Showing 249001 words to 252000 words out of 388021 words

Chapter 84 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8306

baki damu da kiji lafiyan dan uwan ki ba ko dan kina agaban malam tsoho yanzu,
Idan da dane daya fadi hakan da murmushi zanyi amma sai yaji sabanin hakan don shiru nayi saboda wani irin takaicin shi nake ji a lokacin,
Shirun da yaji nayi yasashi tambayana cewa lagiya kike kuwa yau, Meenatu, ?
Nabashi amsa da cewa lafiya kalau nake kawai dai daga barci nake,
Yace to yaya kuke ya baby I hope yau yana kicking fiye da kullun ko ?
Nan ma ban taka mai basai dai kawai hmmm da nace mai, tare da yin shiru,
Hakan ya sashi fahintar cewa akwai matsala ke nan don da yaji na bashi ansa,
Don haka sai kawai na,ji yace ok sai anjima ke nan, zan shigo,,
Wayan na bi da hararan takaici tankar shi ne Sadaukin mazan, a gabana,

Dakaina namike zuwa gurin malam tsoho don na mayar mai da wayan shi, da ya aiko min na karba kira,
Babu mutane gurin shi a lokacin don haka na samu daman sakewa dashi,
Tunda na nufoshi yake murmushi yana cewa yau ina kika shige mijin ki ke neman ki,
Murmushi nayi mai kawau nace ina nana gefe guda ina hutawa malam barci nayi yau sosai don jiya mun sha yawo,
Malam tsoho yace min maigidan naki ya ce min zaku koma gobe ko jibi wai aiki ya taso mai a ma,iakatar su ,,
Nace, tau gaskiya banda labari malam saboda bai fada min ba kuma ma ai ina ganin bazan koma ba saboda makarantar mu suna son ganin mu nan da wani sati mai zuwa,,
Ya amsa da cew na,am gaskiya 8dan hakane tafiyan zai zama maki biyu ke nan ,
Malam yace Meenatu dama ina son ganin ki tun zuwan,ku garin nan sai dai bamu samu lokacin hakan ba saboda yan matsalolin da aka samu,
Nai maza nace mashi to malam gani ai yanzu ko yace to samu guri ki zauna da kyau sai kiji may zan fada maki,
Kamar yadda malam ya umurceni hakan na gyara na fuskance shi a cikin natsuwa ina sauraren shi,
Yace Aminatu ba komai bane yasa na zaunar dake sai akan zaman ki da mutanen duniya musan man ma abokan zaman ki da kuma yanuwan haihuwanku watau yan uwan haihuwan mijikin wa yanda yanzu sun zama kamar dangin miji a gareki,
Mafi yawan su zasu manta da irin alakar dake tsakanin ki dasu kiga suna maki wasu abubuwa tankar ba,a tsatso guda kuka fito da su ba,
Hakan shima maigidan naki duk da nasan cewa ya rike amanar da muka bashi bakamar sauran maza da ake hada alakar zumunci su watsar ba, saboda ba su san muhinmancin yin hakan ba,
To mudai gaskiya Alhamdullahi don zance mai suna na yai muna bazata gurin rike amana da gaskiya,
Abinda malam ya fada gaskiyane don haka nai murmushi nadukar da kaina na kasa don nasan cewa yayi kamar yadda malam din yace din,,,,,,
Afuwan please =?O?=?O?

Jumma,atu mubark to all Muslims ummah,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
[9/23, 8:50 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL - MA,AJID


Malam tsoho yaci gaba da cewa, cikin natsuwa don in fahince shi,
Don haka ko,ba a fada mun san cewa wanan kyautatawan ya fito daga gare ki ne,
Don haka hakan zakici gaba da gyara rayuwan ki da kowa a koda yaushe,,
Yadda kika gyara a tsakanin ki da mijin ki tun farko har ya fahince ki to ko yanzu ma haka ,zakiyi da sauran abokan zaman ki,
Duk da nasan kinayi din don haka sai ki kara zage damtsen ki gurin kyautatawa,
Don haka kiyi ta addu,oin da na baki tun farko babu abinda zai samay ki da yardan Allah,
Ita kuma diyar wanan muguwar da kuke zama atare da ita, barta can da mugun abinsu duk sherin uwar ta ce ke koma mata,
Babu abinda zai samay ki dayardan Allah don Allah yana tare da mai tsarkaken zuciya akoda yaushe ,
Banda wani shakka akan ki Aminatu ko mata nawa mai suna zai yi don na riga da na haka mai TARKON da ba zai iya kurcewa daga cikin sa ba tun farko,
Don haka ke je kiyi tawa mijin ki biyayya yadda zaki kara shiga zuciyar shi akoda yaushe,
A hankali na dan runtse idanuwa na saboda ni dai a gani na banga wani TARKON da aka dana wanda ke aiki ba akan mutumin da ya maida mata kamar wata sana,a ,
Ina cikin wanan tuna nen ne naji muryan malam tsoho yana cewa,
Naso ace a gaban mu zaki haihu don akwai abubuwan ada ya kamata ai maki yayin da cikin ki ya tasan ma haihuwa,
Saidai mai gidan naki san boko ne baida ra,ayin dawowan ki gida nake gani,
A hankali na dago kaina a sanyayye na ce malam idan har ka bukacin hakan ai zai yarda da hakan shima,
Malam yace idan mutum ya kasance mai hakkuri to kada ka yawaita matsa mashi akan al,amuran shi, don kada yaga gazawan ka,
Murmushi nayi a hankali nace malam nasan cewa ba za,a samu wani matsala ba insha Allah,
Yace yanzu dai kafin ki tafi akwai abubuwan da zan baki kki kula da kyau kiyi amfani dasu don Allah,
Nace mai nagode saidai kuma muka dauko hiran yadda rayuwa yake guda a yanzu da gidan mu da kuma duniya, ma gaba daya,
Ina zaune tare da malam Yaya Abubakar ya aje motan shi nisa kadan damu,
Ban motsa ba don nasan cewa zai hangeni idan nace zan shige daga ciki,
Ganin da yai muna zaune tare da malam yasa shi kuro muna ido tun daga nesa cikin mamaki,
Ya karaso da sallama dauke a bakin shi malam ne ya karba mai a fili nikan azuciya na karba mai,
Gaisawa suka fara yi da malam tsoho yayin,da idon shi ke a kaina,
Ya sauke su a saman dan ciki,nada ya turo zanin dake a,jikina,
Ganin haka yasa ni mikewa, tsam da nufin shiga gida a lokacin idon shi ya daga ya na mai bina da kallo,
Lokacin na ke masa ina kwana da kuma tambayan lafiyan shi,
Saida ya lumshe idanun shi cikin bajinta da iya jan aji, ya karba da cewa lafiya,
Gaba na yai mugun faduwa don a lokacin naso na fada mai zancen neman da ake min school din mu,
Ya Abubakar ya dan rage fara,an dake dauke a fuskan shi yayin da ya fuskance ni,
Tambaya ya jefo min da cewa yau may yasa wayan ki yake a kashene tun safe,
Na rasa amsan da zan bashi in wanke kai na don zargi,
Can nace wayan tawa ce ba caji a cikin don jiya a gajiye nake hakan yasani mantawa na sakata caji,,
Ya ce ai wanan ba dabiar alheri bace ace tun safe mutum waya a kashe haka,
Yace daman ina son na sheda maki cewa ki shirya zuwa gobe ko jibi zamu koma insha Allah,
Duk da naji wani iri amma sai na dake ina cewa gashi kuma wai ana neman mu a school next week mukai evaluation form din mu,
Yace cikin wani irin murya bazaki koma tare da mu din ba ke nan ko ?
A hankali na koma na zauna gurin da nake zaune da farko nace,
A,a ba wai bazan koma sa ku bane gani nayi dai cewa tafiyan zai min yawa in tafi gobe next week kuma na dawo
Ok you can go a head duk lokacin da kika gama sai ki dawo,
Malam tsoho wanda ke sauraren zancen mu ya ce abinda zata tsaya yi makarantan ba mai muhin, manci bane sosai ko,
No, ni ban san komai ba akai kawai ta tsaya din ai ba komai idan ta gama sai ta dawo,
Malam tsoho yadago kai yana dubana a take na bata raina don ban son ya tillas,ta ni bin shi don kada nai missing din karatuna,
Ganin haka yasa shi dan yin murmushi yace jeki ciki Meenatu zan nemay ki anjima,
Ina shigewa ya juya gurin Yaya Abubakar yace amma dai kasan cewa tana karatu tun farko ko ?
Ya dago idon shi da atake suka rine sun canza kalla alaman ran shi ya baci,
Yace, anzu ni may nace ta tsaya har ta gama karatun ta ai zaifi,
A,a mai suna may yai zafi haka idan har baka yarda ba ai sai ta biku ku koma tare ba shi ke nan ba,
Amma kunzo dadi, dadi sai kuma gurin koma bacin rai ya shigo,
Yanzu ai bincikawa zakayi kaji idan abin ba mai muhin manci bane kaga sai ku tafi,
Sai a lokacin ya dan sake ran shi, yace zan kira na bincika,
Kawai dai bata son komawa ne ba don komai ba sai don kishi da suka sawa kan su duk kan su,
Dariya malam yayi yace kishi kuma ashe kasan kayi laifine,
Ya gyara zaman shi yana cewa gaba dayan su basu san halina bane don haka zan gyarawa kowar su zama, don ta shiga hankalin ta,
Idan ma aure zanyi ai ba wace ta isa ta hanani yi daga cikin su,
Da sauri mai sunan malam ya juyo yana kallon Abubakar, a cikin mamaki, yace aure ka mai suna,?
Yaushe kuma a ina zakayi shi, ?
Ya bawa kakan ansa da cewa, anan garin ne ina gani,
Malam tsoho wanda mamaki da imani sukai mai yawa sai girgiza kai kawai ya ke ta yi, lokacin,

****** ********** ******
Bayan wayan su da Uncle dina inda Uncle ke sheda mai cewa an bugo mai waya ana neman mu next week a school,
Hakan ne ya dan sashi rage fushin shi akan cewa ba don kar na bishi ba nace hakan,
Badon rashi ya so ba Allah ya kwace ni daga fushin shi,
Ranan da zasu wuce ina , part din mu ban fito ba ,shima kan shi bai iso gidan da wuri ba sai zuwa wani lokaci,
Yan abubuwan da na saya don akaiwa Baba Ramatu, da Fattu tare da,Antyn Saloon nabawa Baba Hamza shi da Baba Wadda,
Ganin cewa ana ta hada,hadan sallaman su ni ban fito ba yashi shiga pary din mu,
Ina zaune ina cin, dan wake da mai da yaji, da fura a kwanon sha mai sanyi a gefe na,
Idon shi suka sauka ga abinda na keyi a kwanon ,
Sai naga ya kada kai alaman yayi sun gaisa da Mama na acikin mutunci da girmamawa,
Yake tambayan ban san cewa suna shirin tafiya bane ban fito ba,
Nai kwal da idona na duka don ban da abin cewa a lokacin,
Ina ganin yana kokarin saka hannuwan shi a aljihun rigar shi, na kauda kai gefe guda,
Muryan shi naji yana cewa, idan zaki tafi sokoto mun yi magana da Aliyu cewa zai zo ya kai ki don ban son shiga motan haya don ganganci,
So da zaran ki shirya ki bugo min sai na turo maki shi,
Ki tabbatar da cewa kina zuwa awo saboda tsaron lafiyan ko dana Baby,
Duk da na so ace mun koma tare sai muje gurin wanan doctor naki inji dalili rufe min zancen cikin ki da yayi alhalin ina mijinki na sunna,
Kaina na dukar kasa azuci nace dama nasan shirun da yaya yayi don muna a gida ne ba wai ya fita zancen bane,
Amma Allah ya kwace ni da ga tarkon shi don da ban san irin hukuncin da zai zarta min ba,
Yamiko min kudi yana cewa idan da wani abu sai ki fada min na turo maki Aliyu da,shi,
Idan yace Aliyu a da ban jin haushi amma a yanzu sai naji wani irin takaici ya turnu ko min a zuciya ta,
Nakarba ina cewa nagode yace Baba ya hada muna tsaraba masu yawa naso na samay shi a gida kafin ya fita in mai godiya,
Sai a lokacin na dago kai na ce Babana, ?
Cikin mamaki ya bani ansa da cewa wa yasan cewa Baban ki ne shi tunda mutane da baban Sadauki suka san shi,
Abinda yasani murmushi ke nan tun shigowa wan shi don nasan nima dai maganar tazo min ne amma ai gaskiya ya fada,
Massage ce ta shigo a wayan shi abinda ya dauke mai hankali ke nan yana karantawa yana dan murmushi,gefen fuska,
A take na gane cewa duk yadda akayi wasu kalaman soyayya ne yake karantawa hakan,
Kafin ya kai ga karshen karatun shi na jefo mai tambaya da cewa ,
Sai ka dawo ne za ,a daura auren naku ko ,?
Ba tare da ya daina karatun da yakeyi ba yadan sake murmushi mai sauti daga fuskan shi,
A hankali ya dago daga karatun da yakeyi a wayan shi yana cewa ko tsoron haka ya hanaki tafiya da mu, ?
Saida na dauki dan wake da tsinke na saka a mai da yaji na kai ga bakina na fara taunawa san, nan ce,
Ba tsoro ya hani bin ku ba yaya , ai da ma sai na bika don ba zan so wata ta shivo ta kwace min Yaya ba don ita ma din ai yayan ta,
Kawai dai don kada in samu matsalane a karatun tun da saura kiris ya rage in gama,
Murmushi yayi yana cewa, ban san munafukin da ya fada maku wanan zancen ba,
Nace babu wanda ya fada muna kawai dai yadda ake kokarin sace zuciyar mijin mu a lokaci guda yasa mu fahinta,
Baiyi magana ba sai mikewa da yayi yana cewa zamu tafi ki kula da kan ki kuma zamuyi waya naji yaushe ne zaki dawo,
Na lumshe idona a hankali tare da kokarin mikewa tsaye, don nai masu rakiya,
Muryan Yaya Abubakar ce ta shigo kunne na idan yake magana tankar mai rada yana cewa miss you ,
Don kin san bada son raina zan barki a gida ba yanzu haka don ina bukatar iyalaina a kusa dani,
Murmushi kawai nayi mai batare da cewa komai ba don nasan abinda ya fada gaskiyane,

Part din Mama Ladi na shiga na samu Anty Sadiya tana zaune kusa da Anty Samira wace aka sallamo daga asibiti,
Mun gaisa da su inda Samira ke cewa ashe ke muna nan da ke ba tare zaku koma ba,
Murmushi nayi ina kokarin kaiwa zaune samira takara cewa Meenatu wanan cikin naki fa da alaman yai nisa sosai,
Da sauri ?nty Sadiya ta juyo tana kallo na acikin mamaki idon ta ya sauka a dan cikina da ya turo gaban zani na,
Damm, dammm gaban ta ya bayar cikin wani irin mamaki ta furta a fili tace,
Meenatu cikin shin akgare ki haka bamu sani ba shin ?
Anty samira tace wai kuna bani mamaki da za,a ce duk wai har mai gidan ku ba ku gane wannan cikin da har ya zama katon baby yanzu,
A take duk wani annurin fuskan Sadiya ya gushe a lokaci guda,
Fuskanta ya matse ya koma na bacin rai mun fahinci hakan gaba dayan mu amma sai muka basar da ita tankar bamu fahince ta ba,
Muna tsaye a bakin kofan gidan mu suka bar gari alokacin naji wani iri a zuciyata,
Take kewan mijina ya fara shiga zuciyata son shi da kaunar shi yana ratsa sassan jikina ta ko ina,
A hankali naji wani irin kasala yana mamaye man sassan jikina ta ko ina,,
Yan uwan Sadiya basu kara shiga ciki ba daga na sukayi muna sallama suka tafi inda Habbi sister din anty sadiya ta ke cewa wai ban zo gidan ta ba,
Nai murmushi tare da bata hakkuri nace zan zo insha Allah mu kai masu sallama suka tafi,abin su,
Suna bada baya Aisha tace min da kin mutu idan kin je gidan su wayan nan mayun masu mugun abu azuciya,,
Najuya daga tafiyan da na fara nace haba dai Anty Aisha may yai zafi haka kike masu wanan zarin haka,?
Cikin mamaki suke hada baki suna cewa ke baki san cewa mahaifiyar su ta kawo hari nan gidan ba malam tsoho ya tona mata asiri,
Labarin da Baba Wadda ya bamu shine ya fado min arai suke kara gaya min harda wanda Baba Wadda bai fada min ba,,
Mamaki sosai naji don zancen ya tabbata ke nan da gaske,
Part din mu na fara shiga gurin mamana nasamay ta tana kwashe abinci,
Take tambayana har sun tafine nace mata eh sun tafi ,
Ganin da Mamana tai min jikina a sanyaye tun shigowa na sai take zaton don tafiyan mijina ne nakoma hakan,
Kin fara da kin sani ki bisu ne ko ?
Da sauri na girgiza kai tare da cewa haba dai kai Mama,
Ina dai tunanen duniya ne yanzu su Anty Aishe ke fada min zance akan mahaifiyar su Sadiya,
Mama tace ai wanan tsohon zancen ne nima a lokacin da abin yafaru hankalina ya tashi kwarai amma daga baya sai na bar wa Allah komai nasan insha Allah bazata iya komai da ke ba,
Nace tare da nisawa cikin damuwa Allah ya kyauta Mama,

****** ********** ******
A zaune gurin da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login