Showing 60001 words to 63000 words out of 388021 words

Chapter 21 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8207

dai wa yan da take ta sakewa kamar wace hankali ya gushewa,
Muryan Baba Buhari ne mukaji yana cewa, ladi barin fada maki duk nakara jin zancen wanan auren acikin fitina agidan nan to ke ce zaki riga, Aminatu barin gidan auren da kike ikirarin zaki raba,
Kisani kikara sani ba ke kadai kika haifi mai sunan malam ba,
Kamar yadda kike ganin dole mai sunan malam yabi umurnin ki nima dole inbi umurnin mahaifina,
Saboda haka sai mu zuba da ni dake indan kin ce ke a kullun bakya girma,
Daga haka Baba Buhari ya wuce waje fuuu cikin fushi ran shi a bace,
Bakin mama ladi bai mutu ba sai cewa takeyi ai duk mu zuba daku a gidan nan indai nice,

Daga dakin mamana Uncle da anty amarya suna jin ta suka ce wai watairin matace wanan,
Mace kamar iblishiya, bazaki ko tausaya wa mutane ba sai dai ki kara masu zafin bakin ciki,,
Anty amarya ta nisa ta ce lalai za a kwasa da wanan tsohuwar ,

****** ******** ******
Gaba daya diyan malam manya mazan su da matan su suna zaune a gurin da ya kira su,
Addu,a bude taro sukayi tare da neman tsari daga shedan,
Shiru yadan biyo baya kowa na sauraren abinda tsohon zai fadi a lokacin,
Can cikin magana irin ta manya yafara magana da cewa,
Nasan dukkan ku gurin nan kuna mamaki ko jin haushin wanan auren da nasa aka daura jiya na diyan ku,
Kafin malam ya ce wani abu baba Shaibu yace gaskiya malam abin ya bamu mamaki,
Don bamu tsan mani cewa wai, Amina ce za,a hada da Abubakar ba,
Bayan ga yayyun ta da suka girmay ma shekarun ta nisa ba kusa ba,,,
Ga Aisha, ga fatima ga su,,,,,,
Dakata inji malam tsoho yacewa dan nashi dake magana a hasale, cikin bacin rai,
Gurin ya dan kara yin shiru na wani lokaci can, batare wani yai magana ba ko kada kan da su,kafara yi,
Malam yace Sha,ibu a gurin ku ne kuke ganin dacewan su,
Amma ni a gurina sam babu wacce ta dace da shi daga cikin duk sauran yaran dake gidan nan,
A dan daburce gabadayan su suke kallon tsohon don basu gane may yaje nufi da cewa diyan su basu dace da irin Abubakar ba,
Kwarai inji malam yace, ina agurin nan duk kun san irin halin matar Abubakar ko ?
Shi irin yar gidan jiya kuke son akoma agidan idan muka kara cusa masa wata kamar waccan, din,
Acikin diyan ku kaf wacece wace aka koya wa hakkuri da juriya a rayuwa irin Aminatu,
Wacece tasan darajan dan uwa kamar yadda Aminatu keyi da yan uwan ta,
Wanan zancen da malam tsoho ya furta a kan Aminatu ya kara kular da mahassada wanan auren,
Amma sai ya kara she zancen shi da cewa, amma wata rana zaku gane abinda zance na ke nufi, da hakan ko ina a mace ko raye,,,,
Akwai abubuwa da dama wanda a yanzu bazaku gane may nake nufi da wanan hadin ba,
Gaba daya gurin kayi tsit suna masu jinjina maganar tsohon a cikin zukatan su,
A take wasun su sika fara hango hikimar wanan tsohon na aurawa Abubakar aure da meenatu,,
Daga haka malam tsoho ya roke su akan bai son jin wani fitina da ya shafi wanan zancen auren kuma,
Aure dai yatiga da ya kullashi har abada, baza,a taba sance shi ba,
Kafin taro ya karasa watsewa ne Uncle di na ya isa gurin malam din suka gaisa a cikin mutunci da girmamawa,
Nan uncle ke tambayar malam yadda za,ayi da zancen karatu na,
Malam yace to da yake maigidan nata baya kasan a halin yanzu,
Kaga sai ni in ari bakinsa ince kana iya komawa da ita can gurin ka sokoto bisa ga amana,
Amma da zaran maigidan ta ya dawo kasan nanda sun samu hutu zata rika tafiya can tayi a gurin shi har zuwa lokacin da zata karasa,
Mun,gode malam tun da har za,abarta ta karasa karatun ta, ai,
Ka manta cewa mijin ta shima dan boko ne irin ta, ai zai so ilimin ina gani,
Uncle Nafi,u ya kara yin godiya tare da fatan alheri ga wanan auren,
Sosai malam tsoho ya yaba da hali irin na su maman mu,
Kudi uncle yadebo daga cikin aljihun shi ya ba malam din,
Malam yace wai bazai karba ba amma sai uncle yace albarka yake nema ,,,,,,

A tare da meenat su uncle suka koma sokoto wanda hakan yaiwa babana dadi sosai a rai,
Don zamana a gida mama ladi tana gani na fitinar bazai kare ba sam,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/17, 9:34 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
2? 6?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-QAHHAAR,,,

Yaya Abubakar ba,a samun shi idan ba shi ya bushi iska ya kira mutum ba,
Don haka duk wani wanda ke da gurin fada mai zancen auren shi da meenatu bazai samay shi ba,
Karatu ya sha mai a kwanakin nan don haka bai da wani time da zai kira kowa,
Sai dai duk abin da yake hankalin shi yana gida gurin Iyayyen shi da kuma matar shi Sadiya, ga kuma masoyiyar shi salawatu,
Bayan ya gama test din dake gaban shi da kwana biyu ya kunna wayar shi,
Sakon farko daga abukin shine Suleiman jega,
Inda yake mai fatan alheri ga auren shi,
Murmushi yayi a lokaci guda yana mai shafan gemun shi,
Ya ce Suleiman bai rabuwa da wasa aure shekara nawa sai yanzu yake masu good wishes,
Next page ma daga wani dan garin su ne yake mai ba,a da cewa ashe ka shiryawa dawo wan ka gida ne,
Murmushi yayi tare da ko karin wuce gurin don bai fahinci may sakon ke nufi ba,
Daga baba wadda ne wanan sakon, kamar haka,
Duk da nagari ya na nuna biyayya ga manyan shi,Allah ya sa alheri ga wanan al,amarin,
Da sauri ya fara kiran Salawati don yaji lafiyan ta kwana biyu,
Da yar shagwaba tadauki wayan cikin eani murya take cewa miss you a lot,
Ya kike Salawa ?
Lafia dear ya kake can ya karatu,
Ya amsa mata tankar mai jin wani irin kasala saboda abinda muryan ta ya haddasa mai, alokacin,
Gamu nan muna ta fama da karatu insha Allah in two, months zan dawo,
Yar hira suka taba da ita zuwa dan wani lokaci suna mai nuwa junan su irin yadda sukai missing din junar su,
Layin Sadiya yana shiga amma ba,adaga wayan bahar kusan sau uku,
Baba Buhari ya fara kira don yai mai ya gajiyar buki kafin ya kira mahaifiyar shi don yasan zasu dauki lokaci basu gama magana da ita ba,
Mama mama yace a zuciyar shi yana mai gode Allah da ya bashi mahaifiya irin mama yai kuma iya zama da halin ta, tun yana yaro,
Baba bai ce mashi komai ba don shi azaton shi ai Abubakar din yasan da zancen don yanzu zamanin waya ne,,

Da sallama shi ya fara zance da mama don jin dadin muryan mahaifiyar shi dayayi,
Mai sunan malam don kar kaji may zance akan hukuncin da malam tsoho ya yanke akan ka yasa ka kashe wayan ka ?
Malam kuma mama may yafaru da har zan kashe waya na don kar in saurare ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ki ?
May kake nufi,?
Kana nufin cewa bakasan da zancen auren da malam ya daura maka ba yarinyar nan maikama da yar ketare,,,
Aure mama ?
Aka daura ma,wa aure shin?
Ni ko wa wai ?
Kai mana, zan maka karya ne,
Gaban shi ne ya yanke yaba da wani sauti dam, dam,
Rana guda ya daura maku aure ai da su Samira,
Acan Nasarawa din ya tura ?
Inane nasarawa kuma ?
Garin yarinyar da zan aura mana wacce na tura su baba suka tafi gurin ne ma,

Kai sauraran ni da kyau kaji,
Aure yadaura maka da yar gidan Baban ka Samaila, nan gida,
What yafadi da wani irin karfi a lokaci guda,
Magana mama ladi keyi a cikin fada da daga harshe
Amma sam bai iya cewa ga abin da taje cewa a wanan lokacin, don rudewar da yayi,
Idan akwai abinda ya tsana yanzu shi ne auren hadi,
Auren hadi masifa ne don da wuya a dace a cikin sa in ba Allah ya gyara ba,
A ka wayar tagaji ta tsunke, don ba wani respond,
Duk irin sanyin da akeyi sai gashi yau yana keta wani gumi, alokaci guda,
Tun daga kwanyar kan shi har izuwa kafafuwan shi wani irin zafi ne yake ji
Atake ya ji yawun bakin shi ya bushe, a lokaci guda,
Daga can kasar makoshin shi yadan furta a hankali malam tsoho why ?
Why malam, ?
Why please ?
Don may iyayyen shi ke yawan tauye shi ne da yawa ?
Shima fa mutum ne yana da ra,ayin kan shi sosai,
Akwai abubuwan da yake so da yawa arayuwan shi amma gashi auren shi da Sadiya ya hana shi,
Yanzu kuma ace ankara mashi wata watan ma kaunar shi dake ganin shi da mutunci,

Direct gurin da window yake ya nufa saboda ya na son shakan fresh air zuwa yanzu,
Inda ace shi yarone yau da yayi kuka son ran shi sosai,
Saboda irin yadda yake ji izuwa yanzu,
Baba Samaila don may zakai min haka ?
Bayan ga yadda mukayi da kai akan da nadawo zaka kama min zancen aure na da Salawa,
Sai kuma inzo inji irin wanan yankar bayan da zakai muna,
Ina, gaskiya sam da sake hakan bazai yuyu ba sam,
Dole su san yadda za suyi da yar su shi ba ruwan shi a wanan zancen,
Baya yadawo inda ya samu guri ya zauna idon shi a lumshe yake tunanen abinda yasa Sadiya taki daga mai waya ke nan ashe ?
Tsuki ya ja tare da dan basarwa yana cewa tana nufin wai tana kishi na ke nan,,,,,

****** ******** ******
Hajja ta shiga wani irin hali jin cewa mijin yar ta da take juyawa aganin ta daga shi har uwar shi,
Duk da tasan cewa jinin gidan malam tdoho akwai karfi,
Da wuya ta shawo kan Abubakar irin yadda take so, tayi,
Amma duk da haka ba laifi tana samun irin yadda takeso a gare shi,
Don dai ba karya ba ta fi iyayyen shi cin abin hannun shi,
Yanzu ga wanan tsohon mai wayo da fasaha yana kokarin kafa TARKO, a tsakanin su,
Amma duk da haka tasan yadda zata nade su daga shi har har wanan yariyar da aka lakaka masa,
Tsuki taja tace kai ni. Hajja aiko ba abin hannu shi akwai TARKO babba atsakanin su inda take cin moriyar shi ,,,
Yanzu abu guda duk taruwa zatayi gaba dayan su ta sa masu irin TARKO ta,
A fanin mama Ladi bata da wani babban matsala amma fanin malam tsoho ta rasa irin yadda zatayi da malam tsoho,
Amma dole dai ta canza zani kafin wanan tsohon ya kware mata wanda ke a jikin ta,
Dakin Dodon ta tafada don su san abin yi kafin ta makara,,,,,

****** ******** ******
A gidan uncle Nafi,u haka Meenat takoma kamar wata wace bata da lafiya,
Ko mummy yanzu tadawo tana tausayin Meenat don ganin dai ai tayi wa dan uwan ta nisa sosai,
Da kyat Anty amarya kan samu ta dan ci wani abin don gudun kar wani ciwo yazo ya shige ta kuma,
A sannu sannu nafara sakin jikina don sai ina ganin kamar abin ba mai yuwa bane
Don aure irin nawa ai tankar almara ne don miji na wata nahiyar ni ina nan,
Kawai sai na dauka a haka auren zai ta tafiya batare da ma mun tab hadu da shi ba,
Izuwa yanzu karatu na ya na cigaba sosai don ban sa wani damuwa ba, atare da ni,
Acikin hikima da kuma fasaha Anty amarya take koya min yadda rayuwan zama auren yake,
Musan man ma mai kishiya iri na da yadda zaka zauna da kowa na tare da maigadan ka
Sauda yawa Anty zatace in raka ta zuwa unguwa idan munje sai inga yanzu ba kamar da bane don ko naso fita daga dakin zata hana tace,
A,a haba meenatu sai kace wata bakuwa ki zauna kawai abinki,
Ina daga gefe zan dinga jin irin yadda suke hurdodin su na matan aure,
Wanda kunya yakan kamani sai dai na komatankar ban fahinci may suke cewa ba,ai,
Iyan,zu nakoyi yadda mace zata dinga kula da tsabatar jikin ta musan man macen aure,
Don idan Anty na ce da girki a gabana tankan zauna tadinga yin duk wani abinda mace ya dace tayi kafin ta tafi zuwa ga mijin ta,
Ni kai na nasan cewa nawaye sosai fiye da tsan manin mai karatu,
Anty takan fada min cewa bakin maigida da tallaka da mai kudi dan birni da dan kauye duk na mace ne,
Ka rungumay su da kyau don watarana suma zasuyi maka amfani
Idan tana irin wanan zancen kai kawai nake kada mata alamar na gamsu,
Abinda nafara fahinta shine aikin gida yanzu kusan mukeyin shi da anty amarya don mummy bata damu ba,
Saboda ita irin matan nan ne masu ji da kan su sosai,,,,,

****** ******** ******
Yasan cewa bai kyauta ba irin yadda tsohon ke kyautata mashi bai kamata ace ya shere shi tsawon zuwa yanzu ba,
Don haka cikin daurewa ya daga waya ya kira layin tsohon,
A kwance yake yana dan duba wani littafi a hannun shi,
Karan wayan yasa yaduba inda yaga mai kiran nashi, yau,
Cikin murmushi ya dauki wayan yana maikarata a kunnen shi,
Dama tun da yaga jikan nashi ya share shi yasan da cewa sunyi mai laifi, amna sanin halin shi yasan zai sauko ne,
Da sallama ya dauki wayan yana ma fadar Assalamu Alaikum,,,
Shima ansa mashi yayi a dayan bangaren a dan sanyaye,
Malam tsoho ya ce a maisuna ai nadauka fushi kakeyi dani shi yasa duk kwanakin nan baka kirani ba kamar yadda ka saba,
Cikin dan sake murya yace haba akan may zan yi fushi da mai sunana,
Murmushi jin dadi tsohon yayi har cikin ran shi, don jin abin da jikan nashi ya fadi,
Tambaya ya jefo wa kakan nashi da cewa don may ka yi min haka malam,?
Bawani tsaiko malam yabashi ansa a gadaran ce da cewa,
Don na isa daku dukkan ku daga kai har ita,
Shiru Abubakar din yayi a lokacin don yasan tsohon nada wani manufa dacewa hakan,
Sai kuma ya kasa daurewa yace amma malam kasan cewa yatiyar kauna tace ko,?
Ashe malam baka ja min raini ba kuwa,
Malam tsoho yace aiko ni na fika,sanin cewa abinda ya yika,shiyayi ta nida nai silar zuwan ku duniya,
Shiru yaya Abubakar yayi a lokacin don bai san may zai cewa wanan tsohon mai magana agadarance ba,
Na tabbatar da cewa zaben da nai maka bazaka taba dana sani akan shi ba,
Saboda ta ko ina wanan yarinyar takai kuma zaka ce nace, ma,
Ya Abubakar yace malam ni fa ba mai kyau na ke so ba ko wani abu can,
Takwarana kai kan wani irin zubune kai ?
Mutum sai kace ba wayayye ba dan boko ?
Kowa na son macen da zai yi alfahari da ita a ko ina amma kai Allah ya baka har kake wani zance,
Shiru yayi don takaicin maganar da tsohon yayi wai Allah ya bashi ,
Allah ya bashi wani sabon wahala ko may ?
Can ya ce malam nasha fadama cewa akwai abubuwan da nake so daga irin matar da nake muradin aure,
Yace to shike nan yanzu zabi ya saura gare ka idan har baka samu abinda kake so daga ita yar uwar naka ba ,
Sai ka sako min ita Allah ya bata daidai da ita,
Ba hakana bane ai malam tun yanzu kafin aje ko ina kasan abin yi,
To Abubakar sai ka yi yadda kake so kaje kayi duk abin da ya dace kake ganin shine daidai,
Dama ai yanzu igiyar auren a hannun ka yake,
Shiru su,kayi gaba dayan su bawani mai iya cewa komai don kowa yakai wuya,
Can ya tsinkayo muryan dan tsohon nacewa,
Abubakar kasani cewa muddin ka ce zaka tsinke igiyoyin nan uku da muka tofa ma, ku a tsakanin ka da yar uwanka,
Lailai ko banda rai zakave na fadamaka nadama yana atattare da kai,
Wanan yarinyar daga ita har mahaifanta basu da labarin komai akan zancen nan,
Yadda kaji shi su ma a haka suka tsince ,shi
Yanzu kai nake sauraro hukuncin da ka yanke akai,
Mukwan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login