Showing 90001 words to 93000 words out of 388021 words

Chapter 31 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8247

cewa zan tafi ba matsala ai,
Sai gaban ta wani irin mugun faduwa yakeyi tankar zata shude a gurin saboda bacin rai,
Saboda wani irin bala,in da take ji sai take ganin ma,aikatan yau yana juya mata,
Tafiya takeyi tana cewa Yallabai ne, yau yake nuna min cewa yana son yarinyan nan ke na,
Yarinya da shi da bakin shi yake ce min a gidane aka hadasu bai ma san ta ba,
Kai lalai,ma namiji abin tsoro ne gaskiya,
Wai yau Yallabai din tane da bakin shi ke fada mata zance akan wata mace,
Tunda har yake bata lokacin shi, haka sosai bai ko iya boye wa,
Zaune take a cikin office din su duk rayuwan ta yai mata kunci ta rasa may ta ke ciki ne wai,
Idan ba tayi da gaske ba fa abin zai bashe ta, gaskiya ita bazata iya zama batare da ta mallaki miji irin yallabai ba,
Gashi ta samu kuma yana batun kurce mata daga hannun ta,
Lubuna ce tsaye a kanta tana karewa kawar nata kallo a cikin mamaki lokaci guda ta ga duk ta canza mata,
Kafadan ta, ta,dafa sai da Salawatu ta dan girgiza kadan don tayi zurfi a cikin tunane ko
Dago idanuwan ta da sukayi jawur tayi saboda bacin rai, ta dan sauke ajiyan zuciya,
Tace Lubuna Abubakar yana son yai min yawo da hankali na wallahi,
Bayan ya gama sani na yarda dashi 100%, sai gashi yana son ya kawo min sabon zance kuma,
Cikin wani irin takaici lubuna ke kallon aminiyar nata ,
Irin yadda ta tsaya saboda so tana son wahal da rayuwan ta ga banza,
A gaskiya Salawatu ki na bani mamaki kwarai da gaske,
Wai shim Oga Abubakar shi kadaine namiji a Abuja?
Kar ki manta kina da masoya da yawa fa akan maye zaki tsaya kina son batawa kan ki lokaci ne haka,?
Kodai kawai don shi yaki ku tsaya kuyi Roncy a waje kamar sauran maza,
Ke kuma kin riga da kin mutu a kan shi, idan ba kin dandana shiba bazaki iya hakuri da shi ba,
Hawaye ne suka biyu fuskan ta zuwa sauka kasan fuskan ta,
A cikin takaici take cewa Lubuna ina son wanan guy din kema kin sani
Kuma I am lucky yace zai aure ni,
Idan bashi din da yazo min da zancen aure ba kinga wani wanda yazo muna da zancen aure ne,
Dubi irin zaman da mukayi da oga,Yusuf har wuce kinji zance aure ga bakin shi,
Gaskiya Lubuna bazan so in kare rayuwana a haka ba?
Don lokaci yayi da ya kamata mutum yaiwa kansa fada ,
A yanzu bani da burin da ya wuce in auri Yallabai Abubakar,
Amma gidan su da yan uwan shi suna son suyi muna tsakani, da shi,
Tausayi taba aminiyar nata don haka takai zaune tana mai kallon ta acikin tausayi,
Mutun mai karfin hali da dauriya irin Salawa ace yana kuka haka akan soyayya,
Salawatu ke nan inji Lubuna tana murmushi irin na bacin rai,
A gaskiya ni nasan cewa dama zaki fuskanci irin wanan matsalan gurin mai mata sai gashi kuma ya kara yin wata matar,
Don a gaskiya yan Yallabai sun nuna maki cewa basu kaunarki acikin su,
Don zancen auren ki yana gaba da na wanan da suka daura mashi,
Yanzu tunda har kin nuna cewa zaki iya zama dashi a hakana da mata dayawa ai ba matsala sai mu san yadda mukayi, ai,
Da sauri Salawatu ta daga kai ta kalle ta cikin mamakin jin abinda ta ce,
Kiyi shiru kawai mugani in har ya ce zai guje ki zai gamu da aikin mu sosai,
Munyiwa banza ma balle wanda muke son zama dashi,,,,

****** *********** ******
Yau, satina gudu atare da yaya Abubakar, wanda dan zaman da mukayi a tare yadan jawo muna yar shakuwa kadan a tsakanin,
Koda yake shakuwar tamu sai idan muna atare ne saman gado inda ba haka ba,
Sam bazaka gane farin cikin dan uwan nawa ba don a koda yaushe fuskan shi a daure nake ganin ta,
Nasan cewa kwana bakwain da mukayi tare da yaya Abubakar,
Ya dan bude min wani sabin babin rayuwan da Anty Amarya ta dade tana lurar da ni amma ban fahinta ba,
Ya Abubakar gwarzon namij ne, wanda yasan yadda zai tafiyar da macd a cikin ruwan sanyi,
Har ta mantar da damuwan ta don sannu a hankali yadan kawar min da damuwar irin zaman da ada nake hage dashi,

Yau Anty Sadiya ce zata karbi girki a gidan don haka kamar yadda na tsamani sai ban ga wani alamar karban girki daga gare ta ba,
Saboda banga fitowan ta zuwa dora muna girki ba kamar yadda yake,
Ina zaune saboda rashin abin yi na gyara daki na da bayi yafi a kirga, sai kamshi ke tashi ta ko ina,,
Karan shigowar motan yaya Abubakar cikin haraban ne yasani gane cewa ya dawo a lokacin,
A hankali ya turo kofan falon gidan hannu shi guda dauke da yar briefcase din shi guda kuma acikin aljihun wandon shi,
Shiru yau ya samu falon don kwana biyu kamshin turaren falo da na girki ne kan tare shi,,
Mamaki ne ya kama shi don ba haka yasaba gani kwana biyu ba,
A hankalo ya tako zuwa cikin falon inda ya aje yar case din shi saman center table,
Dakina ya nufa da ganin shi a gajiye yake, don daga tafiyan shi zaka gane hakan,
Daga kofa ya tsaya inda ya dan jingina jikin shi da dan katangar kofan dakin,
Zaune nake saman stol din dressing mirror dina ina gyara gurin,
Jin shigowan shi dakin nawa ne yasani dan juyowa ina kallon shi,
Cikin jin yar kun ya nake ce mai sannu da dawo yaya,
Sai da yadan tako har zuwa bakin gado yadan zauna yana cewa
Yauwa ya gida, da aiki Meena,?
Ban bashi ansa ba sai murmushi da na dan yi, kawai,
Nagaji wanka nake son yi kafin in dan fita inyo muna shopping,
Yau banga drinks din taro na a saman dining table ba shine nazo jin dalili,
Kaina yana duke a kasa nace cikin yar siririyar murya,
Yau bani ce ya kamata in tare ka ba yaya Anty Sadiya ce da girki,
A take naga annurin fuskan yaya ya gushe waya fada maki hakan?
Yau satinka guda a dakina shi yasa nasan da hakan,
Ok kawai naji ya iya cewa tare da mikewa tsaye lokaci guda,
Sai da ya kai gaf da kofan fita daki yace ke kuma kina ta faman kidayawa ko ?
Daga haka yasa kai yafita batare da ya kara cewa komai ba,
Fafadan bayan shi nabi da kallo har ya shige ma gani na,
Na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da cigaba da abinda na keyi,
Dakin shi ya wuce direct inda, bai tsaya bata lokaci ba ya shiga wanka, kamar yadda yace,
Ya shirya tsab cikin kananin kaya, da suka karbe shi suka fitar mai da kurciyar sa, afili,,
Dakin Anty Sadiya ya shiga inda ya samay ta zaune, tana kokarin dauko wayan ta dake gefen ta,
Gefen dressing mirror din ta yai niyar tsayawa amma sai yaga kura tab a gurin,
Hannu ya dan kai ya lakato kuran da yar yatsan shi yana ce mata,
Haba Sadiya wai ke yaushe zakiwa kanki fada ne har ki koyi tsabta,?
Yanzu duk irin wanan gyaran da yar karamar yarinya ke yi a gidan nan kwana biyu,
Baisa ki fahinci cewa gyara ga mace yana da wani amfani ba,,
Abubakar, dakata haka please ?
Kada ka dinga hada da wanan karamar yarinyar da ka susuce akan ta haka
Tayi irin rayuwar ta in yi kalar tawa don haka daga yau kada ka kara hadani da ita
Dakata kiji Sadiya don naga kin dauko hanyar yi min rashi mutunci ina fadi kina fadi,
Kin san bazan yarda ba sam da wanan sabon halin don bani daukan wulakancin mace sam,,,
Ya fara tafiya a hasale yana cewa Idan kinga dama ki gyara, idan bazaki gyaraba cikin ki tayi,
Kuma ki tashi ki girka muna abinda zamuci don kin san kece da girki yau,
Da sauri ta dago kai tana kallon shi fuskan shi ba wasa acikin shi sam
Abinda yasa tai shiru kenan har ya fita, daga dakin nata ba tare da ta ce komai ,
Sai dai acikin zuciyar ta sai mita takeyi don may zaice sai ta girka bayan ba haka suka saba yi ba,
Suna kai sati biyu uku ba tare da sun girka komai a,gidan ba,,

****** ********** ******
Zaune suke daga ita har shi rayuwan su babu dadi sam alokacin ,
Can dago kai fuska adaure yace gaskiya ba karamin kuskure ki kayi ba Hajja na barin wanan yarinyar ta shiga gidan,
Hajja ta dan gyara zama tana cewa wallahi Mai lassa ba mu san da zancen auren nan ba har tarewan,
Don shammatar mu mugun tsohon nan yayi ta ko ina bai bari mun san da zancen ba,
Gaskiya Hajja sai dai mu bi a sannu don idan mun matsa wanan zancen cikin mu yayi sosai,
Karki manta cewa wa yan nan mutanen sune suka kashe min dayan dodon da, aka hada wa matar gidan,
Duk yadda naso mu dauki fansa akan su abin baiyi ba , fole na kyale su ,
Yanzu kuma kinga ita wanan yarinya ita ma daga cikin su take,
Don haka akwai babban alamari maigirma atare da ita
Malam nima naga alamar haka don ko shi mijin yar nawa har yanzu ban samu yadda nake so ba gare shi
Yace yanzu ba matsala nasan hanyar da zamu bullowa al,amarin,
Sai a lokacin Hajja ta dan saki murshin jin dadi don da duk a rude take,,,
Wasu garin magani tayabata har kala uku wanda zata zubawa dodon ta don samun sauki,,

****** ********* ******
Zaune muke gaba dayan mu saman dinning table din gidan,
Ita da ta girka abincin itace a tsaye tana zubawa cikin daure fuska,
Adole tai girki ta gaji da aiki yau,
Jealoup din taliyane yai wani fari fait, ya cucure guri guda,
Kallo guda nai mai naji hankalina ya tashi sosai saboda yadda na hango shi,
Bayan ta gama zubawa mai gidan ne taturo min kulan agaba na wai in zuba nawa,
Serving spoon guda na dan zuba na tura mata agaban ta,
Da sauri yayana ya dago kan shi yana kallon na da mamaki,
Itako sai naga tana lodawa kamar yadda ta loda mashi,
Na daga hannu a hankali nakai spoon guda a baki, na,
Amaine yaso ya taso min amma sai Allah ya tai make ni na samu na hadiye shi da kyat,
Ruwa dake cikin cup din glass a kusa dani na dauka da sauri nakaiwa baki na samu ya wuce min,
Yayana ma ya diba ya kai abakin shi ya dan kai wani lokaci da shi a cikin bakin shi ya kasa hadewa,
Da karfi naga ya fuzo shi yana cewa Sadiya zaki kashe mune,
Ga tankwa ga gishiri ga kuma maggi bai narke ba kin sa na tura maggi a baki ?
May kake nufi kana nufin bai yi dadiba ko may,
Idan yai dadi sai ki cinye ke,?
Wai ke bazakiyi wa kanki fada bane Sadiya,
Taliya da, daren nan shi zamu ci ?
Bakya ganin yar uwar ki tuwo take muna har kice leda biyu da kusan rabi,
Amma ke don ke ta zakiyi muna taliya taliyan kuma ba ko test abu haka kamar dahuwar jariri,
Gaba dayan mu shiru mukayi kowa kanshi a kasa saboda irin yadda yake magana acikin fada,
Haka kike son mukwana da yuwan wanan yaji ai sai ya halaka mutum abanza,
To ni gaskiya ban san ya kake son inyi ba don dai ni banga abinda wanan taliyan yayi ba,
Ta diba takai a bakin ta da sauri tadawo dashi tare da daukan ruwa takama kwankwada da karfi,
Nikan mikewa nayi tare da daukan plate din wanda na zuba zuwa kitchen,
Ina fitowa na wuce daki na da niyar in kwanta don yau ni kadai ce adakin,
Ban dade da shiga ba naji fitan yaya Abubakar da mota ,
Kayan jikina na sauya zuwa na barci don in yi shirin kwanciya, wayanane yai kara,
Noban anty amaryace takirani ,
Da murna na dauka ina cewa cikin shagwaba,gaskiya Anty kin daina sona yanzu tunda kika tafi sai yau kika kirani,
Dariya tayi tana cewa ba wata ya bayan ke my daughter,
Gaisawa mukayi natambaye ta yaran gidan mu kaf din su,
Sai da muka dan lafane take tambaya na ya zaman mu yake,
Yar dariya nayi nace la Anty babu komai lafiya kalau muke,
Kin tabbatar Meena,
Gaskiya Anty babu komai ,
To haka nake son ji don wallahi kawun ki ne ya hana in kira ki kwana biyu,
Ko yau da kyat na samu ya yarda in kiraki wai kina shan amarci kada in damay ki,
Kunya ne ya kamani kamar tana gabana nace haba anty please ki bari ba wani amarci da nake sha ban da kewan ku,
Ke tafadi da karfi kada kisa inzo abuja gobe in tambayi in-law nawa ko lafiya yake,?
Wayan takashe daga haka batare da mun koyi sallama ba,
Sai dai ina tsanmanin Uncle dina yana kusa da itane alokacin,
Mikewa nayi don in sawa kaina ribon, sai naji anturo kofa,
Yayane hannu dauke da leda guda biyu, ya aje min wanda baikai sauran yawa ba a saman mirror na,
Idon shi kar a kaina yana min wani irin shu,umin kallo,
Godiya nai matare da cewa su anty suna gaishe shi,,,,,
Da yar fara,an shi ga fuska ya ce au yau sun bugo waya ke nan?
Nadaga kai a hankali alamar Eh,,,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/28, 10:09 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 7?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-MU,ZIL,,,,


Sai da na tabbatar da nagama gyaran dakina na fada wanka,
Wani material lace ne milk da adon flower purple kanana, ajikin shi sai duwatsu jefi jefi jikin shi, dinkin buje da riga ne,
Kaina da ya kai kusan kwana goma akitse yadamay ni da kaikayi, sosai,
A hankali nake kokarin daure dankwali a kan naji shigowqn yayana dakin,
Fuskan shi yau yafi na ko yaushe rashin walwala don tamau, yake a daure,
Yana saye cikin wasu yadi fari mau laushi wanda har zaka iya hango farin singilatin shi a fili,
Tun kafin ya karaso dakin na kai kasa cikin ladabi, ina gaishe shi, cikin yar siririyar, murya na,
Sai a lokacin naga ya dan sake fuskan shi ka dan yana amsa min,,
Ya ce lafiya kalau ya dare?
Dakin na ga yaiwa wani irin kallo sai kuma ya fara tafiya yana cewa zan tafi office, sai na dawo
Allah ya tsare yaba da sa,an fita, adawo lafiya,
Murshi yadan yi don jin dadin adduan da na jero mashi da wanan safiyan,
Abinda tun zaman su da Anty Sadiya bai taba jin ta furta ba ko da a wasa ne,
Cikin rawan murya da kuma tsoro da shakka nace mai yaya don Allah ina son inda shiga nan makwabta a min kitso ko kadan ne,
Da sauri naga ya daga kai ya kalli kaina shi a ganin shi ai kitson baiyi komai ba,
Shima da bai saba ganin ana kitso a gidan shi ba balle yasan tsufan shi,
Tambayana yayi da cewa kin san mutanen gidan ne ?
Shiru nayi don ban da ansa bayarwa komay ya tuna kuma sai ya ce anyway ki shiga ki gani idan babu masu yi sai ki bari gobe akai ki, saloon,
Nagode nace mai tare da karayi mai adawo lafiya,

Bayan tafiyan ya da yan mintoci na fito falo don inga komay aka hada muna breakfast in dan ci kafin in fita,
Babu komai a saman table din sai robobin take awaya din da ya siyo muna jiya dadare,
Anciye abin da ke a,ciki ba a kwashe su an,zubar ba a dustbin,
Nawa na tuna dashi wanda nasa a fridge daren jiyan,
Da sauri na nufi hanyar kitchen din na bude fridge na dauko su,
A cikin microwave na sa nadan yi stemming din shi,
Kitchen din yaiwani hargitsewa kamar ba jiya da rana na goge shi ba bayan na gama girki,
Ga taliyan jiya yakara komawa wani iri acikin plate, zaban kazan ta,
Da sauri na kwashe su na zuba a dustbin din baya inda wari bazai damay mu ba, saboda taliyan baida dadin gani,
Nadawo nadan gyara kitchen din tsab yakara komawa daidai,
Najawo abinda na sa a cikin microwave na kashe, shi ta baya,
Da shi na karya kumallo rana na dauko goran five alive, na dan tsiyaya na maida sauran,
Ban karasa cinyewa ba naji fitowan matar gidan acikin nightgown take har zuwa yanzu, yai dauda so,sai don har yar bashi ya,keyi,
Kallon take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login