Showing 231001 words to 234000 words out of 388021 words

Chapter 78 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8278

matar da bata kaunar mune a gidan nan, ne
Hakan yasa tun da malam ya bamu magana na fawalla wa raina hakkuri da kai kukana ga Allah nai ta rokon Allah ya kawo mana alheri ga ala,amarin
Kinga kuwa Allah ya karba muna don yau mu dai Alhamdullahi don kin zama abin alfaharin mu, bamu kawai ba har ma kowa sai dai makiyan Allah, zai ce bai gode ba,
Don har yanzu nasan akwai wa yanda basu kaunar auren ku a gidan nan,
Don basu da aiki sai zuga mama Ladi kawai da su keyi don ta dinga hauka abanza tana cin mutunci
Don dai babu yadda zata yi da ikon Allah don ya riga da ya hada zuri,a a tsakanin ku ko
Shiru nayi ina sauraron mama a lokacin da take cewa yanzu gashi har da rabo wanda Allah kadai yasan iyakar sa,,,
Shiyasa aka horemu da cewa duk abinda kagani yazo maka arayuwa to ka rungumi wanan abin maikyau ko mara kyau,
Mutum dai ya roki Allah ya mayar maida shi alheri,
Na amsa wa Mama da kada kai tare da cewa a ?ikin natsuwa hakane Mama,
Muryan Baba mu kaji yana cewa yau dai Saratu bazaki bari yarinyar nan tai barci ta huta ba,
Gashi dama jikin nata ba lafiya amma kin tsare ta da surutu haka,
Nace Baba nayi barcin ne har ya fita min a ido ai shiyasa,
Yace to ta dai barki ki huta don Allah saboda kina bukatan hutu sosai kada kuma ajawo maki wani sabon ciwo,
Daga ni har mama mun bi umurnin Baba inda ita Mama ta tafi ta daura alwala, don yin Sallah nafila,
Daga gurin da nake a kwance na ji ladanin massalacin kofan gidan mu ya fara, kiran Sallah,
Shedan sai kuma yaso ya samu sa,ata don sai a lokacin na fara jin barci a idona,
Muryan Mamana naji tana cewa ke yar Baba ki tashi kada kiyi barci sallah asuba ya wuce ki,
Badon naso ba idona tab da barci na mike zuwa yin alawala don in bi jam,i,
Bayan na idar da salla na koma na kwanta don indan hantse,kadan,
Sai gashi nayi barci mai nauyi har zuwa karfe goma na safe,
Ina tashi na nufi bandaki inda ina tace min ankai min ruwan wanka nayi,
Ban dau lokaci ba na shirya acikin wani koriyar atampan super wax sabon dinki wanda akaiwa dinkin redemaid kuma ban taba sakawa ba ajikina,
Dinkin wanan kayan yasa dan cikina fitowa filli dan dagwas ya zauna min ,
Mayafin da na tanadar wa kayan na yafa tare da saka plat shoes a kafana,
Na samu Mama da yaranta da, da suka kwana gida da ita, don nisa basu koma gidajen su ba saboda ganin dan uwan su yazo,,
Tun shiga ake min wani irin kallon don dama jiya ganin dare su kai min niko ko ajiki na dai gaidasu a mutunce, da girmamawa, ban wani dade da shiga ba part din
Sai ga bread mai yawa, Yaya Abubakar ya sayo yace a kawo a hada wa kowa breakfast, di shi,
Ina jin lokacin da suke tambayan Mama ko a diban ma mutanen, gida ne ?
Amma sai mama tace wai a,a ahada shayin gaba daya abawa kowa,
Abinda mama bata sani ba shi ne duk part din gidan nan ranan ba wanda Baba Wadda bai kaiwa bread da kayan tea ba,
Sai bayan ta hada aka jawo wani tsoho cup duk datti yai mai kanta aka zuba min wai ga nawa, nai murmushi nace na koshi Baba, ya sayo abun kari mun karya ko,
Sam hankalina baikai ga Anty Sadiya wace ta nade a cikin tulin kayan dake saman gadon mama ba tana barcin ta,
Sai gab da zan fita naji Anty Mariya na cewa wai atada Sadiya ta karya ne ko ?
Sai wanan lokacin na farga da cewa tana cikin dakin ashe bata bi yaya Abubakar masaukin shi ba,,,,
A part din Baba musa na samu su gwago da matan shi a zaune, suna raba bread din da aka kawo masu,
Don ita gwago ita ce ke zama da Anty Samira asibiti, tare suke kwana sai da safe take dawowa gida,
Da murna gwago tarbe ni tana cewa ashe na kusa zuwa zaman abuja, banda labari, Aminatu kin tsufa ne haka ?
Matan Baba musa ce ke tambayan gwago ko may,za ta yi acan gwago tace idan Allah ya sauke muna Aminatu lafiya mana,
Da sauri suka juyo gaba dayan su suna kallona a cikin mamaki sai a lokacin ne suka hankalta da cikin dake a jikina ,
Nidai ban wani zauna ba na juya na nufi sauran sasssan gidan don na gaida su sai faman ya jiki suke min da kallon kurullah,,
Anty Aisha da Anty Nafisa da sauran yan uwana sai farin ciki mu ke da ganin junan mu ida suke kallo na acikin sha,awa,,
Na dade sosai a gurin malam tsoho muna hira idan yake bani labaran yan uwan shi,
Da irin yadda suka bashi baya don baida hali shi a cikin su,
Malam yace duk hakan bai sa na damu ba Aminatu sai ma karamin karfin imani da haka yayi saboda nasan cewa Allah bai manta da mu ba, alokacin ina zaune da albarkan arzikin haihuwan da Allah yai min,,
Yanzu sai gashi Allah bai nufi in gyara gaban gidana da kaina ba,
Bai kuma ba wani daga cikin diyana halin da zasu iya yimin hakan ba ,
Yau sai gashi alkawarin Allah ya cika jikana yazo yasa an,buge a cikin yan kwanaki a gama komai lokaci guda, gida ya koma kaman ba gidan malam Manya ba,
May zanyi ni inba in godewa Allah ubangiji Subbanahu wata,ala ba dawanan nan ni,iman da yai min, na samun jikoki masu albarka kamar ku,
Na ansa dacewa kwarai malam gaskiya hakana ne imani da tawakkalin bawa bai tabewa a banza insha Allah,,
A nan part din malam gwago damu takara samuna zaune da malam ya bani Masa da zuma ina dan ci a hankali,
Bata ko kaiga zama ba sai ga su Yaya Abubakar shida Aliyu da Baba Hamza' ya take mai baya, sun shigo har ciki gaida malam,
Duk a gurin suka samay ni zaune ganin su yasa na dan juya ban wani fuskantar su sosai, ina dan dangwala zuma a hankali ina lasa,
Acikin gaisawa gwago ke cewa kai Aminatu zaki ko ?
Sai gurin haihuwa ki ya bawa aya zaki, ?
Kaina aduke nai murmushi kawai bance komai ba,
Sai malam tsoho ne yace mata ai zuma baiwa mace mai ciki komai illa ma ai ana son su shashi sosai duk safe kiyi bissimillah kafa uku ki lasa,
Saboda samun wankewan kwakwalwan yaro da mahaifan mace,
Yaya Abubakar shi sai dariya suke bashi don ya dauka zance ne irin na mutanen mu kawai
Don su hausawa da anyi aure sai zancen haihuwa kuma, da anga ankwana biyu babu ciki anfara zancen ke nan,
Don wata ko bashi auren da akaci ba,a biya sai kuma ashiga na haihuwa,
Gwago Damu tace maisunan malam ashe yar tawa ta tsufane haka ai,dazu nake cewa nice zan tafi zama can birnin taraiyan don kula da maijego da jaririn ta,
Sai lokacin ne malam yace ni ai banso ace yadda Aminatu take haka ba ya biyo hanya da ita ba
Ai da barinta kayi har in zata haihu sai kuzo tare zaifi,,,
Gaban Yaya Abubakar ne ya ba da wani irin a lokaci guda don haka da sauri ya,daga kan shi ya dube gefen da nake zaune,
Kamar gizo ya fani a idon shi don inba dai idon shi ke mai gizo ba to lalai kam
Cikine kuwa girke zama das a jiki, sai yake ji
tankar mafarki yake yi na wanan zancen,
Kai na yana kasa don sai nake jin wani irin kunya ya rufe ni sosai a gurin,,
Ya Abubakar ya watso min wani irin kallon mamaki wanda ya ma kasa iya boyewa mutane irin kallon, da yake min,
Muryan gwago Damu ce ke cewa, ni dai malam idan za,a zama nice mai zuwa
Don nasan yanzu nuna min baranci za,ayi, ace bani ce zan tafi ba,
Malam yace ai dama du ku huta don kinga dai bata da wani nisa a hakan don haka nasan ba lalai bane ko ta koma ko kuma ba adauki lokaci ba ya dawo da ita gida don dai gaskiya bazan so ace tayi haihuwan farko ba,a birni,
Gaskiya kuma malam inji gwago tace don dai ma anan gida zaifi dadi,
Gaza zama nayi saboda abinda nagani a idon Yayana a lokacin don haka tun bai fashe ba na mike ina cewa Baba Hamza ya bakunta da kewan Maman Bi,u,,,
Malam wanda ya ga na mike nabar Masan da nake ci ya daga kai ya kalleni,
Yace ina kuma zaki tafi baki kare cin Masan ba zaki bar shi a nan nai murmushi kadan nace na koshi ne,
Malam ya ce ja ira ke dai kice kunya kawai don kinga mijinki gurin bazaki ci ba ko
Ina nan tun cikin waya kika damay ni da zancen Masa da zuma kike son ci,,,
Barin sa a biyo ki dashi shiyan ku ai kyaci a can idan kin tafi,,
Ya kira daya daga cikin yaran da ake tayar wa a shiyan shi yace tabini da kula masan sashen mu,,,

****** ********** ******
Inna shiga na samu Baba da Baba Buhari Baba musa da Baba Wadda a part din na mu da alaman kayan tsara ban da mu kazo da su ne su ke rabawa,
Don ina jin Baba Buhari na cewa ai Wadda ka kyauta da ka kawo kayan nan, nan don da sun shiga hannun Ladi babu wanda ya isa ya raba shi sai dai su lalace tana kallon su,,
Kasa na gurfana ina gaishe su a cikin ladabi baba musa ke cewa masha Allah Aminatu ashe karuwa mun,ka samu haka Allah ya raba ku lafiya ke ji,,
Na mike kawai na shige daki abina ina jin Baba Buhari yana cewa, amma abin ya bani mamaki don dai ni ji nayi kwanaki ana cewa tayi barin cikin ko?
Kafin wani yai magana daga cikin su Yaya Abubakar ne ya shigo part din mu sai dai kuma ganin su Baba su na ciki ana kasafi sai kawai hakan ya kare mai ahurin abinda yazo dashi,,
Dole ya dan tsaya gurin su ,suna gaisawa da su tare da mai godiya,irin alherin da yake aiko masu,
Yaya ya kalli Baba na yaga duk wahala tasa wani tsufan dole ya taso mai, tausayin sa ne yaji sosai a cikin ran shi ,,
Bayan sun gama gaisawa da Mama na naji yana cewa maryam kaunata ki fadawa Meenat tazo mu tafi asibiti gurin Samira,
Gaba na ya fadi don wani irin nauyi da kunya ne ga tsoro su ka rufeni a lokaci guda,
Mama tashigo dakin tana cewa tashi ki shirya ga mijin ki a kofa yace kifito kutafi ganin maijiki asibiti,
Ganin yanayi nane ta koma sakwarkwatai tace may ya faru kuma ?
Ta jefo min tambaya daga tsayen, da take tana mai kallo na a cikin damuwa,
Nace cikin kokarin kakaro murmushin dole na ce, babu komai Mama,
Amsa tabani da cewa mijinki ya sani Yanzun ko ?
Na gyada mata kai alaman eh ya sani gaskiya tace ai nasan agidan nan dama dole ne yaji
Na ce mata malam tsoho ne ya fada mai, ai,
Kada ki tsaya musayan komai kawai ki bashi hakuri akan kinyi kuskure,
Kuma ke bakisan yadda zaki fada mai bane shiyasa ki kai shiru idan ya gani azaton ki zai gane ne, da kan shi,
Nace wa Mama to nagode sosai,
Muryan Baba na ne ke cewa wai ina Aminatun ga mijin ta yana jiran ta, a waje, fa kun shige daki,
Malam shiryawa na takai shiyassa, ga ta nan tafe, ai,
Mamana tabashi amsa da hakan
Nafito saye da hijab dina na ce wa su Baba na sai mun dawo,
Sukan hankalin su yana gurin rabo don haka basu kula da yanayin da nake ciki ba, a lokaci,
Uwa uwace kawai ta gane damuwar yar ta a wanan lokacin

****** ********** ******
Yaya Abubakar ne na samu a mota shi kadai hakan yasa nagane cewa shi ne zai jamu zuwa asibitin,
Tun daga nesa fuskan shi babu annuri a tare da shi sam ya daure fuskan shi,
Jiki ba kwari na tako har zuwa bakin motar da yake zaune a cikki na bude a hankali na shiga,
Mutanen dake kofa gidan malam a zaune duk idon su yana a kan mu,
Ina shiga naji ya fisgi mota da karfi muka bar gurin,
Lumshe idona na yi tare da dan hade yawu masu zafi don jiran sababi da zai min kawai nake yi,
Ba lai fi don bai ce min komai ba mu,ka shiga asibitin gurin Anty Samira mun samay ta tana barci ga Baby a gefenta tana barci itama,
Mun gaida dangin mijin ta da ke gurin inda Yaya Abubakar yabasu dubu goma da zamu tafi,
Yace idan ta tashi anjima zamu dawo mu gaida ita,.
Muna kokarin barin gurin ne sai Anty ta farka daga barcin da takeyi
Idon ta na ganina tai kokarin mikewa zaune tana cewa Meenatu ke ta ?
Sai kuma ta kalli gurin da Yaya Abubakar yake tsaye yana kallon yar Baby da ke barci tace, yayin da take kokarin mikewa Ina kwana Yaya ,
Ya gajiyan hanya ya fama da jama,a ya amsa atakaice da lafiya kalau,
Ina kokarin zama gefen gadon da Anty take . x kwance naji muryan Yaya yana cewa mu tafi anjima sai ki dawo,
Banda zabi dole na mike ina ce mata sai nadawo anjima insha Allah,
Zan fara tafiya ne naji muryan Anty Samira tana cewa Meenatu ya jikin naki ?
Na amsa da cewa, Alhamdullahi naji sauki ai Anty tace madallah,
Daidai kan junction din da zai fitar damu asibitin FMC ne naji muryan Yaya Abubakar a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ya na cewa
Meenatu may nayi maki zaki cuce ni haka kisani acikin garari,
Ki jefa zuciya ta acikin maraici ki sa na zama abin zunde ga mutane mara tawakkali ga ubangiji,
Why Meenatu why zaki min haka ki haramta min jin farin cikin da Allah ya alfarkace ni da jin sa na tsawon wani lokaci,
Ban iya tsayawa ya karasa ba sai kawai na saka mashi kuka wiwi a cikin motan ina fadin cewa don Allah Yaya Abubakar ka gafarce banayi haka bane da wani manufa,
Shout,up my friend I don't want to hear from you,,,,
Just keep your mouth off,
Shiru nayi ban iya cewa komai ba don firgita da yanayin sa da na yi,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[9/14, 10:18 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
7? 3?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL -MUMEET,,,,

Yan uwa musulmai yar uwar mu musulma Anty HAFSAT ALIYU tana baran adduan ku gare ta za ai mata aiki gobe ko jibi don Allah kusata ga addu an ku,,,,=?O?=?O?=?O?


Bai tanka min ba sai ci gaba da tukin motan da yaci gaba dayi kawai ,
Sunan gurin da naga ya Parker motar shi yasani sanin cewa masaukin shi ne mu kazo an rubutawa gurin Land Of Equity guests in,
Kaina yana a duke sai ruwan hawaye nake yi da sheshekan kuka,
Tsawa ya daka min da cewa malam dan Allah ki rufa min baki kinji kada mutane su zaci cewa sato ki nayi nazo nan,
Da sauri na bi command din shi don kada na kara wani laifi again,
Ya bude marfin motan yafito ina ciki zaune ban fito ba tunda ba,a bani command na fita ba,
Naga ya zagayo ta kofan da nake zaune ya bude min marfin motan a hankali,
Ya bani umurni da in fito daga motan ba musu nafito yana gaba ina baya har muka kai dakin da ya sauka, a sama,
Shigar mu akin naga ya fada saman gado ta baya ya dafe goshin shi da hannayen shi ,
Idonun shi a rufe lub da su tankar mai barci idan ka gan shi,
Daga grin da nake tsaye na hango kujerar zama a dakin don ba,zan iya tsayuwa mai yawa ba,
Don haka na nufi gurin kujeran a hankali ina kokarin zama,
Muryan shi naji cikin tsawa yace zo nan ina zaki zauna kuma can,
Na taka a hankali zuwa gare shi kamar mai sarsarfa,
Cikin ki wata nawa yanzu ?
Idona ya ciciko da kwalla nai shiru ban bashi ansa ba ina dai tsaye guri guda,
Bake nake tambaya ba yace yayin da yake cire hannuwan shi daga fuskan shi,
Ya kuru min jajayen idon shi da suka kada suka canza kalla don yanayi,
Na langabe kaina kamar zan kara fashewa da kuka nace nima ban sani ba Yaya,
Maganar ta doke shi sosai har cikin ran shi ya ji haushi cewan da nayi nima ban sani ba,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login