Showing 183001 words to 186000 words out of 388021 words

Chapter 62 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8270

Yar karuwan rigan barcin da nasaka mai kama da babu komai ajiki na ya baiyyana,
Sai ganin, Yaya Abubakar nayi a gabana yana cewa masha Allah, Meenat you look so gratuitous,
Na lumshe idona tare da hade wasu miyaun mintin da nake tsotso a bakina,
A hankali naji hannuwan shi a saman wuya na yana dan tafiya dasu kamar tsutsa, a hankali har zuwa kaina,
Harshen shi naji a kunnuwa na yana min magana daga ciki a hankali,
Abinda ya saukar min da wani irin kasala a jikkina lokaci guda,
A take ya fara amfani da harshen shi kamar wanda ya samu Sweet yana tsosa,
Jikina yafara dan karkadawa kamar yaune farkon haduwa na dashi,
Bansan ya akayiba sai jina nayi saman katafaren gadon yaya, yafa aika min da sakon ni, kala kala, a ciki na,
Abinda ya jawo min mutuwan jiki da kasala ke nan a lokaci guda,
Sai nake ga tankar yau ne farkon haduwan mu da Yaya Abubakar,
Shi kadai ke kidan shi da rawan shi har zuwa lokacin da ya gaji don kan shi,
Naji mirginawan shi yana mai maida numfashi a guda guda, daga gefe da yake kwance,
A daidai lokacin da yadan koma normal naji ya damko hannuna ya hada da nashi ya matse guri guda,
He sound in a soft, voice yace, Meena why the you act like this today ?
Is something wrong with you, ?
Runtse ido na nayi guri guda tare da fitar da wani dan siririn hawaye ,
Ban iya yi magana sai dai gyara kwanciyar dana yi a hankali,
Ajiyan zuciya naji yayi daga gefen shi, yana cewa,
You know that i love I don't want to hurt you, ki daina yi min rudeness, please,
Cikin muryq mai kama da ta mai son kuka nace Yaya na fada ma cewa zamu fara teaching practice ne very soon,
Naji ya sauke ajiyan zuciya yana cewa, nafada maki cewa ki bini sannu,
Ya kike son inyi ina a cikin wanan irin tension a lokaci guda abubuwa sun zo min at the same time,
Nima a nawa bangaren yadda naji ya fadi maganar sai tausayin shi ya kamani
A hankali na furta cewa kayi hakkuri yaya dama don kada a wuce ni ga karatuna ne na shiga damuwa,
Dai yana mikewa daga kwancen data ke kobai fada ba nasan cewa wanka zai shiga don baya kwana ba tsarki a jikin shi,
Yace, idon karatu ne insha Allah zaki karas meena kawai ina son inyi styling din gida nane tukun,
Daga haka ya shiga bathroom din don tsarkake jikin shi kamar kullun,,
Sai bayan fitowan shi na shiga ni ma nai wanka nafito, na maida rigan barci nada zani nadake ta faman kamshi,,,

****** ********** ******
Salawatu wace daga dakin ta ke ji tankar tayi ihu don shedan na rudin ta yana anya na mata abubuwa a gamay da mu,,
Waya ta dauka acikin daren nan take fadawa Lubuna cewa gaskiya har yanzu fa bata samu yadda take so a gurin Oga, ba,
Don har yanzu yana rawan kafa ga shegiyar yarinyar nan fitsarara,
Lubuna tace amma ai kin dai ji abinda wanan bokon na masaka yafada muna ko,
Don haka wallahi in har kina son kan ki da lafiya Salawa ki rabu da wanan yarinyar ki sa mata ido,
Tun kafin wani abu mara kyau yazo ya faru da akan son kai irin naki,
Shima wai may nene matsalan ki tunda har kin samu yanzu yana fifita ki fiye da sauran, gaba daya,
Ki fita batun yarinyar mana tunda babu abinda zata diba a gurin ki,
Look Lubuna wallahi ban kaunar in bude idona inga shegiyar yarinyar nan a cikin gidan nan ,
Don idan har tana tare dashi to wallahi ina fada maki bazai ta ba kallon kowace mace ba da daraja,
Idan nai magana sai yace wai banda hakkuri karamar yarinyace shima lalabata yake yi a zauna lafiya,
Shiya sa ranan da tashigo min daki naso in mata dukan tsiya da ko iyayyen ta bazasu sheda ta ba,
Lubuna tai yar dariya tana cewa ita ko tana a tsaye zaki mata irin wanan dukan haka,
Salawatu tace ai ni in fada maki nafi kowa fatin cikin zubewan cikin shegiya,
Da muna zaune muna kallon yar iska yar karama da ita tana haihuwa muna taya ta raino,
Lubuna tace ai gara da kika zubar dashi kowa ma ya huta don abinda zaku gani sai yagi nan,
A to kin mata ance kakan su matsafine shiyasa duk abinda zan masu zai kama su ba,
Mutumin da akace ko ruwa ya duba yace ya zama kifi sai yazama, kifin,
Ke Sallawa banda sheri fa tace wallahi nima malam Abudullahi masinger shi ke bani labarin su,,
Aikin san karbi karbi,baibar ko wa ba, don mutanen yanzu idan kana son sanin abu mikama na kusa da su alheri kasha labari,,
Yanzu ai baki san wani abuba pretending na ke mashi as, pregnant woman,
Ihu Lubuna tasa tace, ke Sallawa kirage sheri wallahi,
Kada yazo ya gane karya ki keyi fa ku hausama dashi,
Ta ce ke don ba ki ga irin yadda da akace yarinyar nan tayi miscarriage yadda ya koma kaman zaiyi hauka,,
Au to ke ki na ganin cewa zai yi wanan rawan kafan akan ki ne Salawa,,,
Sundauki tsawon lokaci suna hira a tsakanin su abinda har yasa Salawa ta dan rage jin zafin da takeyi,

****** ********** ******
Bayan wasu yan awani ina cikin barci naji tankar an tashe ni daga barcin da nake yi,
A hankali na bude idona inda nagane cewa a dakin Yaya Abubakar nake kwance,
Yana daga gefena yana barcin shi acikin kwanciyan hankali,
Wani amai ne ya taso min ya tokare min makoshina inaji tankar zan amaye hanji na,
Cikin sauri na mike zaune don zuwa yin amain, da nake ji yanzu,
Da sauri na isa bathroom din na fara sheka amai, kamar zan dauke, a lokacin,
Da kyat bayan nagama na iya tasowa zuwa cikin daki, don in kwanta,
Yaya Abubakar ne na gani a tsaye hannayen shi harde da juna yana min wani irin kallo acikun mamaki,
Tafiya na keyi kamar zan fadi don irin yadda na kejin jiwa yana dibana,,
Hannun Yaya Abubakar naji ya tallaboni ta bayana yakai ni bakin gado ya aje,
Ya koma bathroom din ya gyara ya fesa abin kamshi,,
Ai bai fito ba daga bayin sai ga ni na shigo da gudu in sheka wani sabon aman,
A take, tausayi ya kama Yaya Abubakar yayi daya sani ya kyale ni kawai,
Acikin wani irin murya mai sanyi yake cewa Meena dama baki da lafiya ne, ?
Aman ne ya kara zo min faaaa da karfi duk na bata mai bathroom din dake a jikin shi,,
Sai faman sannu sannu yake min a cikin nuna damuwan shi, gare ni,
Shida kan shi ya kaini saman gadon shi ya shimfede ni sai karkadawa nake yi,
A take jikina yai min wani irin zafi zazzabi mai karfi ya rufe ni a lokaci guda,
Hankali Yaya Abubakar yai mugun tashi don bai san yadda zaiyi da daren nan ba,
Paracetamol yabani nasha don samun dan sasautawan zafin jikin,
Cikin ikon Allah nasamu dan sauki zuwa tasan ma asuba na samu barci ya kwashe ni,
Daga haka ban farka ba sai kusan takwas na safe ranan ban samu Sallah safe ba, da wuri,
Zaune ya ke a gefe na bayan ya dawo daga massalaci,
Ya kura min ido yana kallon yadda nake maida numfashina a hankali,
Fuska ya ramay sosai na koma wata yar feyau dani kaman na dade a kwance ina ciwo,
A hankali na bude idona don jin nauyin mutum danayi daga cikin barci na a kusa dani,
A hankali na bude idon da sukai min nauyi na furta cikin yanayin ciwo da cewa sannu Yaya,
Na mai da idanuna a hankali na rufe don ci gaba da,barci na,
Sallah ne ya fado min a rai nai zubur na bude idon tare da kokarin mikewa zaune,,
Ina zaki ne kuma ya tambaya cikin yanayin damuwa,
A hankali nace banyi Sallah ba Yaya kuma gashi har gari ya waye sosai,
Yace ki bi a hankali don kin san jikin ki babu karfi sosai, don haka kibi a hankali,
Ina kaiwa zaune na kara jin wani irin luuu kamar dakin yana juya min,
Sai kuma wani irin yunwa da naji ya ziyarci cikina,
Yaya yunwa nake ji sosai wallahi nafadi ina hamma alaman akwai barci a idona,
Ya mike yana cewa kwanta ina zuwa tukun na barin samo maki abinda zaki sha,
Yana fita har kwanta na rufe idon kamar zan koma barci amma sai naji bazan iya ba, don banyi sallah ba,
Don haka namike ahankali na nufi bathroom don in yi alwala wanka nafara na watsa ruwa masu zafi a jiki na,
Hakan ya dan sani jin karfin jikina har na samu nayi sallah ,
Ina zaune a gurin da nai sallah na dan zauna tare da, dan lumshe idona acikin yanayi na mai jin ciwon jiki,
Yaya Abubakar yadauko tea da kwai da ya soya min da hannun shi a kitchen,
Tun yana suyan kwan Salawa ta shigo kitchen ganin shi a tsaye yana hada breakfast da kan shi yasa ta mamaki tana tambayan lafiya yake kitchen da kan shi,
A takaice ya ce Meena bata da lafiya shiyasa nake son in hada mata breakfast,
Gabanta ne yaba da dammm tace cikin karaji may ya samay ta kuma ?
Bai bata amsa ba sai juye kwan acikin plate dayayi tare da kashe gas din da yai amfani dashi,
Ya dauko kwan zuwa gurin da ya hada min tea mai kauri ya nufi hanyar fita,
Salawatu tana tsaya kamar gunki duk imani ya kashe ta kamar ba jiya jiya ta gama bata kudin ta gurin bokan su ba,
A inda nake kwance saman sanyin ties ina jin dadin sanyin kasan,
Kallon mamaki yake min har zuwa lokacin da ya karaso gurina yana cewa, kin samu yin sallah ne ?
Na bude idona a hankali ina cewa eh yaya nayi sallah ,
Idona yana akan cup din dake rike a hannun shi don ji nakeyi tankar in kwace in kafa kai ,
Don irin yuwan da nake ji a lokacin kamar inyi ihu saboda shi,,
Gaf dani ya zauna ya miko min cup din a bakina yana nufin insha daga hannun shi,
Nagane nugin shi don haka banda zabi tun da na kafa kai ban dakata ba har sai da na shanye tea din,
Yaya Abubakar yaji wani irin tausayi na mamakin yadda na shanye cup guda a lokaci guda yace ko akara hado maki ne, ?
Nace a a yaya na gode na koshi sai yace to kici kwan ko kadan ne please ?
Nafara cin kwan a hankali ina taunawa kamar bakina ciwo yake min,,,
Zan kai na hudune naji wani irin tashin zuciya ya ziyarci zuciyana, a lokaci guda idona ya rufe da sauri na ke kokarin mikewa,
Sai kokarin rikeni Yaya keyi ai ko nawanko masa jikin shi duk da amai a lokaci guda ina kokarin mikewa kuma wani aman ya kara zowa,
Hankalin Yaya Abubakar yai mugun tashi a lokacin sai da yaga na dakatar da aman yake ce min sannu ko ?
Da kyat na samu na ke kada kaina ina cewa wayyo Allah na cikina, cikina
Ya Abubakar duk ya rude ya fita hayacin sa yana cewa tashi mu tafi asibiti kn ji
Subbahanallahi wai may ke damun ki ne haka Meenat ?
Kasan naji bazai min ba na mike zuwa saman gadon shi na kwanta na dunkule guri guda kamar jaririya,
A take barci ya daukeni barci mai nauyi yai gaba dani lokaci guda,
Ganin nasamu barci sai zufa na keyi a cikin barcin yasa shi dan sauke ajiyan zuciya,
Nan ya barni a kwance ya fita zuwa, gurin aikin sa amma zuciyar sa tana acikin damuwa,

****** ********** ******
Zaune take a falo tun lokacin da taji fitan maigidan
Idan ba karya zuciyar ta ke mata ba tana iya cewa yau tun safe ban fito daga part din Yaya Abubakar ba,
Hakan ne ya bata daman ya kewa a zuciyan ta cewa ta tashi ta leka dakin Yaya Abubakar tagani,
A kwance ta hangoni nadunkule guri guda ina barci, abina hankali kwance,
Ta dade tana kallon zuciyar ta na kiyas ta mata abubuwa da dama akaina,
Gyara kwanciyar da nayi yasa ta saurin ja da baya da sauri tasake labulen kofan tabar gurin,
Tun kagin ta karasa saukowa daga stairs din ta hango Ramatu tafito daga dakin Anty Sadiya,
Tana saye acikin hijab din ta har kasa tana dauke da flask din ruwan zafi a hannunta,
Ganin ta doshi hanyar kitchen yasa Salawatu wani irin daka mata tsawa,,
Ke dakata lafiya ina zaki shiga wa mutane haka ?
Daga ina kike ne ma wai ?
Ramatu wacce tsawan Salawatu yadan sata yar kaduwa tajuyo tana kare tamata kallo,
Akaron farko da tafara ganin ta ke nan a gidan tun shigowanta jiya,
Cikin dan rusunnawa tace, hajiya ina kwana ?
Ya aiyuka,
Kalafiya ta karba da cewa tare da watsa mata wani irin kallon rainin hankali na ke wacece,
Daga ina kike na haka ? Cikin wani irin kallon tun daga sama har kasan ta,
Ramatu tace daga sashen wacan Hajiya da bata da lafiya nice wace aka kawo don in dinga taimaka mata,
Sai da tai mata wani kallon rainin wayo har zuwa kasa tace,
Uummww kece dai mai kwadai da bata san ciwon kanta ba ko yan uwanta suna gudun ta ke don kwaidai kin zo kin tara ko ?
Murmushi Ramatu tayi tace, ai taimako ne hajiya babu abinda zai faru insha Allah,
Daga haka Salawatu ta,watso mata harara cikin kallon ke kika sani tajuya fuuu ta shige part din ta,
Ramatu tabi ta da kallon mamaki har shigewan ta cikki ta kada kai tana cewa akwai magana ke nan a gidan nan suna da tantiriya, ashe, agidan haka ?

****** ********** ******
Hasken rana ne ya hasko min fuska na daga window dakin ta baya,
Abinda ya sani bude idona kenan nauyi naji jikina yayi sosai ,
Sai daga baya nagane cewa ina dakin Yaya Abubakar ne har wanan lokacin,
A hankali na yunkura na mike zaune nadan dade a zaune bakin gado kafin na yunkura namike tare da tattara duk kayayakina zuwa kasa part dina,
A hankali na tako zuwa kasa inda na hadu da Ramatu ta dauko ruwan zafin da ta dafa ,
Tana ganina ta tsaya tana cewa sannu uwar daki na ashe yau kuma jikin ya tabu ne haka,
Alhaji ne ke fada muna dazun da zai fita yace baki barci da dadi ba daren jiya,
Nadam lumshe ido alamar ciwo nace ai naji sauki sosai, jikin dai ne ba karfi,
Ta dan kauce min kadan duk da ba ko a kusa muke ba amma saboda girmamawa ta dan kauce gefe, guda,
Ina shiga daki na fada saman gadona tare da lumshe idanuwa na
Zuwa can na sauke ajiyan zuciya tare da bude idona,
Sallaman Ramatu naji adakin nawa tana cewz ko akwai abinda zan taimaka maki dashine Hajiya,
Cikin dan lumshe ido nace yuwan nake ji sosai wallahi,
Tace ko may zaki ci yanzu nace ko tea ne ki hada min don Allah,
Fitan ta don zuwa hado min tea din yai daidai da kiran wayan yaya Abubakar,
Nadauka a hankali da cewa Sallamu Alaikum cikin yar siriri yan murya,,
Muryan shi yana cewa Meenat kin tashi yaya jikin naki ne ?
Na lumshe ido na tankar yana kusa dani don jin muryan shi da ya daji kunnuwa na,
Nace eh yaya naji sauki ai,
Kin sauko ne ko kina kwance har yanzu sama, nace ina daki na kwance ne zan sha tea ina jin yunwa ne sosai,
Yace A,a wanan jin yuwa fa Meenat kamar mai Ulcer ?
Murmushi nayi batare da na bashi ansa ba, nace hmmm kawai cikin lumshe ido,
Bayan nasha tea din da Ramatu ta hado min nasha,
Sai wani irin zufa ya fara karyo min duk jikina ta ko ina inajin wani irin zafi,
Don haka na fada bathroom na watsa ruwan don inji dama ajikina,
Bayan fitowan na ne na dan ji karfin jikina ba kamar yadda na tashi ba don haka na dan jawo wani dogon riga jallabiya na saka ajikina.
Cikin daurewa na nufi dakin Anty Sadiya, don in duba lafiyan ta,
Nasamu Ramatu tana hada mata abinci zata ci, da kuma dan gyara mata filo,
Mungaisa da ita ina mai kallon hannuwa ta yau gaskiya babu laifi don hannu ya tsane sosai ba kamar baya ba,
Nace cikin murya ta kasala anty ya jikin ta amsa cikin wani kushe fusaka da cewa,
Da sauki yaya naki jikin dazu yake fadamin cewa wai daren jiya bakuyi barci ba,
Nace cikin murmushin karfin hali


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login