Showing 3001 words to 6000 words out of 388021 words

Chapter 2 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8182

Shiru malam yayi yana nazarin wani abu a cikin zuciyar shi,
Gyaran murya malam yayi da farko tare da gyara zaman shi kadan,
Mai suna inji malam Abubakar din yadan dago da kan shi kadan yana mai kallon malam,
Wanan kudin ka kasa shi kashi hudu,
Kashi biyu ka kwasa nakane,da sauri ya dago kai ya kalli malam don shi a ganin shi ai kudin sun mai yawa duka don ba wani abu yake saye ba ai,
Malam ya gyada kai yace kwarai kashi biyu kai zaka a je a gurin ka,
Kashi guda kabawa mahaifinka da mahaifiyar ka,
Sauran kashi daya sai a rabawa sauran iyayyenka maza da mata,
Cikin sauri Abubakar yace amma malam sai naga kamar ace na baba Samaila zai fi yawa, don bazan manta da irin halarcin da yai min ba gurin ganin ci gaban karatuna,
Kwarai malam yaji dadin wanan zancen don da alama jikan nashi zai yi jin kai ga yan uwa, da sauran al,umma,
Abubakar bai tashi gurin malam ba har sai da suka cirewa kowa abinda ya dace tundaga ubannen shi har zuwa matan gidan,,,

Zaune take wanan karon a gaban malamin ta tana fada mai irin yadda take son sanar ta ya bunkasa a cikin lokaci guda,
Malamin yai yar murmushi yace ai wanan ba komai bane zan maki kokari inga cewa, duk wanan nahiyar ansan da ke,
Hajja ta gyara zama cikin jin dadin zancen malamin nata,
Sun dauki lokaci malam yana mata bayani tace duk taji zata iya abinda yace, mata,
Ta dawo gidan ta da farin ciki, da jin dadi don tana ganin kamar har komai ya kammala ma ko
Yar ta Sadiya ce a zaune tsakar gida tana karatun novel,
Tai mata,sannu da zuwa tare da kawo wa mahaifiyar ta ruwan sha wanda aka surka da kunu, koko,
Tunda hajja ta kafa kai ga kwanon ruwan bata sauke ba har sai da ta shanye ruwan kwanon dukka,
Hakan yasa yar nata tagane cewa ba karamin kishin ruwa mahaifiyar ta ta kwaso ba,
Don haka abinci ta kara gabatar mata,
Hajja na zaune tana cin abincine Sadiya ta kawo wa hajja wani leda baki da ke dauke da sabulan wanka dana wanki,
Tace wai inji mama Ladi tace akawo maki a fada maki cewa danta Abubakar ne yazo jiya da dare daga inda ya samu aiki,
Cak hajja taja ta tsaya don jin sakon da yar ta ke fada mata,
Cikin sauri tace Abubakar din yazo gidan nan ne ,kai sadiya ta gyada mata alamar a,a baizo ba,
May Ladi take nufi da rashin zuwan dan nata gurinki bayn mun riga da munyi magana akan hakan,,,,,

Wanan zuwan mahaifiyar Abubakar bata bata bari ya koma ba,sai da ta gabatar mai da zancen auren da take son hada shi da yar kawar ta aminiyar ta,
Abubakar baida zabi a rayuwar shi don shi ba mutum bane mai,rigima,
Hakan yasa uwar ta samu sa,an shi saboda ita Sadiya irin matan nan ne da basu da fasali,
Doguwa ce baka mai dan kiba hancinta a baje saman fuska, kanta baida gashi mai yawa aciki,
Itama Sadiya mace irin masu mugun hali wa yan da sam basu kaunar na kusa da su ya rabe su,
Ba wai don wani abuba, a,a halin natane kawai a hakan,
Zaku iya kwana guri guda da ita amma ba za zatai ma mutum magana ba, sai in ta kama dole,
Sai dai dama ita tana mutuwan son Abubakar a rayuwar ta, tun farko,

Sam malam Manya bai so wanan hadin ba amma sanin da yayi cewa yanzu mutum bai zagewa sarakan zamani yasa shi jan bakin shi yai shiru,
So sai ake shirin buki daga bangaren amarya da na ango,
Sai dai rashin samun wadattacen lokaci da ango bai yi ba yasa bukin ya dan rage armashi,
Amma duk da hakan ba laifi, don, yan uwa da abokan arziki sun nuna farin cikkin su da wanan bukin gida ya cika sosai a ranan,
Bayan buki da kwana biyu ango da amarya suka kama hanyar Lagos can inda Abubakar yake, aikin sa yake kuma zaune,,
Sai dai da amarya zata bar gidan ma haifiyan ta uwar nata taba wani ruwa tare da yin hayaki, a cewar ta na neman tsari ne, da samun sa,an daki,
Gidane ma daidaici suke a ciki, acikin rufin asiri da wadata,
Zama sukeyi na,rufawa juna, asiri da mutun tawa a tsakanin su,
Sai dai matsala daya shine Sadiya bata da kuzarin aiki, sam, don haka bata damu da wai dafa abinci ba,,
Zata iya kai wani lokaci tana barcin abinta ba tare da ta dafa ko mai taci ba,,
Gyaran gida kusan weekend take yin shi don ita sam kazanta bai damay taba,
Don a gida neman kudi ne kawai a gaban su shine tun safe za,ai tayi batare da an yi wani girki ko gyaran gida ba ,
Saukin al,amarin babu yan uwan Abubakar da suke ziyaran su a lokacin,
Wanan shine, shimfidar labari da zan bayar,,,,


Mama ladi, ce zaune a tare da aminiyar ta, suna dan tataunawa,
Mama, Ladi ta marairai ce kai tana fadawa aminiyar ta, da muwar ta,
Sai da Hajja ta gama sauraron maganar da Aminiyar ta tazo mata da shi,,,
Hajja ta ce tau,Ladi yanzu yarda da mutum abin tsoro ne,
Da sauri Hajja ta dago kai cikin nuna mamakin da jin abinda Hajja tace,
Cikin mamaki tace Hajja ashe yanzu har akwai wani abinda zaki ji shakkun gaya min a tsakanin mu,
Ba hakana ba,ne Ladi abin ne bai son yawan surutu kuma,siri ne mai girma a tsakani,
Kinga ke nan ba zanso har wani yaji wanan zancen ba gaskiya,
Kara matsowa Ladi tayi kusa da Hajja don ganewan da tayi cewa, maganan da zasu yi, mai, muhin mancine sosai
Hajja tace wa Ladi, ki bari zuwa jibi in,Allah ya kai mu akwai inda zan kai ki,
Da murna ladi tabar gidan don farin cikin ta kusa samun mafita,
Buhari yana a majalissan malam mahaifin shi ya hango, dawowan maidakin nashi acikin zafin rana,
Cikin rayuwan shi yake masifa da ita yana fadan rashin zaman gida irin na Ladi,
Amma tana iso gurin da suke sai cewa tayi a gaishe ku,
Yan kadan ne suka karba mata, da ingwaiyya Ladi ke dawo,?
Ta ansa da fadar Awo, Allah ya maisan da ni lafiya,
Daga haka ta,shigewan ta ciki, inda malam da dan shi buhari, takaicin ya hana,su cewa kala,

Acikin gida ma, haka mata suka dinga gaida Ladi da dawo,
Idan sunce mata Aho, yaya,
Ita ko sai cewa takeyi ingwaiyya, agaishe ku, dai,,,
Tas, ta samu shiyan ta don Meena ta gyara mata shi tas,,
Amma halin kiyayya irin na Ladi sai cewa tayi wai Meenat, bata zuba mata ruwa a randar kasar ta ba,
Tun daga inda take take, kwadawa yarinyar kira,
A gigice Meenat tafito tana kokarin daura dan kwalin atamfar dake kan ta,
Cikin masifa take cewa wa kike son ya cika radan ruwan da naga baki debo ruwa ke, zuba min ba?
Meenat ta bude baki da niyar tayi magana amma kuma sai kawai ta kasa saboda idon ta da ya kawo ruwa,
Salati Ladi tasa a lokaci guda tana tafa hannayen ta, cikin mamaki,
Meena ko uwar ki ta hana ki min dan aikin da kike tayani ne kuma,
Cikin mamaki Meenat tadaga kai ta dan kali Ladi don jin cewan da tayi wai aikin da tasha dan ka dan ne,,,
Hakan ya ne yasa Meenat jin wani irin gululu a zuciyan,
Ita dai gaskiya ta gaji da wanan kawaicin da ina ke sa tanayi wa mama Ladi
Wace kuma duk cin mutum cin ta a kan sune yake karewa ko yau she,
Saboda mugun tsanar da mama,Ladi takewa mahaifiyar abin har ya shafi diyan ta,
Wanda hakan ba karamin batawa Meenat rayuwa yakeyi ba,
Don haka azuciyar ta sha alwashin cewa daga yau zata san abin yi
akan mama, Ladi,,,,,,,,
Wacce duk wanan aikin da ta sha tun safe bata gani ba, sai ko karin cima uwar ta fuska takeyi,,,,,,


ZEE MAKAWA YELWA=?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
,=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


Bayan yan bayanin da malamin su yai masu amma ita mama Ladi, ba wai ta fahinci abinda yake nufi bane,
Wani kwalla mai marfi wanda ita mama Ladi din take gani a cikin jeran dakin Hajja tasan shi,
Shine malamin ya rufe da wani bakin kyalle yace su dauka zuwa gida ,
Amma kada su bude sai bayan kwana arba,in cif sanan ta bude,
Daga wananranan da zata bude kwallan duk kukan abinda taji aciki shine zata dinga yankawa,
Dajin an ambaci yanka gaban mama Ladi ya yanke ya fadi ras,
Saboda jin an abaci yanka acikin al,amarin, don dai ita dai a iya sanin ta yanka wani abune na mushirikanci,,,
Tana son tambaya amma Hajja ta tattare da godiya gurin malamin,
Haka suka biyo hanya hajja nata koda malam da aikin shi
Tana kuma yiwa mama Ladi barka da samun wanan abin acikin sauki,

Da yake dare ne mama Ladi bata samu wani matsala ba gurin shiga da kwallan gida,
Can ta samu karkashin gadon ta tatura shi ta boye batare da ta bude ba kamar yadda malam ya umurce ta dayi,
Sai dai tun ranan tasa yarq suka debo mata duwatsu, ta boye.
A kullun tana kidayawa guda guda tana jefawa don gudun mantuwa,,
Sai dai duk abinda take yi sam mama Ladi bata yarda tayi nisa da dakin ta ,
Don gudun kada kaddara ya kai wani gurin kwallah ya bude ya bata mata tsari,,
Wanan kafa kafan da takeyi yasa mutanen gidan gane cewa mama ladi tana acikkin wani yanayi a yan kwanakin nan,

Rana akeyi yau kamar kullun don yanayin garin ke nan da yawan zafin rana,
Daga makarantar boko suke tafe kowacen su sauri takeyi tasamu ta isa gida,
Makarantar jeka,ka dawo ta yan mata dake Badariya suke zuwa watau Salamatu Husaini,
Dake cikin tsohon makarantar Abdullahi Fodio,
Isar su gida acikin gajiya yasa,su kowace ta nufi sashen su,
Meenat na isa, ta samu ta cire takalmin sadal din dake a kafan ta tun a waje ta fara cire hijab din ta,
Saboda bata,son shiga dakin su da kayan makaranta ajikin ta,
Acewan ta, rigar yakan yi warin jemage ne dake makarantan su,
Daga ita sai unders din ta tashige daki inda ta dauro zani zuwa wurin wanka,,
Wani yaro ne cikin masu daukan karatu, yake ce mata wai mama Ladi tana kiran ta,
Kamar bata ji shi ba har zata wuce yaron dan aiken mama ladin,
Saboda wani irin mugun haushi da taji a cikin ranta mutum yadawo ko sallah bai yi ba za,a fara sashi aiki, ke nan,
Muryan mahaifiyarta ce taji tana cewa cikin irin sanyin maganar ta,
Dake fa ake magana yar mama, kin yi kamar bakiji shi ba,
Baki gaba Meenat tace, mama kofa sallah banyi banci abinci ba,
Kai mahaifiyar ta takada kawai don takaici, bazaki je kiji ko may take kiranki akai ba,
Muryan Baba Samaila ne sukaji, a bayan su yana cewa ,
Yanzu fa naga shigowar su daga makaranta bata ko ci abinci baza ki ce yarinya ta je don dole,
Ko ta tafi can wani abinci Ladi zata bata, halan, ?
A,a malam wai gani nayi dama kada yaya tace kuma ba,a tura ta ba,
Anki tura din ,
Ba tana da yara a dakin taba wai taje ma na duk abinda Amina kayi mata tasu suyi mata,
Walle na gaji da,wagga irin bakar dabi,a
Yaro ya dawo ma baida hutu shin,?
Duk yadda akayi haka dan aiken mama Ladi ya zayyana mata zancen,
Inda ba bata lokaci ta nufi sashin na Baba samaila,
Agaida may "ya shin,
Ni ta,zaka gwada ma haihuwa shin?
Au ashe ke haihu Ladi an?
Banga alama ba tunda banga kina gwada masu rashin mutunci kaman wadda kika wa sauran diyan mutane ba,?
O Lailai Samaila yanzu akan "ya ka ta fari ka,kak fada shi, ?
Tai ka jika ta kasha tunda kumya bai i,shi ijjiyanka ba,
Banduk jikata amma yanzu kam da dawon ta da makaranta ko abinci da sallah ba ta yi ba
Kika zuwa kice wai atai zuwa yi maki aikin wahala,
Mamaki sosai ya kama mama Ladi ganin cewa yau wai itace ke magana ana mayar mata da ansa,
Don ita a tunanen ta,duk ta shanye mutanen gidan gabadayan su,
Shiyasa take taka kowa yadda taso,
Abinda bata sani ba shine duk gidan kawici ake mata akan mijin ta baba Buhari,
Dattijon kirki mai mutunci da zumunci da sanin ya kamata,
"Dan kowa agidan tankar nashi yake dauka bai banbanta tsakani sam,,
Wanan dalili ya sa dadewa baba samaila yake wa mama Ladi halar ci akan "yar shi Amina wace mutanen gidan dana shiya suke cewa Meenat,,,,
Juyawa mama Ladi tayi da suraitai abakin ta, zuwa sashen su,
Yar da suka dawo tare da su Meenat daga makaranta,
Tana zaune saman kofar dakin su tana juya shinkafa da miyan manja da nama,
Gefe guda cup ne wanda ta debo, fura mai sanyi aciki ga goran dake dauke da ruwan sanyi,
Tambayar mama takeyi akan yaya akayi don jira takeyi mama ta taso Meena a gaba tazo ta ci mata mutunci,
Ke rufen min baki kin ke ji ya,
Gani da tayi cewa rayuwar mahaifiyar ta ya baci sosai yasa ta ja bakin ta tai shiru,,
Sai dai tanayi tana dan daga kai tana duban hanya shigowa ko zata ga Meenata shigo, sashen nasu,

Daga inda malam yake zaune yaga fitowan Meenat, da wuri zuwa cikin daukan karatu,
Malam yai mamaki kwarai don ganin cewa yau jikan nashi ta fito daukan karatu dawuri ba tare da ta makara ba,
Duk da suna da manyan dakuma wa yanda suka dan dara,su amma hakan bai hana wanan yariyar cinma manyasu ba , ga karatu,
Hakan ke kara,sa kakan nasu najin ta ajikin shi sosai,
Gashi kuma bawai wani dadi mahaifanta ke ji acikin gidan ba,
Hakan ko ya samu asaline na rashin dan uwan haihuwa da shi baba samailan baida acikin gidan,
Gwago hafsi ce kuma tayi aure ita a garin Kalgo bako a cikin gari ba sai in ta shigo gari,,
Baba samaila ba karamin jurumi bane don har aikin soja yatafi, amma bai wani dadeba ya bari saboda mahaifin shi da bayason wanan aikin,
Yanzu mota ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login