Showing 381001 words to 384000 words out of 388021 words

Chapter 128 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8308

iya tashi yayi ba, saboda shedanun da Salawatu ta hada shi dasu suna saukar mai da kasala,
Amma sai yake dan jin karfin gwiwan zai iya yin nafilan a yau don haka yake ta rokon Allah ya bashi ikon tashi yayi,
Ya dawo gida daga gurin aiki a gajiye don hutu kawai yake bukatan samu yadan watsa ruwa ya huta,
Abin mamaki tun a waje yafara ganin alaman rashin gyara muhalin su da Salawatu bata yi ba,
Salawatu tana zaune a saman three seaters ta mike kafa tana kallon wani Nigeria film da tashan television din tcv ke saka duk talata,
Yashigo yana dauke da jakar shi ta documents da laptop din shi a guri guda,
Ya saba idan ya shigo yasamay ta a haka yakan wuce zuwa gurin tane direct yadan mata kiss a kumatu ko a goshi,
Tun shigowan ahi tawani kura mai ido tana jin wani son shi na kara fisganta,
A tsakiyan falon yau ya ja ya tsaya bai karasa inda take zaune ba kamar yadda ya saba yi mata,
Ta dube shi a wani irin yanayi tana cewa Oga har an dawo sannu da shigowa,
Yace eh naga kamar baki share gidan nan ba kamar yadda na umurce ki da kiyi kafin na fita,
Wani guntun murmushin ta sake tana tcewa wai kai da da gaske kake nice zan yi gyaran wanan gidan gaskiya bazan iya ba akan may ma wai za,a ce wa nice zan, yi aiki kan ka daya kuwa,
Mamaki sosai tabashi don jin wai yau shi Salawatu kewa irin wanan zancen, zata ci gaba da magana yace ,
Cikin dakatar da ita, ke saurara ban son shashanci,
Ni keke son na zage na gyara maki gidan ko kuwa ban son jin wani zance idan kina son kanki da lafiya ki mike ki gyaran gidan nan kafin ranki ya baci,
Ido ta zuba mashi tana mashi kallon mamakin yadda a lokaci guda yajuye Abubakar din ahi da ta sani,
Cikin yar rawan murya tace kayi hakkuri yanzu zan tashi inyi ,
Juyawa yayi zuwa ciki a hasale zuviyar shi sai zafi take mai,don yau a wani yanayi yake jin kan shi,
*******
A wanan lokacin malam baida wani hutu akan kikari kwato dan jikan nashi daga halakan mata,
Tun da Meenatu takawo mai aubuwan amfanin Abubakar yake ta aiyuka a kan shi,
Baba na yafara min zancen tafiya cewa Yaya ya bugo mai ga lokacin da zamu koma wai amma sai malam ya watse su daga shi har Baba din yace sai munyi sati uku zamu koma,
Da kyat, Yaya Abubakar ya yarda dazancen kara kwanakin mu, acikin hakane yazo Abuja yin wani aiki inda matan shi na gida suka danga canji daga gare hi kadan,
Don haka ina ganin sati biyu yayi muka fara shirin komawa inda duk wani abinda zan bukata na dinga sayen su a hankali,
Sai faman shirin komawa mukeyi yayinda nake ji tankar nai zamana agida kada mu koma bariki,
Ita ko Salawatu duk ta shiga damuwa tun ranan da taga yana sallah nafilan da ya saba yi duk dare hankalin ta ya tashi, sosai don tasan cewa an samu matsala
Lami ce ta fado mata a rai don haka takirata taba tambayan ta irin halin da mutanen gidan suke aciki,
Nan take aheda mata cewa ai ita uwar yan uku bata gari don ta kwana biyu bata nan tun dawowan hajiya Sadiya itama ta tafigida,
Ita kuma Fatima uwar ta tazo kwanan ta biyar a Abuja ta koma,
Cikin wani irin tsawa Salawatu ta dakatar da ita tana ce wa yanzu Lami shine baki fada min da wuri ba sai yanzu,
Amma dai gaskiya baki kyauta min ba wallahi kin ko san irin masifan dake shirin yaron gabana Lami,
Ki tagi gurin malam ki fada mai irin matsalan da ake ciki idan kinje sai ki bashi wayan muyi magana,
Ba bata lokaci Lami tabi umurnin sabuwar uwar dakin nata zuwa gidan malamin nasu,
Bayan yagama sauraren ta a wayane yayi dariya yana cewa ai dama kin san cewa aiki yana bukatan tushine,
Don kinga yanzu sungane cewa kina aiki don haka gabadayan su sun mike tsaye,
Koda zamuyi wani abu yanzu bazai kai na farko power ba saboda a yanzu kowa tana iya nata sanin,
A take Salawatu ta rikece tana cewa malam a dai duba agani ko akwai abinda za,a taimakq min dashi,
Yace da sauri gaskiya nafada maki tunfarko akwai wa yanda suka rinjaye ki sosai daga cikin su don suna da babban al,amari a tareda su,
Kin san mutum mai yawan ibada sihiri bai faye tasiri akan shi ba sosai,
Shiru Salawatu tayi duk ta rikice ta rude can ta nisa tace malam ko nawane dan Allah aimin aki akan sh yadawo min kaman yadda yake a farko sai yadda nace,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
SEENABU
[12/28, 11:00 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 9?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL BAAQI

JUMMA,T MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADA MU DA ALHERUSA ALLAHUMA AMEEN=?O?=?O?=?O?

Saura kwana, biyar mu dawo Abuja, mu ka tashi da zancen tashin hankali bana komai ba sai na, Uncle dina da zaiyi aure,
Tun farar safiya wayan Anty Amarya ya ta damu daga barci, daga muryan ta da kuma bugo wayan ta da safe hakan yasani gane cewa babu lafiya,
A cikin tashin hankali take ce min Meenatu wai kinji abinda uncle din ki ke shirin yi, saboda ya ganni da tsohon cikine ko may,
A cikin kaguwa nace, Anty may yafaru, don Allah may akayi may ya faru da Uncle, Anty,,
Take ce min wai Uncle din ki zai yi aure ranan Jumma,a mai zuwa idan Allah ya kai mu,
Rasss, rasss naji gabana ya yanke ya fadi, inda na dafe kirjina a tsora ce na shiga uku nace a cikin damuwa da nuna rikicewa Anty aure fa,?
Tace wallahi Meenatu an wai ma abin takaici shine bai taba fada muna ba wai sai kawai muji zance aure daga sama,
Salati na kara sakewa tare da cewa shiko uncle, a ina ya hadu da wata macen haka,
Tace ai barni da shi idan yana ganin cewa zai min cin fuska ne ta wanan hanya wallahi ni daidai nake da duk wace zai kwaso a gidan nan,
Nace Anty kawai, ki saka mai ido ki barshi da halin sa ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka doka,
Tace cikin wani irin murya mai dan rauni tana cewa wai kin san ita mummy ku tana gani kamar cewa wai nice za,aiwa kishiya bada ita ba
Nace wanan shirmay banza ne ai ita kishiya ta kowace, bata mutum guda bace saboda duk bori guda akewa tsafi,
Tace bakiga ni ba ma jiyane fa yake sanar da mu zancen auren nasa, sai wani cewa take wai Allah ya hada hankulan mu,
Nai murmushi tare da gyara kwanciyana ina cewa, ai ko ta shirya don wanan bulalan ta kowace shadi yaro shadi babba,
Tagumi nayi da hannaye na ina sauraren zancen da Anty ke min akan auren da Uncle zai yi in three days, coming,
Saboda na fahinci hankali Anty a tashe yake don irin maganganun da take zuba min,
Nace Anty insha Allahu zan shigo zuwa gobe ko jibi don mu san abinyi,
A cikin bacin rai takewa ni ai duk abinda zaiyi yaje yayi don yanzu ina fama da kainane
Idan ma yayine don yaga yadda zanyi to Allah ya fushi don Allah yana tare dani,
Nace a sanyaye Anty don Allah kiyi hakkuri ki kwantar da hankalinki, don kin ga,
Indan har yayi ne don ki damu yazo yaga baki damu ba kina harkokin ki shi da kan shi zai fara tunanen abinda yai maki,,
Tace hmm Meenat ke nan kamar baki san halin maza ba nace wallahi Anty share shi zai sa ya fara shan jinin jikin sa,
Ki kwantar da hankalin ki tankar babu abinda ke damun zuciyar ki, don dai shi sha,anin kishi akwai shi da cin zuciya,
Tace min tana zuwa don tayi baki a take rayuwana yabani cewa yan uwanta ne daga gidan su,
Hakan na nufin cewa sun kwana da rikici ke nan a gidan da uncle,
Shine yasaka mutanen gidan su yin sakkon zuwa gidan don sulhunta su,
Hijab dina na saka na nufi part din iyayyena don naga Mamana,
Tana ganina take cewa yanzu nake batun zuwa gurin ki ai, hakan ya sani sanin cewa tana da masaniya akan zancen ke nan,
Don tunda nazo mahaifiyata batq zo part din na mu ba har yanzu saidai in ma wani abin ne muyi waya a tsakanin mu,
Amma yau har take cewa wai zata shigo gurina da kanta,
Take ce min cikin dan yanayin rudewa kunyi waya da uwar dakin ki kuwa sumaiyya ?
Nace wallahi yanzu takirani shine na ce bari na zo gurin ki don ko kin jin labarin may dan uwanki ke shirin yi,
Nace Mama shiko uncle mace da tsohon ciki irin haka, za,ai mata kishiya,
Wani kallo naga tai min mai kama da harara tana cewa ke ba,ai maki hakan bane may ya samay ki,
Nace Mama aini lokacin ina gida ba,a gidan miji nake zaune ba,
Ke nan kina bayan Sumaiyya ke nan ko kin bar kawun naki,
Nace gaskiya mama yadda uncle yayi baiyi daidai ba saboda koda bata da lalura kamata yayi ya fada masu tun farko,
Amma namiji yace wai bai fada wa mace zancen zaiyi aure sai dai mace taji zancen girshi ba harkan yi bace,
Kamata yayi a fadawa mace zancen ba wai taji daga sama ba,
Zancen kara aure ko ince kishiya ba karamin zance bane ga mace tare da yan uwan ta,
Sai dai kawai mutum ya bar wa Allah al,amarin kawai don Allah yai mashi mafita,
Sai dai ina ganin ita Anty ta tayar da hankalinta akan haka don naji muryan yan gidan su sun zo ,
Nace kamar yadda malam tsoho ya fada min Lokacin da za,a auri Salawatu har yau da zancen nake aiki Mama,
Sai naga tai murmushi tana cewa ai kin san shi Baba harkan shi ta daban ce don mutum ne mai tarin ilimi da sananya,
Nayi maza nace mata kwarai Mama don wallahi duk abinda yake fada sai kaga kamar ai wasane abin amma abune mai matukar mahinmanci a rayuwan dan Adam,
Mama tunda malam ya fada min cewa in,tafi inyi hakuri don mace ce yar uwata za,a kawo mu zauna tare don haka na fara kwantar da hankalina don na fahinci ko waye ita bakuwar ta mu,
Sai naga Mamana tayi murmushi alaman ta fahince may malam tsoho ke nufi da kalaman da ya fada min,
Inda a cikin natsuwa yake ce min inyi kokari in kyautata mu,amulana da abokan zaman nawa,
Saboda kyautata yana kariya daga kowani irin sheri da za,a nufi mutum da shi,
Yace min nasan yadda zan zauna da kowace daga cikin su do kowa da halinta, sanan kuma dukkan mu matane, ai, halin mu iri dayane,
Dabiun mu daya don duk irin halin da sukazo dashi idan na kwantar da hankali na zan fahinta,
Amma da zaran amarya tashigo ta samu matar gida tana bori tana hauka tun daga wanan lokacin raini da wullakanci zai fara shiga a tsakani,
Amma idan kin kama mutuncin ki da darajan ki koda ana son ai maki wani rainin wayyo babu kafa ko fuskan da za,a ci maki fuska,
A haka nai ta kawo wa Mama irin musalan abubuwan da na fuskanta a tsakanin zamana da su Sadiya da Salawatu da mukayi,
Nace sai suke gani kamar wai hankalin Yaya Abubakar a kaina yake abinda basu fahinta,ba ina shaye hakkurina a dakina da cikina bani nuna komai na bacin rai dake wanzuwa a tsakani na dasu ta yyada zasu fahinci akwai matsala a tsakani na dashi,
Kiran Mama Saratu da akayi waje don tabawa matar Baba musa abu shi yadakatar da mu daga mu daga zancen da mukeyi inda ta nisa tana cewa Allah ya kyauta yasa mufi karfin kowace kishiyar mu, da wacce ta shigo da wace bata shigo ba, nace a cikin dariya Ameen mama amma ai Baba shi ya rufe ke nan tace ke waya fada maki ko kwanaki ai yatashi dauko maku uwa daga kauye,
Dariya sosai zancen ta ya sani tace wallahi wai a Saran Dosa ya samu wata bazawara ,
Daga baya kuma komay yagani sai gashi yanace min Saratu na fasa auren nan kada in dauko mace tazo cikin iyalina tana min rashin mutunci,
Zanyi magana wayata tai kara inda na dauka don ganin mai kiran
Yaya Abubakar ne a layin wanda hakan ya bani mamaki kira da waban safiyan haka
Na dauka acikin sallama ina mashi ina kwana, cikin yar murya,
Can sai nai shiru ina sonjin wata masifa ce kuma yasa shi kirana yanzu ,
Don tun shigan mu wanan matsakan ba wani maganar dadin rai a tsakanin mu dashi,
Nikaina koda kirana yayi sai naji raina yai mugun baci sosai ban ma son magana dashi, ,
Sai naji yana cewa gobe ne zaku dawo ko ,?
A cikin mamaki na maimaita tambayan da cewa gobe kuma ?
Nace saura kwana biyar ko shidda mu dawo, ai sai naji yace a cikin dan daga murya a bisa umurnin wa zaku kai har wanan time din,
Look Meenat ban son abin ganin iyakar mutum daga kwana hudu kunyi har sati biyu yanzu kuma kince wai saura kwana biyar
Da sauri nace amma ai haka malam yace zamuyi da sauri naji yace yayi kyau dake da malam din zanyi maganin ku ai,
Sai naji ya kashe wayan dip batare da ya kara cewa uffan ba abinda ya sani na nufi kofan fita daga dakin ina dan kun,kuni ina cewa don kada Mama na taji,
Mutum duk ya wani biya takura muna wai mudawo, mudawo idan mun dawo wani abu zan yi mai a gidan halan,
Ni gaskiya sai na shirya tsab zan koma bazan fadawa kowa wanan zancen ba ma balle a takura min sai na koma,

****** ********** ******
Sai harkokin gabana nakeyi irin shirin zuwa Sokoto gurin zancen auren Uncle dina don na kara bawa Anty Amarya hakkuri,
Tsab na shirya nayi kitsona da kunshi da sauran yan shirye shiryen zuwa buki,
Muna zaune ina jiran dawowan Asmau wace ta tafi gidan wata makwabciyar mu anso min sakon da zankaiwa Anty Amarya, na kilishi wanda wata mace ke yi, acikin shiya mai dadi,
Shigowan Asmau da leda bakake manya manya a hannuwanta, ina kallo a cikin mamaki, don naga abin yai yawa sosai very chief,
Take ce min in bari tazo zata dauko abu a wajene, yanzu tadawo,
Na cewa Ramatu wanan abu da araha yake Baba Ramatu duk wanan abin akan dubu biyar kawai,
Ban idar da zancen da nakeyi ba naga Asmau tajuyo da sauri da alaman a dan tsorace take,a lokacin,
A tsorace, nake kallon ta ina son sanin ko may kefaruwa tashigo haka agigice,
Aikuwa kafin tai magana sai ganin Baba na, nayi tare da jin sallaman shi,
Da sauri namike tare da dan gyarawa ina cewa sannu da shigowa Baba muke cewa a tare,
Ya amsa kamar mai rada yana cewa kuna dai lafiya ko mamana na amsa dacewa acikin dan girmamawa lafiya kalau muke Baba ,
Ya amsa da cewa yauwa damanazo in sheda maku cewa gobene zaku koma ko ?
Cikin mamaki na dan dago kaina ina dan girgizawa nace Baba ba gobe bane sai zuwa jibi,
Gobe Sokot,,,, zan ke rufe min baki mara hankali Babana yace a cikin dan sakar min harara ranshi a bace, yake cewa sam ban taba zaton haka ba daga gareki,
Mijinki duk ya damu da ya ga kun dawo amma ke don rashin sanin ciwon kai har kitsaya ko jiran may, o,hoo,
Gobe kishirya ki koma dakin ki don ban son inkarajin kince wai malam yace, sai kin kwana biyu,
Ina daga gefe na rakube acikin tsoro don ganin irin yadda hankalin shi ya daga,, akan zancen tafiyan don da alama Yaya Abubakar ya fada mai maganganu akan zancen,, tafiyan irin yadda naga hankalin shi ya daga,
Ya juyo yana cewa inda Baba Ramatu take zaune yana cewa gobe ku kama hanya ku koma kinji boyar Allah,
Kanta ta gyada acikin da nuna tsoracewa take cewa insha Allahu zamu kama hanya goben,
Muna hada ido da Baba naga ya sakar min harara yana cewa rashin sanin ciwon kai zaki tsaya kina gaddamar komawa da mijin ki,
Kaina na kawar gefe cike da jin haushin Yaya Abubakar wanda ya kawo min cikas ga al,amurana da dama,
Ranan harda kuka nayi saboda bacin rai, da bakin ciki ga zancen zuwa gurin uwar dakina Anty Amarya babu shi ,

Washegari shiri sosai na keyi don ko zuwa gurin malam tsoho banyi ba saboda bacin rai gashi nasan cewa tafiyan dare kenan zamuyi yau don rana yai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login