Showing 378001 words to 381000 words out of 388021 words

Chapter 127 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8305

******
Bayan na idar da sallah nashiga cikin gida don na gaida mutane niyata sashen Mama Ladi ta zama karshen shigan mu,
Amma ina shiga sashen malam tsoho sai naga Baba Buhari zaune tare da malam inda naji malam din nacewa yauwa gama yar halas din ta shigo,
Na karasa da mamaki ina gaida duk wani wanda ke gurin a lokaci amma kuma sai na fahinci iyayyenmu maza ne zaune su uku sai Mama Ladi daga dauan gefen tare dasu Mama Dije,
Malam kecewa na samu guri nazauna na saurara da kyau,
Bayan na zauna yai dan gyaran murya sai a lokacin nadan lura da dan tsohon naga yaramay min sosai a idona ga tsufa ya taso mai sosai duk ya yankwamay sosai,
Sai naji wani iri a raina mutumin da yake fari a tsaye karfafa dashi wanda zance hasken shi da yawa yan gidan mu suka kwaso,
Gyaran muryan da yayi ne yasani dawowa daidai daga dan tunanen da na shiga,
Naji yana cewa dama zan aika akira min ke ne sai gaki Allah yakawo muna ke,
Yace Amina ko kin san cewa mijin ku yai maku masauki a gidan nan ?
Cikin mamaki nadaga kai alaman eh nasani sai naji tau madallah don Allah daga yau idan kin zo garin nan a nan zaki dinga sauka bake ba har sauran yan uwanki matan shi,
A cikin sakin fuska batare daxnuna komai ba nace insha Allahu malam haka za,ayi yace madallah Allah yai maku albarka na amsa da amin malam,,
Ya juya inda iyayyen mu su ke yana cewa shike nan kunga yanzu anraba garda sai ta koma dakin ta ta zaunq har tayi kwanakin da zasuyi su koma,
Har zan daga na basu guri sai naji malam nace yaki mana Aminatu dawo mana mu gaisa,
Sai na koma na zauna ina murmushi ina cewa aida zan bari sai da safene mu gaisa,
Asmau kaunata na kira a waya ina fada mata cewa su je can part din mu su gyara min dakin da akace yanazamana,
Wanda lokacin da su Fattu suka zo sunan Amir aka sauke su a cikin sa, ida nace su katbi makulli a gurin Baba Buhari, kamar yadda malam yace,
Ana gama watsewa Dije ke cewa ikon Allah yau Ladi ce wai ke fada a gidan akan zuwan Meenatu, garin nan,
Malam yai murmushi kawai mai nuna alaman yasan may yin hakan ke nufi ko kuma inda Mama Ladi din ta dosa ,
Sai naji kafin Dije taci gaba da magana yace ke Aminatu ,
Nayi maza na amsa mashi da cewa naam malam ,
Yace saurareni ni ki ji may zance maki don ki samu kije gurin yaran ki don dare ya soma,
Jin haka yasa su Dije mikewa don barin gurin saboda sun san cewa zamuyi serious magana kenan, da shi,
A cikin natsuwa ya somayi min magana dacewa kun zo lafiya ko yaya karfin jikin ki,
Na amsa mai dacewa Alhamdullahi na samu lafiya sosai,
Nace min samay su lafiya ko sai naga yar murmushin yake yana cewa lafiyan dai da sauki Aminatu,
Mijinki bai fada maki cewa banda lafiya bane duk yan watannin nan da suka shige,
Mamaki naji sosai jin malam yaji jiki haka wai yai rashin lafiya banda labari,
Ina daga zaune ina mamaki naji yace, ai shi da kanshi ya dinga turo min da magani nai tasha har na samu lafiya haka acikin ikon Allah
Al,amarin yaya Abubakar yai nisa kawai a barshi da halin shi yanzu ace har malam tsoho yai ciwo haka ban da labari daga gurin shi,
Mama Ladi tana barin guri ta daga waya ta kira Abubakar tafada mai karya da gaskiya, dama mai neman fitina ne aiko a take ya hau fam,
Na samu an gyara muna daki yadda ya kamata Nida Ramatu da Aisha sai Asmau na muka kwana a part din da yarana,
Yai kiran layin waya na a cikin daren nan bai samay mu ba take ranshi ya kara bacu sosai, yakira ayin Baba Wadda wai ya kai min waya din,
Amma sai ya samu har mun kwanta mun rufe part din ya buga mai waya yaba sheda mai cewa ya samu mun rufe kofa ko,
Bayan sun kashe wayan ne yake Nanak n jun Baba Wadda yace a part din shi nake zaune sabanin yadda mama ta fada mai, abinda ya dan sasauta mai rai ke nan,
Washegari tun da far safiya Mama Sa,a ta shigo ta kwashi yaran zuwa part din ta tai masu wanka ta shirya su tsab ta dawo min da su,
A take aka cika mu da abin karyawa kala kala daga wani part na cikin gidan mu,
Abinci sai wanda ranka ya zaba zakaci gashi nan a zube inda yan matan gidan mu duk suna a tare da mu munata hira,
Sai da kyat na saci jiki zuwa cikin gida nagaida iyayyena maza kafin su fita sai dai ban samu mahaufina ba don shi mutum ne mai sakko zuwa gurin bida,
Nadawo nashiga raba tsara daga cikin gidan mu har makwabtan gidan mu,
Tsofin tufafina duk na kwaso su na raba wa yan uwana mata don nayi sabbin din kuna,
Iyayyen mu matan na sayo masu turamay zannuwa a Sahad Store danagani very chief sai faman murna suke yi,
Waban rabon shi ya kara tayar wa mama ladi da hankali don sai take gabi dukiyan danta ne na debo nake rabawa a gidan mu, sai faman mita da jinini takeyi tana masifa,
Kwana biyu da zuwan mu nadan shigo cikin part din mahaifana don in gana da Mama ta,
Anan Anty Safiya ta samay mu wace munyi da ita zata shigo mu fita tare don wai Anty Nani ta bata labarin duk irin halin zaman da muke yanzu a ciki gidan mu,
Wanda sam ban so hakan ba don wanan ai sirinane ba abin fadawa wasu bane,
Saukin abin Anty Safiya ce duk da ciki guda suka fito da Yaya Abubakar tana iya nata kokari a kaina,
Zaune muke muna hira da ita da Mama sai wayata tai ringing, ban kula dana dauka ba har ta katse a lokacin kafin na dauko ta acikin jakata ta,
Yaya Abubakar ne yakirani wanda sam ban tsan maci kiranshi ba a lokacin,
Kara kirana yayi inda na dauka a cikin natsuwa ina mai yin mai sallama,
A cikin wata murya mara fara,a naji yakarba sallaman ina kokarin gaishe shine naji muryan shi maikama da fada yana cewa,
Ba,a fada maki cewa na bugo waya abaki bane ranan da kukazo,
Nima acikin muryan da bata da ma,ana na amsa mai da cewa ba wanda ya fada min ni,
Yace OK kuma sai ke baki azanci ki bugo min ba saboda rashin sanin ya kamata ko ?
Mamaki zancen ya bani har nace a ,a acikin wani irin yar sauti,
Yace a gadarance yaushe ne zaku dawo ne wai ?
Da mamaki na ce dawowa kuma Yaya har yaushe mukazo da za a fara zancen dawowa,
A hasale yace OK anan zaku zauna kenan ko nace cikin muryan fushi a dadare ni bance a nan zamu zaunaba amma dai naga duka duka fa yau kwanan mu biyu da zuwa ko gurin yan uwa bamu fara zuwa ziyara ba,
Ok bazaku dawo yanzu ba kenan kike nufi ko ? Nace a cikin yar murya aa bawai bazan dawo bane ,
So nake gaskiya mu dan huta agida mukwana biyu muga yan uwa sosai,,,
Dip naji ya kashe wayan ba tare da mun kai karshen zancen ba,
Na dan dubi wayan ina cewa acikin raina jifa kamar wanda mu kewa wani abu a gidan mutumin da zai yi kwana barkatai baji lafiyan mu ba ma
Shiru Mama da Anty safiya su kayi su na sauraren mu,
Anty Safiya ke cewa wai so yaje ku dawone kuma na gyda mata kai a hankali alaman eh ,
Daga haka mukai shiru sai mamace tace kashen wayan yayi ke nan nace eh rai a bace don duk ya na son bata min lissafina,
Mama tace to ai kiranshi zakyi don kiji yaushe yake son ku dawo Anty Safiya tace gaskiya ne,
Amna ahi kuma yaya tunda ba, agari yake ba ai yabar ku kuyi kwanan k ku mana,
Mama tace kirashi dai kuji idan yace ku koma ne ba sai ku koma ba,
Ban soba amma dole na daga waya na kirashi don mama ta tsureni da ido
Ina kira kamar ba zai dauka ba can naji ya daga wayan yana cewa yaya akayine kuma,
Cikin hade wasu miyau masu daci na ce naga kayi fushi ka kashe wayan bamu gama magana ba,
Yace, kina ina yanzu nadanyi dummm a daure nace ina tare da Mama Sare da Anty Safiya,
Yace OK nasan da hakan idan sati yai maku sai ku shirya ku dawo gida,
Zanyi magana naji ya kara kashe wayan batare da yajira yaji may zance ba,
Nace a dan hasale ni gaskiya da malam zan hada shi don ya barmu muyi kwanaki mu a nan,
Cikin bacin rai mamana take cewa tunda yace ku koma ma may zaku tsaya yi kuma basai ku shirya ku koma ba,
Batare da nacewa Mama komai ba naci gaba da harkokina inda muka shirya ni da Anty Safiya muka fita zuwa unguwa a cikin motan maigidan da nazo da ita,
Duk inda na wuce zaki ga mutane suna kallona gwanin ban sha,awa,
Ba komai ke kara jan hankalin mutane ba sai ganin noban motar da kuma irin kyaun motan da tsadan ta,
Gashi nima din duk da karama ce ni amma sai motar tasakani komawa wata babban mace,
Anan kwatance ya tashi a cikin gari ana kwatancen da Yaya Abubakar wanda mutane ke cewa iyanzu ya zama wani last Don a Abuja,,,
Sai da dare bayan mun dawo daga unguwa da Anty Safiya,
Nasamu malam tsoho ina sheda mai abinda Yaya Abubakar yace na mu dawo zuwa kwana uku,
Fada ya fara yi yana cewa shida baya gari idan kun koma wani abin zakuyi mai acan din,
Dadi naji don nasan cewa zai mai magana sosai, akan yabar mu mu sha gida,
Hakan akayi don yai mai magana cewa shi yace na tsaya gida har a kwana biyu don nadan kara samun sauki,
Murmushi yayi kawai don yagane cewa plan di na ne hakan nice nasa malam din yai mai magana don haka kawai yace ba matsala,
Ashe bada gaske yake ba don waya ya bugawa Babana cewa kada na wuce kwanakin da ya bamu,
Malam yana ta ci gaba da abubuwan da ya kamata ya taimaka muna dashi a cikin tsanaki,

****** ********** ******
Duk kwanakin nan tun bayan komawan su sai faman haba haba yake da ita,
Ko kadan baya son ganin bacin ran ta sai abin da taje so taje bukata take a gidan,
Sam har ta manta da cewa tana da wasu abu wai kishiyoyi a can Abuja saboda duk tafitan da zancen kowa a ranta,
Duk da yana tare da sahibar shi abin son ranshi bai hana shi tunawa yanzu da sauran iyalan shi na gida ba,
Don tunanen su yakan zo mashi a rai jefi jefi sai dai baida yadda zai yine kawai,
Don idan ma har yaji son ganin su yazo mashi a rai yakan yi yunkurin kiran su ga waya ,
Amma kuma sai yaji daga baya sam bai kaunar jin zancen su don yakan rasa may ke mashi dadi a zuciyan shi,
Gashi shi mutum ne mai son yin tsabta amma yanzu sai ya lura da cewa, Salawatu tana da matsala a gurin tsabtace muhalin ta yanzu,
Kodon tana ita kadai ne a nan din yake ganin haka gareta,
Abu gudane a kwaita da kokari gurin kula da bukatun shi na yau da kullun a matsayin shi na matashi mai jini a jika,
Don haka tun a jikin dare da yadawo da ga aiki yaga irin yadda ya bar gidan su a haka ya samay shi,
Musan man makewayin su wanda yake da bukatan a kullun a wanke shi sau biyu ko sau uku amna yanzu har kusan sati guda yake gani ba,a wanke shi ba,
Rayuwan shi a bace yake don duk kazantan gurin ya ishe shi,
Da kan shi ya duka ya wanke ko ina tsab inda ya yadauki lokaci yana wanke bayin,
Sai bayan fitowan shi tana daga kwance da waya a hannun ta inda ya dan juya yana kallon ta yana kokari saka rigan barcin shi a lokacin,
Wani irin baki ne da tsufa yaga yau tai mashi a fuska don haka sai yaji gaban shi ya fadi har sau uku,
Bayan fito wanshi ne tashiga bayin da niyar ta kewaya inda taga ya wanke ko ina na bayin tsab da kan shi,
A take gaban ta ya fadi don tasan cewa da akwai matsala ke nan kamar yadda aka fada mata
Tun da har yau da kan shi yaduka ya wanke bayin da suke amfani dashi mutumin da akace bai gani illar komai da zatayi a tare dashi ,
A haka suka kwana har wayewan garin kowa da abinda yake ji da dan uwa a ranshi,
Yau tun tashin su yake kallon ta yana son yi mata magana amma yana dan jin wani abu a kasan zuciyan shi,
Saboda yadda asiri yasa yana gudun zuciyar ta matuka saboda baya son abinda zai bata mata ran ta,
Can dai acikin daurewa don yau yadda gidan nazu yake a wani hargitse, dole ya sata gyara masu shi,
Cikin daurewa yake cewa, yau kan sai nake gani ai gidan nan yana bukatan gyara sosai, dubi yadda duk kura ya cika falon nan,
Tun da yafara magana ya fuskanci fuskan ta ya sauya daga farin ciki zuwa bacin rai,
Dama yasan za ai hakan amma acikin dakewa yaci gaba da zancen shi, yana cewa wanan gidan aiko babu mace bazai yi irin wanan kuran ba haka,
Cikin wani irin murya tace Ogana kenan yanzu duk girman wanan gidan za,ace nice zan gyara shi,
Gida haka da girma ga kuma kaya ta ko ina za,a ce waini in gyara shi gaba daya,
Yace cikin murmushi Madam Salawatu ke nan ni bance ai duka gidan zaki gyara ba at the same time,
Da kadan kadan zaki fara har ki gyara ko ina, na gidan, ko,
Duk da taji tsoro a ranta yau tana fadi yana bada amsa amma a cikin dakiya tace,
Dakata malam nayi maka kama da mai aikine da zakace nayi wanan aikin haka ?
Galala ya tsaya yana kallon ta a cikin mamaki yana keep ma tunanen cewa wai dama haka take ashe da kazan ta,
Don dai tana a cikin yawane ba,a gane kazantar ta ashe ?
Amma a gurin kwalliya da gyara jiki a fito tsab wanan kan ba a barinta a baya,
Gyaran muryq yayi yana cewa gaskiya bazan dauki kazanta irin hakaba a gidana don ina gudun nayi baki su samay mu a haka cikin datti ,
Wata uwar harara ta sakar mai tare?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? tare da kawar da kanta gefe tana cewa sai yanzu kasan cewa muna zama a cikin datti duk wanda zai zo yace wanan gidan yayi datti yazo yace,
Shima din hararan ta yayi yana ma sakin tsaki tare da kokarin daukan brief case din shi zuwa waje,
Bazaka karya ba tace mashi tare da tsura mai ido don taji mai zaice don yau din yajuya mata yafara zama mata Abubakar din da tasani da farko watau Garba sadauki Garba gagare,,,,,
Ina abinda zan karya din dashi don banga alamar kin dora komai da zamu karya dashi a gidan ba,
Dagama fadar haka sai kawai ya suri jakar sa yakama hanyar fita yana nanata mata cewa lalai ta gyara gidan nan kagin ya dawo,
Zaune ya barta mamaki al,ajabi da tsoro duk sun cika ta a lokaci guda don tasan cewa da akwai matsala a wani guri wanda yakawo rauni ga aikin ta,,
Shiko shigan shi office da wasu yan awoyi malam ya kirashi yana ce mashi yakirashine don yana son yau ya tashi a cikin dare yayi nafila don ya hango wasu alheri tafe gare shi amma sai ya dage har sati guda kuma yana son yai sadaka da hannuwan shi, yau din,
Idan zai bayar ya samu farin mutum yafara bashi koda yarone anfi son abawa wanda yafi haske sadakan farko,
Don haka bai zauna ba yamike don bin umurnin malam ya nufi uguwar da hausawa sukafi yawa don yin sadakan,

Salawatu kuwa tana an duk, zuciyan ta ya kasu biyu tana tambaban cewa kodai yanzu Abubakar bai under control din tane da har ya samu bakin da zaice wai ita ta gyara gida da kanta,
Amma don ta gwada tagani ko hasashen ta gaskiyane sai taki yin aikin da ya sakata yi din,
Yana zaune a office amma zancen malam da yace sai yayi nafilan har na sati ne ya tsaya mai a rai,
Don shi yanzu gashi yana son tashi don yayi sallah nafila amma kuma sai ya dinga ji kamar andaure shi ko kuma duk kasala ya rufe shi,,
Amma kuma da zaran lokacin da sallah yayi duk dare sai ya farka a daidai lokacin sai dai bazai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login