Showing 6001 words to 9000 words out of 388021 words

Chapter 3 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8185

saye yana shiga kauyu ka yana dauko itace da sauran kayayyaki yana shigowa dasu gari,,,,
Amina yau yaya ankayi kin kafito da,wuri ko uwar taki bata nan ne,
Malam ke tambayar ta acikin wasan jika da kaka da yakan mata wani lokaci,
Murmushi tayi tadan noke kan ta acikin hijabin ta ba tare da tabashi ansa ba,
Sai can tace baba na yace min intahowa na makaranta,
Wai daga yau ya yanke aikin nan, da nika zuwa yi wa mama kullun, don kada a wuce ni ga karatu,,
Murmushi malam yayi kawai don yadade da sanin cewa wata rana hakan zai faru,
Don dai irin yadda mama take nuwa bai dace ba sam saboda babu adalci acikin tafiyan,

Baba Buhari ne ya shigo gida dauke da buta a hannun shi, da alamar ruwa yake so acikin butar,
Gurin randar ruwa ya nufa daniyar diban ruwa, don ya zuba a butar,
Muryan mama Ladi ce ta bayan shi take cewa yau kan ai mai diya ya hana diya tai diban ruwa,
Yau samaila ya gwada min baida kunya don ko nauyi bai ji ya kalli ijjiya ta yaka ce wa wai diya tai tadawo ko hutawa batayi zan damay ta da bakin kira,
Sororo yayi tsaye da buta a hannun shi yana sauraren ta,
Saida ya tabbatar tagama ya nunata da hannun shi dake dauke da mudar radan ruwan yace,
Ke, Ladi ke Ladi, Walle kiji tsoron Allah, daga dai yau Samaila yai magana kan Amina kikacewa wai ya gwada,maki rashin kunya, yai fada kan "ya tai ta fari,
Walle Ladi an,kiji tsoron Allah ga al,amarinki,
Duk yadda mutanen ga ka kauda kan su ga al,amarin diyar su, bai,ishe keep ba, sai keyi masu kazafi
To, to ta ka shigan ma dan uwaka ke nan ko don ba yau ba nasan bakason abinda Yarinya taka min,
Dauri ai sai ka hwada min in sani ko,
To ai yanzu ke sani ko ?
To katai zuwa inda zaka samu ruwan zuba ma butan ka tunda bata taho ta debo muna ba,
Wanan maganan shi ne sanadin daina duk wani wahala da meenat keyiwa mama Ladi,
Sai kuma kiyayya abin ya koma masu sosai don sam daga mahaifin da matar har yaran su ba shiri tsakanin su da sahen mama Ladi
Dan dama dama gurin ita kishiyar mama din baraka wace babu ruwan ta da zancen su,

A gajiye yadawo daga gurin aiki, tare da ledoji manya a hannayen shi,
Da kyat ya samu ya shigo gidan nashi don nauyin kayan da ya dauko,
A falo take zaune daga ita sai yar shimi a jikin ta sai littafin dake hannun ta tana karan tawa kanta babu hula ko dan kwali,
Da sallama ya shigo gidan,
Ita ma Sadiya sau guda ta daga kai ta kalle shi takawar izuwa abinda takeyi,
Batare da ta kara daga kai ko ta mike ta taya shi karban kayan ba tace mai sannu da dawo,
Umhumm ya ce mata cikin rashin sakin fuska ko walwala,,
Kayan ya aje a gaban ta saman tebur ya wuce direct gurin fridge,
Goran ruwa mai sanyi yafito dashi daga cikin fridge din,
Kai ya kafa har sai da ya shanye ruwan, sanan ya cilla goran ta bayan shi,
Shi da kan shi yadawo gurin kayan da ya,aje yafara fitar da su guda guda,
Duk hakan baisa ta aje littafin ba ta dube shi saima kara mike kafa da tayi tana kadawa,
Sadiya, Abubakar ya kira sunan ta acikin nuna son ta maida hankalinta zuwa gare shi,
Littafin ta aza saman cinyan ta tadan dawo da diban ta gare shi,
Hankali ta ga ba daya ya koma gare shi, don son jin may zaice, mata,
Da farko kayan siturun da ya,sayo mata,su ya fara turawa gaban ta
Dago kai tayi tana son jin karin bayani daga bakin maigidan nata,
Wanan kayan naki ne ki dinga amfani dasu, pls, sai kuma wa yan nan kayan
Ya nuna mata kayan leda kayan abincine ki kai su duk inda ya dace a aje ko wani daga cikin su,
Daga haka Abubakar ya mike zuwa dakin kwanan su don yadan watsa ruwa ajikin shi,

Abubakar bai fitoba sai gab da sallah magrib don ahi mutum ne mai son yin sallah a cikin jam,i kamar yadda sunna yai ko yi,,,,,
A gurin da ya bar kayan a gurin ya samay su kamar yadda ya barsu, dazun,
Mamaki sosai ya kamashi don shi a iya sanin shi agida idan mahaifan su ,sun shigo da kaya
Tun daga nesa mace zata zo cikin ladabi takarbi leda ko kayan, akai su inda ya dace,
Amma shi sai gashi yau , ya sayowa matar shi abu anma ta nuna mai halin ko in kula, da su,
Agurin da ya barsu a gurin ya samay su kamar dazun,
Shim ko don bata san kudin da ya kashe bane akan sayayyan da ta wulakanta,
Wata zuciya tace, mai kawai rashin da,a da tarbiyan kwarai ne bata samu ba,
Sai bayan ya je sallah ne ya dawo, ya kwashi kayan abinci zuwa inda ya dace akai ko, wani,,,
Daga wanan ranan ne, ya sa wa rayuwan shi hakkuri akan duk wani al,amari na zaman takewan wasu,
Abubakar mutum ne mai kwazo agurin aikin shi don shi dama irin mutanen nan talent ne,
Sosai Yai fice gurin manyan ma,aikatan su wanda hakan yasa yana halar ta seminar kala kala akasan har kasa shen, waje,
Don haka kudi ke shigo mai ta hanyoyi da dama daga gurin aikin,,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA
4?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


Tun safe yau idan ta shiga dakin ta sai ta dinga jin kamar kukan kaza, wace ta haihu,
Amma ita ga tunanen ta kila kazace a bayan dakin ta ke kiwo har take ji a cikin dakin,
Bayan shigar da fitan da takeyi a dakin sai ji take abin ya tsanan ta,
Mamaki sosai takeyi ya akayi har kaza ta shigo mata daki batare da ta sani ba,,
Neman gurin da kazar ke kuka mama Ladi ta fara yi, saboda kukan kara tsanan tawa yakeyi,
Yar ta Samira ce ke taya ta duban kazan, dukawa tayi karkashin gado don taga ni ko da akwai kazar aciki,
Sak kukan a karkashin gadon yake fitowa nan Samira, tadago kai tace wa mama ladi
Mama inaga a nan na tta,boye, don kukan nan, na yaka fitowa,
Shin wai minana a cikin wagga kwallan da nig gani ,
Gaban mama Ladi ne yaba da wani irin dam, a lokaci guda,
Ba abinda yazo mata a rayuwa alokacin sai zancen kwallah da malamin su ya ce kwana arba,in cif ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bude,
In ko ba demuwa ne ya kamata ba tana ganin yau kwana arbain ke nan cif ga lissafin da takeyi na kirga dutse,
Da sauri ta ce wa yar ta ke maza kibar gurin ka ke jiya ko ?
Sai yanzu nat tuna bakazata ba wallah daga waje na sautin ka hitowa ai,
Da mamakin mahaifiyar ta, samira ta dago daga duken da take a karkashin gado,
Kallon uwar takeyi ta ce cikin dan tsoro, mama walle cikin dakin ga na,
Don kega wagga kwallah da nig gani kamar daga ciki naka jin motsi da kukan kazan,
Kai yau Allah ya gwada min yarinya da dumin bazan ,
Shin bana hwada maki cewa ba kazata ba kuma aini hi ma ba anan kukan ka hitowa ba,
Samira dai mikewa tare da nufar kofar fita wajen dakin, zuciyar ta fam da dan zargi da tsoro,,,,
Ita ko mama Ladi, a lokacin tankar ta tsula fitsari a tsaye don tsoro,
A hankali ta dan leka taga ni idan yar nata tabar gurin,
Hanyar fita daga sashen na su ta hango Samiran,
Kira ta sa wa yar nata da sauri Samira ta juyu zuwa kiran maman nata sai dai a zaton ta mama taga kazan da ke kukan ne.
Don dai ita fa tabbas ta ji kukan kaza a gurin, da ta leka kasan gadon mahaifiyar su,,
Mama tace in ni,ji ke hwada ma wani cewa ga abinda mun ka jiya,
Walle yau sai na bata maki rayuwa yau don nasan ki da yawan bakin dumi,
Baki samira ta turo gaba tana cewa kasa, kasa,
Mi ruwa na da wagga maganan shin minzan tai zuwa hwadi ?
Daga haka ta juya abinta tabar gurin zuciyar ta, na mai jin haushin cewan da mama tayi tana da bakin surutu,,,
Da sauri mama taja kofan shigowa dakin ta ta rufe bakin ta dauke da kalman bissimillah ta mika, hannu ahankali ta jawo kwallah,,,
Cikin dan tsoro ta bude bakin kwallah don ganin ko may ye a cikin yake wanan kukan,,,

Zaune yake a office din shi aiki yai mai yawa, don a tsakiyan wata ake,
Irin wanan time din ai,yuka kan yi wa ma,aikata yawa ne, sosai,
Kan shi a duke yake yana fama da rubutu da ke gaban shi,
Massagen su ne ya shigo office din da sallaman shi ,
Mutumin, ya na da kokarin girmama na,gaban shi sosai,,
Duk da yasan cewa ya girmay masu so,sai ba kusa,
Amma hakan bai sa yai masu girman kan kai ba akan aiki,
Hakan ne ya jawo mai,samun alheri ga ma,aikantan da yake aiki tare da su,
Abubakar yadan dago kai don jin anyi sallama an shigo mai office a wanan lokacin da kowa ya natsu ya na aiki,
Duk da yawan daure fuska irin na Abubakar idan yaga baba masinja yakan sake fuska,
A,a baba kai ne tafe shigo ma,na karaso, in ce dai lafiya ko ?
Abubakar din ke tambayar shi ba tare da ya,daga,kan shi daga aikin da yakeyi ba,
Lafiya lau malam sai alheri, dama wani bako ne ke tambayan ka, daga waje,
Shine na ce, barin masa iso ko kasan da zuwan shi ?
Mamaki ne sosai a fuskan Abubakar din don dai shi yasan cewa baida wani wanda zaizo ya samay shi,
Asalima shi tun zuwan shi garin Lagos bai yi aboki da kowa ba,
Iyakar shi daga gurin aiki sai gida sai kuma makwabtan shi da,suke dan gaisawa sama sama da shi,
Cikin mamaki Abubakar din ya kara tambayar baba masinjan shin bakon shine kuwa,
Baba ya dan gyara tsayuwar shi da kyau yace, kwarai kuwa don ma harda sunan ka,da kuma addreshin ka yazo,
Dan shiru ya yi can kuma sai ya ce , ashigo dashi kawai malam mudi,,
Da sauri malam mudi ya juya zuwa, inda ya fito don yai wa bako iso,
Turo, kofan da akayi yasa Abubakar saurin daga kai, don ganin bakon,
Cikin sauri da dago kai, ya mike tsaye,, tare da fadin Baba Wada, da karfi,,
Shima dai Baba Wadan cikin jin dadin rashin shan wahalan da bai yi ba,sosai gurin neman gidan dan yayan nashi yasa shi saurin washe bakin shi,,,
Cikin jin dadi da nuna kulawa sukayi ban hannu da junan su tankar wasu abokai,
Baba daga ina haka, ?
Abubakar ya tambaya cikin mamaki, ?
Ganin bakon nasu ne yasa malam Mudi, masinja ya juya da sauri zuwa, waje,
Ba ai wani dadewa ba sai gashi dauke da kwalban Martina da, take,away a hannun shi,
Wanan Abin yasa Abubakar kara jin dadin malam mudi masinja,
Malam mudi ya kawo wani dan tebur ya aje mai a gaban shi,
Tare da aje abincin a saman tebur din yai wa baba wada wanda ke ta faman raba ido ga office din dan yayan nashi,,,,,,

A tare suka juyo zuwa gida inda Abubakar ke nuna jin dadin shi,
Sai tambayan Wada yake yi labarin kowa a gida, yana bashi ansa,,
Sun iso gida inda suka samu matar gidan kamar kullum a falo zaune, tana kallon TV, ga kuma littafi da cup wanda ke nuna cewa wani abu ta sha acikin shi, amma bata kawar ba ko ta wanke,
Ganin Baba wada bai wani sa Sadiya farin ciki ba sam duk da tagane shi tasan cewa zata iya jin labarin iyayyen ta agurin shi,
Sun dai gaisa sama sama da shi inda hakan bai wa baba wada, dadi ba, sam,
Amma sai dai ya dake saboda ya san cewa ba gurin ta yazo ba ai,
Abinda baba Wada ya fara lura dashi shine, ganin da yayi Abubakar ke ta kokarin, yin hidima da shi,,,
Da mamakin haka ya kwana a dakin da Abubakar ya gyara mai ya kuma kai mai yan abin bukata, na rayuwa,,,,,

A gida hankalin ma haifiyar Wada duk ya tashi don rashin ganin shi da batayi ba tun daren jiya,
Hakan yasa ta duk shiga cikin wani ya na yi don Wada bai taba yin hakan, ba,
Bayan majalissan malam ya tashi ya dan dogaro sanda shi irin wanda malamai tsofaffin hausawa sukan yawan rikawa, zuwa cikin gida,
Wanda sashin malam din kusan shine na farkon shiga gidan,
Shimfidar shi dama a gyare ya ke tun kafin ya shigo,
Da zaran ya shigo ya zauna matan gidan sarakan shi zasu dinga kawo mai gasuwa,
Daga sashe, sashe na gidan suna cewa Baba ho, shiko yana cewa ingwaiyya,
Idan kuma jikoki ne sai su ce A ho, Baba, sai yace shin wata, ta,
Mai shi zai fadi sunan shi sai tsufon ya ce a,a to ke ta,
Ko kuma ya ce kai na , ho dan nema, bakai barci ba, shin,?
Sai bayan duk kusan yan gai da baba malam sun gama sintirin su,
Sanan matan malam suka iso gurin shi,
A lokacin yana kokarin gyara zama da kyau don Abinci da ta gabatar mai da ruwan sha,
Sai bayan ya gama ci ne san,nan maman Wada ta kawo zancen rashin ganin dan ta tun daren jiya,,
Shiru malam yayi don shi ya ma riga ta gane cewa Wada bai gida tun dare, don ba da shi suka yi sallah asuba ba yau,
Maman tace walle tun dazun jiran ka dai ni kai ka, taho malam in hwada maka,
Shin saratu inba abinki ba yanzu da dare na ki hwada min Wada bashi gida ko, ko ya bata,
Da ina ki,ka son in, hwaro?
Da sauri tace
"Ko, ni an malam gani niyyi kana cikin jama,a shinas,sa ban hwada maka ba, malam an,,
Nan malam ya fara fada sosai akan rashin fada mai da mama saratu taki yi da,wuri,
Baba Buhari aka fara kira sai sauran yan uwa, inda atake hankalin mutane duk ya tashi a lokaci guda,,,,,
Kusan a tsaye ranan yan gidan suka kwana don dai su a sanin su Wada bai san ko ina iyakar shi cikin gari,
Baba Samaila wanda sai da safe yadawo daga kauyen da ya tafi lodin shanu don kawo wa kasuwan Kalgo da zata ci washegari,
Shine ya fara cewa cewa shin ko dai
Logos na Wada ya tai,
Inda Abubakar,?
Wa, gwada mai hanyan kurmi inji baba Shaibu,
Baba Buhari ne yace,
"Wane, ?
Rabu da dan yau kaji, ai tunda kaji Samaila ya ce haka to a kawai dai,
Malam dake jin muhawaran diyan nashi yace,,
Missa ka ce haka ?
Baba kwanakin baya da ni,ddawo yaka tambayana
Wai nawa na,ka kai mutum Lagos da nan kebbi, ?
Ni tambayai ko wa kazuwa Lagos din shina yace min wai wani abokinai kason zuwa,,,,


Don Allah kuyi hakkuri da,wanan pls ban da caji ne yan uwa,,,

ZEEE MAKAWA YELWA=?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


ARRAHAMANIN RAHEEM



A hankali take kokarin mika hannun ta don ta bude kwallah da aka bata,
Sai duk a cikin tsoro take yin hakan, amma zuciyar ta ya kagu da ta bude saboda tana tsan manin KUDI,NE, ma su din bin yawa acikin, kwallah akai mata , na sihiri, kamar yadda take zato,
Amma tunanen ta, ya fara harbawa ganin ta a cikin dukiya tana yadda take so da KUDI,,,,,,,
Jawo kwallah tayi zuwa tsakiyan dakin ta a hankali, gurin da haske yake,,
Daga tsugunen da take ta mika hannun ta ta bude kwallah a hankali,
Cikin wani, irin gigicewa ta jefar da marfin kwallah a gefe guda tana mai, fadin
INNA,LILLAHI, WA,INNA,ALAIHIM RAJ,UN,,,
Yau naga shiga uku ne Ladidi may na daukowa kaina a gidan duniyar nan,
Kara kai idon ta tayi a karo na biyu don ta dubi kwallah ta kara ganin abin da ke a cikki karo na biyu,,
Amma ina sam bazata iya jure kallon wanan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login