Showing 75001 words to 78000 words out of 388021 words

Chapter 26 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8250

sheri ba ace wai kin tafi Abuja kai makar Amarya batare da sani na ba,
Bakar amarya ke kika gan ta mukan fara sol muka gani kuma muka kai gidan dan Albarka,
Aiko yadda kuka nade ta kamar amaryan sheri kuka kai haka za a nado maku ita akawo nan,
Tir da zurian yan naci,
May ake da irin zuri,an Fulde,Hausaje,,,
Masu kyau fuska da sura mai kyau ga arziki kamar suyi ihu amma basu da hanlin kwarai sai sheri,
Ai yanzu ke ake ji don nono ya gauraya da, jini ko,
Inji mama sa,a wace taba ta ansa tare da juya don komawa cikin sashen ta,
Saboda bata iya masifan mama ladi wace ko da kaza fada take yi,
Muzuba da ku in dai ni na haifi Abubakar da cikina ya sha nono na sai Amina ta dawo gidan nan, zuwa jibi,,,
Muna sauraren ki ai don gamu ga ki Baba Buhari wanda dawo wan shi ke nan ya bata snsa daga bayan ta,
Tsaya kiji yau Hausi muddin kika matsawa yaron nan akan sai ya sako yarinyan nan gida
Ke ma a bakin auren ki ranan nan kuma har in kince karya ne ki gwada ki gani,
Indai don akan wanan ne ba matsala nayar da a kore ni din ai ina da gidan Da na inda zan zauna har madi,
Daga haka ta juya ta huce kamar kumarci don bacin rai,

****** ********* ******
Zaune nake tun bayan tafiyan iyayyena a tukure ni kadai a cikin daki,
Batare da wani ya leko inda nake zaune ba, har zuwa wani lokaci,
Cikina ne yafara min kiran ciroma don haka naji ina bukatan abin da na ci,
A hankali na mike zuwa, hanyar da zan shiga kitchen don in dan dafa wani Abu inci, mai dan sauki,
Da farko, shiga na cikin kitchen din na rasa may zan dafa mane wai,
Gurin freezer na nufa inda na bude shi turirin hayakin sanyi ne ya daki fuska na a lokaci guda,
Nama ne danye da kifi sai tomatoes da tatasai sun kankare, wani leda na dago ledar na ga ashe danyen kubewa ne a cikin sa,
A take nai sha,awan in yi tuwon store nagani a mane cikin kitchen din,
Natura kofan a hankali naga ya bude, abinci ne kamar su shinkafa, doya semo, drinks, da sauran su,
Ledan semolina na dauko guda na nufi kitchen din da shi,
Abin da na fara yi shi ne wanke tukwanen da nagani a kitchen din har sunyi wani kalakala don dadewa ba,a dora su a wuta ba,
Ruwan zafi nafara dorawa nasa ruwa na kara wanke kubewa sama sama nasa acikin blender na markada shi
Kafin wani lokaci gida ya kauraye da kamshi mai dandano don irun sanadarin dandano da nai amfani da shi,
Sai a lokacin ya fito don zuwa gurin Salawatu wace ke ta kiran shi a waya tun jiya,
Kamshi girkin da na dora ne ya ruda gidan gaba daya,
Cak ya ja ya tsaya guri guda don abinda hancin shi ya shako, mashi
Hanyar da zai sada ka da kitchen din ya dan kalla kadan tare da daukan keys din shi ya yi yabar gidan,,,
Sai da yai mata sayayya kamar yadda ya saba sanan ya isa gurin ta,
Sun zauna zuwa dan wani lokacine take tabayan shi bata gan shi ba wanan jumma,an,
Sai da ya dauki kamar minti biyar sanan yace baki nayi gida,
Tau inji Salawa tare da cewa har sun tafi ne, yace ummm, masu kawo taba,
Amma ita kan ai tana nan, ina zata kuma ?
Ita wa kake nufi wai ne dear ?
Ban fada maki cewa nai aure ba ne wai,
To yarinyae ce mana aka kawo ranan Friday din nan,
Allah yasa Salawatu a zaune take da ta fadi inda tsaya take a lokacin da yake fada mata hakan,
Shiru gurin yayi kowa da irin abin da zuciyar shi ke sakawa a lokacin,
Da zun nan da rana suka koma gida, ai, wani irin takara ji,
Shi ke nan yanzu kan tasan cewa tarasa Abubakar ke nan,
Mutumin da take kwana da zancen shi take tashi da zancen shi azuciyar ta,
Ina son tun da ta tare kin ga naki bukin sai ayi shi zuwa, two month coming,
Da sauri ta dago kan ta don jin may yace ,
Kamar tace so soon ?
Sai dai tai shiru don kada taiwa kanta tuwon tulu,
A,lokacin da ya mike da nufin wuce itama dai mikewa tayi tabi bayan shi a hankali zuwa bakin motar shi,
Har ya wuce tana daga mai hannu a cikin jin dadi da albishir din da yai mata yau din,
Tukiya keyi kamar yadda ya saba kullun idan zai wuce sai ya tsaya ya hada masu take away ,
Amma yau yana wasiwasin azuciyar shi don jin kamshin da yayi a gidan shi,uya motar shi yayi zuwa gida ba tare da ya tsaya saye ba,

Bayan na kammala girki na kwashe su acikin ledoji kamar leda biyar, na zuba a cikin kula mafi girma mai rikon zafi ,
Falo na kai na aje masu asaman dining table, inda naga ana ajewa wasu Gwago Habbi abinci,
Na dauki nawa acikin plate, zuwa dakina wanka na farayi bayan nafito na gyara jiki na
Abinci naci kafin in shirya, cin abincin kawai nakeyi badon ina jin dadin sa ba
Kawai don ya magan ce min yuwar da nake ji ne alokacin
A haka dai na tutura na kora da ruwa mai dan sanyi,
Sannan na dauko wasu English wear dogon riga mai kamar dinkin yan Brazil's nasa na kara murza turare a sassan jikina ko ina,
Dogon gashi na baki da yasha kitso nadan gyara parking din shi baya da kya,
So sai na yi kyau don na kai wani lokaci a,gaban mirror ina kallon kai na,,
Nai mamaki kwarai da irin canjin da naga nayi a lokaci guda,
Da alwala na ajikina don haka time din sallah na duba yanzu karfe bakwai saura,
Sallah na tayar na zauna gurin ina lazumi bayan na idar nakai wani lokavi ina ronkon Ubangiji Allah saukin al,amura,
Har zuwa takwas banji shigowan shi gida ba amma hakan na tabbatar min da ya dawo daga fitar da naga yayi,
Don Anty ta tabbatar min dace kada inyarda in kwanta duk dare batare da nai masa saida safe ba,,,,

****** ********* ******
Ya Abubakar yana shigowa falon kule gida ya fara yi don yasan bazai sake fita ba again,
Ledar dake hannun shi ya nufi dining table ya aje ,
Anan idon shi yai arba da kulolin abincin dake saman table din, sabi fil da su,
Kamar zai wuce sai kuma ya daka yadan bude kulan a hankali,
Tuwon ne kulle a leda sunyi nason, zufa sai daukan ido su ke yi,
Da sauri ya mayar ba tare da ya tsaya bude na miyan ba,
Ya na shiga dakin shi ya fada wanka yadan dauki lokaci yana wanka don dabi,ar shi ce dadewa a bayi,
Wata farar tie shirt mai rubutu ja cikin harshe China, dan gajer hannu ke ga rigar, ya saka ,da wando, iya gwiwa kafar shi,
Dining din yanufa kai tsaye, shigar shi bada dadewa ba ,
Sadiya tafito daga dakin ta tana wani yatsune fuska,
Ala dole fushi take yi ita don komai bata ce mashi ba illa plate din da ta jawo da niyar zuba abincin,
Bude kulanta ke da wuya tai arba da lafiyayyen tuwon Semolina da na tuka, acikin leda,
Da sauri ta bude miyan miyar kubewa tagani shima yana tururi ga stwe a gefe guda,
Ta ce ashe ana sayar da irin tuwo haka shi baka siyo muna shi sai yau
Mamaki ta bashi don jin ko may tace, mai, mace kamar ta wai sai karamar bata iya girka ko da kwatan kwacin haka ba, gashi karamar yarinya ta girka har tana son yin sallo akai,
Tambaya ya jefo mata adaidai lokacin da zata fara diban abincin,
Ita wacan yarinyar da ta girka ta ci ne ?
Cak ta tsaya da spoon din a hannun ta , taji tankar ta aje plate din abin cin tace ta fasa,
Sai dai idan ta aje may zata ci gashi kuma tun bata ci ba kamshi duk ya rufe ta,
Cikin dakewan murya tace ban sani ba don banda labari a kan ta ,
Mikewa yayi da zuman zuwa tambayar Meena din,
Tun da ya tunkari sashen yaje jin wani irin kamshi na tashi
Da kamshi turare da yafi rinjaye da kuma kamshin fentin kayan gado,
Dakin yabi da kallo irin yadda ya ga an gyara shi tankar ba acikin gidan shi dakin yake ba,
Alamar tana bayi yaji don haka ya koma inda ya fito,
Ina fitowa daga bayin kamshin turaren Ya Abubakar ya daki hanci na,
Wanda hakan ya tabbatar min da cewa ya shigo sashen nawa, badadewa ba,
Godiya nayi ga Allah da bai samay ni ba, a lokacin don ban san ya zanyi ba,
Falon na nufa don in gaida su da yini,
Tun daga nesa na hango shi zaune saman kujera da waya a hannun shi,
Anty Sadiya ce ke fitowa kitchen daga gurin kawar da kulolin da tayi,
Tana saye cikin dogon rigar atamfa mai budaden kasa, duk da dare ina iyagane kodewar rigar,
Tun sanyo kaina acikin falon gaba daya ya mai da hankalinshi gare ni,
Ya zuba min idanun sai kace yau ya fara gani na a duniya,
Wani irin nauyi da kunya ne suka lulubeni a lokaci guda da kyat nake iya takawa,
Har na karaso gaban shi na samu gefen kujera na tsugun na acikin ladabi na bude baki a hankali nace,
Yaya Ina wuni,?
Da kyat ya iya bude baki ya ansa mata, gaisuwan nata,
Daga haka na juya gurin da Anty Sadiya take tana kokarin zauna daga gefen shi,
Nace Anty Sadiya ina wuni?
Lafiya kawai tace a takaice, hakan yasa ban kara tanka mata ba,
Mikewa nayi da zumar inbar falon amma sai naji muryan Ya Abube yana cewa dawo ki zauna tukun,
Still gurin da natashi kasa gefen kujeran na samu guri na zauna,
Shiru nadan wani lokaci can ya bude baki da kyat acikin muryan nan nashi, yafara da cewa
Alhamdullahi na godewa Allah da yada ni da ku a matsayin abokan zamana,
Maganar da zan fada maku anan shine bana son jin fitina ko kadan agida na,
Nagaba ya tsaya a matsayin shi babba ke kuma karama ki tsaya a matsayin ki na karama,
Bazan so daya daga cikin ku ya tauyewa dan uwansa hakkin shi ba ko kadan,
Kamar yadda ni ma nake rokon Allah akan yabani ikon baku hakkokin ku,
Magana ta karshe shi ne kada kuji ga wani ko wata taga cewa ban mata daidai ba,
Nan da wata biyu zan kara aure insha Allah, da wata yar nan garin,
Da sauri Anty Sadiya ta dago kai tana duban shi cikin mamakin jin abinda ta ce,
Yaci gaba da cewa ina fatan zakuyi amfani da duk maganan dana fada maku da kunnen basira, ku zauna lafiya atsakani har ita wacan da zata shigo, cikin, mu,
Sai kuma ku raba yadda zaku dinga raba girkin ku don inji,,,
Har zuwa lokacin ina zaune akasa kaina kuma na duke saboda bazan iya daga kai in kalli gurin da yake zaune ba,
Shirun da yaji duk mun yi yasa shi dago kai daga amfanin da ya keyi da wayar shi a lokacin
Yace cikin kara dukar dakan shi ga abinda ya keyi,
May kuka yanke ne akai,
Muryan Anty Sadiya ce ke cewa kwana guda guda zamu dinga yi
Ok hakan yayi maku ko ?
Yana mai kallon Meenat wace kanta ke kasa amma ta daga kai alamar eh
Ok shi ke nanya ce,
Mikewa nayi a hankali nabar gurin cikin irin tafiyana mai kama da rangwada,
Bayan ta yabi da kallo acikin msmaki zuciya shi taf da tunane barkatai akai



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/22, 9:26 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-QAABID


Yan Uwa masoyya novel din, TARKO, duk inda ku ke ina maku fatan alheri,da fatan gamawa da duniya lafiya,
Yan uwa Kusani cewa duk mutum dan tare ne bai cika goma ba,
Masu cewa ina ma mutane wullakanci,saboda Allah akwai wace zata fito filli karta boye tafadi irin wullakancin da naiwa wa wata ko wani,
Sam, sam wanan niba halina bane, wukanta dan Adam,
A haka ne fa Allah ya nufi ku san ni ta gurin novel,
To akan may kuma zan,wa Allah butulci har in ma dan uwa na abin da ba daidai, ba
Idan ma har nayi a cikin rashin sani ne ku yafe min don girman Allah,
YANZU WANNAN LABARIN YA FARA DON DA FARKO SHIMFIDANE NAGODE NAGODE =?O?=?O?

Shigewar ta a cikin corridor din yai daidai da ajiyan zuciyar shi,
Sadiya wace ke daga gefen shi ta waigo shi da sauri a cikin mamaki,
Tambaya ya jefo mata wanan yarinyar diyar Baba Samaila ce ko kuwa rikon ta yake a gidan,?
Wani wawan kallo ne ta jefa mai tana ko karin ta mikewa tsaye don barin falon saboda haushin da ya bata, a,lokacin,
Daga gurin da take tsaye tace, kai da mutane gidan ku baka san, su, ba sai nice zan san su,
Fuuu ta wuce zuwa ciki ita, ma, ba tare da ta tsaya sauraren maganar takai cin da yake ko karin yi mata ba,
Dama ta zauna ne agurin don suyi zancen auren da ya,ke fada mata cewa wai zai kara in two months coming,
Bai,damu da tafiyan ta ba illa tambayar dake cin zuciyar sa a,yanzu,,
A cikin diyan gidan su kaf a,she akwai wacce tai wayewar haka kuwa ?
Akwai wacce ta kara gaba da karatun ta ke nan ake nufi ko kuwa, ?
Amma kuma dai wanan yarinyar ai tana da zubin irin na mama Saratu matar Baba Samaila,
Hannun shi yasa ya shafo kanshi zuwa habar sajen shi,
Daga haka ya fara wasa da yar sajen daya bari a fuska don fashion,,,
Wa zai bashi wanan ansa ne wai don Allah, da kunya ace wai har zuwa yanzu bai san komai ba akan matar da ya aura,,,,

****** ********** ******
Naira hamsi kawai ke a,cikin aljihun shi da ita kawai ya kwana,, ya wayi gari da ita kuma,,
Yau mama Sa,a ce da girki a gidan shi gashi dole ya samo kudin cefane ya bata,
Saboda ita bata da samu kamar mama Ladi wace abubuwa ke shigo mata, tako ina,,,
Ya duba sashen dan uwan shi, mai tallafa mai baba Samaila,
Ance bai kwana gida ba mota ta lalace mai a,daji da kanyan mutane a cikin, ta,,,
Don haka ya mike hanya zuwa gidan wani aminin shi da ke Rafin Atiku,
Atare, su kai wasan kasa lokacin kurciyan su shi da malam Sani
Sai shi malam Sani ya fara bin wani dan kasuwa zuwa lagos fataucin shanu,
Da haka har Allah yasa ya zama wani abu a rayuwar shi yanzu yana da shaguna da kuma tifan kwasan yashi da ake mai jigila, da su,
Baba Buhari ya yanke shawaran ya taka da kafa don ya je Rafin a
Atikun, gidan aminin nashi,
Cikin rashin, sa,a bai samu malam Sani a gida ba,
Don haka ya koma can gefe guda yamma da gidan malam Sani yasamu innuwar iccen darbejiya, (Leem) ya zauna don ya huta gajiya Don dai ko ya koma gida bai san yadda zai yi ba, don babu shi,
Wani dan uguwar su ne da a,kecewa, Audu,fari, shine yazo wucewa da mashin din shi ya gan shi zaune
Audu Fari ya ja ya tsaya don ya ji ko lafiya ya gamshi anan uguwar,
Bayan Sun gaisa ne yake tambayan shi ko lafiya yake nan, ?
A,a lafiya lau malam Abdullahi da ma wurin Sani na zo gashi kuma baya nan wai ya fita,
To idan ka tashi muje in rage maka hanya ko don gida zan tafi, ?
Kamar yace ya wuce sai kuma ya ga cewa, ai kawai gara ya hau don kar ya kara takawa karo na biyu kuma,
A hanya suna tafe saman mashin din Audu Fari, suzuki yar tsohowa,sai wani kara takeyi,
Baba Buhari yace, wlh malam Abdullahi yau garin ba dadi sam,
A, har da ku malam Buhari kar dai in ce ko maganar mutane gaskiya ce, ?
Da a,ke cewa Dan ka yayi kudi amma sam bai taimakon ku,
Dashi da matar shi basu barin kowa ya rabe su wai ,
A salima dai babu ko dan uwa da ya ke zuwa gurin su,
"Kai, Baba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login