Showing 150001 words to 153000 words out of 388021 words

Chapter 51 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8238

kamshi maclean, su tissue, cotton bund, da sauran su,
Sai wani material mai kyau da dauka ido kalan nawa, light pink,
Kalan yai min kyau sosai a idona don nakai wani lokaci ina ta shafan material din,,
Namayar da kayan a leda na dauka na sa cikin wardrobe, dina,,

Dogon riga na yan kasan Niger da na sayo ya ji aiki a gaban shi nasa,,,
Nayi wanan kwalliyan ne don kin san idan kina da kishiya, bawai sai ranan da zaki karbi girki bane zakiyi kwalliya a,a
Next day to kiyi girki zaki gyara jikin ki ta yadda mijin zai rude yaji kamar ace ke ce zakiyi, girki a ranan,
Jin banji motsin kowa a waje ba yasa na koma saman gado na na haye,,,
Gadon da yasha gyara cikin wani zani gado ja mai zanen flowers farare,,,
Dakin yaji room fresh tunga labulen dakin zanin gado da bathroom don sune ake sawa room fresh, sai daki ya dade yana kamshi,
Dan kwantawan da nayi ashe barci ya fara kwasa na saboda gajiya,
Sai muryan Anty Sadiya naji kaman a mafarki, tana cewa
Au, Meenatu kin kwanta ne,?
A hankali na bude idona ina kokarin tashi daga zaune, ina kuma, cewa, yanzu fa na kwanta ashe barci ya dauke ni, ko
Idon ?nty na saman rigan da nasa alokacin, yana daukan ido, ,
Anty ina kwana ?
Tace Alhamdullahi Meenatu,
Ya gajiyan aiki,?
Na tashi naga ko ina gidan yau sai kyalli ya keyi murmushi nayi nace naga idan anyi tun da safe yafi sauki ne shi yasa nayi,
Ta ce to nagode, murmushi nayi yayin da naga ta juya zata bar dakin don fita,
Ni kuma sai na koma saman pillow da nake kwance da farko,
Amma sai kuma Anty ta tsaya tare da juyo wa tana fuskan ta ta,
Tace Meenatu dama yau, tuwon alkama naso in muna kuma sai dai nasan idan nayi zai sake ne, nace to babu matsala Allah ya kaimu anjima lafiya ,
Sai dai ina son idan anbarni zan tafi gurin wanke kai anytime na dawo sai muyi,
Na karashe zancen cikin murmushi ,
Tace ai badamuwa ko sai kin dawo, ke nan don ni zan shige ciki,
Komawa nayi na kwanta sai dai kuma barcin baizo ba again, don haka sai na lumshe ido,na,,,
Tausayin irin rayuwan, Anty Sadiya nake,yi mutum ba ruwan shi da komai shi,
Idan ba ka zauna da ita sosai ba sai ka dauka bata son mutane ne ita,
Kamar tana kyaman zama da mutane don yawan, daure fuskan ta,
Amma daga yau tunda har na fahince ta insha Allah a tare zamu dinga aiyukan mu na gida,
Na nisa nace, aiko banza ita matar yayana ce kuma kaman yan uwa muke don zama gari guda, da muke,
Idona yana daga lumshen da yake ina ta tunanen duniya,
Alaman mutum ya na tsaye a kaina naji sai kuma kanshin turaren da hanci na ya shako, min, na dan baiwa, watau Yaya Abubakar, ke nan,
Hakan yasa ni bude yan daradaran idona sai cikin na Yaya Abubakar wanda ke tsaye, a gaba na, fuska ba yabo ba fallasa, ya kura min idanun nan nashi masu firgita mata,,
Kokarin mikewa nayi zaune ina mashi wani irin murmushin jan ra,ayi,
Kafin in ka daga zaune sai naji muryan shi

Tambaya ya jefo min Barci kike ne ko kuwa hutu ?
Nace, kawai dai ina dan hutawa ne kawai, kafin in fita,
Ina kwana Yaya ?
Lafiya kalau ya kika tashi ,?
Ko da yake naga ai lafiya kike tunda har kin yi wanan irin aikin haka ?
Murmushi nayi nace gidan ne yai min ba dadin gani shi yasa na kamawa Anty gyaran shi,
Kin kyauta yace tare da dan murmusawa, ya ce zai tafi shi sai ya dawo,
Ban san lokacin da na jefo mashi tambaya ba da cewa kayi break fast ne ko Yaya ?
Sai naga ya dan bata rai yana dan jiji ga kai yace yau bazan tsaya break ba agida kifita ku karya,
Na ansa mashi da fadin to Yaya,
Zai fara tafiya nace
Don Allah Yaya ina son yau in tafi saloon gurin gyaran kai ?
Cak ya tsaya yadan yi shiru zuwa can ya nisa yace,
Ok ki dauki ki nan a saman drawer a dakina Hamza ya kai,ku, amma dan Allah ku kula kada yai tukin ganganci da ke ,
Nace tare da Fattu zamu tafi insha Allah zamu kulla,,
Ya ciro kudi daga cikin ajihun wandon shi ya miko min,, yana cewa,
Ba matsala yace yasa kai ya fita abin shi,
Godiya nai masa, tare da fatan a dawo lafiya,,,
Na nisa bayan fitan shi tare da komawa na kwanta,

****** ********** ******
Mun samu mata da yawa a cikin saloon din, don haka muma muka bi layin zama,,
Matar mai shago tafito a take ta shedani, don bata manta da ni ba,
Da murna tare da sakin fuska, ta, tare mu ta na jin dadi,
Ta umurta da a kawo muna ruwan, sha duk yadda naso, kada ta wahal da kan ta gare mu amma sai taki,
Bamu kadai ba ranan harda sauran mutanen da ke shagon ta saya muna ruwa masu sanyi,,
Mata sai hiran duniya akeyi ana ta yan dararaku kowa da abinda ake mata,
Wata daga cikin matan ta dan dubeni take cewa da za a wanke maki kafa, ai maki ado zai yi kyau,
Murmushi nayi ina cewa ai naga kamar da layi da yawa yau, akwai jama,a agurin,
Anty mai shagon tace barin maki da kaina kaunata,
Ba bata lokaci a ka kawo roba a gaba aka fara gyara min kafa,
Matar da tabani shawara a fara gyara min kafa wayan ta yai kara ta dauka suna magana, sai dai a cikin zafin rai take zancen ta,
Bayan taga tafara fada ita kadai tana cewa ita za,a kawo iskan ci ?
Sai Anty mai shago tace to ai shi wanda kike fadan dashi yanzu baya kusa,
Matar tadan ja tsuki gefe tana mai kauda kan ta ,tace,,,
Bari kawai Anty wata shegirya matace ke son shiga gona ta,
Wata mace ce gurin aikin su guda da maigidana shine take ta kokarin shige masa,
Yanzu wai kirana yayi yana ce min wai an kawo lace masu kyau a shagon su amma, Aliya ta zaba muna,
Ina ruwan ta da ni da har zata zaba min a binda zan sa tasan colour din da nake so ne,?
Anty mai Shago ta nisa tace aiko naki ya samay ki wallahi,
Don kin san irin matan nan idan sun lakewa mijin ka sai Allah,
Fattu daga gefena tace, irin amaryan gidan ku ke nan Meenatu,
Nai murmushi kawai batare da nace komai ba don dariya abin ya bani,
Anty mai shago tace, ke kardai ki ce min an ma kauna ta kishiya kuma,
Da ba kun ce su biyu bane,?
Fattu tace wallahi Anty, wata irin garmakekiyar mata na nan a cikin su wai itace amaryan su,
Duk ta girmay masu har maigidan nasu, sai kishin bala,i,,
Anty mai shago tace hmmm,ummm, amma gaskiya abin da mamaki sosai a ciki,
Fattu tace ai ina ga dama kamar zancen auren ta yana gaban na Meenat don da alaman sun dade a tare,,
Sai matar da tafara zancen tace itama wanan din wani brother din maigidana yace min wata mai kama da yar Togo ce, ba yarinya bace irin tsofin barikin nan ne,
Fattu tace shima dai maigidan su Meenatu bazaka ce zai iya auren wanan mace ba wallahi,
Sai Anty mai shago tace o kin mutu wallahi an fada maki cewa baki sake suke rike mazan, ?
Ai sai sun dade suna masu shiri sosai kafin su tun kari na miji tukun,
Wata taso taimin haka ga maigidana na bita har gida na ci ubanta na nuna mata nafita zaman bariki,
Wai har abinci take kawo wa maigidana a office da kuma ziyar a gida idan ban gidan,
Fattu tace ai ina ga ita Meenatu tasu ta samu shigane saboda yadda rayuwan uwargidan su yake na ko in kula,
Abinci fa sai maigidan ya sayo masu take away, don bata iya dafa wa ita bata da time,
Sai matar wace kekira da , Humaira, tace kinga kowa nima halina ke nan don ban da time da safe idan nafita gida ban dawo wa sai, after six kinga a lokacin duk nagaji,
Anty mai shago tace yo kin mutu wallahi Humaira idan zaki gyara maza ki gyara kafin ai maki sakiyar da ba ruwa,

Sai wanan lokacin nasa masu baki a hiran su daidai lokacin da nake kokarin gyara kafana, nace,
Amma gaskiya don kina zuwa makaranta bashine zai baki excuses din kin dafawa maigidan ki abinci ba,
Anji cewa da rana baku a gida gaba dayan ku, to da safe da kuma dare fa, ?
Baki da right da zakice bazaki kula da mijin ki ba idan har kikayi sakaci yanzu ne wata sai ta dafe maki shi,
Duk da dai mun san cewa mata hudu shari,a ta yarda masu dasuyi,
To amma ai mutum sai yayi kokari ya gyara ta ban garen shi kafin yazama ma mitum to latet,
Cikin dan marairai ce murya matar tace, to yaya zanyi ni don Allah wallahi har kunsa duk naji jikina ya mutu,
Fattu tace wallahi wani lokaci mu matan sakacin mu ke kai mu ga halaka ai,
Matar a take duk tashiga damuwa tace wallahi kamar kun sani cewa
Yanzu duk hankalin shi na kula da yana gurin ta don ko da dare na zaki ga yana waya muku muku, da ya gan nin sai ya kashe yana cewa I will call you back,,,
Cab,di,jam inji Anty, maishago, tace gaskiya a kwai aiki sosai Hummaira,
Na ce ba wani aiki kawai, dai sai dai ta gyara mu,amulanta da mijin ta,
Bakin su na haduwa gurin ce min kamar, yaya fa,?
Nace,kamar ta kyautata tsakanin su mana ta yaya za,a ce mace sam bata da time din mijin ta kwata,kwata,
Anty mai shago tace gaskiya Humaira baki da gaskiya anan,
Don ma sai ince kece kika ba da kafa ai maki hakan ma,
Humaira ta ce to, ya zan yi ne ni dan Allah duk na rasa ko may zanyi wallahi,
Na dan ce masu hummm, gaskiya abubuwa da dama,,
Kin ga da farko dai abinda zakiyi, shi ne ki fara sake jiki dashi,
Kamar kuci abinci a tare, ko kuma idan kin rigashi ci idan ya zo zaici, sai, ki zauna gab dashi,
Kece mai service din din shi, kamar suzuba abinci a plate,
Kara miya idan da bukata hakan, kara gishiri ko maggi,
Da farko ki tabbatar da tsabtar gidan ki a kullun kafin ki fita,
Sai kuma ki tabatar da cewa, kin tanadi komai wanda zakiyi abincin dare, da idan, kin dawo daga makaranta,
Sai kuma abinda zakiyi maku breakfast kada ki fara kibar, mijin ki yafita gidan ki bai karya ba,
Don kada keep mantq cewa wanan bokon da kike zuwa yi iya karshi a duniya zaki bar shi,,
Sai ke kuma kikai sakaci da gobe kiyaman ki kika kama duniya kawai,
Shin bakya tunanen, cewa, Allah zai tambaye ki yadda kikai zama da Amanan mijin ki da ke kanki,
Humaira ta wani nisa,wa tace, gaskiya ban san may ma zance ba,
Nace to kinga wanan ke nan Humaira gaskiya akwai matsala gare mu matan yanzu,
Gaba dayan su su kace gaskiya kan,
Sainaci gaba da cewa sanan ki tabbatar da cewa idan kin gama girkin duk saurin da ki keyi ki ba mijin ki time tukun kafin fitar ki,
Zuba ruwa a cup ko drinkis,
Ki dan rika jan shi da fira jefi,jefi, idan ya gama sai ki, zuba ruwan wanke hannu, ko mika tissue, da toothpick, kwashe kayan abincin zuwa kitchen ki gyara gurin cin abincin,
Ki tabbatar da kin tsabtace makwancin ku kin gyaro ko ina a dakin,
Kada ki nuna gazawanki gare shi wurin mu,amulan aurataiyya,
A jiyan zuciya Humaira ta sauke a lokaci guda tare da kallon mu gaba daya,,
Kin ga dai in har zakici gaba dayin haka na insha Allah ba yar Okene ba ko yar Eteku ce dole ta barki,
Tace Meenatu bani noban ki please zamuyi magana
Tafara yi muna, godiya kaman zata fadi kasa,
Nace sai mun kara haduwa zan fada maki yadda zakiyi mu,amullah da yan uwan maigidan ki,
Tace ai kaji wani matsala Babba don sun sani gaba yanzu haka da muna funtata,
Daga haka muka cigaba da kara tattaunawa a tsakanin mu akan yadda irin wayan nan matan masu zaman kansu ke kama mazan mutane su mayar nasu,
Ta hanyar sakaci irin na mu matan hausawa musan,man matasan mu na yanzu,,
Irin yadda mukafi karfi da neman duniya sama ga lahiran mu,
Mun manta da maganan Allah da Annabin sa akan biyayyan aure, muna yawan shagala da rayuwan mu,

Angama min gyaran jikina nafito wata irin shar dani tankar amarya a ranan,
Don,ni kaina nasan cewa nayi kyau sosai tankar wata fure,
Kudin da nabawa Anty mai shago na mu biyu sai cewa tayi bazata karba ba,
Amma nace don Allah ta karba idan ba ta raina bane, takarba don Allah,,
Tun muna saloon naba Baba Hamza, kudi ya sayo muna abin bukatan mu da na yau da gobe,
Ina shigowa gidan Sallawatu ta kyalla ido taga yadda na ke ta wani haskaw ai sai kawai ta rude,
Don haka daki kawai na shiga, na farayin sallah saina fito na nufi dakin Anty Sadiya ina ce mata nadawo,
Tana zaune saman kujera tana kallo wani India
Wani irin kallon mamaki naga tai min tare da saurin kau da kai gefe tana cewa kin dawo nace zan shiga kitchen kafin ki fito,
Nai gaba abina ina murmushi a raina ina cewa kishi kumallon mata Anty Sadiya kuma kishina takeyi ne haka,

Ina shiga kitchen din nafara gyara gurin da Sallawatu ta dan bata da tai girkin rana,,
Sai da na kara wanke pot din gudun ko wani kwaro ya hau saman shi bamu sani ba,
Na tara ruwan a zinc din direct zuwa pot, daga haka na kunna Gas,
A lokacin da zan jawo Ledan da aka,siyo muna fresh, kayan miya don amfanin mu,
Tace to har kin,fara ko nace eh Anty sai nake nuna mata kayan miyan da sayo muna inda nake gwada, mata komai yadda suke,
Tare mukayi girkin mu tsab ranan da anty inda take nuna min gurin, da take nuna min inda take samun kuskuren girkin ta,
Mun gama a cikin lokacin muka kai sama dining table din mu,
Ina gyara kitchen ne sai ga anty tana ce min, ki tsaya, Meenatu intafi in gyara infito sai ke ki shiga,
Ba ta dai fito fili ta fada min ba amma na fahinci manufar ta tana gufun wani abu yafaru da abincin namu,
Kara gyara falo nayi ina kallon Salawatu sau biyu tana fitowa, falo,
Sai ta gan,ni a falo ina aiki sai ta juya ta koma, anjima kadan kuma tafito kamar mai neman wani abu, sai kuma ta juya,
Fitowan Anty Sadiya sanan, na, shige dakin nima na je don inyi sallah,
Ban fito ba sai musalin, takwas da wani abu a lokacin har sun sun hadu don cin abincin su,
Ina saye da wani, dogon riga mai yar karamar hannu iya hammata,
Kaina yana saye da hullan net mai raga irin mai nuna kitson mutum,
Na gaida Yaya Abubakar dazuwa naja kujera na zauna alokacin ya fara kai loma sai naga ya tsayar da hannun shi ya dan juyo gurin da nake tsaye,
Kamar zaiyi, magana sai kuma yaci gaba da cin abincin shi batare da yace uffan ba,
Gabadayan ranan duk mun ci abinci sosai Baba Hamza ne da nace yazo ya karbi abinci dazun shine ya shigo,
Sannu Baba na nace ma Hamza din yakarba da cewa yawa anty sannun ku da gida ya gajiya,
Sallawatu wace tun shigowan shi ta canza fuskan ta duk da haka sai da ya gaishe su gaba dayan su,
Sanan ya shiga kitchen daukan abincin shi, yafito yana cewa saida safen ku,
Nace ka gaida su Fattu da Mama ,
Yaya Abubakar yace kai Hamza da safe kazo akai motan ca baka gurin wanki,
Hamza ya ansa da fadin tau maigida insha Allah zanzo,
Yaya ya ce mashi sai kaikai ta can tukun gurin da ake min service din ta adan dubata,
Yace tau maigida nagane gurin inda muka taba, zuwa kabar ni na karbi karfe ko?
Kai yaya Abubakar ya gyada mai nasan don baison yawan magana yasa shi gyada kai din,
Cup din tatacen kankana da muka gyara ya ce a miko mashi,
Sai da ya kora ruwan kankanna da kyau sana ya aje cup din,
Ina kokarin hada plate din gaba daya naji muryan Yaya Abubakar yana cewa,
Wanan kitson fa Meenat kamar na yan Sudan aiko kin sha zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login