Showing 255001 words to 258000 words out of 388021 words

Chapter 86 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8205

min gida haka ku da yawa, ?
Malam tsoho sai da ya gama tufe ta tas yace wa almajirin da taba sako mika mata abinta kajiya,
Yaro ya mika mata sai taki karba tafara cewa shin laifina kuma don na aikawa Meenatu da alheri,
Cikin wani irin murya malam yace ke dakata ki jiya,
Daga yau daga rana mai kama ta yau ina maki kashedin shiga harkan yan gida na,
Duk wani sheri da makircin ki bai taba tasiri a kan mu, ni da zuria na,
Don haka tun wuri wallahi ki fita harkan yaran nan na fada maki tun wuri inbashi ba sai na tona maki asiri a garin nan kowa yasan dake,
Yanzu wanan mugun abin zakice wai akaiwa jikata ace ta dafa, a,zaton ki, bazan gane ko may ye ba ko,
Shin kin san kuwa nasan lokacin da kikai mugun abu ajiya gidana da sunan wai kn kai boyon jarkokin mangyada a boye maki alhali ba jarka bane mugun abinki,
Kin kai kin aje nufinki yai ta lasan min jikoki na su yi ta ciwo arasa may ke damun su,
Shine kuma yanzu don kinga wancan ba riba ki sauya sallon ki zuwa, kawai jikata wai kaza don taci ki mata aibu ko ?
Hajja a take tasa kuka wai ita sheri akai mata don anga bata da gata yanzu don ta fita zancen kowa agari shine kuma za, a kawo mata sabuwar kazafi har gida
Kaza koma gurin da kika fito take kaza ta sheka zuwa cikin gida da gudu sai dakin Hajja,
Malam tsoho ya ba mutanen shi umurni yace kubi kazan ku kamo min da sauri Hajja ta tare bakin kofan gidan ta tana cewa walle babu mai shiga min gida ,
Da sauri ta koma daga cikin gidan ta rufo kofan gidan da karfin tsiya,
Tana cewa walle babu katon da ka,shiga min gida babu gaira babu dalili,
Malam tsoho yace cikin daga murya ki saurara kiji daga yau nai maki kashe ga duk wani wanda ya shafeni,
Idan ba haka ba sai asirinki ya tonu a garin nan kowa ya gama ganin ki a fili dake da sihirin ki,
Daga haka yacewa jama,an shi su juya su koma gida,
Mutan shiya tsoro ya fara kamasu saboda yanzu sun yarda cewa Hajja muguwa ce ta gaske,
Don haka suka saka mata suna (Hajja gungumanma,)
Labarin duk ya cika gidan suna da gari cewa Hajja tazo kama kurwan yar gidan malam tsoho asirin ta ya tonu,
Ganin haka yasa Anty Amarya yanke shawara cewa mu tafi kawai tare da su duk da dai malam tsoho yace babu wani abinda zai faru insha Allah,
Amma sam Anty bata yarda ba ita dai ta matsa cewa mu tafi tare kawai tunda kwana, hudu ya rage dama na shigo sokoto din,
Don haka na shirya na bisu muka tafi tare dama can ban son bin Aliyu abokin Yaya Abubakar don yanzu ban yarda da,shi ba sam,

****** ********** ******
Hakalin Salawatu yai mugun tashi zuwa yanzu abu goma da goma ya taru ya cakude mata a lokaci guda,
Da zancen ciki zataji ko da fahintar da tayi cewa maigida yana zancen soyayya da wata can daban,
Da farko tana ce ko Meenatu ce yake irin wanan soyewar da ita sai daga baya take fahintar cewa da wata mace can daban yake zance,
Wanan abin yai bala,in tayar mata da hankali idan kuma tai zurfi ga tunane sai zancen cikin jiki na yazo mata, arai ,,,
Don haka ta yanke shawara cewa taje gurin Lubuna don jin yaya zatayi ne wai,
Bata lokaci ta nufi gidan kawarta aminiyarta don su san yadda zasu bullowa al,amarin gaba daya,
Sai da Lubuna ta gama sauraren tsab san nan taja wani dogon tsuki tace,
Amma wanan Meenatun banza ce kamarta first class zata tsaya bata lokacin ta ga namiji,
May zatagane gurin maza da har ta tsaya wani yin ciki haka ?
Saura kiris fa na nuna mata feelings dina gare ta fa wallahi ,
Ina masifan son yarinyar nan kamar na mutu a raina,,
Koda zan bata duk abinda na mallakane idan dai zata yarda dani ba zan damu ba,
Salawatu taja dogon tsuki tace amma dai Lubuna ke wata banza ce wanan yar malaman har kike ganin zaki samu sa,anta haka,
Wa yanda suka sha tabara sun sha yasin tun suna a cikin zanin goyo,
Kadama ki fara wanan zancen don wallahi zaki sha wuya sosai a wajen Ogana idan ya ji ki,
Ke an fada maki cewa ko may zai min idan dai na samu hadin kan ta ni ba zan damu da wani barazanan shi can ba,,,
Wani irin tsukine Salawatu taja tana cewa wai Lubuna yaushe ne zaki daina wanan harkan please ?
Nifa yanzu gaskiya duk itin wanan abubuwan bana sha,awan su tun yin aure na,
Lubuna tace, ke kikace shin dani dake sunan mu gudane please ?
Salawatu tace cikin jan tsuki don Allah ni ki ban shawara ki daina min wanan zancen mafarkin please ,,,
Cikin wani irin rausayar da kaine Lubuna take cewa, yanzu shi wanan dan akuyan mijin naku may zai yi da wata mace can,
Bayan wa yan nan abubuwan da ya tara a gidan shi haka fon bai san irin sa,ar da yasamu na mallakan wanan Meenatun ba yar tsaka,tsaka da ita,
For god sake Lubuna ki daina yawan dada wanan yarinyar haka please, i don't want to hear that please,,,
Ok inji Lubuna tace yanzu dai ina ganin zancen farko shi ki san ko wace irin yarinya ce yake nema a yanzu din,
Kafin duk muce zamu dauki wani mataki dole ne fa sai mun san ko wacece ita din ,
Sai zancen cikin Meenatu kuma shima ya kamata musan ko how may month take yanzu don inda hali kawai mu taushe shi tai ta zama dashi a jiki ina ga hakan zaifi,
Sai, lokacin ne Salawatu tadan ji dan sanyi sanyi a ranta tace muguwa shiyasa nake son ki wallahi badai kawo sharan da zai fitar da mutum ba ,,,
Daga haka su kai sallama da juna Salawatu ta dawo gida don gudun kar maigidan bai dawo daga gurin aikin shi, ba,,

****** ********** ******
Daga gurin da take kwance, suke waya da yar uwar ta, sun gaisa acikin mutunci da Habiba,
Sai can taji Habiba ta fashe da kuka acikin wayan abinda yai mugun tayarwa Sadiya da hankali ke nan,
Cikin daga murya take cewa may yafaru Habiba halan wa ya mutu, ne,
Cikin karfin halin da jan kuka Habiba take cewa, ai da mutuwa, ne da da sauki wallahi,
Subbahanallah inji Sadiya takara tambaya cikin daga murya may yafaru ne wai,
Nan Habiba tafara korowa yar uwar ta irin abin kunyan da mahaifiyar su tajawo masu agidan sararkan su,,
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ne tasake a lokaci guda,,
Daidai lokacin ne, Abubakar ya shigo dakin kamar yadda ya saba,
Da sauri ya karaso gurinta yana cewa ke may ya faru wai lafiya dai ko ?
Na shiga uku, Abubakar yau, mama ta tozarta mu a idon duniya,
Tsaye yayi yana kallon ta cikin tashin hankali yana tambayanta may wai ya farune,
Ta kasa magana sai cewa takeyi wai fa mamata ce fa, wai Meenatu Mennatu fa,
Gaban shi ne yaba da wani irin kara damm, damm a lokaci guda a rude yana cewa Innalillahi Meenatu na tai may wai may yafaru da Meenatun ne wai fada min mana may yafaru nace, maki,
Yadda taga Abubakar ya rude a lokaci gida ya shiga cikin yanayi na tashin hankali yasa ta fada mai exactly yadda yar ta Habiba ta fada mata,
Innalillahi bakin shi ke maimaitawa acikin rudewa yana kokarin ciro wayan shi daga cikin aljihun rigar shi ta gaba,
Yayin da ya fara tafiya acikin rudewa yana kiran layin wayan nawa,
Sai dai bai shigaba a lokacin don banda caji a wayan nawa,
A rude ya karasa gurin daya daga cikin kujerar falon ya zauna yana kokarin kiran layin kakan shi, malam tsoho
A lokacin da wayan ke shiga lokacin ne su Baba Wadda da Baba Hamza, su ka shigo falon don cin abinci,,
Cak suka tsaya sauraren abinda yake cewa malam mun wuni lafiya yaya jama,a
Ina Meenatu take ne nai ta kiran wayan ta ban samay taba ko lafiya taje,
Murmushi malam din yayi yace bata fada maka cewa ta koma sokoto gurin kawunta ba,
Malam yanzu nake jin wani labari da ban fahince shi ba dangane da Meenatu din da mahaifiyar Sadiya,
Daga gurin da baba wadda yake tsaye yace innalillahi,
Meenatu dai Meenatu ta mu Hajja takama ko kuwa dai,?
May ya kai Hajja kuma ga Meenatu wace bata ko shiga mutane
Yaya Abubakar wanda ke waya yana sauraron bayanin malam, tsoho ta waya
Ya dan dago kai ya dubi gurin da matasan samarin biyu su ke a tsaye suna kallon shi da sauraren shi a cikin kaguwa, da son jin may ke faru, ne wai ?
Muryan Yaya Abubakar su kaji don basu jin ta malam tsoho yana, fadi a fili cikin daga murya,
Wallahi malam da ta samu yi wa Meenatu wani illa wallahi da ba zan kyale wanan macuciyar matar ba,
Ashe shiru, shirun ta na muguntane haka harda nata take cuta,,
Wallahi malam in fada maka mutumin na garin suleja mai maganin nan,ya fada min cewa,
Sai munyi matukar mamaki idan mu kaji mugun abinda tai muna tun farko,
Amma sai na hana saboda wai naga cewa hakan bai,dace ba
Saboda saurari irin wa "yan nan mutanen baida amfani gaskiya,
Don yana ragewa mutun ima ni shi sosai dan haka sai kawai na share zancen don zatona,
Kawai wani hanyane na neman kudi ya bullo min dashi,
Duk da dai mutumin bai taba bukatan ko kwandala daga gareni ba, duk zuwan da mu ke yi din,
Kawai dai ni banga dacewan hakan ba shiya sa ban damu da nasan komai akan zancen ba,
Malam ya nisa acikin waya ya kira sunan mai sunan nashi yana cewa saurara kaji maisuna ,
Yanzu fa ya zama dole mu dauki mataki a kanta saboda kaga zakafara tara zuri,a,.
A take hankalin Yaya Abubakar yai matukar don dai zancen tdohon nan da ya fada mai gaskiya ne,
Dole ne yasan mata,kin daunka tun kafin ya kai ga makara daga al,amari,
Sunyi da malam tsoho cewa zai taimaka mashi da yan abubuwan da ya kamata ayi a gida da waje kuma, don riga kafi,

****** ********** ******
Yaran gidan Uncle dina musanman diyan Anty Amarya sai murna da farincikin ganina su keyi
Sunyi hutun makaranta, a,lokacin hakan yasa su ka damu daman lake min,
Gashi wani irin jaraban cin kwai,da kwai (awara) ya zo min a rai sai mu sawo da yawa mu zauna gaba dayan mu yaran gidan muyi taci muna hira,
Ranan da zantafi school don submitting din form dina dake gurin Uncle dina already,
Wani irin dogon riga mai shegen kyau daga cikin kayan lefe na na dauko shi da zan,zo Birnin Kebbi, daga Abuja,,
Duk inda nabi sai kalona suke saboda rigar ta hadu sosai,
Ni kaina nasan da hakan cewa rigar ta hadu sosai don riga tana kyau, kusan duk riginar haka suke akwai ma,wanda "yan suka, fishi kyau sosai, daga cikin kayan,
Ban sha wani wuya ba sosai domin wanda Uncle yace na kawo mai takarda na shine wanda yai min komai gurin submitting,
Ko da na dawo gida duk a gajiye nake kafara yai wani irin sutum sutum ya dan hau,
Tunda na ci abinci na samu guri sai barci mai nauyi da ya ziyarce ni a lokacin
Nasamu barci don nayi shi sosai a ranan don sai da na koshi na kwanta,
Can a cikin barcin ne nake jin wayata dake a gefena yana ringing,
Har ya katse ban iya bude idona don na duba ko waye ba a lokacin,
Sa,ke shigowa wani kiran yayi a lokacin ban san lokacin da nai tsuki ba daga cikin barcin duk da ban san ko waye mai kiran nawa ba,
Dole na mika hannu na na dauki wayan tare da yin wani tsaki,
Batare da na duba mai kiran nawa ba na karata a kunnuwa na cikin murya irin ta mai barci na ce,
Assalamu Alaikum,
A fusace naji maganan shi cikin daga murya yana cewa,
Wanan wani sallon wullakanci ne kuma ki,ka samu Meenatu aita kira kina kin daga waya,
Muryan shi ya sani gane cewa Yaya Abubakar ne ke magana,
Cikin ma rairai ce murya nake cewa Ya, Saudauki wallahi barci nake ji ban ji kiran ba sai yanzu,
Dama kiran nawa bawai ya damay ki bane don da kin ne may ni da baki jini ba kwana biyu,
Ya karashe maganar shi da cewa ke kadai,ce ke min wanan halin don kin san cewa, bazan dauki mataki a kanki mai zafi ba, ,
Indai fada ne irin na Yaya Abubakar zuwa yanzu na saba dashi sosai bai zama min bakon al,amari ba, a gurin shi,
Na amsa da cewa ba hakana bane duk kwana kin nan, ban samun zamane ,shiya sa I am always busy ,,
Ya aiki ya mutanen gida ?
Nai saurin kawar da zancen don ya daina korafi a kai,
Kamar ba zai amsa mn ba sai naji ya amsa cikin dan bacin rai da cewa duk lafiya kalau,
Kafin nayi wani magana ya jefo min tambaya da cewa, Yaya akayi kika tafi baki fada wa Aliyu ba kamar yadda nace maki,
Dan shiru nayi kamar mai nazarin zancen shi ya kara jefo min tambaya rai a bace da cewa tambayar ki na keyi don may kika tafi batare da yadda na tsara maki ba,
Nace a hankali duk na gama rikicewa su Anty Amaryane sukazo shine nace barin biyo su kawai mu zo tare,
Ya ce amma kin san cewa, bsi dace nabarki kizo masu hakana babu komai ba duk da dai ba wai zasu damu da zuwan ki din hakana ba ,
Amma ai ya dace ace kinzo da tsaraba bawai hannu sake ba,
Shiru nayi bance komai ba ina sauraren shi har ya kare zancen shi,
Ni dai sauraren shi na keyi don ba zan yi yadda yace ba don ban yarda da Aliyu ba yanzu,
Sai daga baya bayan ya gama sababinsa yake cewa ya muke ya lafiya na dana baby yake,
Nabashi amsa da cewa Alhamdullahi ranan Tuesday zantafi awo anan sokoto,
Yace ok hakan yana da kyau ai, ba dai inda ke damuwar ki ko ? na amsa mai da cewa banjin komai sai hamdallah,
Munyi sallama dashi babu wani zancen dadin rai da ya wakana a tsakanin mu,

Bayan ya kashe wayan duk da yana jin bacin rai a rayuwar shi ,
A hankali ya lumshe idon shi tare da kai bayan shi a makarin kujerar da yake zaune a office din shi,
Yana tunane kaifin hankalin da nayi na rashin fada mashi zancen matsalar da ya faru tsakani da mahaifiyar Anty Sadiya,

****** ********** ******
Tsayin lokacin nan Fatima ta hana zuciyar Yaya Abubakar shakat ta hanyar turo mashi da zafafan sakon kalaman masu ratsa zukatan masoya,
Wanan abin shi ya kara rikita zuciyar Abubakar sosai har yake jin cewa lokaci fa yayi da zai shi ya shigo da ita cikin iyalinsa,
Saboda haka ya shiga yan tsare, tsaren irin yadda rayuwa zata kasan ce a agaba agidan sa,
Sannu a hankali zancen auren sa ya fara zagaye yan uwa da abokan arziki,
Wanan labarin baiyiwa yan uwan haihuwana da yawan su dadi ba sai kalilan ne su kayi murna da hakan,
Abinda, ya daga wa wasu daga cikin yan uwa na hakali badon komai ba sai don sanin ko wacece Fatima da sukayi,
Hakan yasa Anty Samira da labarin yazo mata bugowa anty Amarya waya,
Sun gaisa take cewa Anty Amarya yanzun take jin labari agurin mahaifiyarta cewa wai Yayansu aure zai kara kuma wai Fatima ce, zai aura,
Nan take ba Anty Amarya labarin rayuwan Fatima da yan gidan su, da yadda suke mai da namiji idan sun shiga gida,,,
Hakali a tashe Samira take ba anty Amarya labarin yan gidan su Fatima,
Sai da Anty ta gama saura ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa Allah ya kyauta,
Daga bangaren Samira ta karba mata da cewa Ameen,
Anty Amarya tace Allah ya na tare da mu insha Allah duk wani sherin da zata nufe su dashi akwai Allah bai bata ikon cin nasara a kan su tunda bada zuciya daya zata shiga cikin su ba,
Samira ta karba da cewa insha Allah tace ni abinda ke bani mamaki shine yadda wai Baba Samaila ke jagorancin auren Yayan mu,
Yar takai, tattacen murmushi mai nuna bacin rai Anty tayi tana cewa wai yana yine don kara da mutuci,
Sun dan dauke lokaci a wayan suna zancen tare mamaki ko may yasa shi wanan auren haka ?
Musalima yanzu da Meenatu ke da ciki inji Anty Amarya tace ai bai kamata ace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login