Showing 321001 words to 324000 words out of 388021 words

Chapter 108 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8302

mu sai shirin dawon maigida akeyi, daga gyaran gida gyaran jiki da sauran su,
A yadda yaso yaso na karbi girki amma sai nake ce mai ya bari Anty Sadiya tayi don girki namu yazo daidai,
Da farko har ya dauki zafi akan zancen amma daga baya sai ya fahinci may nake nufi,
Duk kan mu muna a kofan gida, a lokacin da ya iso a cikin murna da farin cikin isowan shi,
Ya murje yayi kyau da dan kiba, da haske sajen shi ya kwanta mai lub a fuska, sai kamshi ke tashi daga jikin shi,
Tsakanin Fatima da Salawatu sai rige rige akeyi a rungumay shi, inda ya hado su gaba daya ya rugumay su,
Da gudu yaran Fatima suka sheko suka rungumay shi suna mai sannu da zuwa inda ya rungumosu zuwa jikin shi,
Yana dan daga su daya bayan daya, yana dariya tare da kiran sunayen su,cikin jin dadi ita ko uwar tana daga bayan su sai washe baki takeyi don murna, ,
Da,go kan da zaiyi mu ka hada ido daga gurin da muke tsaye ina saye cikin wan buje dariga na atamfar super dinkin ya zauna min dan dagwas a jikina,
Ina rungumay da Amir a kafada na, sai Aisha wace take kusa dani a tsaye, a hankali ya fara tako wa, zu gare ni cikin fara,a, da sakin fuska,
Dani da yaron yarungumo zuwa jikin shi tare da dan sauke ajiyan zuciya, ya sakeniyana kokarin karban yaron a hannuna,
Cikin dan wasa yake cewa kai kai kai wanan yaron ya juya gurin Dije yana cewa may kuke bashi haka yai wanan kiba,
Cikin dariya Dije ke cewa, ai,nonon uwarshi wallahi yana da kyau k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?owa yagan shi sai yai magana,
Daga haka yana zance damu muka bishi baya zuwa cikin gida inda gaba daya aka rufa muna baya,
Wani irin kallon mamaki Fatima tabi mu dashi a zuciyan ta tana cewa lalai akwai rigima a gidan nan,
Don wanan yarinyar shuumace ta karshe yanzu duk plan din da na shirya ta rushe, shi ,
A lokaci guda ta nuna ma duniya cewa itace mai power a gurin wanan mutumin ko,
Gaskiya akwai aiki a gaban ta ja don sai tayi yadda zatayi ta maida Meenatun nan wata sabba can daban,
Mutanen ma, aikatar su da suka rakoshi gida suna daga tsaye suna kallon duk abinda ke wakana sai mamaki sukeyi yadda ya ke ya tara iyali haka masu yawa kuma dirkan dirkan,
Anty Sadiya ta tare shi da girki mai dadi sai wani lumshe ido yake yana ci badon komai ba sai sanin da yayi ko girkin wa yake ci,
Koda a cikin mafarkine zai iya sheda girkin Fatima duk da ya dade bai ci ba amma bazai iya mantawa ba,,
Sadiya ba karamin dadi taji ba da taga yadda yaji dadin girkin sai yabo yake yi,
Acikin zuciyan ta sai take godewa wa Meenatu wace ta bata wanan shawaran amma sai ta nuna ai ba zatayi ba amna Meenatun ta matsa mata har saida ta yarda tai girki tare da taimakon Meenatu din wace za,a iya cewa itace ma ta yi aikin dukka,
Sai gashi sanadin haka albarka ta samu daga maigidan wanda sai dadin hakan yake ji,
Itako a zaton ta zai mata wullakanci akan sherin da mahaifiyar ta ta dinga kulka masu dadewa har asirin ta ya kai ga tonuwa,,
Amma sai taga sabanin hakan daga gare ta inda ya nuna mata cewa bakomai tankar ma baida labarin zancen,
Abinda bata sani shi yayyayin ta sanu suka kirashi suka bashi hakuri tare da iyayyen shi maza can BK, din,
Bayan ya gama ci ya wanke hannayen shi ya saki ajiyan zuciya a hankali,
Gaba daya iyalin shi muna falo a zaune inda yake nuna muna farin cikin samun mu dayi a cikin kwanciyar hakali batare da wani fitina ba,
Nan yake kara kwantar muna da hankali tare da bamu labarin irin nasarorin da ya samu a wanan tafiyan,
Yakuma jadda muna cewa idan munci gaba da zama haka zamu sha mamakin shi sosai ga irin alherin da zamu samu,a gare shi,
A fili duk mun ansa maida cewa insha Allahu zamu kasance kamar yadda yake fatan samun mu,
Saidai a can cikin zukatan mu kowa da irin abinda take kiyastawa a kai,
A gamay da yar uwar ta, kowa sai wanda yake jin haushin sa yakeyi arai yana zagi,
Sallaman da akai mai, yasa taron mu watsewa a lokacin saboda muba masu zuwa gaida shi guri,,
Ai ana watsewa akafara cewa munafunci ne ake kokarin kullawa a gidan nan kawai kuma wallahi ni bazan yarda ba don ba zaman mace nake yi ba balle ta juya ni,
Don may baza,a bari ya dawo ya nuna gurin wace zai sauka ba, sai kawai awani tsara cewa wai a gurin uwargida zai sauka,
Mun fahunci may take nufi da zancen ta amna sai muka kyale ta don zuwa yanzu na fahinci cewa bata da dadin zama ko kadan gata da yawan kyashi da hassadda arayuwan ta ita dai komai ace a gurinta aka gani ko akaji,
Salawtu ce tabata amsa da cewa ai hakan ma yayi daidai tunda abin zaibi layi azo a daidai, don haka ni banga wani abin fitina ba anan,
Sai cewa tayi tunda ke dama baki san ciwon kanki ba ai shine zaki fadi hakan,
Lalai wanan bakauyiyar baki da wayyo yau na yarda cewa ke dabba ce, ta gaske wallahi,
Ba yauba dama, nasan cewa, kina daukan kan ki a wani matsayi kamar wata can,
Nan ko bakauyace ke wace ko normal dress bata iya ba balle, magana,
Ta wani wurga mata harara tare da jan tsuki bata kara tanka mata ba ta sa kai zuwa dakin ta,
Fatima tace uwar ki ce mai irin wanan suffan da kika fada, tafada a zuciye
Har zan saka kafa a part dina naji wanan irin zagin da ta jefawa Salawa ,
Sadiya tace kai amma dai hakan ba daidai bane daga magana sai saka zagin iyayye aciki
Ke tsinanniya algunguma yar azzaluma mai shiga tsakanin masoya Allah ya tona asirin uwarki kowa yagama sani, a duniya ko ita wacece, mayar banza kawai,
Ke ke ke mukaji muryan Yaya Abubakar yana fada duk bamu san da shigowan shi ciki ba alikacin ,
May haka harda irin wanan zagin a gidana haka zagin kuma wai na iyayye can,,
Ta juyo tana duban sa ranta a bace zatai magana a zuciye, ya daka mata tsawa yana cewa shut, up ban son hauka wallahi ki bace min da gani don bazan daukan maki hakan ba wallahi,
Idon Fatima ya kada yai ja saboda balai,ta juyo tana duban shi tace nice mahaukaci saboda wanan bushumar matar taka,
Ya watsa mata harara da cewa idan na kara jin muryanki wallahi yau zan bata maki rqi fiye da tsanmanin ki,
Tsaban bala,i Fatima tagani a idon shi don haka tasan komai zai iya faruwa,
Kawai ta sakai zuwa dakin ta rai abace tana tunane yau kan Sadiya da take gani ba kowa ba bukar din ta ya wullakanta ta gaban kowa,
Lailai namiji baida tabbas abarshi kawai inda aka gan shi
Yau shine harda kwance mata zani a kasuwa gaban duk matan shi har da bakin gida, su Dije,


ZEEE MAKAWA YELWA
[11/14, 9:42 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH Al MUNTAQIM


Washegari, muntashi da baki masu zuwa taron maigida, wanda sai murna ake mai na alherin da ya samu,
Sai zuwa wanan lokacin muka fahinci cewa ba karamin nasara, wanan tafiyan ya jawo muna ba gaba dayan mu,
Bodon komai nace haka ba sai duk yan team din da suka zo da irin alherin da zamu samu daga gare su musan man ma Amir wanda yana tare da mahaifin shi idan an mai kyauta, sai ya ce akawo min, na mu ne,
Tun misalin karfe, biyu muka fara aikin girkin abincin da zamu yi a can main kitchen na gidan,
Tuwon alkama miyan kubewa da fatan, shanu,da nama, sai, man shanu da aka zuba a cikin shi,
Sai kamshi ke tashi sosai ta ko ina, da ka shigo zakaji yadda guri,ya kaure da kamshi,,
Munyi mai hadi drinks na gargajiya zobo da kunun ayya, suna kamshin kayan yaji,
Na samu sauki don Amir sun fita da Baban shi zuwa cikin gari,
Part din Yaya Abubakar na shiga inda na garje na fara aikin gyaran guri da ya ke bukatan gyara,
Kafin wabi lokaci naiwa dakin kwal sai kamshi da sheki ke tashi, tun daga steps din zaka gane cewa dakin ya samu gyara yau,
Sau uku ina cika dustbin, ana zubarwa a kasa, bathroom din shima na gyara shi ta ko ina tsaba sai kamshi ke tashi,
Kafin su dawo, nai wanka na gyara jikina acikin wani simple dress, na dogon riga, mai hannu shara,shara bude, tsakiya a,daure da igiya,
Sai kamshin turare oud ke tashi daga jikina ina kokarin daure, kaina ne ya shigo dakin dauke da yaron dake barci a kafadan shi,
Ban san da shigowan shi ba sai, jin shi nayi ta bayana ya dan rungumoni izuwa jikin shi,
Kusan a tare mu ka sauke a jiyan zuciya, saboda wani shocks da ya ziyarce mu, alokaci guda na lumshe Idanuwa na,,
Daidai setin kunnuwa na naji muryan shi yana cewa, are shock, ban iya cewa komai ba sai sauke numfashin da nayi kawai tare da cewa kun dawo,
Ya amsa a cikin lumshe idanuwan shi, yana cewa mun dawo amma big man yai barci tun a mota, haka naita yawo dashi,
Murmushi nayi ina kokarin karban yaron a hannun shi, ina cewa a hannkali oh, Amir yau ka wahal da Daddy ko ?
Waya fada maki Meenat ni da yau nake ganin cewa nafi kowa, sa,a a duniya ni da Allah ya ba wanan kwalele, yaro abin sha,awa, kin ko ga irin yadda muka samu kasuwa yau,
Murmushi, nayi a lokacin da naga yana ciro kudi, da miko min wasu lededi,
A cikin ladabi na karba tare da juyawa zuwa shifide Amir saman gado tare da dan aje ledan daga gefen gadon,
Farkawa yaron yayi daga barci tare da sake kuka abinda ya kaini ga dan kwantawa don nabawa yaron nono,
Daga gurin da Yaya yake tsaye yake cewa anya Big man, zaka ko tausayawa Abban ka kuwa,
Wayan shi da aka kira ya sa shi dakatawa, sai ma yafita daga dakin inda nabi bayan shi da kallo ina mai lumshe idanuwa na,

****** ********** ******
Tun hawa stairs din dakin shi ya fara ganin canji a part din shi,,
Yana kokarin bude kofan dakin shine kamshin room fresh mai dadi ya daki hancin shi,
Ya dan lumshe idanuwan shi, don jin dadin da yayi, gaba daya dakin ya sake mai a idanuwan shi,
A hankali ya kai zaune saman gadon shi yana mai bin dakin da kallo ta ko ina,
A hankali yake dan girgiza kan shi cikin jin dadi yana kare ma ko ina na dakin kallo,
Sai da ya shiga bathroom don ya watsa ruwa, yakara ganin mamaki a ciki, bathroom din inda komai sai kyalli yake kamar sabon kaya aka saka a ciki,
Yai wankan shi tsab ya shirya yafito daga part din shi inda ya nufi massalaci don Sallah wanan kai,idar shi ce, yin jam,i a massalaci,,
Sai kai,da kawo na ke a cikin falon inda takalman kafana ke bada sauti kwas, kwas kwas
Wanan sautin ne ya tayar wa duk wata mace dake a cikin gidan hankali inda karan takon takalman nawa yake tayar masu da hankali,
A kwai masu dan daga labule don lekena akwai masu fitowa waje don sa ido kawai,
Sai kuma masu zagina a zuciya daga daki suna cewa ayi dai mu gani ai,
Har yanzu akwai akidar zaman falo a gidan da dare kaman da can baya, sai dai abinda na fuskan ta yanzu zaman yadan canza sallo zuwa zaman fito na fito,
Abinci na fito na gabatar wa maigidan dashi, inda nake zaune daga gefen shi cikin kwalliya ina mashi service,
Tare da zuba mai ruwan wake hannu da kuma drinks mai sanyi, a cup daga gefen shi,
Yana ci muna dan taba hira sai dai hiran namu tunda ba wani sabo mukayi can ba akan malam tsoho ne da matan shi,
Wanan dalilin ne ya saka mu kwashewa da dariya don tunawa da abinda yafaru,
Saida ya kammala cin abincin tsab na mike don na tsabtace gurin da yaci abinci,
Inda yake ce min kada na kara cin abinci idan bai dawo ba don shi da matar shi yake cin abinci,
Kamar yadda na san cewa bai barci batare da matar shi ba a saman gado guda,
Da guda guda matan gidan suka fara fitowa, don hiran dare a main Palon gidan,
Salawatu ce ta fara fitowa tana saye cikin wani dogon riga daya matse ta,
Sai ga Fatima tafito tare da yaran ta ida ta nufi saman kujera da su suka zauna,
Na fahinci cewa tana cusa diyan ta ga maigidan don su samu shiga,
Hakan ya sakani shu,umin murmushi don zan fito mata ta baya nima, saboda ance biri ga maigona nan,
Part dina na koma inda na samu su Dije suna kallon wani shirin film a tashan, NTA,,
Ban fito daga part dina ba sai da na dan kara gyara jikina sai kamshi nake yi ni kaina nasan cewa yau a jike, nake tako ina saboda na shayu,
Tunda na nufo falon idon su yake a kaina, kamar sun ga wata bakuwa gani,
Ina dauke da Amir a hannuna sai Aisha dake rike a hannu na guda,
Kamar yadda na saba zama a kasa idan Yayana yana a saman kujera yau ma hakane don a gefen hannun kujera kasa na fara zama,
Miko min yaron yace tare da kokarin dan gyarawa don ya karbe shi, inda na mika mai yaron, cikin dan dukawa,
Idon Fatima kar a kaina tare da nuna mamakin na karara a fili,,
Nadawo na zauna a kasa ina mai kallon su ina cewa ina wuni anty Sadiya, Na juya ina gurin Salawatu ina cewa ina tare dan dawo da kaina inda Fatima take nace ina wuni,
Ban san ko,ta karba min ko bata karba ba don dai banji muryan ta ba,
Sai muryan yar ta da take cewa mama dubi Baby a gurin Daddy mu,
Yarinyar ta matsa da zancen cewa a dubi Baby akarbo mata shi wai kada Daddy ya dauke shi,
Wanan abin da yarinyar ke yi ya saka uwar jin kunya da nauyi don haka sai ta fara dan zarewa yarinyar ido,,
Sai yarinyar tafara kuka tana batun shiga kasan kujera,wai ita tayi fushi,
Kowa na harkan gaban shin babu wanda ya kulla da yarinyar a gurin,
Sai nace zo ,zo, zonan kyale mama kina son a goya maki Baby ne,
Shiru tayi tana kallon tana nazarin zance na hannu na kara mika mata ina cewa oya zo na goya maki Baby a bayanki,
Sai ko ga yarinyar ta mike ta nufo inda nake tana dan murza idanuwan ta, a hankali na mika hannu na jawota zuwa jikina, inda ta zauna a saman cinyata,
Idon uwar ta yana a kan mu don duk hankalinta a fakaice yana a gare mu don taga ko may zan ma yar nata,
Ledan da na shigo dashi a hannu na mikawa Anty Sadiya ina cewa Anty ga wanan Amir ne akabawa, su ,
Shine na tara nace sai mu raba abawa kowa nashi kaso,
Sadiya tace ba yaron ne akaiwa alheri ba don may zamu karba mu, ai kibar shi sai ki saya mai wani abu,
Ita da akabawa dan ta batai kyashin ta fitar mu raba ba sai kece zaki ce wai ta barshi don itace uwar dan,
Salawatu ce ke wanan zancen cikin dan hasala, don haushin da Sadiya ta bata,
Ina anyiwa yaron alheri ne don ubansa inko hakane ai muma muna da kaso a cikin kudin ke nan,
A dan hasale ya juyo inda nake zaune yayin da ya dakatar da wasan da yakewa yaron, yana cewa ke, Meenat na amsa da sauri na,am yace karbi ledan nan ki mayar daki,
Ba mussu na karbi ledan da Anty Sadiya take miko min na mike kamae yadda yace na mayar, daki,,,
Daga can na tsaya don hada, kayan da zamu kwanta dasu a cikin Baby bag guri guda,
Nafito zuwa falo inda na samu ana rikici, don na samu shi Yaya Abubakar yana cewa, idan badon kun samay ta yarinya a cikin ku ba wacece zata yarda don anbawa dan ta alheri tafito dashi gurin rabawa da kishiya,
Fatima tace ai don ka aka ba su ko muna albarkacin ka zamuci tunda tasan cewa saboda kai akayi kyautan,
Wani irin hararan ki natsufa ya jefa mata tare da cewa amma dai kunya bai ishe ki ba wallahi,
Yanzu ke har kina bukatan karban alherin da yafito a sanadin wanan yaron, ?
Yaron da zan iya rantsewa kilama ko sunan shi baki taba sani ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login