Showing 366001 words to 369000 words out of 388021 words

Chapter 123 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8210

nan,

ZEEE MAKAWA YELWA
[12/14, 11:19 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 5?

ZAINAB IDRIS MAKWA

ALLAH AN NAAFI


JUMMA,AT, MUBARAK TO, ALL MUSLIMS UMMAH IN THESES WORLD,,,

Washegari ban fito daga part dina ba sai da dare bayan kowa ya idar da duk abinda ya keyi a lokacin,
Ina saye da wata doguwar riga baka maidan zuben jallabiya saidai rigan tanada dan fadi don bata matse ni ba sosai,
A hankali nake tafiya don gudun tangarda ga jikina shi yasa nake dagwa dagwa, ina kafa kafa da komai,
Tun ban karaso ba jikina yabani yanzu gurin zai sauya inda na isa,
A zaune su ke a na dan hiran sama, sama hiran gwale junan su kowan su da abinda yakeyi ,
Maigidan yana, duke a jikin computer yana aiki ga goran ruwa a gefen shi guda, yayin da naga yar wurin Fatima daga dayan gefen shi kadan,
Abu ga dan Adam kuma mace da kishi ina ganin yarinyar sai naji wani irin kishi ya dan turnukeni amma sai na dake na wayance nan nunawa a fuskana,,
Sai dai acan cikin raina ina fadin Innalillahi don samun sauki,
Ganin nafito falon ya saka su gaba daya sako min idanuwan su don suna bala,in,bakin ciki su ga na fito wanan zaman, falon cikin su,
Sannun ku da hutawa nace bayan nai masu sallaman da ban tsanmanin sun karba min ba,
Idan har nace zan zauna a kasa yanzu bazan ji dadin hakan ba, don haka sai na dan zagaya daga bayan kujera na dan duka a kai,
aa@ Yayin da na tokare hannaye na asaman kujeran na dan kwanto da jikina a sama,
Yaya Abubakar dake a duke jin nice na fito kuma har nai masauki a bayan kujeran shi ya saka shi kokarin juyowa, don ya fuskance ni,
Yarinyar dake a kwace tana dan wasa a cikin gwalanci tana daga kafan ta nake danyi wa wasa a lokacin ,
Yayin da idanuwan uwar ta yake kyam a kaina kamar tana zaton zan wa yar nata wani mugun abu nan,
Nace cikin sakin fuska kece babu ko sock's a kafan ki bakyajin sanyi ko
Uwar wace ta tsureni da idanuwan ta fuska ba yabo ba fallasa aciki ta ce ai yau babu sanyi sosai,
Fuska Yaya a kaina acikin murmushi yake cewa,
Ya jikin naki yau kuwa nurse din ta shigo gidan nan kuwa, ?
Gaba daya naga sun sha mur kowace tadan daure fuskanta
Nace cikin wani muryan jan aji wanda ya sake masu jin haushinna
Na amsa eh tazo har ta dan sani indan dinga yawata,wa don na kara jin karfin jikin nawa,
Fuskan shi dauke da murmushi yace Good , good hakan na da kyau, don zaki dinga yin exercises din jikin ki a hankali don gurin ya hade sosai,
Nace dama nazo na fadama cewa mun samu gifts daga kungiyoyi da dama da zamu dawo gida yan asibiti su ka ba mu tare da list din masu kyautan,
Kokarin mika mai takardan na keyi don ya duba na kara da cewa doctor yace yaso ya kawo gida tun kana nan amma sai yaga a lokacin ba,a gaba kawowa ba shi yasa su kai parking dinsu a side,
List din ya karba a cikin farin ciki tare da jn dadi yana fadin masha Allah inda yafara kiran sunayen wa yanda suka kawo muna gifts din tare da alakarshi da su,
Inda yake cewa sai da safe zai shigo ya bude ya gani don ya ga abubuwan dake a cikin parks din,
A lokacin da muke magana shiru gurin yayi babu mai motsi daga cikin su tankar babu kowa a gurin,
A, a yan uku kan Alhamdullahi gaskiya yanzu duk wanan tarin kayan na gifts ne haka ashe ?
Mu muna ma ce ai ko duk na uban su ne wanan sayayan mai yawa haka
Sadiya ce mai wanan maganan acikin mamaki take ce lalai zato zunubi don ni wallahi nazaci duk wanan sayayyan uban su ne, ai,
Lalai munga haihuwan arziki aike Meenatu kin iya haihuwa wallahi na Amir ma naga haka aka tara maku kayan kaman zaku bude shago,
A to ai yanzu bamu gani kayan ba mu don haka babu abinda zai damu mutum wallahi,
Kaya ai basai keep n gani ba don mu bamu gaji yin riya ba a gidan mu,
Idan kina son ganin su kije rugga fullani kisha kallo ikon Allah wallahi,
Asmau ce daga gurin hawa steps din da zai kai mutum kitchen din gida take bama Salawatu amsa,
Sai mukaji muryan Fatima tana cewa ai idan fitsari banza ne to kaza tayi mugani don zancen banza wai har ace wata ta ita haihuwa wata vata iya ba,
Ai sai agwada mu wanda bai iya ba mugani afili zancen banza zancen wofi,
Cikin tsawatawa Maigidan ke cewa kada ku kawo min zancen fitina a gida yanzu rayukan ki ya baci,
Yayin da Salawatu ke cewa wallahi Oga kayi wa yarinyar nan kashedi don wallahi ta rainani da yawa a gidan nan,
Ni ko yar ki wallahi gatanan ba sa,ar yina bace, balle ke,
Ita kuma Sadiya sai cewa tayi ai sai kiyi don ni zancena a gida nake magana da akace kayan da mutanen gida suka tara akawo wa su yan uku wai Mama ta rike tace baza,a kawo ba tunda na Amir ma suna nan ba, ai komai da su ba,
Shine ke azaton ki kike gani wai ke nakewa shagube ke ma ina antara maki gwargwadon samun ku,
Enough don Allah zancen ya isa haka please don ban son yawan fitina wallahi,
Ganin wuri ya rikice ba kuma lafiya gareni ba yasani juyawa zuwa part dina cike da mamakin zancen wai Mama Ladi ta hana akawo min kayan da muka samu,
Bance komai ba na shige falona inda na samu su Gwago a zaune nadan hau two seaters na kwanta na dunkule guri guda ina mai sauraren hiran su,
Shigowan Asmau nake cewa Asmau don Allah ki fita harkan Salawatu a gidan nan please ban son abin fitina wallahi,
Tace wallahi Anty wanan matar muguwace kullun zancen kine a bakin ta idan kuma tagan ki sai tayi kamar tana kaunar ki da gaske
Murmushi nayi nadan gyara kwanci ina fuskantar ta da kyau nace Asamau ke nan ke kin taba ganin inda kishiya taso kishaya ko na rana guda, ai saidai na dariyan hakora kawai,
Wani kallo tai min na mamaki tana cewa amma dai ba harda ke ba nace cikin dariya ni ba mutum bace Asmau.
Suna kishina ina kishin su don haka kinga ai kowa nayi
Sai dai kawai na wata yafi na watane kawai amma ai ba macen da zatace bata da kishi a duniyan nan,
Tace amma Anty wanan matar wallahi, nata yai yawa don munafukace,
Bata kaunar ki sam keep duba fa ranan naji suna gulma wai duk wanan gifts din da kika dawo dasu daga asibiti wai Yayan mu ne ya saya maki su,
Zanyi magana Baba Ramatu ce ta hana nai mata magana take ce min wai na kyale ta halinta ke nan,

****** ********** ******
Da tsaban balai Salawatu ta samu Yaya Abubakar a daki tana mashi fitina akan Asmau,
Wai wallahi yai wa yarinyar nan Asamau fada idan ba hakaba zata ci mata mutunci sosai wallahi,
A zuciye ya juyo inda take a tsaye cikin fitina yana cewa, ban son hauka ki fice min daga daki tunda ke bakya girma ko yaushe,
Ke kadaice mace a gidan nan, da zata sakaki a gaba to kin yi kadan ki hana yan uwana zuwa gidan nan,
Kallon shi take rai a bace tace ni bada ita nake kishi ba da yar ta nake kishi wallahi,
Tunda yarta bata kulaki ba yadda kike so yanzu kin samu mai kula dake sai kuyi tayi,
Zan kuwa bata maku rai keda ita gabad??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ayan ku wallahi, don bazan laminci fitina ba agidan nan,
Bayan kwana biyu ina kwance a dakina ina barci naji kamar ana taba min kafana,
Karfin halin bude idanuwa na nayi inda nagan shi a tsaye a kaina,
Fuskan shi ba walwala yake cewa kiban list din abinda za,a saya maku don zan shiga gari kafin na koma,
Cikin karfin hali na mike zaune ina cewa ya zancen komawan Gwago kaga Dijema ta tafi baka a kasan, lokacin,
Maimaita maganata yayi cikin kwaikwayona a shagwabe, yace ke gwagotace fa bataki ba, ko kin mantane wai,
Abinda ya sakani yin murmushi kenan tare da kokarin mikewa da kyau nace a,a ai ina zaton ko ka manta da zancen tafiyan nata ne, ai,
Yace Ranan laraba su Baba Wadda zasu kai Gwago sai suzo da wace zata dinga kulawa da yaran ko ?
Da sauri nace to amma Yaya ai da sai abar Ramatu da Asamau da yaran kawai ko, ?
Yace ba maganarki bane mun riga mun gama zancen da malam ko har an samo wace zata zauna dasu,
A sake nace Allah ya kawota lafiya Allah yasa ta kwaraice zan samu irin Ramatu,
Har juya zai fita daga dakin bayan nagama yi mai list din abin da muke bukata,
Sai kuma naga ya juyo wanan karon fuskan shi babu wasa ko kadan a cikin sa,
Ya ja ya tsaya yana cewa kiwa Asamau magana ta daina shiga harkan Salawatu please ?
Dan rage murya nayi ina cewa, anyi wani abine kuma, again,
Bai bani amsaba sai jan kofan yayi yafita daga dakin
A yadda na lura shine karar Asamau Salawatu takai gurin shi
Shiru nayi iya tunane na ban san may Asamau taiwa Salawatu ba kuma again,
Amma dai zan mata magana kamar yadda ya ce nai mata din tun da shi bazai mata ba,
Da Gwago zata tafi shirina musan man ne Yaya yai mata don duk abinda tace tana so ansaya mata su,
Tafiyan shi da kwana biyu Gwagona tai muna ta baki takoma gidan Birnin Kebbi acikin murna da jin dadi, da tarin abin arzikin da aka siya mata,
Matar da akazo min da ita, mai suna Luba bata da matsala gata da zafin nama da tsabta,
Don haka na godewa Allah da kuma neman hadin kansu ita da Ramatu,
Dole don kwana da yara suka dawo part dina da kwana inda nida Ramatu muke kwana adaki guda,
Asamau da Amir da Aisha da Luba a dayan dakin suke,,.

****** ********** ******
Yarana basu da fitina sosai don haka nake samun sauki sosai gurin shayar dasu,
Anytime ina dakina bamu fita wanan hiran na gulma da ake duk dare a falon gidan,
Sai dai mu dinga tsinkayo hira da dariya da hayaniyar yara daga falon,
Sadiyace bata faye damuwa da fitowa ba duk da dai takan dan fito ayi harka da ita,
Amma ba fada ba gaba a tsakani na dasu muna gaisuwa idan an hadu wani lokaci,
Sun so su ja Luba yar aikina ajiki amma da yake wayayace sai taki yarda don dama tana da dan labarin irin zaman da ake agidan daga gurin Anty Safiya don yar uwar mijinta ce,
Yanzu lami yar aiki itace tare da Sadiya da salawatu inda tabasu shawaran cewa ya kamata su tafi gurin wani mutumi wanda yake bada magani na gargajiya akan haihuwa,
Allah da ikon shi a lokacin da zasu fita ina a dakina kamar ance infita sai nace zan shiga gidan su Fattu don na mike kafana,
Nai mamaki kwarai naganin su a tare Salawa ce ke jan motar Sadiya ta zaune daga gefen ta Lami tana a baya,
Nai mamaki kwarai don bantaba ganin su a tare zasu uguwa ba ko wani guri
Har shedan zai min huduban zargi amna sai nakawar da zancen da cewa Fattu wace ta rakoni kila Soloon zasu tafi,
Fattu bata yarda da zance na ba sai cewa tayi Saloon har da Lami,

Zaune su ke su uku agaban malamin da suka tafi gurin shi, inda yake sauraren bayanin su,
Salawatu ce ke cewa malam wata bukatace muka zo da ita akan neman haihuwa,
Mu hudune a gurin maigidan mu inda sauran biyun su sun samu ko, dayan ma har yan uku ta haifa bada dewanan ba,
Yace ikon Allah,cikin jinjina kai yace ina sauraren ku, tace
Wanan ita ce uwargidan mu nikuma nice ta uku, agidan
Ita tabiyun mu mai diya ukun yar uwar maigidan mu ce, dayan kuma bawai wani zumunta bane amma a gari guda duk suke da maigidan na mu,
Murmushi mutumin yayi yana cewa to zamu fara gwadawa mugani ko akwai rabon samun haihuwa a gidan,
Wasu sake saki ya basu yace su dafa su dinga sha suna kuma dama kunu dashi da jar kanwa ake amfani dashi,
Sadiya wace duk ta matsu da sufita subar gurin saboda gaban ta sai faduwa yake don tsoro saboda ita irin wa yan nan abubuwan ba damuwar ta yayi ba,
Sai Salawtu ta gyara zaman tace malam sai kuma zancen ,
Sadiya takatse da cewa sai may kuma don Allah tashi mu tafi kawai don ban son mu bata lokaci,
A,a Hajiya Sadiya kinga ki tafi kawai a mota gani tafe don wanan zancen na kowane agidan nan,
Ba musu Sadiya ta mike tana cewa malamin sai anjima itama Lami bayan ta tabiyo su kabar Salawtu aciki,
Tana fita Salawatu tace yeye kawai malam kana jina, wallahi matar shi ta biyu ne nake bukatan akawar muna da ita a gidan idan kuma hakan bazai yi ba a danbalata ta yadda akoda yaushe sai fitina a tsakanin ta da maigidan,
Murmushi yayi karo na biyu yana cewa idan don wanan ne kadai ba matsala don komai zai dawo a hannun ki,
Nan ya shiga yan zane zanen sa a kasa yana kada kai yana gogewa har dan lokaci,
Can yadago kai ya na duban ta yace wanan yarinyar da kike zance akanta gaskiya akwai matsala,
Don zamu iya yin nasara da farko a kanta amma kuma asiri baya wani tasiri sosai a kan ta,
Tace cikin kaguwa malam badai abin zaiyi tadiri ba ba akanta ko na kwana gudane,?
Sai dai kuma fa ba wai lalaine aikin yai wani tasiri mai tsawo akanta ba,
Saboda kamar yadda na fada maki yarinyar tana da babban al,amari mai girma kanta ,,
Cikin wani irin murya Salawatu tace wallahi malam shegiyar yarinyace ni wallahi idan ma son samu ne duk ayi ,,,,
Sai ta dan dakata ta duba kofan gudun kada Sadiya taji ta idan tana kusa,
Sai ta sauta muryan taje malam so nake duk ayi waje da su gaba dayan su har shegun diyan su,
Yace to zamu gwada mugani indan hakan zai yiyu sai muyi,
Ta balle jakarta ta zube mai kudi bayan na farko da suka bashi tai mai sallama,
Sadiya wace ke tsaye duk haushi da takaici ya cikata alokacin tana hango ta tafe taja wani tsuki, ta ce ,
Haba malama don Allah may kika tsaya jira kuma bayan munyi abinda ya kawo mu,,
Murmushi tayi a cikin tace uwargida ke nan aikin san abubuwa ba karewa sukeyi ba akan zancen ciwon kafanane na dan koka mai,
Ai kawi kibari da alama kila aikin wanan mutumin akwai sa,a acikin sa,
Sadiya tace cikin dan tsaki ni kin san ban faye son irin wanan abubuwan malam ba wallahi,
Tuki take a cikin nishadi sai dai tana tuna nen irin halin mace kamar Sadiya dake zaune dirin bawani gyara ko kwas kkwarima
Wai kuma a haka take son miji yaso ta kamar ko wace mace, kai amma dai tir wallahi
Namiji madai mugune wallahi wai a haka Oga ke kwana da wanan mace dirin haka ba wani show,
Ita ko Sadiya sai Allah Allah take su isa gida lafiya kada wani abu ya samay su a hanya ace agun malami suka , fito,,,
A cikin ikon Allah suna dawowa dani suka fara arba ina zaune a falo ina waya da Anty Amarya acikin jin dadi da farin ciki,
Inaganin su kawai naji gabana ya fadi hakan ya tabbatar min cewa fitan su ba alheri bane,,
A fili na furta Innalillahi wa,ina alaihim raj,un Allahuma ajirni fimasibati wa,akalifli hairum min ha,,,

****** ********** ******
Lokacin dawowan maigidan yayi don haka sai shirye shiryen taron maigida matan gidan keyi,
Wanan ranan ne kuma Salawatu ke kokarin ganin ta aiwatar da duk wani shiri akan kudirin ta, ga maigidan,
Tayi hade hade wanda yasha tsumi acikin sa kasancewa itace da maigidan yau,
Allah ya kawo shi lafiya sai zuwa sannu da zuwa ake mai,
Nima nafito nasamay shi zaune atsakiyan matan shi ana ta yan darara ku
Naimai sannu da zuwa tare da tambayan shi aiki da kuma hanyanya ban eani dade ba na shige abina nabarsu,
Saida yai wanka ta gabatar maida abinci da abin sha wanda ya sha jiko da tsimi acikin sa,
Nan yaci yasha yai kat dashi kafin su shige daki ya karasa sauran ajikinta,,


ZEEE MAKAWA YELWA
SEENABU
[12/20,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login