Showing 348001 words to 351000 words out of 388021 words

Chapter 117 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8284

ta har ya dan turo daga jikin ta,
Ta ramay tayi baki duk ta fita daga hayacin ta da gani nadama duk ya baiyyana a tare da ita,
Hawaye sai har yanzu sintiri yake a fuskanta, tana dan kokarin gogewa, da habar hannun ta,
Wani bala,in tausayin tane ya lulube shi yasan cewa yanzu tai nadama daga irin halaiyar ta ,,
Muryan shi taji yana kiran sunan ta yayin da kanta yake sade a kasa tana sharban kuka,
Yace Fatima ki bar wanan kuka ki dakata muyi magana dake please,
Kala batace mai ba sai dan kaiwa zaune da tayi daga inda take a tsugune da farko,
Kafin ya kai ga yin magana saiga Salawatu ta fado dakin cikin wani irn tako tana taunan chew gun kas kas, da ita,
Sweet Oga abinci fa yana a table tun dazun nan gashi naga baka sauko ba,
Zan sauko yanzu insha Allahu, idan na gama abinda nakeyi,
Maimakon ta fita sai ta dan tsaya rai a bace ya juyo gurin da take tsaye yace, bakiji bane
Naji tace a sanyayye ta wuce buguzun buguzun da ita rai a bace,,
Gaba dayan su binta da kallo su kayi don kowa ya fahinci may take nufi da hakan da tayi,
Ya juya inda Fatima take a zaune agurin mirror din dakin nashi, yace mata yanzu dai ishara ta saura a gare ki don ko haka dakike gani ya isheki ishara,
Ki godewa Allah, ki kuma godewa yar uwaki meenatu
Don Meenatu ce wace tun kan nashigo gidan nan ta taushi zuciyata akan zancen ki,
Don tun ina asibiti gurin ta labarin dawowar ki garin nan ya samay ni,
Irin yadda ta ga na dauki zafi ya sata kwantar min da zuciya da kalamai masu fahintar da mutum,
Wani irin kallon mamaki take mai ashe ma watace har ta tausasa mai zuciyar shi a kan ta abin da take tunane ke nan a zuciyar ta ,,,
Tace cikin dan dago kai da wani irin murya, mai rauni ita Meenatu dai ta bada hakkuri akaina cikin daga kai yace kwarai da gaske,,
Wani irin murmushi yayi mai sauti yace kinga Allah ya warware maki, idan har kina da fasaha,
Mikewa yayi yana cewa ni zan sauka kasa zamu karasa maganan zuwa gobe insha Allah,
Ya fara tafiya tace Yaya Aliyu bai san cewa mundawo ba yau din nan don bamu fadawa kowa zancen dawowan mu ba,
Cikin mamaki ya juyo yana kallon ta a cikin wani irin kallo yace k ko yaza,ayi kizo bada sani yan gidan ku ba,
Idan su kaji cewa kina anan zargin wani abu fa daga baya idan sunji cewa kina nan,
A hankali ta dago kai tana mai fuskantar shi
Acikin muryan kuka tace saboda bamu san irin karban da zakai muna bane a lokacin,
Idan har zaka karbe mu duk abinda zasu fada ba zai damay ni muddin ina dakina zaune,
Tausayi ne takara bashi watau so ne ya rufe mata ido har ta iya barin yan uwan ta duk da dinbin wullakancin da yai mata na,rashin zuwa duban ta tunbayan zuwan ta gida gashi harda cikin shi ke tare da ita a jikin ta,
Amma, duk bai sa ya tafi, gurin ta ya duba lafiyan taba gashi yanzu ta kwaso jiki kuma again ta dawo gare shi,
Wanan ma kawai ya isa yai hakkuri ya mayar da ita dakinta, suci g?ba da zaman hakkuri, atsakanin su,
A hankali ta mike jiki ba kwari tabi bayan, maigidan suka sauko tare, daga sama,
Wanda a lokacin duk Salawatu ta riga ta cika fam kamar zata fashe don takaici,
Fatima dakin ta tanufa inda tasamu har yaran ta sunci abincin da nasaka Ramatu ta kawo masu daga part dina,
Takara jin wani irin nauyi da tasamu yaran sunci abinci har suyi barci a cikin dadin rai,

****** ********** ******
Ina kwance a saman gadon sabon dakina watau dakin asibiti wanda ya koma tankar dakina na gida, yanzu don a ciki nake komai,
Inda nake under control din likita shi da nurse's ke ta kokari akan mu ni da sauran yan uwa masu irin matsalata,
Ya Abubakar ne ya shigo dakin yana dauke da Amir a kafadan shi sai Dije wace daga bayan shi take tafe da Aisha da Ramatu,
Yaron yana hangoni yafara wagale baki yana mika hannu yana son indauke shi,
Tausayi sosai yaron ya bani don nasan cewa yana a cikin kewar uwa a lokacin,
A hankali na mike ina kokarin kaiwa daga zaune, duk kan su idanuwan su yana a kaina, har na kai zaune sai faman yi min sanu kawai su keyi,
Idanuwan Yayana duk suna a kaina kamar ace ya kama min ciwon na mike ni,
Sai da yaga na kai zaune sanan ya gyara farar kujerar roban da aka bashi dan ya zauna,
Gwago Habbi ce ta shigo tana kokarin mika mai takardan da likita ya bayar a bashi idan yazo,
A hankali yake bin takardan da karatu har ya kai karshen ta ida ya dago kai yana ce min takarda scanning ce ta karshen wata da ake maki duk karshen wata,
Sam bani kaunar wanan scanning din don idan akai min na kan koma tankar an doke ni ne sosai,
Nace ni gaskiya normal nake ba,sai nayi wanan awon nasu ba,
Murmushi kawai Yaya yayi tare da cewa daurewa zakiyi ai maki kamar yadda suka bukata daga gare ki,
Kaina na kawar gefe cike da jin haushin wanan bukatar ta likita a gare ni,
Muryan Yaya Abubakar naji ya na cewa wanan abin yana da sanyi kuwa,
Yana nufin drink's din da Ramatu ta hado min don in sha,
Kamar may rada yace cikin dan gyara zaman shi azubo min kadan nasha please, don duk a gajiye nake,
Dije tace ita amaryan taka da ta dawo bata hado maka bane kasha,?
Yace cikin murmushi kina kishi ke nan ko don banga abinda ya kawo zancen taba a nan a daidai lokacin da ake mika mai kofin drinks din Ayya da ta hado min yaji kayan yaji, sai kamshi ya ke tashi daga ciki,
Amfanin shi shine yana taimakawa Baby dake aciki da abubuwa da dama kamar su, wanke kwakwalwa, wanke idonuwa sukara hasken gani da karfi,
Yana kuma gyara mahaifan mace maiciki don ta fitar da zaki da kazantar dake a jikin ta,
A hankali yake dan kurba ruwan kunun ayyan yayin da Dije ke ci gaba da mashi sheri akan cewa shi ai angone,
Sai da ya kusa shanyewa yake cewa Dije kema dai na gane kina kishin Fatima sosai,
Tace matar da ta tsufa da ita da wanan ai ina ganin ba wani tseraiya a tsakanin haihuwan su,
Tankar baiji ta ba sai saidai satar kallon reaction din da zan nuna don jin cewa cikine wai a jiikin Fatima,
Azaton shi yadda su kai ta hauka a lokacin da na samu ciki nima a yanzu irin shi zan yi da naji zancen a yanzu,
Amma sabanin hakan sai ya gani kawai ina dan murmushi ina cewa Dije ai idan mun haihu a lokaci guda kinga sai a hade sunan a cashe kawai,,
Bai juyo ya kalleni ba amma hankalin shi yana a gareni yace wa Dije kinga babu zancen komawan ki gurin malam ke nan sai ki zauna anan mu ci gaba da, zama dake kina tsare mu na yaro,
Dariya akasa adakin inda suke cewa cafdi yaya akasamu ma har tazo saida Baba musa yasaka baki,
Ya lura cewa ba abinda ya damau nida zancen wai ina kishi ko bakin ciki akan zancen cikin jikin Fatima,
Sun dauki lokaci a dakin suna tayani hira har zuwa wani lokaci sukai min sallama auka tafi,
Wani irin sanyi Yaya Abubakar yaji a zuciyar shi fuskan shi ta baiyyana farinciki,
Don a zaton shi zanyi zanyi ta fitina har na tayar da hankalina gani da ciki a jikina Kuma ba lafiya a tare dabi,
Shine dayake boye min zance yanzu haka baiso Dije ta kawo cen ba agabana,
Mun rabu dashi inda sheda min cewa zai dawo da dare mu je gurin scanning din,
Na ansa mai da cewa Alkah yadawo dashi lafiya
Abinda bai sani ba shine nima daurewa nake don nima mace ce tankar kowace irin mace mai kishi,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
=?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL GHANI

MUNA GODIYA GA ALLAH UBANGIJI SUBBAHANAHU, WATA,ALA DA YA BADA KON YIN TARON WA,AZIN KASA LAFIYA AKA KUMA WATSE LAFIYA A GARIN MU YELWA YAURI KEBBI STATE,
ALLA YAMAI DA KOWA GIDA LAFIYA ALLAHUMA AMEEN
SUNNAH SAK INSHA ALLAH,
=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?

Abubuwa nata faruwa a cikin yan watani daga ciki harda, samun canjin gurin aikin da Yaya Abubakar yasamu
Yanzu an mai da shi branch din su dake garin photercouht ya samu General Manager na maikatar gaba daya,,
Wanda hakan ne ya sa shi barin gari badon ran shi yaso ba duk da ci gaban da ya samu,
Wanan mu,kamin yasamay shi ne da ga Allah sai kuma, chief din maaikatar nasu wanda yai sanadin zaman shi hakan
Don sani halin kwazon aikin da yake dashi tun zaman da sukayi a garin Lagos dashi,
Yaso ace a lokacin mun haihu saboda ya,samu kwanciyan hankali ,
Dole hakace ta saka shi yawan zuwa gida akai akai don ya duba lafiyan mu musan man ni da na,ke kwance asibiti da, dadewa,
Kamar kullun yau ma da ya shigo garin weekend ya samu iyalin shi lafiya inda ya gudanar da abubuwan da suka kama ga ko wani daga cikin iyalin nashi,
Sai da har yanzu baida kwanciyan hankali saboda, irin yadda yaga doctor's din asibitin suna faman bani special kulawa,
Wanan ne ke tayar mai da hankalin shi don sai yake ganin cewa akwai fa matsala ne atare dani, a hakan,
Bayan yazo ya idar da duk wani abinda ya dace yaiwa iyalinshi, ana gobe zai koma ne fitina ya taso a tsakanin matan shi na gida,
Salawatu da Sadiya inda Salawatu tace, sai Sadiya ta sakar mata duty ta wai saboda gobe maigida zai koma gurin aikin shi,
A take fitina ya tashi inda Sadiya tace mata ina tafito mai ma take nufi da hakan don bata fahince ta ba,
Fada da rikici ne sosai ya wanzu a tsakanin su, inda suka rikice da yaya acikin gidan,
Maigidan yana ciki yana jin su haka yafito yadan gega ta gefen su ya dauki keys din shi zuwa waje,,batare da yace masu uffan, ba,
Ya samay ni kwance ina karanta novel din ?nty Rufaida, Umar sallaman shi ce ya sani dakatar da karatun da nakeyi a lokacin,
Fuskana dauke da murmushi nake mai sannu da zuwa don tun jiya da ya iso yazo gaida ni bai samu dawowa guri na ba sai yanzu da ya shigo, din nan ,
Ganin yanayin fuskan shi kawai ya sa ni gane cewa yana acikin yar damuwa,
Da wasa nake ce mai, nidai gaskiya a maidani gida nagaji da wanan zaman ace sai mutum ya wani haihu zaibar wanan gurin,
Da kyat, na samu nadan dago daga kwancen da nake ina kokari gyara daurin zanina da ya sance a lokacin,
Kallon tsab yabini dashi yana cewa amma dai wanan cikin yafi na Amir girma nake gani,
Nace cikin dan cije baki wata kila mace ce zan samu yayana,
Yace yana mai kallon cikin nawa Allah dai ya saukeki lafiya koma wani iri ne ,
Nace yayin da na dan mike da kyau ina cewa, to Yaya ba ance cikin diya mace yafi girma ba sosai ,
Haka kuma haihuwan diya mace yafi fitina da wahala, sosai,
Murmushi yayi batare da yace komai ba naji ya sauke ajiyqn zuciya,
Abinda yasani maida hankalina ke nan don nasan wanan irin nishin magana ce kumshe a cikin shi,
Yace Meenatu naso ace zuwa yanzu ban daga zuwa ko ina ba ina zaune a tare da ku, don naga lafiyan ku,
Murmushi nayi na kai zaune ina cewa, haba yaya ai adduan ka yafi komai a gare mu,
Don ko kana nan shine kawai zamu bukata a gare ka,
Sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana dan girgiza kan shi a hankali, yayin da idanuwan shi suke a lumshe yana dan buga kafan shi a hankali saman ties, din dakin,
Meenatu haihuwan ki yana bukatana a kusa don hankali baya a kwance can inda nake don zama kawai na keyi a gurin,
Nace haba yayana ai insha Allahu lafiya zan sauka yan kuda na kwana,
Magana ta dariya ta saka shi don sai yake ganin ni babu abinda ya damay ni, ko kadan
Shi duk hankalin shi a tashe yake don zamana asibiti yafi komai daga mai hankali duk abinda yakeyi hankalin shi yana guri na kamar yai tsutsuwa ya dawo,
Yace yanzu transfer nake kokarin nema don na dawo nan kowa ma ya huta don, hakan banda kwanciyan hakali wallahi,
Haba Yayana don Allah kabar zancen neman transfer din nan don gaskiya, zaman ka a can aiwani karuwane agare mu baki daya,
Idanuwan shi naga ya lumshe a hankali tare da, dan gyara zaman shi a saman kujera,
Ina daga kwance nake ta yi mai magana a cikin kwanciyan hankali, batare da yace min komai ba yake saurare na,

****** ********** ******
Yana zaune a cikin jirgi kanshi yana sagale a makarin kujerar da yake a zaune, a hankali ya lumshe idanuwan shi,
Ya sauke numfashi, ya,gyara harde hannayen shi da kyau, a saman kirjin shi, zancen fitinan da su kayi a daren jiya ya fado mai a rai,,
Dan guntu tsuki yaja a ran shi, yana cewa, bai san lokacin da wa yan nan matan zasuyi hankali ba,
Weekend kawai da nazo yi amna ace sai anyi fitina a kanshi, may yasa mata suke da son kan su haka da yawa,
May yasa mata kishi ke rufe masu idanuwan su har su manta, da gaskiya su afka shirmay akan abinda suka san cewa bazai yiyu ba,
Kowace mace abinda ya fahinta da farko shine, kanta kawai tasani take kauna sama ga kishiyar ta,
Bata kaunan taga karuwa kona kwasan masai a akan yar uwar zaman ta,
Kishiya komai lalacewanta sai anyi kishin a kanta, ita dai koda yaushe taga cewa, yar uwa tana cikin fitina ko tashin hankali, wanda hakan shine dadin ta,
Da wuya idan antara mata dubu asamu mutum goma masu haskwn zuciya da,sukewa kishiya fahintar alheri, a rayuwa,
Zancen hiran da sukayi da Meenatu a daren jiya yasaka shi dan murmshi,
Don shi har yanzu ya rasa gane a wani class zai a je Meenatu yarinyace karama amma kuma tana da kwakwalwan manya,
Idan ba don Meenatu ba ya zai yi da wanan weekend din rikicacen weekend da yazo mai cike da fitina agidan shi don har Sadiya, wace bata, damu da harkan kowa ba amma ta buge ga tashin hankali da fitina a kan kishi, duk da yasan cewa itama tana da zazzafan kishi,
To amma tana kwantatawa tana kokarin dannewa da boyewa tabar wa cikin ta, wanan ne Salawatu ta gani har ta gwada hudawa don ta gani idan da ci a kan,ta samu gurin cutawa,
Amna sai taga ashe Sadiya har ta cuna mata gurin fitina da kishi, a rayuwan ta, don sai da ta gaji tagudu tabar Sadiya a falon,
Zaman shi ya dan gyara tare da fesar da iska ya ce Meenatu, you mean everything to me,
Amon muryan nane yake mai yawo, a kunuwan shi lokacin da nake cewa,
Yaya Abubakar katafi, kawai ka bar mu ai akwai mutane a gida daga cikin mu duk wace ta fara haihuwa zata samu kulla tankar kana a garin,
Nace ga su Baba Wadda ga mijin Fattu ga mallam Abudullahi kai mutanema da yawa da su kulama da mu, tankar kana a gida,
Ya nufasa a hankali yace, nasan cewa zasu kula da ku din but amma wani abin ya kamata ace ina a kusa da ku ai,
Haba Yayana ka kwantar da hankali akwai Allah Allah zai tsare mu ya kare mu ya kawo muna sauki insha Allah,
Idan ka koma ka kwantar da hankalinka kaci gaba da aiyukan ka tunda muna tare da kai a waya, ai,
Wanan ne, yasa shi dan jin kwarin gwiwa da har, ya samu karfin tafiya, zuwa gurin aikin shi,
Inda muke samun kyakyawan kulawa daga yan uwa da abokan arziki ta ko ina acikin garin Abuja,
Mutane suna muna kulawa na musan man, ida akoda yaushe suna kawo muna ziyara, don ganin halin da nake a ciki,
Ga gwagona Habbi tare da Maman Biu muke zaune da su asibiti,
Sam ban damu ba ban kuma,saka a raina ba rashin zuwa gaidani da kishiyoyina basa yi,,
Fatima ce idan ta shigo asibiti gurin awo take kan karaso gurina mu dan gaisa sama, sama da ita,
Ta wuce tana turo ciki a gaba tana wani tafiya guda guda wai ita a dole ga mai ciki,
Sai dai idan har ta shigo dakin a cikin second guda, duk


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login