Showing 102001 words to 105000 words out of 388021 words

Chapter 35 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8254

?
Gani yayana Ibrahim nayi acikin a lokacin da nake raraba ido inga Baba na, daga cikin su,
Murna sosai nayi tare da kasa boye farin cikina a fili,
Abinsha dana tanadar masu agaban su sun fara dauka Anty Sadiya wace, yaya Abubakar ya taso agaba tafito falon cikin yar sakin fuska, tana cewa,
A,Baba kune tafe ashe ?
Sannun ku da zuwa ?
Nan suka shiga gaisawa da su tare da mata ya kwana biyu,
Abokin tafiyan su Baba makwabcin mu da malam ya turo tare da su ne ke cewa,
Abubakar munyi murna munyi farin ciki da wanan karin girma da a,kasamu Allah ya kara daukaka ,
Sai sauran su Baba su ma suka dauka kowa da abinda yake cewa gurin iyin addu,an shi,
Gani su babane zallah yaya na Ibrahim ne kawai yaro yasani cewa barin kai mashi abinci daki na,

****** ********* ******
Zaune a dakina tare da dan uwana yana cin abinci,
Sai kallon mamaki yake min a lokacin ya na cewa Meena kega yadda kinka koma kuwa,
Murmushi nayi ina tsiyaya mashi lemo a cup, nace kai haba ya Ibrahim har yaushe nabar ku dazaka wani ce na canza,
Tambayan shi labarin kowa agidan mu nayi tundai mamana da Baba na sai malam tsoho,
Nan yaje sheda min yadda malam tsoho ya dage da cewa sai anzo dashi, dole don ya dubu ma shi ni,,
Yaya Abubakar ne ya shivo dakin yana waya kuma hankali na gare mu,
Da hannu yai min alamar inzo, nadan taso da sauri zuwa kiran da yai min,
A bakin kofa ya tsaya ni kuma ina daga cikin labulen dakin na dan daga labulen fuskana yana facing din shi,
Ya Ibrahim daga cikin daki sai mamaki yakeyi haka kuma su baba su da wutsiyan ido suke satan kallon mu,
Tambaya na yaya Abubakar keyi wai yaron nan da yaga ina aike hamza yaken son suje su diba masauki, tare,
Nace O,Babana Hamza batin ce Fattu ta turo min shi,
A waya na fada mata cewa ta turo shi inji yaya Abubakar,
Ba bata lokaci ya zo ya samay shi suka fita tare, zuwa wani masaukin baki mafi kusa,
Yayana Ibrahim tare da Baba Wadda suka bisu zuwa gurin don su ga gari da kyau duk da dai yamma ya yi a lokacin,
Sosai su Baba su kaji dadin wanan ziyaran da suka kawo muna,
Anty Sadiya itace da girki amma sai ta ki fitowa ta yi wani abu,
Har dare nake ta faman dawainiya dasu batare da gajiya ba,
Suko sai faman samin albarka sukeyi don jin dadi,
Bayan sun dawo daga sallah Isha,i ne ina dakina a lokacin,
Na gama gyara ko ina na gidan don haka na samu na gyara jiki, tsab,
Ajiyan zuciya na saukar a hankali ganin cewa na gama hada komai har zuwa abinda zan yi da safe gobe idan Allah yakai mu,
Jin shigowan yaya Abubakar dakin cikin shigar kananan kaya sai faman kamshi yakeyi,
Kaina sunkuyar kasa daga inda nake kwance bakin gado,
Kokarin mikewa nake yi zaune amma sai ya dakatar dani ta hanyan dan rankwafo min,
Daf da fuskana yakawo fuskan shi ta yadda zamu iya shakan numfashin junan mu,
A hankali kamar da wani adakin yake ce min wanan kayan sun karbi jikin ki har na kasa daurewa,
Sai naji ya hada bakinshi da nawa ya fara tsotsawa, a hankali,
Idona na kara lumshe saboda bakon abinda ya ziyarce ni,
Kanshi nadan shafo daga baya abinda ya bashi mamaki da daurewa ke nan
Kokarin kara shige min jiki yake yi amma sai na daure nace , mai cikin murya mai kama da kasala,
Yaya kayi hakkuri banice da kai ba ba yau kuma gamu da baki a falo fa,
Wani tsaki naji ya ja tare da mikewa daga samana gaba daya yana maida numfashi guda guda,
Muryan shi naji a yayinda idona yake dan lumshe, saboda re,action din da na samu a lokacin
Zan tafi da su in kaisu masauki kizo kuyi sallama da su kafin su tafi,
Mikewa nayi tare da gyara rigana da yaya ya mutsuke min,
Najawo hijjab dina har kasa nazumbuda sama a tare muka fito falon nidashi,
Wanda duk wanda ya ganmu a lokacin dole yaji sha,awan mu,
Daga bayan kujera na dan tsaya ina masu saida safe, cikin girmamawa,
Ina tsaye har suka gama fita daga falon gaba dayan su,
Yaya Abubakar kusan shine mutum na karshen fita daga falon,
Kada ki kwanta kidan jirani indawo please yafadi cikin daure fuska,
Nikan ina jin tashin motar su nai saurin komawa dakina nakullo, kofa,
Dama agajiye nake barci ne ya daukeni mai karfi,
Ban tashi farkawa ba sai zuwa karfe daya na dawani abuna dare, nadan bude idona,
Gaba daya kaman a mafarki nake jin kamar nishi akeyi aduk gidan namu, ta ko ina,
A hankali nadan fare bude idona dake tare da barci acikin shi,
Sai kara jin wanan sautin daya tayar dani barci nake ji,
Addu,a nafara jerowa don nai man tsari daga sherin shedan,
Tsoro sosai ya kamani don ban ko iya motsa koda yatsan hannu na alokacin saboda tsoro,
Wani abu nake ji dadaren kamar guguwa ya turnike ko ina,
Gashi fitsari nake ji sosai a lokacin kuma ban iya shiga bandaki don tsoro,
Addu,an naci gaba da yi can naji wanan abin yana lafawa a hankali,
Da fitsarin ya matse hakana namike a cikin tsoro na shiga bandakin, nasake shi ,
Wani irin mugun kara naji daga waje tabayan bathroom din nawa,
Da sauri nafito najawa kofan bathroom din na fada gado don tsoro,,
Sai kusan asuba shedan ya rudeni barci ya kwashe ni,
Abinda ya jawo min makara ke nan aranan, sai da haske yadan yi na farka da ga barci,
Koshi saida yaya yadawo daga sallah yaga har zuwa lokacin ban fitoba shine ysi ta bufamin kofa har na farka,
Da kyat na iya mikewa zuwa kofan dakin na bude kofa,
Tsaye yake kofan yana saye da farar jallabiyan sa da yar fulla fara kal, akanshi,
Hannu shi dauke da tasbaha yana ja a hankali,
Yadda ya ganni a hargitse ya sa shi saurin cewa subbahanallah may ya faru Meena ?
A hankali cikin daurewa nake ce mai babu komai bawai ya yarda bane amma sai ke ce min kinyi sallah,
Yanzu zanyi nace tare da kokarin shigewa na nufi hanyar bathroom,,
Kallon zargi yake min har na shige, bathroom din, girgiza kan shi yayi tare da komawa sashen shi batare da ya yarda da ansan dana bashi ba,,
Kafin wani lokaci har na,gama hada ma bakin mu breakfast ko,
A ranan zasu koma birnin kebbi don haka yaya ke ta zirga,zirga akan su da motar da su kazo da ita,,
A zaune nake ina son in karya a daki na saboda falo akwai su baba aciki,
Zan iyacewa, tun safe yau banga Anty Sadiya ga idona ba,
Wanan dan zamana dasu yazama mata tankae dabi,a aduk ranan da tai girki takwana dakin maigidan bata fitowa da wuri,
Kuma haka zata wuni acikin wani orin yanayi atare da ita,
Shigowan shi dakin yasani dan dago kai na kalleshi ga abincin da na tasa gaba ina kallo na kasa ci.
Saboda damuwan da na tashi dashi yau, a raina, don nakasa fitar da tunanen abinda naji agidan daren jiya ,,,
A hankali ya karaso har zuwa inda nake zaune, irish da kwan da nazuba a plate na kasa ci
Shi yasa hannun shi ya dauki spoon din abincin ya, debo ,
A,zato,na shi zai ci amma sai naga yamiko min alamar in bude baki,
Ba musu don banga fuskan haka ba na bude bakina a hankali yasa mun,
Sai dana tane ina kokarin hadewa shima ya mai da spoon din yadebo yasawa bakin shi,
Bayan ya hadiye ya na shirin debo wani ne yake cewa,
Na rasa abinda zan ba su Baba Musa wallahi don sunce lalai yau zasu tafi, ba fashi,
Ido na dan dago nadan kalleshi sai kuma nai saurin saukewa
Yaya ka basu kudi mana sai su je su sayi abinda suke bukata, dashi,
Don ka ga za sufi bukatan kudin akan wani tarkace,
Kallo na yayi tare da nisawa, yace amma kin sa innace zan basu kudi to kaman nawa ke nan,
Nace yaya ai kaike da aljihunka , don haka sai ka kiyasta,
Yadda zasu iya sayen tsaraba a hanya da kuma in su isa gida su sai abinci da sauran kudin
Wani iska naji ya furzar daga baki shi tare da sauke ajiyan zuciya,
Kudi kaman nawa sai naga ya mike ba tare da ya ji may zance ba,
Fitan shi dakin ba,a da deba yayana Ibrahim yashigo dakin, nawa da sallaman shi,
Bayan mun gaisa ne da shi na mike na nufi wardrobe dina na dauko kudin da ke ciki,
Gaba daya kudin da suke a hannu na na mikawa, yaya Ibrahim su,
Sai naga ya bude baki yana mamaki,
Zaunawa nayi ina cewa ka kaiwa baba kace ya sai abinci saura sai ya gyara motar shi,
Meena ina kika samo wanan kudin haka masu yawa, ?
A takaice nabashi ansa da cewa yaya ne yabamu su jiya wai musai abinda muke bukata,
To ni may zanyi dasu, ni da zan koma sokoto kwanan nan, insh? Allah,
Ok tau yayi zan masu bayani nan yake fada min bayanin sokon kayan da sukazo min dashi,
Shima dubu biyar nabashi na ce kuma yaba Baba wada da suke tare dubu biyu,
A tare muka fito falo da yayana a lokacin ne nake jin su Baba Musa suna ta zabga godiya,
Suna ganina naji suna cewa Amina kiyi muna godiya gurin mai sunan malam,
Yaba kudi masu yawa, muda mukazo murna kuma mun kawo mashi dawainiya,
Kudi yaba yaya Ibrahim wai yakai ma Baba na da kuma sako akaiwa nashi mahaifan,
Sun tafi sun barmu acikin jin kewan su
Tafiyan su bada dadewa ba zazzabi ya rufe ni saboda rashin barcin da ban samu ba,,,



ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[8/1, 9:33 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
4? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-A'DL

Sai yama lis su Baba Musa suka isa Birnin Kebbi,
Kowanen su dauke da tsaraban shi kamar su Manja, Doya, da sauran su,
Nan take gida ya hargitse da murna cewa sun,dawo, sundawo,
Mama Ladi da sauri ta tura jikanta,waje don tagano mata ko da may suka dawo,,
Wanan tafiyan kowa sashe na gidan mu sunyi farinciki dashi sosai
Da wanda ya tafi da wanda bai tafi ba ma ya sheda cewa an tafi, din,
Malam tsoho wanda yan aiken nashi su na zaune a gaban shi suna bashi sakon shi da labarin abin da suka gano mai acan,
Sai kada kai ya keyi ya na dan murmusawa a hankali,
Labari suke bashi amma zuciyan shi sai hamdala ya ke yi saboda TARKO shi ya fara kamawa ko,
Sakon kudin da suka zube mai agaban shi kuma suke sheda mai abinda Abubakar yace, akan sakon,
Murmushi yayi bayan yagama sanin cewa TARKO shine yai aiki,
In ba haka ba sau nawa Abubakar ke zuwa amma bai ce ya sha fruit's da kaji ba da kudin shi ,
Lalai wanan zancen daga aikin Meenatu ce don duk cikin jikokin,shi itace tasan cewa yana shan fruit sosai don mahaifin ta na yawan sayo mai idan ya tafi kauye,
Itace ke kawo mai idan an sawo takan ce mashi mai kwadan diyan icce,
Kuma alhalin idan ta kawo bata wucewa sai an,sha shi tare da ita,
Murmushi ya karayi yana cewa nasan cewa zaki iya Meenatu don hakkurin ko zai kai ki ga cin riba, gabadayan mu,
Amma duk yanzu ba,za,a gane may ya ke nufi da wanan hadin ba sam,

****** ********* ******
Daga Baba har Mama na shiru su kayi suna kallon sakon kudin da na turo masu dashi,
Kowa da abinda yake kiyastawa a zuciyar shi a lokacin har zuwa lokacin da yaya Ibrahim ya gama masu bayani kamar yadda nai mashi,
Ajiyan zuciya Baba na ya sauke tare da numfasawa,
Yace wa yaya Ibrahim ita Aminatun ce taba ka duk wanan kudin duka,
Yaya Ibrahim ya ce wallahi ba,
Nima abin sai da ya bani tsoro nake tambayan ta ina ta samo kudi masu yawa haka?
Sai tace min wai shine ya basu ranan Jumma,a yace ko,wacen su ta sai abin bukatan ta,
To ita kuma taga cewa ai sokoto zata dawo makaranta
Bazata yi komai da su ba shiyasa tace in kawo maka ka gyara motar ka da shi,, saura kuma kasai muna abinci,
Dubu Dari da hamsim ke nan har wanda yaya Abubakar ya aiko masu dashi,
Shi kuma yaya Ibrahim ya tashi da dubu,sha biyar,
Ni na bashi dubu biyae yaya ya basu goma,goma shida Baba Wadda,
Daga inda Mama na take zaune ta kurawa kudin ido tace malam a dai bincika tukun kafin ataba,
Baba yace mata ai dole duk da nasan irin tarbiyan da nai ma diya na amma dai dan yau ne baka shedan shi,,
Kudin ne ya hada gaba daya tare da mikewa zuwa gurin malam, da,su,

Saida baba ya gama mashi bayani komai sanan malam tsoho ya dan tofar da miyaun goron dake bakin shi,
Yace, masha Allahu Aminatu Allah yai maki albarka,
Yanzu sai kaje kayi yadda tace dasu saboda babu dadi mutum yana taimaka maka bai ga kayi abinda yake son kayi ba da kudin,
Yarinyar ka irin tarbiyan da kai matane take aiwatar wa,
Don haka addu,a zaku bita dashi Allah ya kare muna ita daga sherin masu sheri,
Ameen inji Baba na wanda ya mike jikin shi duk ya mutu saboda murna,
Shekara nawa yana neman kudi amma bai iya tara su haka ba alokaci guda,
Yau sai gashi yar shi Allah ya azurta , ta jikin dan uwan ta,
Kamar yadda malam yai mashi bayani shima haka yaiwa Mama na wace ya samu a cikin damuwa, tana ta faman tunane kala,kala,
Baba bai tsaya wani dogon guri ba fitar da kudin da zai shiga kasuwa don sayen abinci, dasu,
Saura kuma ya kasafa su ta yadda ya dace ayi da komai,

****** ********* ******
Mama ladi wace take ji kamar ta suke don bacin rai ,
Yadda yar rahoton ta tai mata bayanin irin kayan da taga matafiya sun shigo dasu gidajen su,
Har sashen ta Baba Musa ya shigo yabata sakon da Yaya Abubakar ya bashi ya kawo mata tare da fada mata sakon baki,
Ya juya zai tafine yaji muryan Mama Ladi tana ce mashi,
Baka fada min ko may ku,ka samo ba a gurin shi da kukaje,
Don yara sun fada min sun,gan ku da tsarba kaya masu yawa kun shigo gida da su,
A hasale Baba musa wanda babu ruwan shi dama da harkan kowa a gidan don bai son raini
Haka yake kamar Baba gurin rashin kula kowa acikin gidan mu,
Dam Baba na ya dan mutunci da babban wansu watau Baba Buhari,,
Cikin irin muryan shi na masu saurin magana yace ai sai kije ki tambaya ko gurin wanda ya ba mu don yafi maki sauki,
Fuuuuu, ya wuce batare da ya tsaya kara sauraren may zatace ba,
Nan Mama ta hau sababi tana kumfan baki ita adole anje gurin dan ta an yi mai maula,
Amma shi Baba Buhari da Baba musa ya kai mai nashi sakon yadade yana kallon gudin,
Can dai ya nisa yana cewa tau musa nagode Allah yai masu albarka ya kara rufa asiri,
Ameen, Ameen inji Baba Musa wanda ke tsaye tare da yayan shi,
Ai Buhari baka ga irin taron da muka samu gurin yaranan ba wallahi,
Kaga ikon Allah ko kai ai shi Wadda wanda ya saba zuwa yace,
A gaskiya gidan mai sunan malam ya samu canji sosai,
Ga abinci an,muna lafiyayye ga kuma gurin kwana mai kyau sanan ga wanan irin alheri haka,?
Madalla inji Baba Buhari yace aiko abu yai kyau ke nan gaskiya,
Suna watsewa da,ga gurin kowa ya tafi yin abin bukata da kudin,,
Ganin yau Baba sai harkoki yakeyi yasa mama ladi jin wani irin bakin ciki a rayuwan ta,
Idan akwai abinda taki jini shine taga Baba Buhari a cikin walwala yana sayen abu ana girkawa mama ladi na ci,,,

****** ********** ******
Kayan tsaraban da aka kawo min daga gida na dan bude su ina dubawa,
Kayan yaji ne da man shanu da daddawa, kuka, suborodo, da bussashen kubewa,da kuma garin farar masara mai yawa,
Abinda nasan zan mu bukata kafin in wuce kawai na bari sauran na kira nobar wayan, Fattu ta turo Baba na Hamza yazo ya daun masu ,
Ba,afi wasu mintina ba sai ga Maman, Bi,u da kanta ta shigo yi min godiya,
Har kasa tsohuwar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login