Showing 297001 words to 300000 words out of 388021 words

Chapter 100 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8215

shiga parts din gidan mu,
Ina masu ya gajiyan buki wanda na koma wata yar mulmulmul dani sai sheki nake zubawa don kyau,
Nasamu yan uwan haihuwan mahaifina agida sai godiya suke min suna cewa
Meenatu duk wadda akai kunyi keda mijin ki don kun gwada muna cewa, kudiya ne masu albarka don wanga hadin auren da malam yayi munga alfanun shi tun ba aje ko ina ba,
Don da ace ke wata bare ce can daban ya aura da duk wanan abin sai dai muji labari nai,
Amma yanzu kinga hikimar tsoho duk abinan ya dawo gida a hannuwan mu,
Baba musa yace amma yanzu kinga sai yarda mukayi da abin mu,
Matsalar mu guda yanzu shi na Ladi ta gane gaskiya, ta dawo ga hanya,
Don wanga irin hauka da takai banga ranan da zatabar shi ba tunda hassadace ke cin ta,,
Murmushi nayi tare da mikewa don bari part din Baba Musa kada ya ja min wani sabon matsala don da nace tak yanzu ji mama zatayi,
Don ma aini maganar bata shafeni ba zancen su ne na manya,
Har sabon part din mu na shiga gurin su Anty Sadiya wace tun case din mahaifiyar ta da akayi bata sake jiki ba har yanzu,
Don ko jiya gurin yinin taron suna suna dakin ta da yan uwan ta suna ta tattaunawa a kan zancen mahaifiyar su,,
Wanan ne karona na farko dana shiga wanan sabon, part din namu,
Kofan dakin Salawa a rufe yake don haka sai na tsaya a tsakar gidan ina kwada sallama,
Fattu ce tafi daga dakin da suka sauka wanda nake ganin shine a matsayin nawa dakin,
Tace a,a maijego kece da kanko kika taso na dan murmusa kawai tare da cewa wanne dakin Anty a ciki ta nuna min wanda nake tuhuma din shine nata dama,
Da sallama na karasa bakin kofan kafin ta dan leko tana cewa, Meenatu ke ce kika shigo nace eh,
Take ce min shigo mana yayanki ma ai yana a cikin daki,
Da sallama na shiga, dakin inda na hango yayana daga can gefe,
Na samay shi kwance yana barci a saman wani katon katifa dan tsale, dake gefen guda na dakin wanda ya sha ties sai walkiya yakeyi,
Jin sallamana yasa shi a hankali ya dago kan shi daga kwanciyar da yake,
Bai amsa sallamata ba bai amsa gaisuwata ba sai cewa yayi ina Baba din yake,
Saida na dan murmusa sanan nake ce mai, yana can a bayan Dije yana barci,
Gaishe shi na kara yi tare da tambayar shi gajiyan jama,a ya amsa min da cewa
Alhamdullahi, ya kuka kwana ya jama,a yace min a lokacin da yake kokarin dagowa zaune daga kwance,
Tambayana yayi dacewa kun bawa wa yan,nan bakin komai da ya kamata ko don asubanci zamuyi gobe asubanci zamuyi,
Idan akwai abinda za,a kara saya masu sai kiyi min magana a sayo masu kafin su tafi,
A hankali nace ina ga kamar ai babu komai da za,a sai masu inba dai kara masu za,ayi ba,
Yace ok zan duba anjima nagani idan da,a kwai din sai ai masu don sunyi kokari sosai wallahi,
Daga haka ya mike ya shiga bathroom din dake manne a gefe gudan dakin,,
Shigan shi yasa dan sauke numfashi ina cewa jiya ankawo wa su Anty nasu kayan bukin kuwa,
Tace ankawo Meenatu mun,gode, mamace dai bata basu ba,
Murmushi nayi gami da mikewa ina cewa barin gaida Salawatu sai na tafi na karasa gaida sauran mutanen gida,
Na dan dauki lokaci ina sallama kofan Salawatu dake rufe sai waka nakeji daga wayan ta yana tashi,
Nakara nocking sai a lokacin ne ta bude min kofan saidai ta tsaya daga kofa bata bani hanyar shiga daga ciki ba,
Nagane mai take nufi bata son na shiga sai wani kallon kurulla take min tun daga kafana har samana
Da kyat ta iya bude bakin ta ta karba min ciki ciki tana cewa kun tashi lafiya ya ?
Acikin sakin fuska nake amsa mata ina cewa lafiya kalau ya gajiyan jama,a da tafiya,?
Vikin ya mutse fuska take ce min lafiya kalau sannu ko ?
Nace Allah bamu wuni lafiya a huta gajiya sai anjima,
Dakin bakina mai suna nawa wanda ke a tsakiyan dakunan su na shiga,
Shima kamar sauran yake saidai katifa biyu da karami nagani acikin sa duk sabbi kamar sauran a nan na zauna muna gaisawa dasu cikin so da kauna,
Matar Abdullahi masijan Yaya Abubakar wace bata faye yawan magana ba,
Nace Suwaiba ya zafin Kebbi tai dan murmushi tace aida sauki amarya tunda kuna da wutan Nepa, ko yaushe,
Aida ban san ya zanyi da wanan zafin ba wallahi don sam ban son zafi arayuwa na,
Anty Saloon dake kwance saman dayan katifan tace kai kaunata sai fawani shining kike karawa,
Murmushinayi mata tare dacewa kai haba anty duk wanan ruwan zafin da mama Dije ke gasani da shi,
Muryan Yayana naji yana kirana cikin muryan nan nashi da ya ke rikitar da ni,
Natashi zuwa amsa mai kiran nashi na samay shi yana saka kaya ajikin shi
Kallo guda nai ma shi na kawar da kaina gefe guda nace gani yaya, sai yake ce min na fadawa su Fattu su shirya a shiga da su kasuwa ,
Yaciro kudi yace na ba kowar su ta sai abinda take so idan sun tafi,
Zanyi godiya yadaga min hannu yace ki bawa kowar su kawai,
Lokacin da zan fitone naga sisters dina sun shigo da kayan break fast acikin kuloli manya,
Wanda hakan yasani gane cewa daga part din mu ake kawo masu abin karyawa,
Dama Maman Biu acan take zaune tare da mamana da yan uwana,
Sosai sukayi farin ciki da wanan sakon suna cewa gaskiya baza mu iyacewa maigida komai ba don ai la lura muka kawo mai nan

A part din Mama Ladi na shiga kafin na shiga namu
Na samay su anty duk a gida wanda hakan ya nuna min cewa a gida suka kwana gaba dayan su,
Nan na kai har kasa ina gaida Mama Ladi kamar yadda na tsan mana haka din ne don fuska a daure ta karba min gaisuwan,
Mundan taba hira da yan uwana namike zuwa part din iyayyena wanda tun haihuwana sai yau naga Mamana
Mundauki lokaci da su kafin na koma partdin malam tsoho inda nake zama,

Washegari baki suka koma suka bar mu cike da kewan su,


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/25, 10:35 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AZ ZAAHIR


Bayan tafiyan su duk sai naji ba dadi a rai na don ji nake tankar na bisu a lokacin,
Dan saukin da na samu gurin kewan su shine Anty Amarya bata tafi ba ta na nan sai mun gama komai zata koma ,
Mun shirya komai yadda ya kama inda na umurci Anty da ta dauki duk wani abin da take bukata daga cikin kayan,
Amma sai ta nuna min cewa wai bata bukatan komai daga cikin kayan,
Har saida nai mata hawaye ta dauki turmim zani guda amma nace sam bazan yarda ba,
Dole ta hada da dinkakkun redemaide da waturmi again,
Muna zauna muna hira take ce min Meenatu dama ina son nai maki magana gaskiya idan zaku koma dole mu sake wani sabon shiri fiye da na farko,
Da sauri na juyo ina kallon anty don jin may tace min,
Ta kada kai tana cewa akan yadda nake ta jin zan cen wanan kishiyar ta ku da alaman sai tayi makirci sosai,
Don haka duk wani abinda kikaji ance tanayiwa wayance to ki shirya a kan shi don ke ma naki na tafe,
A jiyan zuciya na sauke mai karfi tare da cewa nima ai tunanen da nakeyi ke nan,
Nace ni dama Yaya zai barni na zauna nan garin ba sai na koma can tare dasu ba da yafi ,min wallahi,
Aiko da bakin ciki ya ci ki Meenatu akan wata can zaki zauna a nan ,
Nace cikin dan marairaice murya gaskiya anty ni sai nake ga kamar hakan zaifi min sauki,
Bazaki zauna ba Meenat ai zuwa tayi ta samay ki a gidan a kan may zaki bar mata guri,
Hmmm nace tare da kara sauke numfashina nace Anty yanzu fa ina da yaro yaya zanyi a cikin su,,
Kada na kara jin kin fadi hakan da zaran lokacin komawan ki yayi zanzo mu shirya komawan ki,
Tau Anty nace, tare da dan kada kaina alaman to sai dai a can kasan zuciya na ina tunanen abubuwa da dama, akan komawar mu,
Kafin muce wani abu saiga wasu mata sun zo barka daga Gese wai basu san cewa har anyi suna ba,
Bayan fitan matan bada wani dadewa ba sai mu ka jiyo muryan mahaufina,
Baba na ya shigo gida cikin farin ciki yake cewa Amaryan Nafiu dama ina son jin gaskiyan wanan al,amarin da kukayi, daga gareki,
Don hankalina bai kwantaba saboda ina gudun magana,
Kowan mu da mamaki yake kallon Baba saboda ba mu fahince shi ba mu san akan may yake son karin haske,
Yace zance ko ina akan irin y?dda kukayi harkokinku cikin wadata haka,
Murmushi tayi tana cewa har hankalina ya daga don ina ce ko wani zance ne can na daban, ,
Nan ta kwashe duk yadda al,amari yake ta fada mai da kudin dana bata da wanda suka bata sai kuma Uncle dina wanda ban san may zan mai ba na sakaiyya, saboda irin alherin da yake min, tun tasowa na
Sai jijiga kai Baba keyi cikin mamaki yana cewa lalai kun kai yan zamani wa,yanga diya,
Yanzu ashe kifina kun ka gasa da ruwan shi har ankaci,
Lalai Ladi ta hadu da yan zamani sun sa ta kwana in takamar ga fitina,
Baba yace to in har shi mai sunan malam yaga kayan yagane su fa,
Anty tace may zaice Baba tunda rufa mai asiri ne mu kayi da ace mu ji kunya ai gara ace mai munyi irin haka ,
Balle namiji maishi ba ruwan shi da yawan binciken matan shi,
Hakane inji mahaifina yace gaskiya Amarya ban mu da abinda zamu ce maki saidai addu,a
Wadda kun kayi, muna ke da mijin ki Allah ya mayar maku da shi alheri Allah yasa wa diyan ku albarka,
Sai amin muke cewa irin addu,an da mahaifina ke ta kwararo wa uncle da Anty Amarya na alheri,
Kamar yadda mama bata dawo muna da kayan goyon mu ba haka muma ba muyi mata magana ba sai fa da ta tabbatar da cewa Anty Amarya tabar gari sanan ta yarda cewa ai ba kayan aro bane,

****** ********** ******
Matafiya sun isa gida lafiya sai dai duk a gajiye suke saboda nisan hanya da suka sha,
Don haka kowa kokari yake yaga cewa ya samu gurin hutawa,
Sun samu gida angyara ko ina anyi masu girki lafiyayye sai kamshi ke tashi ta ko ina a gidan,
Fatima tana zaune a falo tasha kwalliya sai kamshi takeyi da kyalli,
Idon ta kyam a kofan shigowa falon wanda basai an fadawa mutum ba yasan cewa shigowan maigida ne kawai take dako,
Matan ne har da Ramatu suka fara shigowa gidan a cikin gajiya tare da su,
Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya shigo gidan,
Yana saye da rigar shadda mai ruwan brown colour tayi sequsing a lamar cewa ya sha zaman mota da su,
Waya yake a lokacin da ya shigo gidan Fatima tana ganin shi ta mike tsaye daga gurin da take zaune,
Ta nufe shi cikin wani irin tako da ka saita tana wani rangwada tana karasowa gurin shi, ta rungumay shi, zuwa jikin ta,
Bai daina wayan da yake yi ba sai dai dan bubuga mata baya da yayi kadan yayin da take cewa cikin wani irin murya miss you sweet Bukar,
Kai ya daga mata ya na mata alaman cewa yaji dadi amna baidaina wayan ba,
Salawatu wace ta fito, daga dakin ta don shiga kitchen ta dauko ruwan sha,
Sai take ganin irin abinda Fatima keyi ma maigidan wani irin bacin raine ya sauka mata lokaci guda,
Da sauri ta kawatlr da kanta a gefe guda tare da fadawa kitchen tana maida numfashin ta, guda guda don kishi,
Har ta koma daki Fatima tana lake a jikin Abubakar da yake wayan shi hankali kwance,
Bab ta fada sanan gadon ta da karfi tana mai sauke numfashi a hankali idon ta ya kada yai ja,
A irin wanan halin itama sadiya ta riske su amma sai ta kawar da kanta duk da taji wani mugun zafi da kishi sosai itama,,
Yana gama wayan yadan juya yana ce mata ya kuke ya gida daga haka yasa kai zuwa sama abin shi,
Mamakine sosai ya kama Fatima yayin da tabi bayan shi da kallo har zuwa lokacin da ya bace mata dagani,
A gurin da take tsaye ta hade wasu miyau masu zafi da suka sulalo mata da ga bakin ta,
Hakan yasa tasan cewa akwai magana ke nan a tare da, ita, don Bukar, din ta is not normal
Batai fushi ba inda tabi bayan shi zuwa dakin ta samay shi har ya cire rigar jikin shi yana son shiga wanka, singlet ce kawai a jikin shi sai wando,
Wanka zakayi tace yayin da take karasowa gare shi cikin wani tako na jan hankali,
Ummh yace mata tare da kokarin karasa cire kayan shi, da yakeyi ,
Ta karaso gab da shi cikin jan ra,ayi take cewa duk gajiya ya wahal min dai kai ko,?
Murmushi yayi don yagane nufinta sai cewa yayi barin watsa ruwa ko zanji dadi,
Ya shige bathroom yayin da ta dan kara binshi da kallo har ya shige,wankan,
Falo ta dawo ta kara gyara ko ina don gurin ya kara yin kyau,
Ta kara feshe gurin da turare masu kyau don ya kara daukan idon maigidan da duk wanda ya gani,

Fitowan shi wanka kenan na kira layin shi don naji saukan su gida lafiya,
Yadauki wayan a cikin farin ciki mu ke gaisawa inda yake cewa yanzunan nan nake son na kiraki ai naji ya kuke,
Murmushi nayi nace kun isa ke nan tun dazun ko, ?
Yace ar kasalance don har ina jin alaman zaman shi a bakin gado ta wayan,
Maman Boy ya muka barku ina Boy, ?
Wani dadi ne ya mamaye min zuciyata saboda kasan cewa tare da shi,
Acikin wani sallon murya nace cikin lumshe idona ga boy a kwance yana kewan Baban shi yau,
Hmmm naji yace tare da cewa gaskiya ban so ace nima na barku can ba naso ace na dawo tare da ku,
Sai dai kuma wanan zancen na tafiyan mu ce yasa na bar ku a can,
Cikin yar dariyar zolaya nace ai malam ba zai bari ba na biyo ka a hakan,
May ye a cikin don nace zan dawo da iyalina, mu tafo tare, nan, shine zai min fitina,
Nan Fatima ta shigo dakin taja ta tsaya daga bakin kofa tana mai wani irin kallon tuhuma saboda yadda taga yana zance a cikin shauki,
A hankali ta, tako zuwa gare shi tana takowa tana wani hade yawu masu zafi don takaici,,
Zaunawa tayi daga gefen shi inda idanuwan ta suke kallon center carpet din dake a tsakiyan dakin,
Har zuwa, lokacin da mukayi sallama dashi tana zaune sai sake sake takeyi a zuciyar ta,
Ya dai, ina son nayi sallah, ne ?
Cikin wani irin sarkewan murya take cewa dama abinci nazo na ce maka, is ready,
Idan nai sallah zan fito muci ai ko sauran sun fito ne su don mu ci,
Take fuskan ta ya matse don ita azaton ta daga ita sai shi za su ci abincin,,
Amma babu yadda ta iya dole ta shirya abincin muttun hudu,,
Ganin ya mike tsaye zai gabatar da sallah, hakan yasa ta mikewa don fita daga dakin, ,
Yau ta san cewa akwai aiki gurin maigidan yana rike da ita kan zancen wayan su,,
Kai kai ashe akwai jan aiki kenan a gaban ta don kawai tai, magana akan meenatu da dan ta,
Gaskiya wanan Meenatun ta girma Azuciya Bukar da a kwai jan aiki a gaban ta sosai,.
Don ta dauki alwashin, cewa sai ta ga bayan wanan Meenatun a rayuwan Bukar din ta,
Batai fushi ba domin yau fushi ba nata bane saboda tana son ta shawo kan dan Bukar din ta,
Ta hanyar abubuwa da dama sai faman sake sake take yi a zuciyar ta,
Duk yadda ta so ya sauko a ranan ba ta samu sa,an hakaba daga gare shi don gaba daya ya daure mata ta rasa gane kan shi,,

****** ********** ******
Ba,ayan kamar kwana hudu da tafiyan su tafiyan mahajjata yataso don haka duk gida ya rude zancen tafiya saboda da yawan su basu tabbatar da zancen tafiyan mahaifina da Mama Ladi tace bata yarda,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login