Showing 117001 words to 120000 words out of 388021 words

Chapter 40 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8268

sai washe gari da ta kawo masu, tea da breads kawai ba kwai ba Irish,
Tun shi bata kara lekosu ba,daga gidan su Fattu aka kawo masu abin kari lafiyyaye, suka ci,
Da rana Jeloup din macroni, ta dafa masu bai ko karasa dahuwa ba tsatsaye,
Suna ta zullumin yadda zasuci shine sai ga maman Bi,u da kan ta ta kawo masu abinci tuwon garin farar masa da miyar danyen kubewa,


ZEEE MAKAWA YELWA
[8/5, 9:41 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
4? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-AZEEM,,,,

Wanan irin wullakanci da tuzarci da Sadiya taima mahaifiyar shi da yan uwan shi,
Yasa yadan shiga wani halin tunane acikin kwanakin nan,
Kamar shi ace wai sai makwabta sun kawo abinci agidan shi,
Amma koda yake madadi Mama ke fuskanta,
Don ita ce ta hana shi auren wace yake so ta hada shi da Sadiya diyar kawarta,
A lokacin shi Fatima kaunar Aliyu abokin shi yake so da da ita yai soyayya sosai,
Amma sai mama tace madadin ya auri fatima wace boko ya ratsa ga Sadiya nan diyar aminiyar ta suyi auren su na rufin asiri,
Alokacin abinda yasa ya yarda yana gudun irin tozarcin da mahaifiyar shi zata shiga ne,
Ga Fatima yanzu inda take aure yaran ta biyu kuma ta zama yar business sosai,
Tsuki ya ja tare da cewa Sadiya, Sadiya why please ?
Kin zama min kayan kafa, babu inda nake jin daman ki,
Wayan shi dake gefen side drower din shi ya jawo,,
Noban Babana Samaila ya ke nema, yakira shi don ya san abin da yake ciki,
Kira na uku Baba Samaila ya dauki wayan, tare da sallama wa dan shi surikin shi,
Sun gaisa Baba Samaila ya ke tambayan, jikin Mama Ladi,?
Inda yake sheda mashi cewa jiki Alhamdullahi da sauki sosai don har sun sami sallama
Yana son sai jikin nata ya kara samun sauki ne su, dawo gida,
Madallah madallah Alhamdullahi Allah ya tsare gaba inji Baba Samaila,
Dan shirune ya biyo bayan zancen su sai shi yaya Abubakar din ya dan kau, da shirun ta cewa,
Baba dama akan zancen auren da zankara da mukayi ne yasa na bugo maka waya,
Duk da Baba na yaji wani iri acikin ran shi amma sai yadaure yana cewa, to, to, to,
Zance ya taso ke nan dai ko ya Abubakar ya amsa da cewa eh Baba, don dama na ce bayan Wata biyu da auren Meenatu zan yi wanan din,
Yanzu ga shi har ankusa ma wata biyar da auren meenat din,,
To ba matsala zan yi magana da malam dashi yaya Buhari akan zancen,
In yaso sai inkiraka asa lokaci ko?
Tau Baba na gode da wanan kokarin nagode kwarai,
A, a aiba damuwa yiwa kai ne hakan ai,

****** ********* ******
Bayan gama wayan su Baba na yakai wani lokaci tsaye bakin motar shi yana tunane,
Ya tausayawa Meenatu sosai, yarinya karama kamar Meenatu tashiga cikin manyan mata haka,?
A zaton shi yadda yaga ya karbi auren Meenatu yana zaton Abubakar din ya janye zancen auren shi da waccen yar barikin ne ai,
Amma sai gashi yanzu gatsau ya tayar da zance idan har bai bashi goyon baya ba sai ace saboda yana auren yarshi ne bai son yayi auren,
Amma shi gaskiya bai so ace Abubakar ya auri wanan irin mace ba gaskiya,

Malam tsoho bayan ya gama sauren bayanin Baba, Samaila,
Sai faman girgiza kai ya keyi, yana cewa,hmmm, hmmm kaiyya,
Ta yaro kyau takai bata karko, amma bai kamata ace wanan halarcin da yai mashi kuma yanzu ya watsa masu kasa a ido ba,
Ganin cewa malam zai hana zancen yasa Baba Samaila ba malam hakkuri akan ya bari ayi auren don kada su aikata sabo a dalilin hanasu yin auren,
Yace kaga baba inda Abubakar mazinacine bazai kawo zancen aure ba sai dai suyi ta zaman banza a waje kawai,
Amma tun,da yana son ta aduk yadda take abari kawai, suyi auren su zai fi,,
Badon malam tsoho yaso ba ya yarda da zancen karin auren yaya Abubakar wanda za,a yi a karshen wata lokacin ina batun fara exam ke nan,

****** ********* ******
Bayan sallah isha,i malam tsoho ne ya kira yaya Abubakar da kan shi a wayan shi sabanin yaya Abubakar ne mai kiranshi su gaisa dama,
Ganin mai kiran nashi yasa shi dan tsayawa gefen hanya don ya karba kiran,
Bayan sallama da gaisawa, sai kuma yar shiru,
Ga irin yadda yaji yanayi muryan malam sai yake jin badadi ba a rayuwar shi,
Malam tsoho ne ya fara cewa, Abubakar, ina son in kara jaddada maka cewa Amanan yarinyar ga Aminatu na baka,
Ko bayan raina ka cuta mata bazan yafe maka ba Abubakar,,
Wani irin abu yaji azuciyar shi, tare da mutuwan gabban jikin shi,
Tunda yake da malam tsoho maganan bacin rai bai taba shiga tsakanin su ba sai wanan zancen,
Kafin yayi yunkurin yin wani magana sai yaji malam tsoho ya kashe wayan shi dif,
A jiyan zuviya ya sauke tare da share gumin da ya dan feso mai a goshi da bayan hannun shi,,
Ci gaba yayi da tukin motar shi sai dai hankalin shi duk a tashe yake,
Gab da zai shiga get din gidan shine kiran wayana ya shigo mashi,
Meenatu ya furta sunan a hankali, tare da tunanen zancen ne zan mashi,
Ya dauka da Sallama tare da sauke numfashi, murya na babu fushi acikin ta ko sarkewa,
Hakan yasa shi dan sake jiki yana tambayana ya nake,ya karatu, ya mutanen gida,
Na bashi amsa cikin lumshe idona dan jin dadin muryan shi dana yi da fadin lafiya kalau,
Tambayan jikin Mama Ladi nayi inda ya ke ce min ta samu lafiya sosai,
Sai kuma yaje gamba ana da ba matsalan komai dai ko ?
Na bashi ansa da fadin babu komai yaya,
Murmushi naji yayi kawai tare da cewa fadi dai gaskiya yar kauna,ta
Murmushi mai hade da dariya na sakar mashi tare da cewa Lah yaya gaskiya babu komai,
Yace kedai kodai inzo in dauke ki ne ?
Yaya ni da zan fara exam ina zani kuma, haka?
Ai, to ba yanzu zaki fara exam din ba kibari kawai inzo in dauke ki kizo ki kwana muna biyu ko na ce a,a yaya sai munyi hutu dai, to kidai yi shawara zan kiraki inji may kika yan,ke akai?
Da haka mu ka yi sallama dashi kamar kada mu rabu da junan mu,,
Kafin in kashe wayan ina ta jin wani kira yana shigo min,
Sai da na kashe sai naga ashe malam tsohone, ke kirana,
Da sauri na kara kiran shi sai dai zuciya ta na cike da mamakin kiranshi a wanan lokacin,,
Mungaisa acikin girmamawa kamar kullun, ina sauraren shi,
Sai na ji muryan shi yana kiran suna na yana cewa Meenatu ki saurare ni da kyau ki ji abinda zan fada maki,,
Kara natsuwa nayi guri guda don sauraren shi kamar yadda ya umurce ni da yi,
A lokacin ne kuma sai ga Anty Amarya ta shigo dakin namu dauke da bakar leda,
A cikin sa kayan tsaraban dare da Uncle ka siyo muna, kamar meat, chicking pepping, snacks drinks da sauran su,
Ganin irin yanayin da nake ya sa ta tsayawa batai magana ba,
Hand's free na wayan nasa don muji a tare don babu abinda zan boyewa Anty amarya na rayuwa na,
Matar da take tsaye akan al,amari tankar ciki guda muka fito da ita,
Malam tsoho yafara da kiran sunana da cewa Amina,
Na,ansa da na,am malam yace kiyi hakkuri kinji ?
Duk abinda kika gani a rayuwan bawa jarrabawa ne daga Allah,
Don komai,mukaddari don haka ina son wanan auren da ki kaga mijin ku zai yi ban son ko kadan ki tayar da hankalin ki,
Wani irin faduwan gaba naji ya ziyarce ni a lokacin amma sai kawai na daure na ci gaba da sauraren tsohon,
Malam ya ce sai gaba zai gane dalilin hadin auren ku da nayi,
Bama shi kadai ba har kowa dake gidan nan gaba daya koda a lokacin bana a raye nasan za a fada, insha Allah,
Idona da suka sauya zuwa ja na daga na kalli Anty amarya wace ke tsaye muna sauraro,
Kai ta kada min alamar kada inyi kuka na daure nace malam na gode insha Allah bazanyi komai ba,
Ya ce to Allah yai maki albarka ya baku zuri,a dayyaba,
Wanan ban iya ansawa afili ba sai nai shiru, malam ya ci gaba da cewa,
Abarshi kawai yayi auren yaji abinda ke nan ga Wadda ya bugo waya yana fada min irin wullakancin da Ladi ke gani gurin ita wanan matar tashi dake gida,
Yace ba ta ba su abinci sai dai ansayo masu ko kuma akawo masu daga makwabta,
Daga idona nayi mu ka hada ido muna kallon junan ni da ita,
Sai muka kadawa junan mu kai alaman, tooo,pa,
Malam yaci gaba da cewa,
Shine zai kara jajibowa kan shi wani auren wahala kuma,,
Munyi shiru, muna ta sauraren nasihan tsohon har yai muna sallama na kashe wayan,
Lokaci guda, muka numfasa ni da Anty Amarya tare da kallon juna,
Anty Amarya tace ashe shi har yanzu bai fasa zancen auren ba ke nan,?
Kada kisawa kan ki damuwar komai kowa tashi tafisshe shi kawai,
Don haka ban son jin kin yi wani fitina a,kai ki,bari zamu tafi gida wurin Hajiya Mama muji may za tace, (Hajiya mama mahaifiyar su Anty,)
To na amsa mata da shi tare da cewa nagode Anty,
Ledan da tashigo min dashi na kayan tsaraban Uncle dina ta miko min tana cewa bari taje ta kwaso yara falo don kila sunyi barci,
Fitan Anty banbi ta kan ledan ba na kwanta saman katifa na zuciya na duk ya cakushe min wuri guda,
Tunane na keyi yaya zan zauna a tsakiyan wa yan nan manya matan, da suka ma kusa haihuwana,
A haka barci yai gaba dani batare da nakara koda motsawa ba,
Sai cikin dare na dan farka sai dai tunanen bai yi wani tasiri ba na koma barcin,

****** ********* ******
Baba Samaila da su Baba Musa da sauran jama,a suka tafi don nemawa dan su aure acan wani kauye cikin NASAWA STATE,
Sai dai suna zuwa sai iyayyen Salawatu sukace sai dai a tsaya a daura aure gaba daya,
Hakan akayi inda Baba na Samaila ya ba da dubu hamsin sadakin auren kamar yadda suka yanke masu,
Sai daga bayane aka kawo zancen kayan lefe, amarya,
Baba Musa yace ai mungaya maku cewa neman aure mukazo ba daurewa ba kuka ce, a daura,
Yanzu wanan ya rage a tsakanin, su shi da matar shi,
Iyayyen Salawatu sun yake cewa Sati biyu tarewa don haka, sai a shirya,

Sai bayan su Baba sun dawo ne suke sheda masu yadda abin ya kaya a can, garin,
Duk suna zaune a falo har Mama Ladi, suna sauraren abinda suke fadi,
Mama Ladi tace ai dole su yi gagawan daura auren, don kar a ce anfasa,
Amma ta yaya tana zaune a cikin gida zai daira aure bada sanin ta ba,
Matar shima batada labarin auren sai kawai aji daga sama,
To kiyi hakkuri Ladi haka Allah ya nufi ayi auren ba shiri,
Ta ce tunda ya maryar da kan shi wanda bai daukan shawara ba,
In ba shi ba dan may zai ce haka zaita aure ba da sanin ta ba,,
Daga can baya Baba Musa yace to ai yanzu Ladi sai kiyi yadda zakiyi don mu samu akayi mun kuma aiwatar, don haka zance ya saura gare ki,
Dakike cewa haka ita Meenatu ba matar shi bace,
Wazo daurin auren ba mahaifin ta ba, ni wallahi irin rayuwan nan naki na jahilci shiyasa bazan taba shiri da ke ba,
Dariya sauran mutanen gurin suka sa masu don sanin cewa sun saba wanan badakalar a tsakanin su dama,
Su Baba basu tsatsaya ba washegari suka juyo zuwa Kebbi, abin su
Baba Wadda yaso ya biyo su, su dawo amma yaya Abubakar, yace yadan dakata su dawo tare dasu Mama Ladi,
Badon yaso ba yana gani suka juyo abin su zuwa gida,

****** ********* ******
?nty Amarya ce bayan nadawo school take sheda min cewa har andaura auren yaya Abubakar da Salawatu,
Duk labarin bai min dadi ba amma sai kawai na dake a zuciya na,
A fili cewa nayi tau, Allah bada zaman lafiya, yasa ace gwanma da akayi,
Wanka na shiga tare da dauro alwalan Sallah la,asar,
Nakai wani lokaci zaune a gurin tun ina addu,a har na koma tunane,
Irin halin rayuwan da zan yi cikin manyan mata yar karama dani,
Yanzu duk irin zumudin da idan muna tare da yaya Abubakar yake nuna min ashe halin mazane,
Shiko dai don an bashi ni ne yasa zai min haka ?
Aure da wata hudu yace zai auro wata baya na, may narage shi dashi kamar yadda ake ta min nasiha akai,
Wasu irin hawayen bakin ciki da takaici ne naji sun silalo daga cikin idona zuwa kumatuna, duk sun wanke min fuska,
Waya na dake saman mirror dakin mu tana chaji naji tana kukan neman agaji,
Hannu na mika a hankali na dauko wayan sunan, yaya Abubakar ne na gani jikin wayan,
Ina kallon wayan har tagama ringing din ta tagaji ta katse don kanta, ban dauka ba,
Kira uku ban daga ba har ya gaji naji ya daina kiran nawa,
Daga karshs ma sai na kashe wayan gaba daya ta yadda ko ankira baza,a samay ni ba,
Mikewa nayi na fara shirin kwanciya duk da dai nasan cewa ba barcin zanyi ba amma sai nake ga kwancin yafi min a lokacin,,,
Anty Amarya ce ta shigo dakin tun daga kofa ta hangoni a kwance fuskana yana kallon rufin dakin,
Muryan Anty naji tana cewa, Meenatu badai damuwa kikasa a ranki ba haka ko ?
Murmushi na kirkiro a fuskana na dole, badon naso yin sa ba,
Gefena tasamu tazauna tana ce min, Meenatu ban son kisa damuwa ga al,amarin mazan zamani,
Duk namiji idan yana son aure, baijin has azamanin nan da muke a ciki,
Sai fa idan sunyi sun ji abinda ke nan, sanan hankali su ya kwanta su fara neman hanyar ceto,
Don haka tunda kikaga har iyayyen ku basu iya hana shi wanan auren ba ki sa masa ido, kawai kamar yadda na fada maki da farko,
Ke dai kawai ki rike mutuncin ki da kuma ibada kina kai kukan ki ga Allah,
Saboda haka idan ya kira ki dauka kar ki kara share ahi don Allah ,
Kyale shi ai shima yasan bai yi daidai ba tunda bai sanar da ke ba akai,
Ido na dago ina kallon ta yadda har tasan cewa ban dauki wayar shi ba,
Anty Amarya tace, yanzu ya bugo waya yana tambarya Uncle din ki ke wai ya kira baki daga waya ba,
Shine nake ce masu kin kewaya ne shi yasa isan kin fito zan fada maki cewa ya bugo,

****** ********* ******
Yaya Abubakar da yaga cewa yai kira uku ban dauki wayan ba yasa shi dan yi murmshi don yasan cewa yayi laifi, sosai, tunda har ba,a daga mashi wayan shi, ba yau,,
Don haka sai ya kira nomban Uncle dina don su gaisai kuma ya tambaya ko ina lafiya,
A lokacin Anty Amarya tana kusa da Uncle dina shinw take fada masu cewa, ai ina bandaki ne a lokacin,
Sai yake cewa Uncle ayi hakkuri fa auren ne nasa yazo mashi ba shiri,
Sundan taba hira da Uncle dina sanan sukayi sallama ya kashe wayan,
Shiru yadan yi tare da lumshe idon shi don yasan cewa kawai an dai kareni ne kawai,
Amma ina cikin fushi ne kawai irin na mata, murmushi ya dan yi kawai don yasan cewa sai kana son mutum kake kishin sa,
Wayan Salawatu ne daya shigo a lokacin ya katse shi ,,
Acikin wani irin muryan shagwaba take mai magana yau,
Sundauki lokaci mai tsawo suna hiran irin ta masoya,

Washegari koda ya shiga office mutane sai murna suke mashi cewa Ango Ango,
Shiko sai murmushi ya keyi baki yaki rufuwa sai nagode yake cewa jama,a kawai,
Yau, Salawatu shigan zani da riga tayi na atamfa, zuwa office din nasu,
Sai wani gyale mai shara,shara da ta yafa akanta har zuwa rabin kirjin ta,
Ita a ganin ta ,tarufe jikin ta ke nan,a hakan ta yi shigan matan aure,
Sai da tafara zuwa office din su suka gaisa da mutane suna ta mata, murna da fatan alheri,
Sai, nagode nagode take cewa da kuma Allahuma Ameen,
Acikin wani irin jin dadi ta isa office din maigidan nata,
Yana zaune aiki yai mai yawa yana kokarin tura sakonni,
Yaji an turo kofan shiga office din shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login