Showing 171001 words to 174000 words out of 388021 words

Chapter 58 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8265

Ya Abubakar yace malam al,amarin ne kamar na jinnu wallahi don abin ma ban san yaya zan fada maka ba,
Amna dai gaskiya zan iya ce wa aikin jinnune kawai don yadda abinke mata,
A take Yaya Abubakar ya kwashe duk yadda abin yafaru ya gayawa kakan nashi,
Sai da malam ya gama sauraren sai ya nisa yana cewa lalai duniya tai nisa, sosai Abubakar,
Da a kusa kake dani da akwai maganan da zamuyi na musan man akan wanan zancen
Shiru yaya Abubakar yayi yana sauran malam din acikin tashin hankali
Shiru su kayi na dan wani lokaci bayan malam din ya kare zancen shi,
Ya Abubakar ne ya dan kau da shirun da cewa, yanzu malam may nene mafita,?
Malam ya nisa yace Allah ya kare ya tsare amma gaskiya dole mu san abinyi,
Malam tsoho yacs amma duk da haka Wadda zai taso yau din nan in sha Allah,
Sai dai duk wani bayani sai bayan ya iso insha Allah zata samu lafiya, sai daga baya musan abin yi akan zancen,
Yanzu lafiyan ta yafi muna komai don haka sai mu tashi muci gaba da mata addu,a,
Ya Abubakar yace gaskiya ne malam nan ma akwai wani wanda mu ka fara zuwa gurin shi kuma da alaman aikin sa na da kyau.
Malam tsoho ya ce hakan na da kyau, amma don Allah idan Allah ya kawo Wadda lafiya ka tabatar da cewa kasha magani,
Insha Allah inji Yaya Abubakar yana mai cewa kakan nashi,
Malam tsoho yakara tambayan jikin Meenatu da fatan babu wani matsala atare da ita, yanzu,
Nan yaya ya tabbatar mashi da cewa na samu lafiya sosai,,,
Sukayi Sallama inda yaya Abubakar ke ta godiya sai dai zuciyar shi fam da mamakin yadda akayi kakan na shi ya san zancen Sadiya,

****** ********** ******
Har zuwa wani lokaci babu abin kari a gidan don Salawatu tana can tana barci abin ta,
Ga mara lafiya tana neman abinda zataci don yunwa,
Sai bayan dawowansu Ya Abubakar daga kauyen da suka tafi karbo magani, suka, dawo,
Yake tambayan abin karyawan shi Sadiya ce tafara mashi korafin rashin cin abinci tunda safe har yanzu sha dayan rana da wani abu,
A fusace ya shiga dakin Sadiya wace ke kwance share,share saman gado,
Tana kwasan barcin ta hankali a kwance da gani ko wanka batayi ba alokacin,
Wani wawan duka ya kai mata abaya, ta mike a firgice tana cewa my dear, kadawo ne,
Tambaya ya jefo mata da cewa ina breakfast din su
Sai cewa tayi ban samu yi ba don nagaji sosai wallahi hakan ya sa ban tashi ba takarashe tana bata fuska,
Ido Ya Abubakar ya kura mata cikin takaici yana cewa,
Yanzu har da yar uwar ki da bata da lafiya baki masu breakfast ba ki ka bar su hakana,
Mika tayi tare da daga hannayen ta sama ta hada su guri guda,,
Tai wani mika wanda ya bayanar mata da duk wani sassan jikin ta, a fili,
Wani irin tsukin takaici yayi yabar dakin cikin takaici, da bacin rai,
Yana fitowa adaidai lokacin da nafito daga dakina zan shiga kitchen saboda wani irin yuwan da nake ji tankar banda komai a cikina don sai nike ji ko hanji babu,,
Batare da nace mai komai ba na wuce gigice zuwa kitchen din, don neman abinda naci,
Tun bayan dawowa na daga asibiti nake yawan jin wanan yuwan haka,
Indomie na dafa nacika mai ruwa da yaji tun yana asaman wuta nafara diba ina ci,
Ban juye a plate ba tun a cikin tukunya na cinye abina sai da na kusa gamawa na tuna da ruwa,
Gurin fridge na nufa da sauri na balle goran ruwa na kafa kai,,
Sai da na kusa rabin goran ruwan san na kula da Ya Abubakar wanda ke tsaye a kofan kitchen din hannayen shi a harde saman kirjin shi,
Cikin dan kaduwa da firgita nace cikin dan in,in iniya Sannu yaya,
Lafiya kike kuwa ina kokarin tatara natsuwa na nake cewa,
Lafiya kalau nake yaya
Kina lafiya kike cin abinvi haka kamar mayunwaciya,
Nai murmushi kadan nace yuwan dai naji kawai shiyasa,
Don tun da naji sauki sai na fara wanan yawan cin,
Inaga kamar maganin da suka bani na karin jini ke sani wanan yawan cin da yawa,
Ok kawai yace tare da tamvayana may Sadiya zataci ne mai sauki,
Nace ko adafa mata noodles din itama ?
Idan zataci a dafa mata shi din ko ?
Na dafa mata nakai mata sai dai na samu kamar tana barci ne,
Don haka na aje tare da juyawa, a lokacin naji fitowan Mama wace ashe tana bayi tana wankewa,
Nan nake fada mata cewa idan ta tashi ga abinci nan,
Maman Biu ta tabe baki tana cewa gidan ku babu tsari sam wallahi ,
Gida da mara lafiya za,a ce ba,a girka abincin safe ba har yanzun nan ?
Murmushi nayi nace mama yanzu ne dai abin ya juta haka amma da farko ba haka zancen yake ba,
Sadiyace ta bude idon ta daga gurin da take tana cewa tana son cin abinci,
Ba bata lokaci aka bata abincin da na kawo mata tafara ci,
Zan fita waje alokacin ne Sallawatu ta shigo dakin daniyar gaida Sadiya da jiki,
Tun safe bata shigo gaida Sadiya da jikin ba wai sai yanzu,
Ban tsan manin cewa Anty Sadiya ta karba mata gaisuwan nata ba,
Don banji muryan ta ba agaskiya,
Bata wani tsaya basai faman wani ya tsune fuska takeyi wai ita dakin ba ventilation, a cikin sa sam,
Ni dai nai tankar ban fahinci abinda ke wakana a tdakanin su ba,
Sai muryan Salawa mukaji tana cewa Ok Allah ya sauwaka ko,
Ta sa kai ta fita tana wani irin karairaya ga tafiyan nata,
Ina daga inda nake tsaye wani murmushine ya subbuce, min
Sai naji Sadiya na cewa muguwa kawai sai ta cuci mutun tazo tana nuna ita bata san komai ba,
Nan Sadiya ta fara cewa nasan babu inda wanan abin yake sai daga gurin Salawa,
Don na fahinci muguwa ce ta karshe sosai, saboda,
Ance idan mutun yai maka mugun asiri bazai zo gaisheka ba,
Ban san ya akayi bakina yace to ai gata tazo gaishe ki ita, ko ?
Inda nake tsaye Sadiya ta kalla tace cikin takaici, Meenatu baki san komai ba,
Wanan matar da kike gani muguwa ce don ni sam ban yarda da ita ba tun farko,
Baki ganin ko mutum yana ciwo bata damu da ta gaida mutum ba,
Nace niko sai na dauka kishine yake sata yin hakana,
Don idan kin kula ita ra,ayinta duk a watse abar mata Ya Abubakar ita kadai,
Sadiya tace ai tasan yana da mata ta aure shi dn may bata tafi ta auri wanda baida mata ba,
Murmushi nayi ina cewa kowa dai da halinsa wallahi mna ai zaman lafiya yafi zaman irin wanan,
Kishiya fa idan ka hadu da ta kwarai abokiyar zamace,
Sadiya tace kikace ko Meenatu ni ba zan taba yarda da kishiya ba,
Don duk yadda kuke tana son jin sherin ka sabanin hairan,
Wani irin mamaki naji a lokacin da ta fadi hakan don tana nufin har ni bata yarda dani ba don zan iya mata sheri,
Muryan Maman Biu naji tana cewa ni dai wanan matar batai min ba gaskiya bata dace da maigidan ku ba,
Ai duk matar da bata son kwanciyan hankalin mijin ta bata san may ta keyi ba ke nan,
Sadiya tace ba kowa ke harin rayuwa na ba sai wanan makiran don nasan cewa kowa rantsuwa nayi ban kaffara,
Mamakin ta daine ya kara kamani don jin ko may tace akan Sallawatu,,

****** ********** ******
Da yamman ranan suka koma gurin maimagani harda Sadiya, sai dai mama bata samu zuwa ba tace kan ta na ciwo,
Sun samu malamin a gida sabanin dazun da safe da suka zo,,
Amma yace ace da safe yamna su dawo su samay shi,
Bayan yadan dade yana wasu yan abubuwa irin nasu na malamai, ya dago kai yana kallon su,
Yace gaskiya Alhaji a kwai matsala sosai a gidan ka,
Saboda idan har ba a fitar da wanan fitinar ba a gidan to irin haka zaku dinga gani,
Wani irin nisawa Yaya Abubakar ya sauke don jin may malam yace,
Don haka ya tambaya da cewa malam ai sai in sake gida ko,
Don ina ganin cewa hakan zaifi man sauki don ba musan ina wana mugun abin yake aje ba,
Malam wanda yai shiru yana kallon wani tasbaha dake hannun shi,
Can ya nisa ya na cewa ai ba a ainifin gidan akasa wanan kullin ba,
Asalima ba a wanan gatin da kuke yake ba, don haka kaga ba zanven gida bane,
Yace tun can garin ku kazo da abinka, don haka sai katashi tsaye sosai don neman mafita,
Saboda ai ba wanan ne karo na farko da hakan yafaru ba,
Sai dai ku baku iya gane hakan kuma du inda kuka tafi wanan abin yana bibiyan ku,
Yanzu duk yadda akayi akwai akasin da akasamu da har kuka gan shi da idon ku,
Malamin yace barin fada maka gaskiya Alhaji idan har a gidan ka za ai ciki to ba zai taba samuwa ba ga matan ka,
Sai dai idan har babu wanan kullin akusa za,a iya samun ciki bance maka a,a ba,
Wani irin firgicin rayuwa suka shiga gabadayan su sai Lawal ne ya ke kara tambayan malamin da cewa,
Yanzu malam baka fada muna yadda al,amarin yake ba sai magana kake muna adunkule
Murmushi malam yayi yana cewa bazan ce komai ba amma bada dadewa ba komai zai walwale insha Allah,,,
Kuje kuci gabada yin abinda na baku mu gani har Allah ya bata lafiya,

Baba Wadda ya iso garin alokacin su yaya basu gida sun tafi gurin katban magani,
Don haka ni kadaice agida saboda Salawa tafita ita ma alokacin,
Nan Baba Wadda ya fitar da sakon da malam ya bayar akawo min harda zuma mai yawa acikin sakon nakarba tarr da godiya nakai dakina na boye, inda babu maigani,
Abincin da na girka na debowa Baba Wadda, tare da bashi abin sanyi don jika makoshin sa,

A hanya su Yaya Abubakar suna dawo wa daga suleja sai zufa yake faman sharewa,
Don maganganun malamin yana mashi yawo a rai,
Kenan ita Meenatu da ta samu ciki ba,a nan ta samay shi ba ke nan ko?
Sai ya tuna cewa ai, duk yadda akayi kenan tafiyan mu kasar Niger Republic nasamu cikin da ya zube kenan,
Bai san lokacin da ya furta Innalilahi, Wa,inna,Alaihim Raj,un
Yanzu yaya zaiyi ke nan ana nufin crwa idan har zaiyi ciki da wata mace sai bai kusa dawa ke nan,
Bayani dai ya nuna cewa, Meenatu dai bata aciki ke nan tunda har ta samu ciki,
Innalillahi ya kara furtawa a filli, tare da goge gumin da ya karyo mai agoshi,
Watau rashin haihuwa agidan shi yana da wani nasaba kenan da wanan abin sihirin da ya gani,
Ashe zama bai gan shi ba ke nan don dole ne ya mike,
on neman mafita akan al,amarin kafin yai yawa don gaskiya iyanzu yafara son haihuwa, a rayuwan shi,,,


ZEEE MAKAWA YELWA,,
[8/23, 3:53 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-BAAITH

SAKON GAISUWA DA BARKA DA SALLAH GARE KU MASOYA ZAINAB MAKAWA,
FATAN ALHERI ZUWA GARE KU KAMAR YADDA KU KE MIN,
IDAN NACE ZAN TSAYA ZANA SUNAYEN KU BAZAMU SAMU ZANA LABARIN BA YAU,
AMMA DUK MAI KAUNATA DAKU MA YAN UWA MUSULMAI NA DUNIYA
ZAINAB NA MAKU BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA,,,,,,

Tashin hankali wanda yafi karfin furta zance shi Yaya Abubakar ya shiga ciki,
Don sai gumi ke feso mashi da kafafen jikin saboda irin yadda ya ke ji, a lokacin,
Allah kawai ya tsare su don tuki kawai yakeyi batare da yasan may yakeyi ba,
Tunane kala kala sun zo mai a lokaci guda batare da yasan yana yi ba,
Sun iso gida sun samu Baba Wadda ya iso a lokacin don har yaci abinci yai sallah ko,
Nan suka zauna da Baba Wadda a falon gaba dayan su a na gaisawa,
Ina kitchen ina yan aiyu kana tare da kara rusa abincin a cikina,
Jin shigowan su yasa na fito don in masu barka da dawowa,
Kallo guda naiwa yanayin Yaya Abubakar nagane cewa yana cikin tashin hankali,
A take naji banji dadi ba don gabadaya a rude yake sai faman mazurai da idanu yakeyi yana kallon ko wani sashe nagidan kamar mai nemqn wani abu,
A lokacin da naji Baba Wadda zai fara mashi bayanin akan Sakon da yazo dashi sai na bargurin zuwa part dina,
Ganin irin halin da Sadiya take ciki ne Baba Wadda wanda yaro ne sosai amma ya kawo shawaran cewa ya kamata fa asanar da yan uwan Sadiya don a samu wanda zaizo jinyar ta,
Cikin murya mai nuna damuwa da kasala Yaya Abubakar kecewa saida nai tunanen hakan nima,
Don kaga wanan tsohuwa dai tai muna mutunci sosai gaskiya,
Ba kuma zatai ta zama a nan haka ba, don ita ma tana da nata laluran ai,
Matsala guda yanzu shine ai kasan halin irin na Sadiya, ba kirki ne gare ta ba,
Ba ruwan ta da yan uwanta bakajin tana zancen kowa daga cikin yan uwan ta,
Ba ta damu sam da yan uwan ta ba balle wani daga cikin su yaji dadin zuwa gurin ta,
Ai akwai wata wace ta taba zuwa lokacin da nafita karatun wata shidda amma kafin in dawo matar ta wuce saboda irin zaman da su kayi,
Baba Wadda yace amma dai duk da haka ni sai nake gani da dai a sanar dasu zai fi,
Don kada daga baya su zo su ce ai ba,a fada masu ba,
Gaskiya ne kuma inji Yaya Abubakar wanda ya fada cikin bata rai,
Yana cewa zan kirasu in sanar da su idan sun zo to idan babu wanda yazo kuma shi ke nan,

A lokacin Salawatu ta shigo gidan saye da wani dogon riga sai dan wani yalalon gyale daidai wuyan ta,
Gaba dayan su kallon ta sukeyi kowa da irin kallon mamakin da yake mata,
Duk da ta sheda Baba Wadda amma sai batai masa sannu da zuwa ba tasa kai zata shige,
Cikin wani murya Yaya Abubakar yace, Salawatu da karfi abinda yasa ta juyowa tare da dawowa baya,
A cikin bacin rai yace baki ga Baba bane zaune ko baki san shi bane ?
Kunya taji amma sai ta dake tana cewa, gaskitan kula dashi ba don ban kalle gurin ba,
Sannu da zuwa ya hanya tace tare da wuce wa ?iki,
Yaya Abubakar ya dan rintse idon shi don shima halin shi kaman namune don bamu kaunan a taba yan uwan mu,
Baba Wadda bayan shigewan wata ya dubi Yaya Abubakar yace
Maisunan malam wanan matar taka ai ba sa,an yin ka bace, don da alama zatai wuyan saitituwa, kamar sauran mata,
Murmushin yake kawai Yaya Abubakar yayiwa Baba Wadda don jin abinda yace,
Ya san halin Baba Wadda shi bai boye zancen zuciyar shi sam
Wayan shi ya jawo daga aljihun shi inda yafara neman layin wayan mahaifiyan Sadiya,,
Kamar bazata daga wayan ba amma sai yaji muryan ta tana cewa Salamu Alaikum,
Sun gaisa acikin mutunci sai dan shiru ya biyo baya,
Can Yaya Abubakar yace Mama dama Sadiya ce ba lafiya yau kwana biyu ke nan,
Gaban Hajja ne ya fadi don itama kwana biyu kenan da take fama da Dodon ta wan da ya dawo duk jikin shi ya salle saboda tabin da Sadiya tai masa,
Amma karfin hali irin na Hajja sai cewa tayi yanzu may zan yi mata nida ke nan, ku kuna can,
Allah dai ya bata lafiya
Daga haka ta kashe wayan ta tabar gurin cikin kunan rai don a lokacin taji hamman Dodon ta wanda idan yai hamman zakaji wani irin wari, mai doyi, yana tashi, a guri,
Wani irin mamakine ya kama Yaya Abubakar a lokaci guda,
Yadade da sanin cewa,Sadiya halaiyan uwar ta ke gare ta, na rashin mutunci,
Bai kara gaskan tawa ba sai yau din ya tabbatar da hakan ,
Ace yar ki ga halin rayuwan da take ciki amma sai ki cewai, ke ya zakiyi babu Allah ya sauwa sai kawai ki kashe waya don rashin imani,,
Baba Wadda wanda ke daga gefe yana nazarin yadda suke waya da Hajja yace,
Ya ce tayi ma halin nata ko ?
Murmushi mai kama da yake Yaya yayi kawai tare da hade wasu miyau masu zafi,
Daga gurin da yaya Abubakar yake zaune, kasan carpet, ya jingina bayan shi ga kujera,
Ya sanya hannayen shi guda biyu ya dafe goshin sa da su,
Zuciyar shi sai wani harbawa takeyi tana masa ciwo,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login