Showing 138001 words to 141000 words out of 388021 words

Chapter 47 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8251

ta kula dani,
Washe gari na tashi jikin nawa da sauki don muyi waya da Anty ina mata bayanin yadda jikin ya kasance min,
Ta tambayeni ko ya muka kwashe da Salawatu, sai da na ja tsaki nace ni tun shigowa na ban ganta ba ma har yau,
Kina nufin ba tazo dubaki ba ke nan na cewa Anty gaskiya hakane,
Share muna fuka kawai ki kama harkokin ki bakin ciki takeyi dake don may ki kazo,,
Kada ki yarda ki biyewa jikin ki ki mike kifara harkokin ki a cikin gida kamar kowa,,
Na amsa mata da to ?nty na gode takara ce min kadafa kiji tsoron kowa ki dake kawai ki kama harkokinki na kara cewa to Anty nagode,
Muna gama wayan da Anty sai naji tankar tabani wani magani ne a jikina don sai kawai na mike tsaye, na shiga yan gyare gyare a dakina har zuwa dan corridor din sashe na,
Daga nan na fada kitchen don indan sa ruwan zafi wanda zan sha ruwan Lipton shayi,
Salawatu tana cikin kitchen din tana aiki wanda hakan ne yasani gane cewa, ita ce da girki a gidan,
Sallamu Alaikum na ce tare, cewa ina kwana lafiya kawai tabani ansa,
Direct gurin Gas din da ba bu komai a sama na nufa don in kunna wuta,,
Muryan Salawa naji daga baya na tana cewa, wanan dayan Gas din zan yi amfani dashi yanzu,
Amsa na bata a takaice da cewa ruwa kawai zan dafa sama,
Naci gaba da abinda nakeyi, sai dai bakina ya dauke da addu,an haduwa da muguwar kishiyya,
Komai na hada daga Lipton har kayan yaji a cikin ruwan har ya fara batun tafasa,
Muryan Yaya Abubakar naji daga baya na yana cewa,Sallawa har kin samu lafiyan fitowa hada girki,
Dan murmushin irin ta ma,ana na sake nace ba girki bane Yaya dan ruwan Lipton zan dan dafa da kayan yaji inzuba a flasks dina,
Ashe Salawa tana a bayan shi sai naji yana cewa bakin ce ta,tare maki gurin girki da nata girkin ba, ?
Batare da na kula suba tankar basu gurin najawo flasks dina a gaban shi na fara daurayewa tare da daukan dan soyoyon tace ruwan zafi, nafara tace ruwan a cikin flasks,
Ina jin lokacin da yaya ya juya yana cewa cikin murya kamar a zafi zuciya yace, bazan yarda da zaman fitina a gidana ba fa,
Idan ke baki sani ba su sun sani ai don na riga na fada masu, tun farko
So, Mind your self,,,
Sororo Salawatu tayi tabi bayan mijin su da kallo don ita ba haka tazo ba,
Daga in da nake tsaye na sake wani irin ajiyan zuciya,tare da numfasa,
Na kashe Gas din tare da dauraye tukunyar na zubar da kayan yajin a dustbin, din kitchen,,
Fitana daga kitchen din tabi bayan nawa nima da kallo har na bace mata ga gani,
Dakina na fada na aje flasks din a gefen mirror na,
Bakin gadona na zauna nafara tuna nen cewa ashe zancen Anty Amarya gaskiyane, na cewa sai nayi fama da kishin Salawatu,
Na mike tsaye ina cewa ashe akwai aiki kenan a gaba na bari kawai in murjewa wanan macen ido,
Abincin da yasa dokar cewa a tare za,a dinga ci sai naga ba,a kirani ci ba
Tunda nadan sha ruwan Lipton dina tare da magani na sai na samu guri na kwan ta don dama ina bukatan hutu,,

Sau kusan biyu Yaya Abubakar ya yana lekowa ya ga ko na farka daga barci, don yaji ko nasha magani na,
Wanan abin ya matukar bakan tawa Salawatu rai don tun zuwan ta gidan ta, tare komai tana nuna kamar ita ka dai ce matar gidan,,
Ita Anty Sadiya ko a jikinta, don ita har kan su baya gaban ta
Duk wani duniyan cin da Salawatu zatayi bai a gaban ta,
Hakan ke sa bata damu da fita waje ba don bata da lokacin su,
Ita ko Salawatu sai take gani kamar duk a cikin samun gurine hakan agareta,
Amma yau sai gashi kan yar karamar matar sa har yake ta zuwa da dawowa,

****** ********* ******
Driver yana shiga garin Birnin Kebbi bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan malam ,
Abinda ya jawo hankalin al,umman uguwar ke nan zuwa kallon motan da ta tsaya kofar gidan tsohon,
Driver wanda ya fito ya nufi wurin da malam yake cikin rufan kofar gidan shi,
Babu abinda zaka hango sai farin gemun shi tun daga nesa,
Shima kansa malam din kallon mamaki ya kewa driver motan,
Sun gaisa da malam a cikin mutunci tare da taron hababa daga malam din har sauran mutanen dake gurin,
Mutumin ya dubi malam yace sako ne da Alh Abubakar na gidan nan,
Yace ina zo in,baka wanan sakon hannu da hannu ya mika masa envelope,
Kudi ne acikin envelope din da yar takarda, mutumin yace, yace wa yancan kayan aba Wadda ya rabawa kowa ga takarda wai a bashi,
Cikin mamaki malam yace a ina ka gan shi bawan Allah,
Yace Sokoto sun fito Niger da shi da matar sa, saboda bai samun zuwa shi da matar sa yaba da sakon akawo,
Take guri ya dauki zance cewa Abubakar ta turo wa iyayyen shi da abinci mota guda taf da kaya,
Baba Wadda aka nemo a cikin gari yazo da sauri inda ya fara fitar ma da kowa da nasa rabon,
Har zuwa makwabtan su da ya sa sunan su a cikin don sun zama tankar yan uwa,
Sai kuma kudin sabon mashi wanda za a saiwa Baba Buhari,,
Baba Wadda yaba kowa shadda da kudin dinkin da yaya Abubakar yace masu nice na sayo masu tsaraba a kasar Niger,
Haba gari ya dauki ciri cewa, Abubakar ya aiko wa iyayyen shi da sako,
Wasu ce ai yanzu ya daina daukan shawaran Mama Ladi ne,
Wasu suce ai saboda yanzu yana auren yar gida yasa yafara kula da gida, tau kowa dai yasan halin dan Adam,,,
Ranan Mama Ladi kamar zata kama da wuta don may zai yo sako bai fada mata ba sunyi shawara,
Ita Meenatu aiki takeyi da zata samu kudin sayen irin wanan kayan haka?
Sam baza ta yarda a mallake mata da ba kamar yadda uwata ta mallake ubana ya kasa kara aure ,sai abinda tace kuma take so akeyi a cikin gidan mu,
Zagi dai kala kala mun sha shi gurin mama Ladi ni mahaifiyata a ranan,
Malam tsoho yasa arabawa mutanen shiya mabukata kason shi tare da cewa Abubakar ne ya aiko masu dashi,,

****** ********* ******
Ina zaune a dakina ina dan shan faten wanken da Fattu ta,shigo min dashi don faten yai min dadin sha dosai,
Ya Abubakar yabude labule ya shigo da sallamar shi,
Na amsa tare da dan dago kaina plate din dake gaba yake kallo,
Tambaya ya jefo min da cewa mayye wanan haka a gaban ki,
Nai dan murmushi nace fate ne nake sha,
Yakara kallon plate din yace, fate kuma,?
Nace Fattu ce ta dafa min wai ko zanji dadin bakina sai naga fuskan shi ya matse da ga yar fara,ar da ya shigo da ita, da farko,
Meenatu bana son mutanen nan suna shigo min da abinci dafafe a gida,
Idan basu, dauka agidana ba ashe kuma baza,a kawo saga gidan su ba don dai ba alfahari ba nasan cewa nafi karfi,
Jiki na yai sanyi sosai da jin zance Yaya Abubakar
Don haka a hankali na dago kai nace masa nice nace ta da famin
Don bazan iya dafa abinci yadda nake ji, jikina ba,
Na fadi hakane don yasan cewa ba a, bani abinci ba agidan,
Na karashe zance da kwantar da muryana na ce amma kayi hakkuri baza,a sake ba insha Allah,
Ya juya batare da yace min komai ba ya nufi waje, cikin fushi,
Nima murmushi nayi daga inda nake zaune don ko banza na rama abinda Salawatu tai min da safe,
Dakin Salawa ya nufa ya samay ta zaune tana waya tana fadawa Salawtu ce nazo garin Abuja,
Kallon da yai mata kawai yasa ta gane cewa da magana yazo,
Don haka ta kashe wayan ba shiri tana mai kako murmushi a fuskan ta,
Oga lafiya dai ko?
Ko kana son wani abune ?
Lafiya kalau yace, tare da fuskan tar ta da kyau ya ce ina abincin Meenat,
Meenat ta tambaya cikin maimaita sunan,
Yace eh Meenat my second wife,
Kai tsaye tace ban sama mata ba saboda naga gaba daya ake zubawa agidan, aiko,
Yace amma kin san aibata da lafiya ?
May yahana ki kai mata a daki ?
Ta katse shi da sauri cikin murya mai baiyana mama tace,
Sir nice zan kaiwa wanan yarinyar abinci har daki ?
Don kin kai mata abini laifine, ?
Ba kishiyar ki bace ita,?
Idan akwai abinda yafi muni Salawatu taji shine wanan kalman da ya fadi
Gaba daya duk jikin ta sai yai sanyi rayuwar ta ya baci,
Amma sai ta dake tace ma shi ban yi wanan tunanen ba gaskiya amma kayi hakuri please ,
Tashin hankali Salawatu duban Yaya Abubakar takeyi yadda ya sake mata a lokaci guda,
Kamar ba Ogan ta ba da suke ta zuba soyayya da amarci tare,
Juyawa yayi ya haye sama dakin shi rai bace don duk mun taba shi,
Salawa ta dafa bakin gadon ta takai zaune da kyat,
Idon ta sunjuye sunyi jajir akan wanan little baby din yau Oga ke batun ci mata mutunci haka ?
Lai ko wani abu sai aure wanan yar karamar yarinya za,ace takaiwa abinci har daki nerve gaskiya da sake,,,,,


ZEEE MAKAWA. YELWA
[8/12, 10:09 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
5? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HASEEB,,,,,

Gaba dayan mu, mu uku, Yaya Abubakar ya bukaci da muzo falo gurin shi,
Kusan nice ta karshen fitowa sai da na natsaya na gyara jiki na tsab,
Nasa wani English wear, baki mai tsaga a kowani gefe ta kasa,
Yana da yagwai iya kwankwaso, na daurewa, rigar ta matseni tafitar min da sharp dina tson,
Tun kafin in karaso gurin su kamshina ya iso gare su,
Kamar yadda Anty Amarya tai min baya cewa kamshin kishi yana sa kishiya tashin hankali,
Hakan ne ashe don wani irin harara da mugun kallo nake sha tun da na nufo su,
Ya Abubakar wanda ke zaune a saman kujerar tsakiya yana waya,
Tun fitowa na hankalisa ya dauke gareni ido ya zuba min baba kawarwa
Waya yakeyi don tun ban karaso ba nake jin alaman da yan gidan mu ya ke waya,
Daidai karasowa na naji sunyi sallama, da mai wayan ya kashe, tare da ajitan zuciya,
Kujeran da Yaya ke zaune sama ita na samu gefen kafar ta kasa saman center carpet na zauna,
Cikin mamaki ya dan kalle ni yace, taso mana ga guri nan ki zauna, yana mai buga gefen kujeran da yake zaune,
Kai na girgiza na dukar da fuskana kasa nace nan is ok Yaya,
Ko da kaina ke a kasa nan san bakowa yai wani irin ajiyan zuciya mai baiyana takaici ba sai Salawatu,
A hankali nace Yaya ina wuni,?
Ya karba min a cikin sakin fuska da lafiya kalau Meenat ya jikin ki ?
Alhamdullah, na amsa dashi,
Sai na juya gurin da su Anty ke zaune sun sashi tsakiya kowace na saman kujeran da ke gefe, gefen shi, nasan ko cewa an tare guri ne kada in zauna akusa da Yaya din,
Ce masu nayi ina wunin ku Anty, ?
Ba laifi don ita Anty Sadiya ta katba da cewa lafiya Meenat jiki yai sauki ko ?
Duk fuskan ta a hade yake wanan kuma aiba wani bakon al,amari bane ga Anty,
Ji mu kayi Yaya Abubakar ya sauke wata kakkarfan ajiyan zuciya tare da sauya fuskan sa zuwa damuwa,
Kowan mu na ganin yadda annurin fuskan Yaya ya dauke, a take kowa ta shiga natsuwa,
Ina wasa da yan yatsun hannu na a hankali kai na duke a kasa,
Magana ya fara a cikin wani irin murya mai nuna alamar serious a tare da shi,
Dan gyaran murya ya fara yi wanda hankalin kowa ya koma gare shi gaba daya,
Yafara da sallama da addu,a tare, da magana a cikin dakewa, kamar haka ?
Ina son ku san cewa duk kan ku Allah ne ya hada zaman akan amana,
Gaba dayan ku duk abu gudane ya hada mu, aure, babu daya daga cikin ku da zata fi karfi na,
Abu na farko shine, ina son hadin kai daga gare ku kamar farko don ci gaban gidan ,
Ya nuna mu da yatsa nida Anty Sadiya yace, su wa yan nan biyun sun sanda irin dokokin da na sa agidan nan,,
Don haka ina son a cigaba da yadda akeyi da farko,
Kafin ya rufe bakin sa sai Salawatu ta ce amna aini ban san wanan dokan ba a gidan,
Zaki sani yanzu ai don tun zuwan ki abinda yasa ban fada maki ba shine, don wanan bata gidan a lokacin,
Dafarko idan baku man ta ba kun raba kwana a tsakanin ku,
Sai kuma yadda girkin ku zai kasance duk a wanan can lokacin a dan samu matsala a gurin girkin da fatan wanan karon za,a gyara,
Idan angama abinci wajibi,ne mai girki idan ta kare girki ta fadawa kowa donba fito a ci a tare, gaba daya har ni, idan kuma bana gida sai kuci a tare ,
Salawatu ta bude baki tace to amma Sir sai,nake ganin,
Wani tsawa ya daga mata ya ce, shout, up my friend iam talking you are talking who is the master,,
Cikin muzan ta Salawatu tai wani irin dukar da kai tana ajiyan zuciya,
Kawunan mu na kasa ni da Anty Sadiya saboda, sanin halin gogan namu da mukayi, don mutum ne wanda bai son raini ko kadan, shi,
Bayan dan shiru da yayi tare da kuraw Salawatu ido sai yaci gaba da cewa,
Wajibine duk wata wace ke girki tafara yiwa yan uwa ina kwana da safe ranan itace zata guda nar da komai na gida alhakinn kowa yana gurin ta,
Karfe, takwas zuwa tara da rabi kowacen ku ta tabbatar da cewa tana cikin falon nan da dare,
Da sauri Salawatu ta kara dago kai ta na duban shi a cikin mamaki,
Bazan taba lamuntar hayaniya a gida na a tsakanin ku,
Duk wace akaiwa ba daidai a sanar dani don inbincike akai,
Dafatan za ku kiyaye gaba daya abin da na sheda maku akai,,
Shiru mu kayi gaba dayan mu kowa da abinda take tunane a rayuwan ta a lokacin,
Tv da ke aiki a falon muka tsurawa idon muna kallo da saurare,,
Don faba dayan mu ba wanda ke iya magana a lokacin duk jikin kowacen mu yai sanyi,
Wayan Yaya Abubakar yai kara ya bar abinda yake a system din shi, yadauki wayan da sauri naga ya gyara zaman shi
Jin da nayi yana cewa Baba ina wuni, yasa ni saurin dago kai na na dan dube shi,
Batare da ya dube ni ba yaci gaba da maganan shi
Ina tsan manin ko wani Baba,ne, mai shi godiya ya keyi don sai Ameen, Yaya Abubakar ke ta cewa tare da kada kai yana lumshe, idon shi a hankali,
Sai ji mu kayi yana cewa su na lafiya, Baba, da alamar mai shi ya tambaye ni sai miko min wayan Yaya Abubakar yayi da sauri na karba ina cewa,
Baba ina wuni ?
Daga murya nagane cewa Baba Buhari ne maihaifin Yaya Abubakar don haka nakara dan magana acikin girmamawa,,
Sai addu,a Baba yake muna akan Allah ya bamu zaman lafiya tare da samun zuria dayyaba,
Baba Buhari yace Aminatu muna alfari dake don zuwan ki cikin rayuwan dan Uwan ki,ya kawo canji sosai,
Hakki Aminatu Ubangiji shi yasan yadda yake tsara abinsa cikin ikon sa da mulkin sa,
Baba na gode nace don in takaita maganan Saboda idona da ya kawo hawaye, a lokacin
Saboda yadda nake jin maganar ta Baba Buhari yasa jikina yin sanyi,
Baba Buhari yace, Aminatu idan Allah ya so mutum da alkhari ko arziki ba wanda ya isa ya hana,
Hakana kana zaune zai kawo maka har inda kake zaune ta inda baka zata ba,,
Nasan kina kokari sosai gurin gyara halaiyyan dan Uwanki,
Zamanki a tare dashi ya kawo muna cigaba sosai a rayuwan gidan mu,
Murmushi nayi wanda har sai da Yaya Abubakar yadago kai daga abin da ya keyi, ya dan kalle ni, tare da kura min ido ,
Salawatu dake daga gefe, ji take kamar ta shakeni a lokacin don batai zaton cewa zata samu matsala daga gare ni don tasan cewa auren hadi akai min da yaya Abubakar ba wani so a tsakanin mu,
Na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login