Showing 267001 words to 270000 words out of 388021 words

Chapter 90 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8186

min da cewa wa,alaikis salam, Meenatu ya kuke ya yau, dai ?
Cikin sauke yar ajiyar zuciya don jin mai kiran ta sani ba wani bakon nomba bane,
Kina lafiya nice don naga baki gane ni ba dama na bugo waya ne don naji ko brother dinki yana kusa,
Don nayi kiran layinshi bai jeba tun dazun, ana tashi sai daga bayana gane ko wacece,
Nace au Salawatu ce ashe ?
Tace O baki ganeni ba ke nan ko ?
Murmushi nayi sai nace mata, aini kin san a sokoto nake zaune,
Ok ok naji tace tare da kashe wayan bamu koyi sallama da ita ba,
Wani irin mamakine yakamani har nabi wayan nawa da kallon mamaki tankar wayane Salawatu din,,
Tunda nake da ita bata taba kirana ba a waya sai yau din nan data kira ni,
Kuma may nene dalilin ta na tambayana cewa ina Yaya Abubakar yake ne wai ?
Mamaki sosai Salawatu tabani yau don ban taba zaton irin wanan rashin hankalin daga gare ta ba,
Ita ko a nata bangaren mu gama wayan ta jefa watan ta da karfi saman gado tare da sake wani irin uban ihu,
Ita kadai a cikin daki sai sambatu take sakewa tana cewa yanzu shi kenan aiki yagama ko tunda har ya kwana tare da ita,
Ta fada saman gadon ta da karfi zaune tana cewa wayyo ni Allah wanan abin wai da may yai kama,
Mutumin da nake muradin ace na mallake shi ni kadai a ratuwata shine yanzu za,a ce wai ya kara wata mace again mun cika mu hudu ke nan ake nufi,
Kai ina gaskiya hakan ba zai yi ba wsi may ya kawo wanan abine haka wai please,
Mata hudu mu zauna desame house kamar wasu matan kauye can ina gaskiya da sake,
Tambayan kan ta tayi da cewa to wani sake sake gudune kawai ki zage damtse ki zama star din gidan yar gaban goshin gida gaba daya,
A hankali ta kai kwance da irin wanan tunanen wanda baida iya ka sai faman kullawa takeyi tana walwalewa ita kadai,
Gaskiya wanan tafiyan da suka yi da ga ita sai shi yakara sa,mata so da kaunar maigidan kamar zata shude,
Ba karamin farin ciki tayi ba alokacin wanan tafiyan da sukayi,
Ga ta daga ita sai miji ga kuma tarin alheri da tasamu ta dalilin wanan tafiyan da su kayi,

****** ********** ******
Zaune yake yana kallon irin breakfast din da aka hada mai a gaban shi,
Sai kamshi ke tashi amma kuma, zuciyar shi sai wasiwasin yakeyi mai ,,
Babu abinda yake tunane sai irin kasancewar shi da amaryan shi a daren jiyan badon komai sai debe wa junan su kishin ruwan da suka dade suna dakon shi a ran su,
Gaskiya Fatima ba laifi ita ma takai mace ga kokari ga kwazo irin na gogaggun mata da suka san kan su,
Amma duk da hakan hankalin dan Bukari yana wajen yar kaunar shi wace tun ganin da yai mata jiya yana mashi tsaye azuciya har zuwa wayewa gari,
Sun yi breakfast atare da Fatima inda suka shayar da junan su a cikin so da kauna,
Fatima taso ace sun koma bedroom bayan sun gama amma sai ya nuna mata baida enough time din yin hakan, do gobe yake son ya koma saboda jibi zasu shiga office,
Nan tai wani narkewa kamar zatayi kuka tana cewa haba dai,Bukar gobe goben nan fa,?


ZEEE MAKAWA YELWA
[10/3, 10:21 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-QADIRR


Alokacin da,yadawo daga Birnin Kebbi ranan ina lectures a wanan time din don haka ba mu samu ganin juna ba da shi, har suka wuce,
Nayi hakan ne kuma da gangan don a ranan bar shiya haduwan mu ba, da shi ,
Sai bayan su isa ne mu kai waya dashi inda nake masu sannu da hanya, da a huta gajiya,
Ina kokarin kashe wayan ne naji ya kira sunana da wani karamin murya,
Nima din a hakan na amsa mai tare da dan marairaicewa nace na,am,
Amma dai da wani manufa kika kashe wayoyin ki yau, din, ko, shiru nayi ina sauraren shi,
Sai can n? kara jin muryan shi yana kara tambayana,
Cikin dan ma rairaicewa nake cewa ba hakana bane yaya duk lecture din da nake da su yau top one dole ne yasani fita,
A karshe dai na ce nima ban so hakan ba don naso na ganshi inbada sako aikaiwa Baba Ramatu,
Bai amsa min ba sai cewan da yayi munyi magana da Anty Amarya don tace bazaku dade ba zaku samu hutu a school,
Nace amma hutun baida yawa ai sosai, ya karashe da cewa don haka bazaki zo nan ba ke nan tunda ba yawa hutun ko,
Shiru nayi ina magana kasa kasa can nake cewa, ni ba haka nake nufi ba,
Kawai dai naga hutun bawani mai yawa bane sosai, gashi kuma akwai dan nisa sosai daga nan zuwa abuja,
Murmushin a takaice naji yayi yana cewa ba matsala kiyi zaman ki,
Nace azuciyana ai ba wani matsala bane tunda kana da matan ka agida dayawa,
Sai ji nayi yace ai na gansu nace ki dawo gida kiyi hutu anan, don muna shirin tafiya ne,
Sai a lokacin na tuna cewa zasu tafi saudiya har da su Baba na,
Murya a sanyaye nace, Allah ya kai mu lokaci lafiya,
Bai bari nakai karshen maganata ba yace mata na da kike cewa sunanan ai suna,nan, don nasan da zaman kowacen su,
Da sauri na ke cewa ni bawai wani abu yasa nace hakaba fa don naga dai ai da mutane a,,,,,
Ban kai karshe ba yace don na kara aure ko kema kina kishin ke nan irin na sauran ko,?
Murmushi nayi nace kowa ba kishi takeyi ba gani dai mu kayi duk muna iya kokarin mu da kai ai,
Ai saboda kokarin na kune yasani, sha,awan karawa don kukara kaimi akai,
Murmushi zancencen shi ya bani maimakon, takaici don ma maganar tashi ta zama zolaya
Nace aiko sai asha amarci lafiya don ni dai ina a nan,
Dariya naji yayi tare da cewa next week da zaran an gama hina zata tare ai kinga koda zaki zo zaki samu amarya agida, ke nan,
Dariyan yake nayi nace ai kawai sai nai zamana gurin uwata anan ,
Don ko nazo ba batun mu akeyi ba ana zancen zukakan amare har biyu haka,,
Dariya sosai na bashi dan injin yadda ya kwashe da dariyan a cikin raha wanda abin yabani mamaki azuciyata nace namiji mugu ke nan,
Munyi sallama dashi yana ta faman jaddada min cewa na tabbatar da cewa na shirya kafin ya turo dauka na,
Sai bayan mun kashe wayan ne kishin zancen tarewan Fatima ya turnuko min a zuciyata,
Shigowan Anty gurin mu ne nake ce mata ashe wai next week Fatima zata tare Abuja,
Fuska a daure tace kinji halin maza ke nan ya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tafi an masa dandane haukace,
Yadawo yana santin buje agida ko idan ba shi ke da keda tsohon ciki ina shi ina fada maki wanan zancen kuma,
Baki na tabe na Oho dai wallahi gashi kuma ya matsa da cewa wai sai naje can nayi hutu,
Ido a waje tace kije ina a hakan ke da keda wanan tsohon cikin haka wai,?
Idan zuwa lokacin kin haihu fa ba sai muga tsiyar naci ba kuma,
Dan yatsina nayi nace ai sai yasha amarci har yafita ranshi kafin ya gan,ni a gidan nan,

****** ********** ******
Zagayen aikin ginan shi keyi don tun da ya dawo agajiye yake,
Saboda ba,a gidan suke zaune ba suna a wani dan karamin gidane a kusa da mu, mai Tree bedroom, nan suke zaune yanzu,
Ya fitanan ya fada can yana kallo yana ya bawa aikin da akayi, har yazo nawa part din da mamaki yai wani juyowa yana kallon Lawal,
Shi kan Lawal bai fahinci may yake nufi ba, don haka sai bai damu da kallon ba,
Cikin wani irin kakausar murya yake cewa Lawal wanan kuma part din ya akayi ya samu karin wanan extra room din,
Shima lawal din a cikin mamaki yake kallon shi yace ai ina ce ko kai kace ayi shi ko
Don ranan na yi ma magana naga bakace min komai ba sai daga baya da nadawo na samu sun fitar da plan din,
Nan ko idon shi ya kankance yafara masifa kan cewa akira mai, engineer din,
Nan yaiwa mutumin masifa kan cewa don may zai fifita dayan part din fiye dana kowa, haka,
Shikuma engineer din yace gani yayi cewa wanan filin idan an fitar da plan din a haka zaifi yin kyau, da abar filin abanza,
Daga karshe dai yaba yaya Abubakar akan kuskuren dayayi don yaga rayuwan shi ya baci sosai a lokacin,
Iya bacin rai yaya Abubakar yayi shi a ranan don sam bai so ace wanan part din ya fita daban da na sauran ba,
Haka ya isa gida rai bace yana huci idon shi sun rine sunyi ja don bacin rai,
Duk wace taji motsin shi a falo sai tazo yi mai sannu da zuwa a lokacin ganin yanayin shi, yasa hankalin su dagawa,
Hakan yasa su fitowa dan karamin falon gidan da suke a cikin sa,
Anty Sadiya ce tai karfin halin fara tambayan shi wai may ke faruwa ne duk taga ya canza,
Yai tsuki yana cewa, banda wanan banzan engineer din wanda nasa ya fitar min da plan, din ginan gidan can wai sai kawai yai min karin wani extra room a dayan part din, na Meenatu,
Salawatu tace akan may zaiyi haka shi kuma bayan ga yadda mai abu yace ayi ma shi,da abinshi,
Yai tsuki tare da kawar da kai yana cewa daki har uku a part guda haka har may mace zata saka acikin shi,
Ya dago jajayen idanun shi da suka rine sukai ja,ya dubu gurin da Sadiya take zaune yana cewa sai ki koma wanan part din ke,
Itama da sauri ta dago kai tana duban shi tace wani ,
Yace ke man da wa nake nufi inbake ba, da sauri take ce mai don Allah a barni part dina,
Takarshe zancen harda daga hannuwan ta alamar a,a bazata koma ba,
Salawatu tace ni part dina saboda wanan corner din da nace ai min ne in bashi ba dani sai in koma a ciki,
Sadiya tace a,a bazaki koma ba kawai abarwa Meenatu abinta tunda dama part din ta ne can din,,
Salawatu tace gaskiya da abar ma wata kawai abarwa Meenatu part din nata ta zauna hakana,
Sadiya tace to ai ni banga wani abin bata rai ba anan da har rayuwanka zai baci haka,
Jajjayen idanuwan shi ya sauke mata yana cewa idan mutane suka ga rashin adalci na agare kufa tun akan gina dakunan ku,
Salawatu tace wanan ai mun san cewa bawai ra,ayinka bane mistake ne akasamu don haka baza mu maidashi wani abin fitina ba can,
Sai a lokacin ne hankalin Yaya Abubakar yadan kwanta saboda fahintar junan da ya samu daga matan shi amna a gaskiya bai so ace hakan ya kasance ba sam,
Hannuwan shi dafe da goshin shi ya sauke ajiyan zuciya, tare da furzar da iska mai zafi yanisa tare da mayar da bayan shi ga makarin kujeran da yake zaune akai,
Yadan lumshe idanuwan shi a hankali yake tunanen cewa wai ita wanan yariyar haka Allah yayi ta da sa,a arayuwan ta ne,
Komai nata na daban ne zaka ganta a cikin nasara, watau abin daga Allah ne kawai,
Muryan Salawatu ce take sheda mai cewa kayan gadajen su da suka sayo ance zasu shigo next weeek insha Allahu,
Sai a lokacin ne ya dan bude idon shi da suke a lumshe yana cewa ai na kira masu decoration din gida sunce zasu shigo su duba,
Sadiya tana zaune daga gefe tana rike da habanta da yan yatsun hannun ta tana kallon su,
Tace a rayuwan ta shi ke nan duk Yaya Abubakar yanzu rayuwar shi ta canza a lokaci guda,
Mutumin da da can baya ko sutura bai damu da dinkawa ba,
Amma yanzu ga kudi suna shigo mai kamar hauka, ga kuma buri yana karuwa mai,
Rayuwa kenan haka zamani ke tafiya da rayuwan mutane the more suke samu the more bukatocin su yana karuwa,

****** ********** ******
Sai Amarya Fatima aka shirya tafiyanta Abuja gurin sauran abokan zaman ta,
Duk da maigidan yace mata,baya bukatan komai tazo daga ita sai kayan ta,
Ta samu rakiya mata mutum shidda inda suka samu gida fiye da tsanmanin su,
Suna shiga part din ta taga irin yadda aka gyara daki ta kware muna fukin mayafin da ta yafa a jikin ta,
Tare da sauke numfashin ta a hankali wani irin shewa ta sake tare da sauran yan rakiyae ta,
A nan tafara raraba idanu tane cewa ai ita kan gaba wanan auren ya kai ta yaushe ta taba tsan manin irin wanan ratuwar haka,,
Nan suka shega dube duben part din gidan lungu lungu sako sako suna yaba kyaun shi,
Sunci sun sha daga daulan Baba Ramatu wace tai ta faman yin da wai,niyar girka masu abinci,
Kwanan su uku, suka juyo dawowa gida birnin kebbi cike da abin arziki
Amarya Fatima ta shigo da irin nata sallon a gidan don,
Maigida ya samu kyakyawan taro daga amaryan shi ida duk kan su suka debi takaicin amarci,
Salawatu wace zuwa lokacin takai,ka, mar ta kama da wuta saboda kishi,
Duk da dai babu abinda maigidan ya rage su dashi yana dan kokarin kaman tawa,
Suna zaune a falo yayin da Fatima wace tana tsaye a gaban maigidan da jug din drinks din gargajiya da ta hada mai a hannun ta,
Sai wani juye juye take keyi tana rausaya a gaban maigidan,
Bayan ta sai shocking yake yi tana wani mazayawa don kawai ta tayar wa maigida da hankalin shi,
Daidai lokacin da ta dauki cup zata tsiyaya mai drinks din ne Salawatu ta shigo Falon ,
Tun daga kofa tace ke, ke ke kada ki fara don munan da kika samu ba wai bamu iya irin wanan kissan naki bane,
Fatima tai wani irin juyowa tare da watsa wa Salawatu wani irin hararan ke kuma fa,
A gagauce ta karaso gaban su tana cewa amma dai kin san cewa yau bake ce da girki ba a gidan nan ko ?
Da sauri yadago idon shi yana duban Salawatu tare da nazarin abin da tace,,
Ya saurin juyawa gurin Fatima yana cewa may na tambaye ki da safen nan,
Tace cikin daure fuska, kwana hudu bazawara keyi yau kuma biyu nayi a gidan nan,
Ya daga kai ya dubi Salawatu wace ke tsaye a kan su cikin masifa,
Salawatu tace wancan kwana biyu da ya tafi yai maki a kwana garin ku na may ye shi,
Nufin ki kin samu garori zaki juya su yadda kike so ko may kike nufi da hakan,
Cikin tsawa yace masu da karfi enough please ban son fita a ratuwata, don haka ku tausasa harshen ku a fahinci juna,
Salawatu ta mika hannu ta dauke cup din da Fatima, ta cika shi da drinks acikin sa ,da ta aje a gaban shi,,
Ta kai shi can nesa kadan da ida shi ke zaune hakan yadan sa shi lumshe idon shi a hankali,
Yace yanzu dai ke nan ranakun girkin ki sun kare ke nan Fatima,
Nan ta juya ta watsa wa Salawtu harara tana cewa inji wanan muguwae tsohuwar ba,
Salawatu a cikin bacin rai tace muguwar tsohuwan tana can ai kin barta a baya tana sauraren ki,
Tana nufin wai mahaifiyar Fatima na gidan tana jiran jin bayani daga gurin yar ta,
Fatima tace ke wallahi,banda mutunci da kika gane ni gurin nan,
Salawatu tace ai irin ki nake bukata dama amma wanan girkin yau ba ke ce dashi ba,
Anty Sadiya ta shigo falon fuska a daure tana kallon su wani irin cikin mamaki,
Ta samu guri a can gefe ta zauna yayin da ya dago jajayen idon shi ya sauke a gare ta,
Yace yauwa Sadiya yaya wanan zancen yake ne wai don Salawatu tazo da cewa ba Fatima ce da girki ba yau ai,
Anty Sadiya ta watsawa Fatima harara tace ai itama tasan cewa ba ita bace da girki yau,
Kwana hudu tati tana girki wanda a kaida kwana uku ne idan bazawara ce,
Da sauri Fatima ta kalli gurin da Sadiyan take a zaune tace wai kuna nufin cewa kun hada min kai ke nan, ko,
Sadiya tace hadin kai sam, sam sam ni bani hadin kai ai da kishiya sam,
Kawai dai magana ce ta gaskiya sahihiyar ta domin ai ke ba yarinya bace, don kin san komai,
Cikin wani irin harara Fatima ta ce, ki ce nice uwar matan duniya baki daya, karewar ta, kenan,,
Ya isah haka please tunda har bata lissafi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login