Showing 84001 words to 87000 words out of 388021 words

Chapter 29 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8295

falo,
Bayan shi nabi da kallon mamaki don sai naga kamar a mafarkine muke zancen nan,,
Ban fitoba sai da gyara dakina tas nakara feshe ko ina da kamshin da Anty Amarya ta saya min ,

****** ********** ******
Gidan ta a rufe yake don shiyan ta can yake daban da na mutane,
Yinin yau mutanen gidan sun ga sai sintiri takeyi ta ta fama diban ruwa zuwa cikin sashen ta,
Sai dai babu mai ikon tambayan ta don gudun masifar ta,
Hankalin ta atashe sai masifa takeyi a cin ranta tana cewa malam tsoho aiko zaka san cewa ni Hajja ce,
Karya kake wallahi, sam baza ka bata min shirina ba
Ma zai taba yuyuwa ba ace Abubakar ya kauce muna,
Shekara nawa ina amfana da al,amarin shi da zaka kawo min cikas,
Kugin Dodon ta ne da ke jinya yau yasa tagane cewa ruwa yake bukata,
Roban penti ta dauka zuwa bakin famfo inda take debo ruwan,
Sai da ta cika katon radan roban da yake a ciki da ruwan san,nan ta huta,
Abinda tai tayi ke nan rana saboda ruwa Dodo ke son ya shiga viki yau don yaji sanyi,
Sai zuwa dare ta samu hutu sosai akan wanan bakar wahalan da jikanyar malam tsoho ta jawo mata yau,
Dole ne gobe tunda safe ta tafi gurin boka ta sheda mai, TARKO da malam tsoho take ganin ya haka mata,
Ita a yanzu tafi ganin laifin Mama Ladi da wace ta kasa tsawatawa dan ta,
A gaskiya itama tayi kuskure da har ta yarda ta bada sunan gidan Abubakar da iyalin shi,,,,

****** ********** ******
Malam ya kamata ace mun kira yar baba don muji lafiyan ta aiko?
Loman tuwon da baba ya diba daga cikin kula ya mayar,
Cikin wani irin murya mai razanarwa ya,ce karki fara shi Saratu,
Kada inji cewa kin kira wanan yarinyar a yanzu kubarta har ta kiramu da kanta,
Mama Saratu sai kuma tafara cewa maigidan nata wanda taga ya hasala,
Tace kayi hakkuri malam ban yi tunanen haka zai iya tayar mata da hankali bane,
Tou kin dai ji abinda na fada maki kar wanda ya kirata, muddin ba ita ce ta kira ku ba,
Abincin da bai ciba Mama Saratu ke kallo bata dauki cewa maganan zai iya bata mashi rai haka ba,
Da batai zancen a lokacin da yake kokarin cin abincin shi ba,
Muryan Mama Ladi ce suka jiyo daga cikin gida tana fada da kishiyar ta Mama Sa a
Wai bata sa masu abin miya ba acikin miyan da ta aiko masu dashi,
Mama Sa,a tace yau ba,a sayo abin miya ba sauran wanda ya ragene shekaran jiya na murje muna a ciki,
Sai masifan fada takeyi a cikin daga harshs take sababin,
Baba Buhari ya shigo gida tun daga nesa yake cewa ke arr da halinki ladi,
Yanzun bakiji kunya ba ace harshenki har wajen gida saboda fadan abin miya,
Kunya shin kunya fa kace ?
Don na tambayi hakkina shine kunya malam ?
Eh lalai kuwa Sa,a kin shigo da sa,a tunda har kin iya sa adanne ma wasu hakkin su haka,
Ke dakata mara kunya inji Baba Buhari baki san kuya ba sam a rayuwan ki,
Ace ina da Da kamar Abubakar amma sai naje yawon maula gurin jama,an Annabi,
Wani kallon raini tajefo su dashi tace oho in da ka dogara ke nan dama,
Yana can yana wahala yana turo maka ku na ci da wata mai babban duwawu,
To na hana din baza a ci ba,
To inkin hana kinyiwa kan,ki ai don gaki kina fadan naman miya ko kifi,
Juyawa yayi gurin Mama Sa,a dake tsaye tana kallon ikon Allah yace ke shige ciki kar nakara jin muryan ki kuma,
Shima wucewa yayi ba tare da ya tsaya kara ce mata wani abuba can ?
Mama Ladi a cikin fada take cewa, ni nace kada ya kara taimakawa in dai har ba nawa zaifi yawa ba,
Kuma yana aikowa din ni ce ke karbe naka in kana da karfi ka kwata mana,
Allah ya shirye ki inji Mama Sa,a wace ke daga shiyan ta tana jin muryan Mama ladi ratatatata,,,,,,

****** ********** ******
Zaune nake bayan na idar da sallah ina karatun Alkur,ani maigirma kamar yadda munkayi agida,
Muryan ta kawai naji don ban tsan manin tayi sallama da zata shigo dakin,
Cewa tayi acikin wani irin murya
Ki zo yana neman ki a falo wai,?
Nima dai ban ansa mata ba sai ci gaba na yi da karatuna har nakai aya,
Nashafa tare da mikewa don zuwa katba kiran da ake min,a falon,,
Da sallama a dauke a bakina a lokacin da na karaso gurin da suke zaunen,
Jugun jugun ba mai wa wani magana ita idon ta kuri a tv kamar bakauya,
Shiko sai faman dannan wayar shi yake hankali kwance abin shi,
Gaishe shi da wuni na karayi
Sai a,lokavin yaya Abubakar ya dago idon shi ya dan dube ni
Yace ya kike ?
Na ansa a sanyaye da cewa lafiya lau,
Ki zauna yace min a lokacin da ya mai da fuskan shi ga abin da yakeyi,
Gefe na samu a kasa center carpet na zauna inda yadan dago kai ya kalle ni tare da sauke murmushi mai sauti,
Gyaran muryan da ya yi ne yadawo da hankalin mu gaba daya gare shi,,,
Ya soma da cewa Alhamdullahi na godewa Allah da ya hadani da ku a matsayin abokan zama,
Nakirakune don in sheda makucewa yau Allah ya nufa an kara min girma a ma,aikatar mu,
Cikin murna da jin dadin abinda yace, ya sani dago kai na, na kalle shi cikin farin,
Wani irin sanyi da dadi gami da murna suka ratsa min zuciya na alokaci guda,
Har na kasa boye farin ciki na afili,
Kunshi na da anty amarya tasa akai min da zamuzo wanda har yau ya ke sheki kamar yau akayi shi,
Saboda ya yi baki wulk da dashi ya zauna min akafa gwanin ban sha,awa,
Shi nake kallo cikin mutnan jin dan uwa ya samu karuwa,
Ban san lokacin da nace yaya mutanen gida ko sun sani ?
Sai kuma nai saurin toshe bakina don ban san lokacin da tambayan yazo min ba,
Ga mamaki na sai naga yai saurin girgiza kai alamar bai fada masu ba,
Sharp ya manta da zancen yafadawa iyayyen shi asa mai albarka, ga al,amarin,,,
Wayan shi dake hannun shi ya shiga dadan,nawa don kiran malam tsoho kakan mu
Ji kawai nayi ya na cewa Allah Gafarta malam mun wuni lafiya, ?
Da sauri na dago kaina don fahintar danayi da malam tsoho yake waya a ,lokacin,
Gaisawa su kayi a cikin mutunci, tare da yar taba hiran tambayan lafiyan iyali,
Shiru yadan biyo bayan sai yaya Abubakar ne yace malam dama na bugone in sheda maku cewa yu na samu karin girma a ma,aikatar mu
Masha Allah Masha, Allah,
Allah ya kara dauka ya rufa asiri,
Allah sa wa zuri a albarka,
Wani dadi yaya Abubakar yaji a lokacin don tun yana yaro rabon da suyi irin haka da malam, din,
Malam yaci gaba da cewa,
Sai ka kula da Amana, kwarai da gaske saboda nauyi ya kara hawan kan ka, takwarana,
Wani irin dadi yake ji yana kara,shigan shi sosai don sam shi bai kawo fasan cewa ya fada masu ba tun rana,
Amma ga yarinya karama ta bashi shawara mai amfani,
Niko sam ban kawo komai araina ba danace hakan,
Muna daga zane ni da Anty Sadiya wace tai tankar bata gurin ma lokacin don tabi lafiyan cushion tana kallon seasons film ,
Lokacin da na ga yagama wayan nace Allah ya sanya alheri acikin al,amarin tare da mikewa don barin gurin,
Da katar dani yaya Abubakar ya yi da cewa , ji nan,
Abinda yasani dawowa na zauna ke nan cikin natsuwa,
Daga yau duk dare karfe takwas kowace daga cikin ku ta tabbatar da cewa tana falon nan har zuwa tara da rabi,
Wanan doka ne da umurni na bayar bawai, fade ba,
A tare za mu dinga cin abinci gaba dayan mu a nan dining,
Saboda haka daga yanzu sai ku tashi mu je aci abinci,
A nutse na dago kai ina kallon shi don dai ni a koshe nake,,
Nasan yaya ya fahince ni, amna ba fuskan da zan yi comment,
Dole na mike nabi bayan su inda ya umurce ni da in fara zuba masu tunda nice na girka,
Kamshi ne kawai ke tashi gurin don kulolin da na bude,na girkin dare,
Kafin na zuba wa yayan mu Anty Sadiya tace in miko mata plate ta zubawa kan ta,
Saida ta shake plate bam da tuwon farin shinkafa miyan shuwaka,

Kafin mubar gurin cin abinci, wayan mutanen gidane yafara zariya a wayan yaya,
Babana shine mutum na uku daya fara kiran yaya Abubakar don yai mashi murna,
Jin ya ambaci sunan mahaifina ya sani alokacin ina kokatin kwashe kuloli da plate din abincin,
Da sauri na dan dago kai cikkin dan sauraren su ina jin dadin gani irin yadda yaya ke, magana tankar mahaifinn nawa yana a gaban shi ne,
Lokacin da naga yaya ya dago ya dubi gurin da nake nai sauri na sadda kai na kasa,
Saboda naji kunyan irin yadda nayi mashi a lokacin don na kasa boye murnan jin hiran su da mahaifina,
A sanyaye nai saurin kwashe kayan don barin gurin don kar yai min magana,
Sosai yaya Abubakar ke tajin dadin yau yan uwa sun nuna mashi kauna sosai,
Fuskan shi dauke da yalwataccen fara,a yake kallon gurin da muke zaune,
Ni dai tankar a takure nake gurin don duk ban iya sakewa a cikin su,
Dan juyowa yayi inda nake zaune, tare da dan kura min ido,
Kaina na kara dukarwa kasa ina wasa da yan yatsuna
Muryan yaya Abubakar ne yana cewa hado min ruwa,insha, pls
A cikin natsuwa namike zuwa kitchen sai yunane nakeyi,
Ina shiga Kitchen na rasa may zan yi can nace to bari dai na dan hado mashi, simply drink,,
Zobo drinks dana hada da rana shina juyo a jug na dora masu cups a saman tire, din
A gaban su tsakiya nadire tire din ina mai cewa gashi yaya,
Anty Sadiya wace tun zaman mu take wani basarwa,
Anty ga drinks din nan,
Kan ta, takawar gefe cike da jin haushi na ita a ganin ta muna hanata kallon ta alokacin

****** ********** ******
Malam tsoho wanda ke zaune yana dan murmusawa
Saboda ganin cewa TARKO shi ya fara kama kurciya,
Meenatu zaki iya, zaki iya na sani da zuciya guda zaki taimaka muna,
Lalai idan ba ita yasa ba a halin yanzu babu wanda zai mashi yadda yake so,
Wanan aikin sai mai hakkuri da juriya da kuma sanin ya kamata,
Bawai sauran yaran ba su iyawa bane zasu iya amma da wata manufa,
Bada irin manufar shi tayadda yake bukatan yayi kamu a,cikin ruwan sanyi, sosai,,
Godiya yakara yiwa Allah Ubangiji Subbahanahu Wata,allah da tun ba akai ko ina ba har yafara samun yadda yakeso,
Yasan cewa a sannu komai zai zo daidai insaha Allahu,

Matsala guda shine irin yadda yasan cewa jikokin nashi na cikkin wani TARKO mai wuyan wallawala,
Yasan cewa zasu yi daga sosai da Hajja a gurare da dama don ta dade tana mai barna acikkin zuri,an shi,
Duk da yasan cewa bazata iya yin komai ba shine ma dalilin da ya bullo mata ta inda bata zata ba,,
Ita azaton ta bai fahinci abinda take aiwatarwa ba kamar yadda take ganin duk gari kamar ba,a fahinci halin da take ciki ba,
Da sannu zai nuna mata cewa wutsiyan rakumi yafi gaban yaro,
Don shi malam tun farkon ganin ta yagane cewa muguwa ce,
Abuguda saboda sun fito yanki guda da sarrakuwar shi kuma suna zumunci,,
Hakan,ne yasa ya kyale ta yasa mata idon sai gashi har sunkai ga hada zuria dashi ,
Tunfarko ko haihuwa akayi agidan shi sai yasan abinda yayi agidan do shi mugu baya shiga gidan shi sam,
Wanan dalilin ne yasa hajja bata zuwa gidan malam tsoho sam,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/26, 9:27 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 5?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AR- RAAFI,,,,

JIN,JINA GARE KI UWAR MARAYU DA TAL,LAKAWAN KEBBI HJY DR ZAINAB UMAR SHIMKAFI ATIKU ABUBAKAR, MATAR GWAUNAN KEBBI STATE,,, KINYI MUN GANI WALLAHI AIKIN,KI NA KYAUGA MATA ALLAH YAJA ZAMANI
KIN SA MATA ACIKIN HANYOYI RAYUWAN NA ALHERI,,
MUNGODE KWARAI DA GASKE,,,,,


Gidan yayi tsit baka jin komai sai karan na,urori dake cikin gidana kunne, sai kuma tsuntsayen dare da ke kuka jefi jefi,
A zaune nake, saboda a kida tace hakan yar tocilar wayana ne nake hassakawa,
Karatun na keyi a cikin littafi mai tsarki don tsoron da nake yawan ji a lokacin,
Muryw kasa, kasa, acikin sautin karatuna da ba yabo ba don dadin sauraro,
Ww Har ya turo kofan dakin ya shigo,kaina yana aduke,
Daga kofa ya tsaya ya tsura min ido yana dubana da sauraro,
Natsuwata da kwarewa na ga,karatu ya dauki hankalin shi ga saurarona,
Bai katse ni ba sai da yaji nakai karshen sura dai dai lokacin da zan shafa ne mu kayi ar,raba da yayana a tsaye akofan dakin, a lokacin shi ma zai shafa,,,,
Da sauri na dukar da kaina sai da kuma acikin zuciya na ina tuna nen may ya kawo shi dakina,
Don a gidan mu da gidan Uncle da na zauna ai naga miji ba ya shiga dakin wace ya kwana again ,,,,
Tafiyan shi naji ya na takowa zuwa gare ni kaina aduke ina kokarin aje littafina, inda yake,
Cikin yar siriri yan murya nake mashi ina wuni,
Zaman shi da ansawan shi sunyi daidai da daga kaina acikin mamaki,
Wani irin kallo a cikin shu,umin murmushi yake sake min
Ke nan ana nufin kin yi har da tulawa, a gurin malam
Sai a lokcin na dan sake fusakana kadan nace ai dole, ne in dai agidan malam ne,
Ya ai Babana yace min kai babban malami ne agidan mu don haka naji yana wa yaya Ibrahim fada
Sai naji ya saki yar dariya yace to ai, Baba samaila Baba na ne ba naki ba ke kadai,
Murmushi na danyi tare da gyada kai na ce shima Baban haka naji yana cewa, wai kai dan shine da yake ji da kai aduk gidan mu,
Da alaman zance yai wa yaya Abubakar dadi a irin yadda naga ya lumshe idon shi,
Can kuma ya bude idon shi a hankali ya kalli gurin da nake tsugune a takure,
Da hannun shi yai amfani gurin buga gefen katifan da yake zaune,
Ya mai kallo na kai tsaye yace zo nan ki zauna,
Idon shi ya na kokarin mu hada ido cikin ido dashi,
Daidai Gurin da ya dan buga da nufin wai in zo inzauna nake kallo a cikin mamaki,
Dago kai nayi don in kalle shi amma sai ya daga min gira alamar eh,da dan rausaya kan shi,
Yace ina malam yace ne kizo ki kula da yayan naki ne wai ?
Wani iri naji a take hankali na ya tashi, abinda ya faru jiya ya fado min a rai, irin yadda yayan namu ya jagwalgwalani a daren jiyan,
Kasa nayi da kaina yayin da wasu zafafun, hawaye suka ziyarci ido na,
Saboda tuno min da abinda ya faru a tsakanin mu a daren jiya,
No, No, bana son ganin wanan hawayen daga yau muddin kina gidan nan,
Ban aune ba sai ji nayi hannun shi a jikin nawa ya,namai jawo ni izuwa gare shi,
Saman ciyan shi, ya zaunar da ni, ya yin da ya ke kokarin daga fuskana,
Subbahanallah, Meenat kukan may kuma a haka zaki kuladain din kina wanan hawaye haka, ?
A hankali yasa hannayen shi yana share min hawayen,
Yana mai kallon fuskana, ya ce, kin ga dakata muyi magana, da ke,
Naga hankalin ki a tashe ya ke da ni Meena har yanzu,
Ko dai, ba kya son zama da mune wai ?
Idan har bakya son yanzu fada min in kira malam da su baba in fada masu sai su san yadda zasu yi da mu,,,
Da sauri na shiga goge hawayen fuskana ina cewa cikin murya mai kama da rada, dan Allah yaya kayi hakkuri kada ka fada masu,
Dariya na ba shi amma sai ya daure yana cewa cikin murmushi,
No ai kawai ki bari na fada ma malam tsoho din kawai don ya aiko a dauke ki,
Da Allah yaya kayi hakuri kada ka fada masu don naiwa Babana alkawari bazan kunya ta su ba, insha Allah,
Tausayi na ne ya kamashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login