Showing 315001 words to 318000 words out of 388021 words

Chapter 106 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8222

inda yake naga ta daga pillow ta aje, Hijab dinta da wani abu,
Tankar bai san shigowan ta dakin ba yake cewa zauna mana Meenatu ina zuwa na saka kaya kama min yaron,
Na karbi yarona tare da bin umurnin shi na zauna a bakin gadon kamar yadda yace min,
Zaka sha tea din ne yanzu na hada maka, fatima ce ke tambayan shi hakan ?
Sai kokarin saka kayan shi yajeyi batare da ya kalle ta ba balle ya bata amsa,
Amir ne yadan yi kuka irin nasu na yara da akecewa mafarki,
Da sauri naga ya juyo a lokacin yana kokarin saka bottoms din rigar shi,
Yana cewa yaya dai may ya samay shi kuma yake son tashi daga barcin, ?
Kaina nadan girgiza nace jiki a sanyaye don irin yadda naga ya basar da Fatima sai banji dadi ba duk da dai nasan cewa laifintane tunda tasan ina dakin ta shigo,
Nace babu wani abinda ya samay shi illa sanyin da yaji yana ratsa jikin shi kasan can mun saba da zafi ne,
Sai ina kokarin gyarawa yaron rufi jiki da towel din dake hannu na,
Gami da dan shirin mikewa tsaye daga zaunen da nake alaman zan bar ldakin,
Cikin mamaki ya kallo ni yana cewa ina kuma zaki ba nace ki jirani na zo ba,
Dole badon naso ba na koma na zauna ina kallon ikon Allah, har ya gama kimtsawan, shi,,
Yazo gab da inda nake zaune tare da miko hannun shi yana fadin bani yaron in kara daukan shi,
Ba bata lokaci na mika mashi shi ya rugumay yaron tsan a jikin shi yana mai furta Alhamdullahi,
Ya dan juyo yana cewa yanzu yakai wata hudu, ko da haihuwa ?
Nadan murmusa tare da dan gyara zama nace saura dai yan kwanaki mikai four months din,
Ban idar da zancen da zan fada mai ba naji muryan Fatima tana cewa na tambayeka yanzu zaka sha tea din kane ka kyaleni,
Yace sai kin koma kin koyo yadda ake sallama kafin nabaki amsa, ai don naga mutane kika sama adakin kika shigo babu ko sallama,
Tace cikin wani irin murya mai nuna fusata aini ban san cewa suna nan bane,
Tare da kawar da kanta gefe guda cike da jin haushi tana cewa, ciki, ciki wanan ma ai rainin wayyone wallahi,
Nace amma gaskiya ginan gidan nan yayi kyau sosai wallahi sai mutum ya ratse cewa ba wanan plan din a ciki,
Sai da ya sakar min wani tsadaden murmushi, wadda nasan cewa dawuya yai irinshi a banza,
Yace cikin dan kwantar da murya yana kokarin dago yaron daga kafadan shi,
Ke nan tsarin yai maki kyau sosai ko ?
Sai,da na mike tsaye nake cewa ai abin ba,a cewa komai kawai,
Na mika hannuna da niyar karban yaron don na basu guri ,
Yace No kibarshi idan zan kwanta sai na kawo shi cikin murmushi nace magani dama nake son na bashi,
Don naji jikin shi kamar da dan zafi zafi, kila gajiyan tafiyane
Ok zan sauko yanzu ai sai na karasa jin labarin gida ko,
Tsuki taja mai karfi kamar wace wani abu ya sama inda gaba daya muka juya gurin da take tsaye tana zuba ruwan zafi a cup,
Nidai na karbi yaro na, na fito kawai abina inda na barsu can ,
Ina fita daga dakin banko kai ga rufe kofa ba naji muryan Fatima tana cewa cabdijam ashe ko akwai magana ke nan a gidan nan,
Tankar da dutse take yi don ko motsi baiyi ba, sai kallon wayan shi da hankalinshi ke akai yakeyi,
Taci gaba da dan magana irin na mata tana cewa gaskiya ita bazata dauki irin wanan ba wallahi,
Ita indai har ance haka za,a yi to da magana ke nan a gidan,
Wani irin tsawa ya daka mata yaba maicewa Ke, Fatima ban son raini kin sani,
May kike nufi ne ke ?
Ko wa ki kafi da zaki ce ba macen da zata shigo gurina idan kina duty,
Ke da kike fita kuma ki shigo har nan ki ce min kin dawo ko bakece da duty ba fa,
To barin fada maki ya isheki hakanan don ban son yawan fitina wallahi,
Shike nan don ana tsoron ki duk da sun dawo kada tazo ta gaidani ,
Saboda gudun zuciyar ki ko may kike nufi da wanan maganan,
Ko so kike ta tsaya a gaban iyayyen mu muna maganan da ya shafi rayuwan mu,
To ki shiga hankalinki na fada maki ,
Ai kin san ina da iyali ki aure ni a hakan, balle kice zaki kawo min wani kishin ki can na bazan ki kafa min doka a gida,
Kina nufin cewa duk wace keda matsala baza ta zo tagani ba personally, don kada ran ki ya baci,
Har na sauka kasa Yaya yana ta surfa mata jidali inda tai shiru don tasan ranshi ya baci ne da yawa hakan,

****** ********** ******
Tunda safe shi ya buga muna part din mu don yai muna sallama don jirgin safe zai bi zuwa Lagos,
Sunyi sallama da kowa inda ya ce min zai bawa Lawal sako yabani aba ma Anty Amarya da zata wuce bai gari,
Mikewa yayi tare da tambayan ina Amir aka bashi amsa da cewa yana daga ciki yana barci,
Dakin kwanan nawa ya shiga don yaga yaron da ido Anty Amarya taimin signal da nashi ciki,
Na samay shi a duke yana dan taba kumatun yaron dake barcin shi cikin jin dadi,
Jin motsina da yayi yasa shi dan juyowa a hankali,
Yayin da naji ya wani sake ajiyan zuciya,gami da fesar da wata iska irin mai saka relief din nan,
Ban aune ba naji ya rugumoni izuwa jikin shi yana kai min kiss ta ko ina,
Da kyat na samu muka samu natsuwa inda ya harde hannayen shi a cikin nawa yana cewa,
Dan Allah ku kula da kanku da bakin mu Meenatu har zuwa lokacin da zandawo,
Duk abinda kuke bukata ku fadawa Lawal zai yi iya kokarin shi insha Allahu,
Ban son jin fitin ki da ko wace mace a gidan nan har indawo please,
Duk abinda ya dace kiwa Anty Amarya na sallama don Allah ai mata kuma ki kara yi min godiya a gurin ta,
A take naji wani iri araina tankar kada ya tafi ya bar mu amma ina tafiyan nan ba fashi don mai muhinmanci ce sosai,
Yadan kai min kiss a kumatuna yana cewa take care please Allah sada mu da alherin sa,
Na amsa ciki ciki da fadan Ameen ya Allah Allah ya tsare hanya aje a sa,a adawo a sa,a,
Ya amsa cikin jin dadi da fadin Ameen maman Big man,
Daga haka yafito inda ya kara yin sallama da su Mama Dije ,
Yaron nafito dashi a kafadana saye da wani katon hijab har kasa mukai mashi rakiya,
Gaba daya gidan kowa, yafito zuwa kofan gida gurin motoci don raka maigidan,
Anan ne naga yaran Fatima du biyu da alama daga barvi suka tashi ko kuma antada sune,
Ya tsaya yana magana da Salawatu inda Fatima dake tsaye rike da hannuwan yaranta tace Bukar zancen makarantan yaran fa,
Sai ya juyo yana fuskantar ta yana cewa Lawal zaiyi komai insha Allahu zai kaisu ai madu interview, nabar zancen ai a hannun,shi,
Tace OK Allah ya tsare hanya ke nan sai ya juta gurin Sadiya yana cewa, na bar makullin motan da zaku dinga amfani dashi a boye sauran har na dawo,
Yashiga mota kowa na fadan Allah ya tsare har mota tafara tafiya sai suka tsaya yana cewa nazo
A hankali kamar mai tafiyan dawisu na tako har zuwa gefen window da yake na dan tsaya ce min yayi
Kikulamin da matan malam fa kinsan tsohon dadi yake bata acan,
Lokaci daya mukasaka dariya dani dashi abinda ya bakanta rayukan mutane da yawa ke nan,a gurin,,
Ina wuta a sakani yayin dana dan dago kaina ina kaucewa motan su da fara fita get ina maiyi mai Allah ya tsare har suka tafi,,
Mama Sa,a da Mama Dije suna kallon ikon Allah, gutin maran Yaya Abubakar inda Sadiya take dan masu ina kwana a tsatsaye,
Salawatu ta karaso har inda nake ta dan lakuci kumatun yaron da ke barci tana cewa kai dan masu gida barci kake har mahaifinka ya tafi baka bude ido ya ganka ba,
Fatima wace take magana da yaranta ta wani juyoyo tana cewa kuzo mu shiga in hada maku break ko ba,a so dai kuna nan daram, dakwam,
Mun fahinci cewa za,a rikice tunda an fara sakewa juna zance don haka
Da guda guda muka fara, shigewa, cikin gidan abin mu ida muka koma part din mu,
Baba Ramatu ta gama hada muna breakfast lafiyayye har ta aje wa kowa inda ya kamata,
Bayan mun gama karyawa ne mu ka fara, raba tsaraban da mu ka zo da shi, daga Birnin Kebbi,
Man shanu kowacen su saida na bata dan karamin galon din shi daddawa kuka busassan kubewa, garin masara, fara kal, shinkafan yin dambu, kayan yaji da abubuwa da, dama,
Baba Ramatu ce ta ke kai wa kowacen su nata a cikin vacco bag, baka,
Na karshen da ta tafi dashi ne sai gata ta dawo dashi wai Fatima tace bazata karba ba,
A daidai lokacin Sadiya ta shigo dakin tana cewa tsarabane muka samu mai yawa haka,
Mama Dije ke cewa Amaryan ku tace a dawo dashi wai bazata karba ba , ita,
Tabe baki Sadiya tayi tare da dan jan tsuki tana cewa wanan ai bata da dadi don ko ke wace bata karban abu a gurin kowa,
Halin ta wallahi baida kya bata da dadin al,amari ita kanta kawai ta sani da na yaran ta,
A she ko akwai aiki ke na don irin wanan halin a gidan yawa baida amfani don wata rana a cikin mutum halin ke komawa,
Andauki dan lokaci Salawatu tashigo tana cewa lalai mutane hausa sun dawo wanan tsaraba irin haka, mai yawa, gaskiya munsha godiya,
Amma dai kin san cewa ban cin daddawa ni shine kawai abinda zan dawo maki da shi amna sauran har na fara amfani dashi,
Anty Amarya ce tace idan ke bakya ci ranan da kike da girki bazaki girkawa maigida nau,in abincin gargajiya ba yaci,
Tace hakane fa gaskitaj kai amma matan nan nagode maki da shawaran nan, don shi kin san mutum ne mai son cin abincin gargajiya,
A cikin ba,a ta hango wanda Fatima ta dawo muna dashi tace to ga wani can sai a kara min mana,
Dije tace ta dayan kishiyar ku ce tadawo dashi wai bata so
Wani wawan dariya Salawatu ta sake tare da cewa cikin tabe baki wai mai kaza a aljihu bai jimirin ass,
Ita tana zaton cewa irin rayuwar ta ce kowa keyi azaton ta zaki saka mata wani mugun abune a cikjn kayan,
Itace fa tazo muna da sabon sanfari a gidan nan kwanaki da suka tafi, can garin ku da maigidan bayan sun dawo a dinga dirka mai wani mugun abu a cikin drinks da abincin sa,
Salati naji su Dije da su Mama Sa,a har Anty Amarya sun saka a lokaci guda,
Aiko a nan Salawatu ta shiga sharara muna labarin yadda a kai rikici a gidan tsakanin maigidan da Amaryan shi,
Wani irin mugun tsanar Fatima ne ya kamani tare da jin haushin maigidan wanda yake zaune da ita har zuwa yanzu kaman dole,
Saboda jiya zuwa yau sai na fahinci halin Fatima kaman irin mutanen nan ne masu son kan su a kan wani, don bata damu da damuwar wani ba ita,,

****** ********** ******
Duk wani abinda ya kamata naiwa yaron nai mashi amma sai kuka yake tsulawa ba sasautawa,
Gaba daya hankalin mu duk ya koma ga yaron wanda ke kuka tankar sai suke,
A cikin wanan yanayin na rudanin kukan Amir yaya Abubakar yakira wayana yana cewa cikin sallama,
Sweetness sister na ya kuke ya na barku dazun ?
Kafin nai magana yaji irin kukan da yaron keyi a cikin tashin hankali,
Tambayana yake a rude may ya samay shi, may yake so wai may ke faruwa ne wanan irin kukan haka,
Tambaya kusan uku a lokaci guda duk ukun na rasa wanda ma zan amsa daga ciki,
A cikin dasasshiyar murya nake cewa, Yaya tun daren jiya yake wanan kukan haka kuma bai bari na huta,
Shiru naji yayi can naji yana cewa ko nono yake so ne, murya tankar zanyi kuka nake cewa,
Sam yaki kama nonon kuma ga jikin shi yai zafi duk ya gashe don zafin,
Subbahanallahi kuma lafiya kalau kukazo dashi jiyadin,ko dama baida lafiya ne tun can gida,
Wayan Anty Amarya takarba don ganin yadda nake a rude inda tai mashi bayani dalla,dallah
Hankalin Yaya Abubakar yai matukar tashi don sai yai da yasanin barin gidan da yayi a yau din,
Baiko yi sallama ba yakashe wayan Lawal ya kira a gigice yana mai bayanin abin dake faruwa a gidan,
Lawal da Mama Biu suka shigo gidan hankalin su a tashe duk abinda yadace anyi har asibiti sun tafi da yaron amma likita yace lafiyan shi kalau abashi paracetamol kawai yasha,
Tun fitan su gidan yaron ya ci gaba da barcin shi hankali kwance a hannun Anty Amarya, sai ajiyan zuciya yake saukewa,
Abin mamaki suna saka kafa a gidan aiko yafara yanka wani irin ihu cikin tashin hankali,
Ance matar malam malama ce, Mama Dije tace a miko mata yaron inda tace Ramatu ta ta ludayi na karfe da sauri tadauko a kitchen, takawo mata ruwan zamzam ta dauko a cikin yar hand bag din ta tai addu,a acikin ruwa ta matse akin shi ta tura mai,
Ta cire mai riga ta shafe, mai duk jikin shi da sauran ruwan ta dan rugumay shi a jikin ta, sai ajiyan zuciya yake saukewa wani bisa wani,
Duk da dare yayi amma saida Lawal dasu Baba Wadda suka tafi Suleja,
Sun dawo da abubuwa inda yaiwa Mama bayani yadda za yi amfani dashi,
Gaba daya gidan hankalin mu a tashe yake ranan don duk muna Babban falon gidan,
Har Fatima wace ke nuna ko inkula akai tana tare damu sai ajiyan zuciya yaron ke faman saukewa, a hankali, zafin jikin shi tun da Dije taimai addu,a ya rage,
Ina gefen kujera zaune, a kasa tare da Ausha wace itama gann muna a cikin tashin hakali duk ta tsorata don haka najawota zuwa jikina,,
Kamata yayi a gwada bashi nono a gani ko zai karba yanzu,
Haka suka sani gyarawa don in bashi nono ya sha ai yana jin shi a hannuna sai ko ya kara saka wani sabon kuka mai karfi a lokaci guda,
Take hankalin kowa a gidan ya tashi a lokacin ne su Baba Wadda suka shigo inda aka shafa mai wani mai acikin kwalba sai kuma hayakin da aka saka a gidan kowani sako da lungun cikin gidan,
Allah da ikon shi sai yaronnya fara dan jan nono yana sha a hankali sai ya baka tausayi sosai,
Mama Dije tayi kokari sosai don har zuwa wani lokaci yaron yana tare da ita, kamar yadda ta saba yi mai,
Hankalina ya fara kwanciya ganin yanzu yana ta barci a bayan Mama Dije kowa sai fadan albarkacin bakin shi yakeyi
Wayan malam tsoho ya shigo acikin daren nan inda yake kwantar muna da hankali cewa da yardan Allah komai zaizo karshe,
Bayan angama waya da malam tsayin lokaci babu wanda yace kala acikin mu kowa da irin abinda yake kiyas,tawa a zciyar shi,
Cikin bacin rai Dije tace wanan ai, zalunci ne a rasa abincutawa sai wanan dan karamin yaron karamin alhaki, wanda bai san komai ba,
Ranan a haka muka kwana rabi a raye idon muna akan Yaron da kuma tsaron namu lafiyan,
Can cikin dare misalin ukun dare barci ya dan dauke mu ke nan, sai nai mafarki kamar kuma ido a bude ina jin irin huci da nishin da na taba ji a waani lokaci ina sabuwar zuwa agidan,
Ruwane a hannuna masu zafi, na watsawa wani abu dake dunkule a guri guda sai ga abin yana wani irin ihu tare da birgima yana juyawa cikin tashin hankali,
Addu,an ayatulkursiyu na ketayi a mafarki cikin tashin hankali,
A haka na farko daga barcin yayin dana dinga jin wanan irin hucin da nishi daga wajen gidan a cikin ta shin hankali,
Ramatu ke cewa cikin kwantar da murya uwardakina kema kinji wanan abin kuwa,



ZEEE MAKAWA YELWA
[11/12, 10:18 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
9? 3?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AT TAWWAAB

Mafarkin danayi da abinda naji a daren jiya ya tsaya min a rai na don tsoro da fargaba,,
Baba Ramatu ta kayo kayan break fast amma na kasa cin komai, daga cikin abincin,
Dije da Anty ke min magana cewa kada na sa damuwa a raina insha Alkahu Allah zai tsare ya kare ,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login