Showing 285001 words to 288000 words out of 388021 words

Chapter 96 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8293

tubarkallah masha Allah,
Al,ajabi gami da mamakine suka rufeni a lokaci guda duk da ina kokarin bude zip din rigana da ya matse ni don naji dadin bude nonon,
Na kasa furta ko mai sai mamakin Anty Samira nakeyi wace ta nuna cewa jaririn ne dan bangarenta har ta manta da nawa bangaren yadda muke da ita,
Ban fargaba sai ji nayi Mama Abu ta sa hannuwa ta ta jawo nonuwa na ta fara wanke wa,
A tsorace na juyo da sauri daga kallon mamakin da nake ma Anty Samira din,
Nonon nawa sun dan wani canza kama a cikin dan kwana gudan da mukayi sun wani fara cikowa, fan
A hankali ta miko min yaron tare da gyara mai kwanciya a saman cinyana tana mai kama mashi nonon yadda zaiji dadin sha da kyau,
Jan farko da yayi ban san lokacin da na tsala ihu ba don zafin da naji dariyan keta anty Samira ta sake min tana cewa,
Yaro ka zuki abinka da kyau Allah ya sa kasha masu albarka duk da dai kayi wa yayana ritaya a gurin hutawan shi,
Wani irin harara na kara sake ma Antyn nawa wace yau ta rikide min ta koma dangin miji,,
Na bude baki da zuman nai magana nakara jin wani irin dankan nonon da yaron yayi ai ban san lokacin da hawaye suka silalomin a idona ba saboda zafi, da azaban da naji,
A daidai wanan lokacin ne kuma wayata dake daga gefen filona yai kara,
Har kiran ya katse ban daukaba muna ta faman daga da shan nono da su Dije,da mama Abu,
Shigowan wani kirane again hakan yasa Anty Samira tadauki wayan don taga mai kirana,
Yaya Love, tagani hakan yasa ta gane cewa yaya Abubakar ne a layin ke kirana, don haka sai ta dauka don su gaisai,
Tana cewa salamu alaikum yana cewa Mama Baby ina nawa ruwan zafin yake,
Tace yaya ina wuni Samirata Meenatu ga tanan ana bawa yaro nono ne shiyassa,
Cikin dan dakewan murya yace OK Samira kuna lafiya ko ya duke,
Tace Alhamdullahi duk lafiya lau mu ke yaya, yaya su Anty sadiya ya amsa atakaice da cewa lafiya, tace mai barin baka Meenatu din,
A hankali ta karamin waya a kunnuwa na ina jin shi ya sauke ajiyan zuciya,
Abin sai yazama min biyu a lokaci guda zafin shan nono da nake fuskan ta ga kuma muryan yaya Abubakar da nake ji,
A hankali naji ya kira sunana cikin wani irin shauki da kuma kulawa, inda na amsa mashi da naam,
Ya kuke kuna dai lafiya ko ? Nace lafiya a takaice tare da murda baki don zafin da nake ji na kama nonon,
I hope ba wani matsala a tare da ku ko don na kira dazun wayan tana a rufe lokacin,
Kan na amsa mai maganar shi yaron wanda yaji dadin jan nono yakara tsuke bakin shi gurin shan nono,
Ai ban san lokacin da nai wanikaraba sai na saka kuka kawai hankan yasa har nai cilli da wayan gefe guda,
Nan yake jin irin takai din da mukeyi da matan kakan namu alokacin don nace bazan karaba yaro nono sai hawaye nakeyi, don zafin wahala dama can ni matsoraciya ce,ban son abinda ya taba min lafiyan jikina,
Duk draman da mukeyi a kunnuwan yaya Abubakar mukeyin shi tsaba,
Kashe wayan yayi a bangaren shi tare da jin haushin kin ba yaro nonon da yaji ina yi, a zaton shi da gangan ne nake hakan,
Anty Amarya ce ya kira, yana mata korafi wai saboda kawai akwai dan matsala a tsakanin mu da shi shine nace bazan bawa yaro nono ba ya sha,
Ita kuma rayuwan ta ya baci ta bugo min waya a hasale tana fada cewa may yaro yai man da zan dauki fansa a kanshi,
Shiru nayi ina sauraren ta hakan yasa jikin ta yin sanyi ni ko sai mamaki abinda take fadi nakeyi,
Sai da na bari ta idar nake cewa Anty shi ya fada maki hakan,
Tace kwarai kuwa, don yanzu ina kitchen ya kirani yana sheda min abinda ke faruwa,
Nan nake bata labarin abinda yafaru har yake zargin hakan sai take tambayana to dama akwai wani abu a tsakanin ki da shi ne can baya,
Boyewa mata nayi nace babu komai anty abinda kawai akayi ke nan,
Allah ya kyauta tace tare da, tambayan lafiyan mu cikin kulawa, da damuwa,
Nan dai mu ka dan yi hira sama sama da ita, saboda tace a kitchen take a lokacin tana aiki, inda tai min alkawarin idan ta rarage aikin da takeyi zata kira ni don a kwai maganan da take son muyi akai,
Don haka muna gama magana da ita na sake wani irin ajiyan zuciya tare da kokarin kai kaina saman filo don na kwanta da kyau, inji dadin nazari,
Muryan Mama Dije ce ke cewa kin kwanta ne da kin tashi kin sha kunun kanwa da aka dama maki dayani,
Ba musu duk da ban so ba haka na mike zaune ina kokarin saukowa saman, gado don na zauna a kasa,saboda nasha kunun,
Yayi Kore yayi kyau sai, kamshin kayan yaji ke shi daga cikin shi yayin da take dan motsawa,
Cikke a wani cup ta turo min a gabana tana cewa yi ki sauri ki shanye kafin yai sanyi,
Ba musu, nadauka nafara kaiwa a baki na da sauri na cire cup din daga bakin saboda mugun zafin da kunun yayi a lokacin ga yaji yana cin harshe,
Dije wace ban san ta na tsaye tana kallona ba tai saurin cewa, yaya akayi ne Meenatu, ki daure ki, shanye da sauri don Allah dai,
Na daga kai na ina cewa acikin dan bata fuska akwai zafine fa sosai Dije,
Baki bude tace a, Meenatu dama mai sanyi kike son sha ke ? ba mai zafi ba,
Badon naso ba nadauka acikin bata rai ina dan kurbawa a hankali a hankali,
Yayin da nake ji tankar harshe na duk ya sale saboda zugin da yake min,
Sai wani irin zuba ke tsiyayo min tun daga cikin kaina har zuwa, duk wani sassan jikina,,
Sai kokarin gogewa na keyi a hannuwa saboda irin yadda nake jin zafi yana fita min daga jikina
Shigowan kaunata a dakin taga irin yadda nake ta yarfan zufa wani na tsiyayowa,
Tace Anty Meenat wanan irin zufan haka kamar kin shiga oven haka,
Gurin gado ta isa ta zauna ana dan wasa da kumatun baby dake barci abin shi kamar nace tabari kada ya farka saboda ina tsoron ya tashi yace zai sha nono,
Niko yanzu in akwai a binda nake tsoro ko gudu shine, ya farka daga barci yace kuma nono,
Ai ban kai ga karshen tunane na ba sai kawai na ga yadan fara motsi da kafan shi a hankali alaman yana son tashi daga barcin,

****** ********** ******
Abin duniya ya taru yai ma ko wacen su yawa zuwa yanzu don sam basu gane kan maigidan ba,
Don ko suna zaune ne zakaji ya buga waya yana cewa idan sun gaisa da mutun ko cikin hausa ko turanci yana cewa wife din shi ta haihu ya samu baby boy,
Sai kaji ana mai murna yana wani irin kwasan dariyan jin dadi afili ba tare da ya iya boye farin cikin shi ba,
Yau, ma irin haka ne ke faruwa don suna daga gefe a zaune suna sauraren irin yadda yake kwasan dariya da wani abokin shi da suke wayan,
Daga gurin da Salawatu take zaune tana faman dakila wayan ta sai dai zuciyar tankar ya fashe a lokacin don takaici,
Fatima wace ta hankal ta da irin yadda Salawatu ke cika tana batsewa a lokacin sai tai kokarin controlling din nata fushin,
Cikin iya kissan tsofin mata tace mai bayan taga ya gama wayan wai, Sweet Bukar ya masu jegone suna lafiya ko ?
Cike da kwarewa a fanin kissa da shagwaba ta fadi wanan maganan,
Da sauri salawatu ta dago kai a hankali tana mata kallon mamaki,
Cikin murmushi da jin dadi ya ke ce, mata, lafiya kalau suke wallahi munyi waya da su bada dewa ba
Tawani ce Allah sarki tana can da wanan zafin tana fama da ruwan zafi don tsaron lafiya,
Wanan zancen natane yashi dan lumshe idon shi saboda tunawan da yayi da irin artabun da akayi dani gurin ba wa yaro nono,
Can cikin cikin Fatima wani irin takaicin shi taji don irin yadda yake nuna jin dadin shi a fili,
A ran ta tace anya wanan Meenatun batai min mugun tazara ba fiye da yadda nake zato,
Kai gaskiya dole ne na kira mama ta don ta san abinyi kafin na makara,
Sa kuma a fili tadan kakaro murmushi tana ci gaba da bugun cikin shi da cewa,
Amma dai nasan cewa yanzu acan za ai duk wani program muba zamu samu ganiba, kenan muna nan,,,,


, ZEEE MAKAWA YELWA,
[10/18, 10:18 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUAKHKHIR

Gwagona Habbi ta iso washegari wace saukan ta rabi tana tare dani rabi kuma suna tare da mahaifana a na ta yan sha war warin yadda za a kayya,
Yaran Mama Ladi irin su Anty Mariya da Anty maimuna wace tun haihuwana da safe ta iso gidan,
Kullun a gida suke wuni ana ta aikin saka ido da kuma kullawa da warwarewa, akan abin yi kamar yadda ake yi idan an haihu,
Duk yawan masifan Mama bai hana a aiwatar da abinda akeyi a bisa ga al,ada ba ,
Don ko da mama tace kada ayi abu kaza idan Anty Safiya tazo sai ta lalaba ta fadawa Baba sai ya shigo a tsakar part din Mama yake tsayawa da farko ya fara cewa ,
Bayan duk sunyi mashi sannu da zuwa da kuma gaishe da jama,a,
Sai yaje cewa Safiya wai ko ankai kayan wanke fitsar a gurin masu jego,
Yana nufin su Clean da sabulu da icce, da kayan yaji da gero
Take fuskan Mama ya matse don bata so hakan ba sam saboda tasan cewa magana ce kawai ya kawo shi,
Anty Safiya wace dama plan suka hada da Baba tafito daga daki tana daura dan kwali tana fadin Baba shine yanzu muke kokarin hadawa mukai,
Yace idan an hada sai ku kirani na gani, ko mama bata ce komai ba sai wani bata fuska da tayi ta wani hade rai kamar ra kurma ihu,
Sai bayan wucewar shi tace ai shina ya kamata yayi su tunda haihuwan fari ne dan shi yayi,
Sai Anty maimuna tace a,a to tunda Allah ya hutar da shi har 'Dan shi ya samu halin da zaiwa kan shi may zai sa shi kuma wahal da rayuwan shi, yanzu,
Takaicin zancen ta bai bar Mama tace komai ba saboda wani irin takaicin da take ji a rayuwan ta,
Mama tana gani a gaban ta a ka hada kayan Kauri daga dangin kayan yaji buhun gero, sabulun wanki, da su omo clean, Sai kan shanu da kafafun shi, chew gun da kwalayen Sweets,
Tsaye take sai masifa da take tun tanayi a zuciyar ta har ta fara a fili, tana cewa wanan ai rashin sanin ciwon kai ne,
Mutanen da ko alaman yin nasu kaurin baku gani ba shine ku zaku kwashi kaya haka kukai masu indai zurian su Fuldeni ne aikuwa kuna da shan kunya don dai ko kwara basu da niyar yi su,
Baba Buhari wanda ke tsaye yana jiran yaga fitan kayan daga part din Mama Wanda ya jagula mata lissafin ta, akan abinda ta shirya
Don da ita nufin ta duk ta zabge kayan ta mika dan kadan kawai,
Niki, niki a ka kai wanan kayan part din Baba Hamza wanda yake madaurin aure na, saboda kara,
Jama,a sai farin ciki da sa albarka su keyi amma sai Baba Hamza yace a mayar da kayan a part din Baba Musa wanda yake gaba dashi don girmamawa,
Kafin wani lokaci zance har makwabtan gidan mu ya kai don an fara shigowa kallon kayan kauri,
Sam Mama Ladi bata san da cewa za,a kawo komai daga fanin iyayye na ba,
Saboda irin yadda taga babu wani shiri da akeyi daga part din mahaifan nawa,
Sai bayan sallah la,asar ne aka shigo da kulolin kunun kanwa da aka dama daga can gidan wan mahaifiyana, dake uguwar Badariya, bayan Abdullahi Fodio,
Kula biyu na kunun kawa da sugar a cikin wani plastic bucket fari mai marfi,
Sai kamshin kayan yaji ke tashi daga cikin kuloli, da kuma ruwan zubawa na sabon dakan garin gero abin gwanin ban sha,awa,
Haba take kuma sai guri ya kara rudewa aka shiga rabo ana aikawa makwabta, da yan uwa da abokan arziki,
Mama Ladi sai kuma aka fara dan kamay kamay tsegumi tana cewa shi kunnun ma saboda iya kisisina baza,a dama shi nan ba sai ankai, har wani uguwa, yi nai,
Anty Maimuna tace hey Innar mu badai har sunyi sun kawo ba to may ya rage kuma don Allah,,,
Tace naga na Samira cewa kikayi baza,a dama masu su sha banza ba, duk sa Samira ta sai geron ta har kwano, ashirin,
Mama Ladi tace cikin masifa wai shin ke da kike wanga zance kina wani tare magana kada a fadi nawa kin ka kawo,
Murmushi kawai Anty maimuna tayi don inda sabo ta saba da irin gorin mahaifiyar nata yanzu,

****** ********** ******
Sosai yake ta hada hadan hada komai da ya kamata yayi ta fannin shi,
Batare da iyalin gidan shi sun san may yake shiryawa ba, a zahiri, don Hajiya Jummai Dubai ta riga da ta hado mai komai kamar yadda ya bukata,
Ganin bai wani shirin akan bukin yasa uwar iya, bugun ciki kokarin bugun cikin shi da tambayar bata ga fa yana wani shiri a kan sunan dake tafe ba, ko da yake ku yan dangi ne kai da maijegon,
Murmushi yayi batare da ya dakata daga daura agogon hannun shi da ya ke yi ba
Sai da ya daura a gogon shi, tsab san,nan ya karasa gurin da turaren shi suke ya na cewa,,
Shirin may zanyi, ?
Da mamakin jin abinda ya,fada take kallon shi sai wani dadi da ya kumay ta cikin ranta lokaci guda,,
Amma sai tace kai ko dai, Sweet Bukar shirin suna mana wanda zakayi a matsayin ka na uba,
Murmushi yayi a daidai lokacin da ya isa gurin aje takalmomin sa, yana cewa a yayin da yake saka takalma a kafan shi,
Ba a kwai mutane a gida ba, su za su gabatar da komai basai nayi ba ni, ko kina son ace dan fari bana kunyan shi ya fada a cikkn zolaya,
Taji wani irin dadi ya kumay mata zuciya, sai cewa tayi to amma ai ya kamata ace mu a nan fannin mu munyi wani abu dai ko aje dashi,
Yace OK to ai ku iyayyen yaro ne dama sai kuyi shawara akai kuga may za,ayi ko kafin in tafi don kila zuwa gobe ko jib zan tafi,
Bari na fita idan na dawo sai muyi magana akai,muga, yadda ya dace, ayi ko,
Tace cikin kissa tau Sweet Bukar nagode sai in kadawo din asan abinda za,a yi ke nan,
Don dai gaskiya dole ne ayi shiri daga nan badon komai basai don ana zaton cewa muna a birni,
Murmushi yayi yayin da yasa kai ya fita daga dakin fuskan shi dauke da murmshin mamaki,

Tafe yake a motar shi sai mamakin halin irin na mata ya keyi don idan badon kunnuwan shi sun ji mai abinda ya tsura Fatima tana fadi a waya ba
Da babu abinda zai hana shi cewa tsakani da Allah take zancen ta, da shi a yanzu,
Yadda abin ya,faru kuwa shine, ya shigo gida kamar yadda yasaba idan ya dawo daga gurin aiki,
Ka,ida ce sai ya ziyarci dakin, ko wace mace ya dubi lafiyan yinin ta, sai dai ba wai dole kullun yake wanan zagayen ba sai ranan da ya dawo da wuri daga gurin aikin,
Hakan yasa yau ya fara shiga gurin Fatima don itace wace tai girkin rana, a ranan,
Daga gurinta ya nufi gurin sadiya wace zata karbi girkin dare a ranan a dakin Salawatu ce last din shigan shi ranan,
Sai ya tuna cewa bai fadawa Fatima cewa yana son ta hado mai zobo wanda zuwa yanzu yazama mai abinsha,
Zai saka kafa shiga dakin na,ta ne yaji muryan ta tana waya tana cewa ai kawai barshi, Asiya sai na bugi cikin shi inji irin abinda zai kashe mata
Mai makon ya shiga sai ya tsaya daga baki kofa a lokaci guda yana jin kalaman ta sai yai wani irin zufa ya fara zubo mai da yaji tana cewa
Bakiga yadda ya wani susuceba, ne shi a,dole matar shi ta haihu, ya samu yaro,
Ni wallahi har mamaki yake bani wai fa akan Meenatu Bukar ke wanan rawan kafan, haka
Yar yarinyar da duk a cikin yan uwanta a lokacin itace karaman su,
Cak ya tsaya ba tare da ya karasa daga second cotton din dakin ba don haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login