Showing 39001 words to 42000 words out of 388021 words

Chapter 14 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8221

matuka,
Kai kawai ya iya gyadawa a lokacin tare da cewa jeka dai Wadda am na gode,
Ya mike yana cewa mahaifin nashi mu yini lahiya ba,
Allah shiba da sa,a da rabo na alheri, inji tsohon wanda duk yaron da yazo sallaman shi don zuwa gurin aiki, ko wani harka, hakana suke samun wanan adduan daga bakin shi,
Wanda su kuma al,umman gidan wanan adduan na masu dadi don ko fita za su yi za kaji yara na cewa mu je gurin baba neman tubarki,,,,

****** ******* ******
Shakuwa mai karfi ne ya shiga tsakanin Abubakar da Salawatu zuwa yanzu,
Shakuwar da har takai dan uwa idan baiga dan uwa ba zai iya shiga damuwa sosai,
Kusan zuwa yanzu mutane sun san wanan alakar dake tsakanin Abubakar da salawatu din,
Abu guda,ne shine Abubakar bai iya aikata alfasha a waje ba sam ,
Don duk yadda salawatu ke kokarin gwada mai hanyan lalacewa sai ya nuna mata tankar bai bahince ta ba,
Haka yasa tafara shiga cikin halin damuwa saboda tana ganin cewa ba zata iya samun abin da take so ba,
Don dai a zaton ta na ganin cewa, Abubakar ba zai taba auren ta, ba,
Hakan ne ya kara tayar mata da hankali sosai, har ta fara shawaran shiga malaman Abuja,,
Ranan da ta fara zuwa gurin malamin ta don ai mata aiki,
Tun kafin akai ga aikin da ta bayar din ai mata sai ga dan halas din na cewa,,,
A lokacin da suka kama hanya don zuwa gida bayan sun tashi daga gurin aiki,
Abubakar wanda ke tuki tankar yana tsoron sitiyarin motar
Fuskan shi na kallon titi inda kira,a ke tashi daga cikin motar nashi,
Salawa ya kira sunan a cikin wani irin shaukin so da kulawa,
Itama amsawa tayi batare da ta kalle shi ba cikin wani yanayi,
Tambayar bazata ne ya jefo mata alokacin da cewa,
When are we getting, marriage ?
Sai da Salawata gigice don jin wanan tambayan da Abubakar ya jefo ta dashi,,,
Hannu takai ga gaban ta tana kokarin nuna kan ta da yar yatsar hannun ta alamar ita, ? Yake nufi, da zancen aure,
Kai Abubakar ya kada cikin nuna alamar eh yana mai lumshe mata idon shi masu kama da yana jin laziness,
Yau don jin dadi Salawatu bata iya cewa Sir din ba sai cewa tayi
Abubakar kana nufin zaka iya aure na, ? yanzu haka ?
Yes,
Of course
May ya yasa kike mamaki ko zan iya auren ki ?
Sai a lokacin ta dan hada natsuwan ta a guri daya san nan ta dan kalle shi acikin kunya tace,
Naga most of the hausa fulani Guy's basa aure haka a waje da wuri,
Sai dai su yi a gida a cikin dangi,
Waya fada maki hakane ?
Kawai a kwai dalilin da yasa mutane su kafi yin aure a garin su,,,
Wani dadi har acikin ranta ya ratsa ta don hakan ta ya kusa cin ma ruwa ke nan, very soon,
So daga yau ina fatan zaki zauna a cikin shiri don any time aure zai iya zuwa,
Kunya taji don jin zancen shi don haka sai ta dan dukar da kai tana wasa da ya tsun hannun ta
Jin tayi shiru yasa Abubakar kara jefo mata tambaya da cewa ko
Ban isa in aje irin wanan madam din a gidana bane ?
Kai haba Sir wace ni da zance ma haka ?
Kawai dai ban san bakin da zanyi ma godiyan hakan da shi bane,
Ki aje wanan godiyan naki har ki shigo hannu na ina ga zai fi ai,
Dariya da yar kunya ya bata wanda ya sa ta saurin rufe,fuskan ta da hannun, ta ,,,,,,,,

****** ******* ******
Zaune suke a saman wani katon tabarman kaba,mai mai ruwan kala,kala,
Duk da yake zuwa yanzu sama sama suke da junan su ba kamar da ba da suke kut, da kut,
Mama Ladi wace ta wanko takalman ta har zuwa gidan Hajja din don su tatauna akan yaran nasu ma,auratan juna,
Mama Ladi din ke cewa Hajja gani nayi ya kamata ace mun san abin yi akan yaran nan haka kafin idan mu dangin uban shi masu tsurku su fara tofa miyon su akan abin da bai shafe su ba,
Don ke ga matan yaron ga dan wurin shaibu gashi ammare, jiya, jiya ga ciki Allah ya basuwa ankai ga ribar ammare,
Kai ke ji min Ladi da wata magana shin cikin ga ni ka basuwa ko Allah ka basuwa, ?
Da zaki taho na, nanga da wata magana mara dadin sauraro,
Walleh da nasan cewa wagga magana ta at, tahe dake da ban tsaya sauraronki ba,,
Shin Hajja maganan ga da na taho da ita ba maganan da aka zama adubata ta ba ?
Ammre shekara kusan shidda ace ba wani karuwa acikinai ?
Gaskiya nikan na hwara shiga maganar da nikawa mutane ruhwa ruhwa, (rufa,rufa) akanta
Don yanzu banda abin cewa in ana wagga zancen a gabana,
Abin da kashrin faruwa ne nazo maki akan zancen shi,
To ba sai ki tai ke da mutanen gidan naku kuyi abinda Allah bai tashi yi ba,,,,
Mama Ladi , wace bata taba data sani ada na hada auren da tayi tsakanin dan ta da diyar Hajja din,
Auren da yanzu ta ke jin dan wani iri akan shi duk da dai duk sallah ko azumi sai Hajja ta kawo mata, garan sallah gudan mai yawa,
Duk da ba aikawa wasu Abubakar din takeyi da kayan ba,
Kayan garan kamar su shinkafa, mangyada manja maggi gishiri dadawa, gero da masara, duk a matsayin garan sallah wa yar ta sadiya,,,,,

****** ******* ******
Kusan dangin Anty amarya duk sun san Meena yar albarka kamar yadda suka lakaka mata sunan,
Meena yatinya ce mara girman kai ga aiki ga sanin ya kamata, ga girmama na gaban ta, duk yadda yake,
Wanan halin ne ya jawo mata samun farin jini da kuma alheri ga yan zurian, su anty amaryan,din,
Gama secondary din ta uncle din ta ya samo mata guribin cigaba a Shehu shagari, COE,
Ba bata lokaci Meena ta fara karatun hankali kwance,
Hakan ne ya jawo mata rashin zuwa gida birnin kebbi a kai,akai,
Yanzu takan dauki lokaci mai tsawo batare da ta je ziyara gida ba,
Badon komai ba sai don gudun irin hassadan da mama ladi ke yawan gwada masu ita da iyayenta a fili karara,,
Ga habaici da suke mata wai bata isa ace ta kare, karatun ta ba shi ne za,ace takai har gaba da secondary,
Wanan abin da mutanen gidan su ke ya,wan nuna mata idan ta je kebbi din shi yasa sam yanzu bata faye son zuwa can din ba ,
Sai dai in dogon hutu a,kasamu zata iya zuwa tayi kusan rabin shi a can din,
Zuwa yanzu da girma yazo mata har yakai Meena ta fahinci irin kiyayyan da mutanen gidan su ke nuna ma mahaifanta,
Tagane cewa kishine kawai irin na matan hausa ba komai bane sai yan ubanci,
Saboda mahaifin ta ya kasance shi daban ne daga shi sai gwagon su wace ke aure, a kalgo,
Wanan dalilin ne kawai ya jawo wa, masu bakin jini harsu,
Acewan mutanen gidan wai malam bai taba auren macen da yake so kamar kakan su Meena ba sai kuma Allah bai mata tsowon rai ba ta rasu,,,,,
Jin wanan dalilin yasa Meena tafara kenkeshe idon ta ga duk wani mai kawowa iyayyen ta suka da sara akan rayuwan su,,,
Zaune take a gaban mirror dakin Anty amarya tana kwalliya don yau ba kara tu
Abdulhamed saurayin ta zaizo kawo mata ziyara kamar yadda yai alkawari zuwa,
Tsab tafito cikin wani dinkin atamfa masu ruwan blue da ratsin fari ajikinsu,
Dinkin buje da riga ne akai masu wanda ya fitar mata da surar ta tsab,
Ita kanta ta yaba da wanan kwalliyan da tayi don sai take gani kamar ba ita bace Meena diyan gidan baba Samaila,
Anty Amarya ce ta shigo dakin tana cewa, a,a a shin wata,ta an nan,?
(Wacece nan haka) ?
Murmushi Meena tayi alokacin da take kokarin dauko zumbodeden hijab din ta fari don ta sa,
Shin me zakiyi kuma da wanga hijaba,?
Makin kisa gyale don kara fito da ke shar shar da ke ya,
A,a inji Meena walleh anty am ban iya fita dashi ko nan da kofan gida da gyale,,
Don ji nike awa ban rufe jikina ba sam kamar haka na nake tafiya,
Ke kinka sani da halinku na diyan gidan malamai,
Murmushi meena tayi alokacin da take zumbuda hijabin nata, a wuyan ta,
Zaune yake a cikin motar shi kafa guda waje yana dan dane danen a motar,
Assalamu Alaikum tace acikin muryan ta mai kama da busa sarwan sharo,
Firgigit Abduhamed yadawo daga abinda yake yi amotar inda ya dago kai da murmushi yace,
Ameen wa alaikis salam giyabata,
Yar murmushi Meena ta sake cikin jin dadi tana cewa karaso mana daga can waje,
A,a Meena ai nan ma yai min ki zagayo ki shiga mota kawai ki zauna ko ?
Kai ta girgiza mai alamar a,a tana cewa ai na fada ma ba darajata bane shiga mota yin hira,
Murmushi Abdull din yayi don sanin irin ba,hagon halin meena don dai ita kulun takar mutumiyar da take,
Bata taba nuna waye wa ga al,amarin ta sam,
Sai dai ta nuna gidadanci,
Ok tunda hakakike so ba matsala ai barin fito mutafi can din,
Kafin duk yafito a motar har meena ta juya da sauri ta nufi gurin don gudun kada ta ya ga tafiyan ta,
Murmushi Abdullahameed din yayi don ya gane nufin Meena din,
Nisa kadan ta zauna akan saman tabarman da ta shimfida mai,
Inda take wasa da dan wani kara a hannun ta,

****** ******* ******
Shiri sosai Abubakar keyi wa wanan tafiyan dake gaban shi don a kwai abubuwa da dama da yake kokarin yi idan yaje,
Saboda kasancewar shi na wanda ya dade bai zo gida ba sai dai yayo aike kawai ga wanda Allah ya ba rabo,
Ga labarin da yan uwa ke ji akan shi cewa yazama wani irin baba a ma,aikatar su, matsala dai guda ne rashin kula gida da yan uwa da baiyi,
Yasan cewa idan yazo zasu kwashi rikici da dan tsohon kakan nashi sosai don dai yasan cewa shi mai laifine sosai agaresu,
Ga kuma sabon zancen auren da zai zo masu dashi don su tafi agabatar da komai acan kauyen salawatu dake cikin jahar nasarawa,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/12, 6:28 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 8?

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

ALLAH-AL-MUHAYMIN,,,


Tuki yake a cikin natsuwa, da gwanin ta, sai dai hankalin shi na ga irin yadda zai tunkari mahaifan shi da zancen karin auren da yake son yi,
Musanman mahaifiyar shi mama Ladi wace yake gani tankar tama fi son matar shi Sadiya sama da shi,
Hannun shi ya daga guda ya shafo kyakyawan fuskan shi dashi tare da sauke ajiyan zuciya mai karfi,
Abubakar Buhari Birnin Kebbi kenan kyakyawan matashi mai,tashe ga kyau ga ilimi, ga Naira ,,,,
Daidai kofan gidan su inda malam tsoho kakan shi, da jama,ar sa suke zaune suka daukan karatun marance,
Duk wanda ke gurin a lokacin idon shi naga wanan kyakyawan bakar motar da ta tsaya a kofan gidan dattijon malamin,
Sannu a hankali ya bude motar inda ya sako kafar shi guda waje yana kokarin dauko wayoyin shi daga gaban motar,
Kafar shi kawai ya isawa wanda ke gurin ko waye zai fito a motar mai, ji da kansa ne,
Fitowar shi daga motar gaba daya yasa mutanen dake gurin gane cewa ai Abubakar ne, watau (mai sunan Malam),
Ai nsn take mutane suka gane cewa shi ne kusan gaba daya suka tashi zuwa mashi murnan da barka da zuwa,,,
Malam tsoho wanda ke daga zaune yana biya wa wani tsohon bafillace karatu,
Sai murmushi yake yi yana gyada kai don jin dadin ganin yadda jikan nashi ya koma a lokaci guda,
Direct daga gurin da masu taron shi suke, gurin tsohon ya nufa,
Takalman da ke a kafan shi yake kokarin cirewa don girmamawa,
Wanan ya,na daya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? daga cikin dabi,un duk, wani yaron gidan malam Manya,
Babba da karami dole ne idan zaka wuce ta gurin ka cire takalmin ka,
Cikin jin dadin ganin jikan nashi bai yarda tarbiyan gida ba,
Yake dan yake fararen hakoran shi wanda akasarin jikokin gida duk shi suka biyo, da fararen hakora, da kyau,
Abubakar kai ne tafe babu labatin zuwan ka a yau din,?
Murmushi yayi ya cewa kakan nashi nayi marmarin ganin ka ne malam shi yasa na taso don in duba ka,
Nan ya samu gefen tabarman da malam din yake, zaune,
Gaisawa sukayi a cikin girmamawa, inda malam yace ai sauri a shiga gida wurin maman Wadda a karbo ma Abubakar ruwa da fura,mai sanyi,
Ga mamakinbmalam tsoho sai ga Abubakar ya sha kusan rabin kufin furan da aka kawo mashi,
Wani sabon gaisawa suka kara shiga yi inda yake tambayan shi lafiyan mai dakin shi da kuma gurin aikin shi,,,

****** ****** ******
A can cikin gida kuwa labarin zuwan Abubakar ya iske mama Ladi wace duk ta kasa boye farin cikin ta afili,
Sai, rawan jiki ta,keyi tana cewa a yi sauri a aje a anso mata dan drinks ta bashi da kuma sakon abin miya wanda zata dafa mai abinci,
Duk da idan yazo daga ko wani sashe na gidan a na kawo mashi abinci, har izuwa ranan da ya tashi komawa,
Amma duk wanan bai sa mama Ladi ta daina dafa mai abinci da kanta,ba idan yazo,
Da sauri ta tura yaro gidan su Sadiya matar shi gurin Hajja don a sanar da ita,
Hajja tabawa yaron Naira hamsi wai ya sha Sweet da shi idan ya koma,
Yaro ya koma da murnan shi gida ya na, farin ciki,
Bai nuwa mama Ladi Naira hamsin din ba don yasan idan ya nuna mata zata iya cewa suraba shi da ita,
Sai bayan Sallah isha,i Abubakar ya shigo cikin gidan don ya gaisa da mahaifiyar shi da sauran, mutanen gidan,
Nan fa yai ido biyu da jerin kwanonin abincin da aka aiko mai da shi daga kowa shiya na gidan
A hankali ya samu gefen tabarman da aka shimfida mai,a tsakar dakin na mama,Ladi ya ksi zaune,
Cikin murna da farin cikin ganin dan nata take cewa,
Mai sunan malam kana tafe shine baka sanar da kowa cewa kana saman hanya ba,
Sai dai kawai mu ka gan ka kwatsam ba tsanmanin ka a yau din,
Murmushi yayi don yasan cewa duk a lokacin da mama ta ganshi tana cikin farin ciki da jin dadi,
Shima haka yana jin dadin kasan cewa mahaifiyar tashi sosai duk yasan cewa wasu daga cikin halaiyan mama tun suna yara baida dadi sam,
Tambayar shi mama tayi labarin matar shi Sadiya,
Tana cewa har yanzu dai shiru a gidan ka mai sunan malam ?
A hankali ya dago kai ya dube mahaifiyar wace ta tsura mashi ido don jin ansar da zai bata,,
Yadda ya kalli mama sai ya bata tausayi don ko bai yi magana ba tasan cewa ba wani ansa gamsasshe daga bakin shi,
Murmushi ya danyi tare da cewa mama har yanzu dai muna baran adduan ku ,
Akan Allah ya kawao muna mai albarka insha Allah,
Daga haka Abubakar yajawo daya daga cikin kulolin abincinbdake a gaban shi wanda yasan cewa,shi aka ajewa wanan abincin,
Mama dake gefe tace cikin sauri a,a aida ka dakata har a karasa abincin da nasa Samira ta dafa maka,,,
No, mama ki barshi kawai wanan din ma ai is Ok,
Kawai dai dama ina son cin abincin gida ne wanda nai missing dadewa,
Kai idon mama taga ko wani kulane yajawo sai idon ta ya sauka akan kulan da mama Saratu ta aiko mai dasu,,,
Kai, mai sunan malam ga kuloli da yawa masu dadi zakaci wanan ?
Yace cikin kai hannu ga kulan da ya bude din yana cewa,
Wanan din ma ai zai yi mama bari kawai inci, don bada yawa zanci ba,
Tuwon dawa, surfafe ne, da miyar karkashi danye, wanda yaji nama da man shanu,
Fuska mama ta daure don jin haushin daukan kulan sashen Baba buhari da yayi,
Daga sunan kadan zaici sai ga Abubakar ya buge fiye da rabin kulan abincin,
Ganin irin yadda ya kwashi wanan girkin da mama ke dauka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login