Showing 207001 words to 210000 words out of 388021 words

Chapter 70 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8256

dinga yi a hankali don Allah,
Har zan shiga bayi sai na dakata najuyo da sauri ina kallon ta a cikin mamaki,
Nace Ramatun ban fahinci ki ba nacewa bani kadai bace da kikace,
Tai murmushi tace hmm uwar dakina aiko makaho ya lalaba yagan ki haka ya san akwai tsiron Allah a tare dake,
Ga shi ko ina naki ya nuna hakan a fili, jikin nawa da tace ya nuna nakai wa kallo ko ina ni banga wani canji da ta tace yayi ba sam,
Sai na kallo ta nai murmushi na shige bayi kawai batare da nai magana ba,
Awala nakeyi amma ina ta tunanen zancen Ramatu har nafito na tada sallah,
Ramatu bata dakin a lokacin da na idar ina zaune ina jan casbi ta shigo dakin dauke da cup din ruwan zafi tana cewa naga ruwan shayi kawai kike so shine na hado maki ,
Kamar tasan yuwa nake ji ban bata lokaci ba na karba nai bissimillah na dan fara kurbawa ahankali,
Nakai rabin cup din sai na dakata na dubi Ramatu nace Ramatu bakinki don Allah don kin san yadda gidan nan yake hakan yasa ko maigidan ban fada mai ba sai in har abin ya tabbata,
Tana kads kai tana cewa wanan gaskiyane uwar dakina,
Hakika kinyi gaskiya wallahi sosai da wanan dabara taki don rashin imani zai iya sa akawo hari ko kuma mugun baki ya har kai ga yaro tun yana cikki,
Nace ashe kin gane tace niko na gane tunda ni, na san abinda baki sani ba,
Naci gaba da kurban ruwan Lipton dina ina tajin dadin shan sa,
Ramatu ta tashi tana gyara gado da yan goge gogen abubuwa,
Ina gamawa na mike don zuwa duba Anty Sadiya,
Baki yana mai fadar addu,oin tsarin da na sani nasa kai na fita,
A tsakiyan falo mu kayi kicibis da Salawatu wace ta ramay tayi baki,
Tana gani na naga tayi wani irin shock kamar ta juya sai kuma ta dan tsaya taci gaba da tafiyan ta,
Murmushi nayi tare da ce sannu da zuwa,
Kamar bazata amsa ba sai kuma naji tace, Ya gida ?
Na amsa da fadar Alhamdullahi, kawai na wuce abina,
Da sallama na shiga dakin ta tana tsaye tana kokarin gyara zani gadon ta,
Sai na ce mata ina wuni anty ta ansa min a dasashe kamar bata son ansawan nace ya karfin jikin tace taji sauki, taci gaba da abinda takeyi,
Sai a lokacin na fahinci cewa fushi fa anty sadiya ke yi dani,
Ina tafe ina tunanen ko may ye dalili sai na tuna zancen Ramatu ko ?
To ai don zance Ramatu ce Ramatu dai tun farko gurina aka kawo ta ba ta dalilin ta nasan ta ba,
So don na rike ta yanzu ba wani abin jin haushi bane inda ba da wani magana a kasa bane,

****** ********** ******
Yana zaune office sai tunanen yadda suka kwashe da Mama yau yake yi,
Don yasan sherin Salawatu ne ba kowa yakai sukan gurin mama ba sai ita,
Zai ko yi maganin ta don ba zai lamunci mace ta hada shi da mahaifiyan shi ba ko yan uwan shi,
To wai ma har may nakewa Meenatu da Salawatu ke ganin wai nafi kulata,
Ita Salawatu da ba kwana biyu cif batai request din abu a wurin shi ba,
Kuma ko ya bata babu godiya, sai dai takarba ma tana korafin bazasu ishe ta ba,
Amma daga Meenatu har sadiya babu wace ke rokan sa kudi indai bashi ya dauka ya bata ba,
Asalima ita Sadiya ko dinki bata iya tiwa kanta sai dai idan shi ya dinko mata, su,,
Kuma bata sawa don zata iya wuni saye da rigar barci a jikin ta har wani daren,
Shi dai yasan abu guda shine ita Meenatu zancen ta duk bai wuce na yan gidan su ba,
Zance mutanen gida kuma ai nashine shima don shi take gyarawa hanya,
To wanan ne so din da ake nufin yafi gwada mata ko ko may,
Yasan cewa Salawatu koda baya tare da Meenatu bazata bar Sadiya ta wala ba agidan don ya riga da ya karanci halayen ta ko,
Ita arayuwan ta kanta kawai ta sani kuma inhar son samu ne ta maida shi shanun tatsa,
Sallaman malam Abdullahi ne ya katse mashi tunanen da yakeyi yake sheda mai ga hajiya Jummai Dubai nan ta zo,
Ya ce ace ta shivo tashigo tana cewa gaskiya kanina naga ka ramay fa ko dai sarakan nawa suna maka rowane,
Yaya yai murmushi kasancewar matar suna dan shiri dashi sosai don itace mai kawo masu kaya suna saye a ma,aikatar su,
Itama ba wai irin shashashun matan nan bane tana da kamun kai sosai,
Shiyasa yadan sake jiki da ita har yake fada mata cewa yana da bukatan ta hada mai kayan irin na lefe,,
Take tambayan ko aure zai yi yake ce mata, a ina da mata wace na aura ban mata laife ba sai yake bata dan labarin auren mu,
Matar tace gaskiya ya kamata ya hada min tunda ita Salawatu ta karbi kudin tane maimakon lefe,
Yau ma da tazo abinda wanda yasaba hutda da mutane kallo guda taiwa Yaya Abubakar tagane yanayin sa na damuwa,
Yaya yai murmushi yace Hajiya ai basu bari azauna lafiya,
Tai dariyan manya tace, ai dama mai mata sai ya kai ga wanan stage din,
Ya ce hajiya yau wanan fitina gobe wacen ciwon ni wallahi abin har ya fara kwance min lissafi na,
Sun dan dauki lokaci da ita tana bashi shawaran akan halin kowan mu ,
Sanna ta gabatar mai da kayan da ta sayo mai tare fada mai kudaden su,
Sosai Yaya Abubakar yaji dadin shawaran Hajiya Jumai Dubai,
Sunyi sallama inda yasa malam Abdullahi da malam mudi su kwashe kayan zuwa motar shi
Yaya Abubakar ya dawo gida da akwatina lates model,
Har guda shidda da kit din su Allah ya taimaka har su Baba Hamza da Baba Wadda suka shigo dasu dakina kamar yadda mai gidan ya umurce su da yi,
Salawatu ko Anty Sadiya babu kowan su a waje basu masan anyi ba, Anty Sadiya babu kowan su a waje basu masan anyi ba,
Tun daga waje kafin ya shigo gidan ya gane cewa Salawatu tana a cikin gidan shi,
Yaja ya dan tsaya da mamaki karfin hali irin na Salawatu din,
A take zuciyar shi ta fara buguwa atake ya karanto adduan neman
tsari daga Allah,
Ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? karaso cikin gidan a hankali bai ga kowa a waje ba don haka ya nufi dakin Meenatu don yaga lafiyan jikin na ta,
Tun da kofa yake jin murnan mu ni da Ramatu wace ke cewa kodai Alhaji yasan da zancen ne yayo wanan kayan haka
Ya bude labulen dakin ya gan mu mun a zaune akwatunan suna daga gefe aje, inda aka jera su,
Sannu da zuwa mukayi mashi ya ansa adan gajiye yace yawwa,
Ramatu ta mike don ta fita daga dakin amma sai Yaya ya dakatar da ita, da hannu yana cewa,
No zauna abinki ba tsayawa zanyi ba ai zan fita ne yanzu,,
Nadago kai na dube shi ido cikin ido nace Yaya wanan kayan fa haka ?
Yaya Abubakar yadan dubecni shi ma sai kuma ya dubi kayan yace lefen ki ke nan ya iso yau,
Wani irin duban mamaki nai mai na bude baki kamar zanyi magana sai kuma na kasa yi,
Na noke kaina acikin filon dake a kusa dani saboda kunya,
Yace sai a kira Anty Amarya a sanar mata yau ba bashin yar ta akai na da akai min tuni ko ?
Wani irin kunyan ne ya kara kamani ban san sanda na ce Yaya duk wanan kayan masu yawa haka,
Yai murmushi tare da dan lumshe idon shi yana cewa ai,kin fi haka agurina Meenat,
Ya juya ya bar dakin cikin nuna jin dadin yadda na karbi kayan acikkn farin ciki da murna ga godiya danayi ba,adadi,
Ya na fitowa daga part dina a daidai tsakiyan falo su kayi kicibis da Salawatu ta dauko flask din ruwan zafin shan tea din yaya Abubakar zuwa kitchen,
Wani kallo ne ya watsa mata yai saurin kauda kan shi gefe guda, tankar bai ganta ba,
Kamar yadda mu kayi da ita hakan ne sai duk ta daburce don ganin irin kallon da yai mata,
Dakin Anty Sadiya ya shige abin shi batare da ya karba ma ta gaisuwan ta ba,
Yadan jima adakin gutin Sadiya yafito ya shige dakin shi don ya dan rage kayan jikin shi,
Ya fara balle maballin rigar shi ke nan Salawatu ta shigo dakin,
Ta bayan shi ta karaso tana kokarin taya shi balle aninin rigar, ta shi,
Cikin wani murya yace mata stop it please, kada ki fara ki taba min jiki,
Waya baki izinin dawowa gidan nan da kika dawo yau din,
Kallon shi take ti a cikin mamaki sai taga ya kara mata wani irin kwarjini a fuskan ta,
Kuka ta sake a lokaci guda tana cewa, don Allah dai Oga kayi. hakkuri,
Bazan iya kara jure rashin kaba atare dani don haka kayi hakkuri ka yafe min bazan sake tayar ma da hankali a gida ba,
Kallon ta yaya yayi ido da ido yace Salawa ban san may yasa kike son kawo min matsala da fitina ba a rayuwan gida,
Tun sati hudu da kika tafi gidana ya koma min normal babu wani matsala a tsakanin iyalina,
Idan har zaki amin ce da duk wani fokan da zansaka maki a yanzu to a shirye nake da nabarki a dakin ki,
Cikin sauri Salawatu ke ce wa zan kiyayen insha Allah kuma zaka samay ni kamar yadda kake bukata, agidan nan,
Dadi yaji a zuciyar shi ganin yadda ta horu don jikin ta har rawa yakeyi, don kaduwa, da fargaba,
Nan Yaya ya dinga kidaya mata dokokin shi tana cewa ta dauka yayi hakkuri da ita please,
Tausayi ta bashi daga karshe saboda irin son da take mashi,
Amma sai dai ya boye mata ya nuna mata cewa har yanzu fa yana da fushin ta akai,
A hankali ta dago kan ta tana kallon Yaya Abubakar tana duban shi hawaye na tsiyaya mata aido,
Tana cewa, Sweet Oga ka yarda dani har a cikin zuciya na gaskiya nake fada maka,
Yaya Abubakar yadaga idon shi da suke nuna fushi da tsana a gare ta ya kalle ta, da su,
Yace mata Idan da hakan ne ai da baki kai sukan wani ba agurin Mama ko,?
Kince sai abinda Meenatu tace nakeyi a gidan nan ban ganin kowa idan ba ita ba,
Yanzu ke idan ace ki ratse abinda kika fada gaskiyane zaki iya rantsewa,?
Ta hada hannayen ta biyu guri guda tana cewa wanan sherin shedan ne amma irin yadda kake tsan manin ba haka bane gaskiya, zamana adakina yafi min zama a gida,
Ido yadan tsura mata tankar mai nazarin son gano gaskiya daga gare ta,
Ya wuce ta gefen ta batare, da ya kara cewa uffan ba again,
Ido Salawatu tabi bayan shi da shi tana kallon shi cikin wani irin yanayi,
Wanka ya fada ya fito ya samu ta aje mai kayan da zai canza tare da takalman zama gida,
Wanan ranan bamu ga Yaya Abubakar ba a part din mu yazo muna sai da safe ba,
Sai washe gari muka gan shi zaune a falo yana kurba shayi a hankali shi kadai saman dining table,
Ni kuma na fito don zuwa kitchen gurin Ramatu a lokacin,
Kallon guda nai mashi na ga yanayin shi a cikin annuri yake,
Ban karaso ba don nasan rayuwan Salawatu bata bukatan mutum ya je kusa da Yaya Abubakar idan tana tare da shi,
Don haka, daga inda nake na tsaya nace ina kwana Yaya ?
Ya dago ido a cikin annuri yana cewa lafiya kalai Meenat ya kuka kwana,
Na amsa da fadar Alhamdullaj na juya abina zuwa kitchen,
A lokacin Salawatu ta iso gurin shi a cikin wani ado da kwalliyan da ta caba,
A take fuskan ta ya canza yanayi ganin da tai min da Yaya Abubakar duk da banzo kusa dashi din ba
Ta daure fuskan ta daga yar annurin da ta fito dashi daga dakin ta,
Nagane nufin ta amma sai na nuna tankar ban fahinta ba,
Don ita fa haka take saboda duk cikin mu tanawa Yaya Abubakar wani itin mugun so,
Wanda ke haddasa mata mugun kinshi sa idan tagan shi a tare da wata daga cikin mu,,
Ban fito ba don ma kada in katse masu jin dadin su duk da naga cewa shi kan shi yaya akwai dan canjin yanayi a tare da shi, tsakanin daren jiya zuwa safiyan yau,,,
Ban kara gaskanta zargina ba sai da na tsinkayo muryan Salawatu tanawa yaya Abubakar adawo lafiya,
Abinda Yaya bai taba yi muna tun dan zamana dashi ya fita bai muna sai ya dawo ba,,
Abinci nake ci a kitchen din don da yunwa na kwana ranan,
Hakan yasa na kasa hakkuri har Ramatu ta kawo min,
Daga inda Ramatu take a tsaye tana tsiya min ruwa ta hango Salawatu tana murmushin keta, ita kadai tana kada kai, alaman tayi nasara,
Gurin da nake tsaye ina kai spoon din indomie a bakina da zafin shi Ramatu ta kalla tace min Uwar dakina mu tafi daki ki karasa acan don nan din a tsaye kike,
Ban faye musu ba nabi zancen Ramatu muka koma daga daki alokacin Salawatu ta dan shiga dakin ta,
Ramatu tsohuwar yar hannu ce don haka tasan makircin kishiya kamar may fa,
Zama tayi ta dinga jana da hira har naci nai kat na sha ruwa tare da magani na,
Ban dauki wani lokaci ba mai tsawo barci ya kwashe ni ta yi murmushi ta mike daga gurin da take zaune
Ta fara gyara min ko ina taja min kofan dakin ta rufe don gudun kada tana daga waje ashiga min dakin,

****** ********** ******
Yana tukin mota acikin nishadi gab da zai shiga ma,aikatar sune ya tuna cewa bai muna sallama ba,
Asalima yau bai fa leka kowacen mu ba kamar yadda ya saba, dan gara Meenatu ma yagan ta a falo zata shiga kitchen,
Ajiyan zuciya ya sake cikin yanayin damuwa ya nasa cewa gara kawai idan ya shiga office yakira layin mu,

Yana shiga office din kuma sai duk ai yuka sukai mai yawa on haka ya manta da zancen kiran,
Sai da Salawatu wace ke ta faman kiran layin shi don jin lafiyan shi tare da dan mashi hiran last night din su wanda ke sashi murmushi,
Don haka sam bai tuna da zancen kiran layukan wayan mu ba,
?nty Sadiya yau abin yai bala,in bata mamaki sosai on tasan hakan ba halin shi bane,
Daga gurin da Ramatu take wanki abayan tagan dakin Salawatu
Ta na jiyo muryan Salawatu tana waya akan yasa Ramatu dakatar da wankin da takeyi
Kina ji Lubuna ban zata cewa aikin wanan mutumin zaiyi tasiri haka da sauri ba akan wanan mutumin da na ke gani tankar ko aljani bai galaba akan shi sai gashi adan kan kanin lokaci munyi galaba akan shi,
Bata dai jin may Lubuna ke fadi, don haka takara kashe jikin ta gurin sauraren ta,
Ramatu ta samu ta gama wankin ta acikin tashin hankalin abinda kunuwan ta suka ji mata,
Ta dawo daki ta samay ni ina barci har zuwa lokacin don haka ta wuce don dafa muna abinda zamu ci,
Tunda ta dora girkin shigan Salawatu uku a kitchen din amma Ramatu tai, kicinkicin da rai, don kar Salawa taga damar ta,
Sabodata fahinci may Salawatu ke nufi da wanan shige da ficen da takeyi a kitchen din,
Muryan Salawatu ce ke cewa kizo ki karbo min kanwa a gidan can please ?
Tankar ba, da ita Salawatu ke magana ba sai ta kara nanata abinda tace,
Ramatu tace Allah sarki hajiya kiyi hakkuri ina dafawa uwar dakina abinci idan na gama sai in tafi in karbo maki,
Cikin bacin rai Salawatu take cewa Ramatu kina nufin bazaki ida nace ba ke nan,
Batai magana ba taci gaba da aikin ta tana kwshe abinci tana zubawa a kula, tana gamawa tarufe ta hada kan wankewa ta wanke plates din zamu yi amfani da su har tabar kitchen din Salawatu na tsaye a cikin mamaki,
Abu guda ya sata kyalewa shine taima maigidan alkawarin bazata kara fitina ba,
Amma idan bashi ita wanan yar aikin ai bata isa ba,
Tana fitowa daga kitchen Ramatu tafito daga daki na tana cewa na idar Hajiya may za,a karbo maki ?
Wani wawan kallo taiwa Ramatu tana cewa keep bar shi kawai don ban son harka da rainin wayo ,
Kiyi hakkuri Hajiya itace tafara sakani in mata aiki shi yasa naga rashin dacewan hakan in tafi ban girka mata ba,
Tsuki mai karfi Salawata taja tare da hararan Ramatu ta kauda kan kata ta wuce,
Murmushin kasa kasa Salawatu tayi a lokacin don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login