yaron addu,a kamar yadda ya umurceni,
A hankali na kara bude idona nace cikin muryan mai sanyi ina wuni Yaya, ya amsa da cewa kin tashi Meena,
Barkan mu da arziki fa kuna dai lafiya ko bakya jin komai, na amsa a hankali da cewa Alhamdullahi yaya,
Daidai lokacin da ake mika mashi dan yake cewa tare dan juyowa gurin da nake kwance yana ce min,
Abubakar yace nazo nai ma yaron nan addu,a yau din nan kafin gobe hakan yasani shigowa yanzu,
Dan lumshe ido nayi tare da cewa kai haba Yaya ni ina ruwana da zancen ku,
Yayin da na juya na basu baya ida Yaya Mustapha ya fara yiwa yaron addu,a kamar haka,
( Huduban Bismillahi) Fatiha)
Bismillahi Rahamanin Rahim, Allahumma,inni as, aluka Bissirin fatihatu , wafalalu, li Fatihatu wabarkatu Fatihatu, wama anzawah Fatihatu, wama unzillatu, Alaihin Fatihatu, Ataftaha Alayya, Hairun Dunya wa la Lahiratun Innaka ala, kulli,Shain Kadir,,,,
Yana wanan adduan adaidai kunuwan dama na dan jaririn ta yadda nake iya jiyu shi daga gurin da nake a kwance,
Yana idarwa ya mikawa Mama Dije yaron yana cewa Allah ya raya muna yashirya muna yasa albarka duniya da lahira Allah yasa dadin musulmi ne,
Inajin Mama Dije tana cewa amin a lokacin da nima na karba da fadan amin din a cikin raina,
Yace wa Mama Dije idan Allah ya kaimu gobe zan dawo insha Allahu akwai abinda zanyi mai,
Yai muna sai da safe tare da dan taba barkwanci wa yan tsofin matan da ake wasan jika da su,
Yana fita abinda yafara fado min arai shine rabuwan mu na karshe da Yaya Abubakar inda cikin rikicin mu nake ce mai idan ma har wani abu yake so ai mai ai kamata yayi ya umurci Yaya Mustapha ko ya Suleiman k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o Ya Sa,adu duk diyan gidan mu ne kuma magidantane ba wai wani bare sabba ba can daban wai Aliyu,
Ina ganin shine dalilin da yasa yau ya umurci yaya Mustapha da yazo yaiwa yaron wanan adduan da kan shi,
Dan murmushi na sake a fuskana ina cewa, ai naka sai na gurin wuya don Aliyu da yake gani akwai inda bazai dace ace komai shi zai aiwatar ba akan mu,
Ko ada can bayama da babu aure a tsakanin shi da Fatima balle yanzu da take zaman kishiya a gare mu,
Don yasan cewa idan shi yaturo bazan yarda ba ya taba yaron nan irin yadda yake ganin take takena akan Aliyu,,
A take naji wani irin son mijina ya shigeni lokaci guda badon komai sai don duk irin shaaran da zan bashi idan har yai naziri yaga cewa ta alheri ce to zai bi wanan shawaran,
Gashi yau da kanshi ya umarci, Yaya Mustapha, dayazo yai wa dan shi huduba,
Mutumin da da can baya babu ko ga maciji a tsakanin su saboda akidan iyayyen su da suke bi zakace ba kaka guda ta haifi iyayyen su ba,
Ajiyan zuciya na sauke tare da yin hamdalla don ganin cewa wanan gaban dake a tsakanin iyayyen mu diyan su, sun fara kawar dashi,
A haka har barci ya kwashe ni ban sani ba said ai kuma zuwa dare can sai barci ya kauracewa idona ,,
Dole ina ganin Mama Dije wace taja dan jaririn a kusa da jikinta suna ta kwasan barci abinsu,,,

****** ********** ******
Muryan malam tsoho yadan fakal dani daga barcin da ya kwasheni da asubah,
Naji yana cewa Mama Dije yaya dare ya kuka kwana tace lafiya lau malam babu matsalan komai,
A raina nace, ai dole kice haka tunda ke kin samu barcin ki akalahe, babu ko farkawa,
Wanka nayi tun da dan sauran duhu acewan Mama Dije wai a wanan lokacin yafi dadi,
Bayan nafito na samu ankawo min kunu mai zafi a wani cup din silver sai suraci ya keyi,
Mama ce mai cewa ki kafa kai da sauri ki shanye wanan kunun dukka Meenatu,
Cikin sauri nadago kai na dubi kunun na dubeta ita ma wanan kunun mai yawa haka za,a ce wai na shaye shi dukka a cikina,
Ina saka riga na zauna a bakin yar kujeran dakin na dauki cup din kamar yaddaMama Sa,a ta umurce ni na kafa kai don tace min wai ba,a sha da ludayi, don zai yi sanyi,
Ina sha ina runtse idona tare da tausayin kaina da kaina gazafi ga dan yaji duk a bakina ina konewa, dole kuma nake daurewa ina ci gaba da sha, hakanan,
Ina gama shan kunu sai ga Mama Abudauke da wani kwanan silver sabo ta shigo dakin, sai faman sannu da aiki ake mata,
Tana cewa Mama Dije idan na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login