Showing 351001 words to 354000 words out of 388021 words

Chapter 118 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8214

tagama haddace abubuwan da ke a dakin da nake,
Ba don komai ba sai don kawai ta samu abinda zatace ansaya min ita ba,a saya mata ba,
Ni,ko irin wanan halin tun a gida nasan da irin shi adalilin zaman babban gida danayi sai kuma gurin Salawatu wace sana,ar tace sa,ido,
Don ita ko maigadi yake al,amari sai ta saka idon ta balle matar gida komai idon ta na a kai don kada kishiya tafita da koda tsinke ne,,
Ita kuma Sadiya kishin shiru, shirune nata don duk a cikin matan Yaya Abubakar tafi kowa kishi wanan kishi nunuka takeyi wanda idan kishiya bata kwantar da hankali ba bata fahintar irin halin ta,
Don a fili zata gwadawa mutum cewa ita yar I don't care ce amma da zaran ta kebe da miji tashiga korafin ita baya kula ta baya son ta yafita zancen ta ya daina kwana da ita yanzu, saboda ya samu wata ya daina yayinta,
Wanan ke saka namiji ko baya so ya maida hankalin shi a gareta don gudun fadawa a halaka, ,

****** ********** ******
Tun safe labari ya samay mu cewa Fatima ta haihu diya mace, a cikin asibitin da nake a kwance,
Munyi murna kwarai da haihuwan ta sai dai su gwago da suka tafi anki bari su dauki yarinyar wai ba,a bawa mutane,
Sun dawo suna fada min nace masu kada su sa zancen a ran su don watarana ita da kan ta zata kawo kanta gare ku ai,
Abin baiwa gwagona dadi ba sam amma na bata hakkuri da cewa haba Gwago na ke ma kiyi fatan Allah ya sauke yar ki lafiya ki dauki naki tace min amin yar nan,
A ko,da yaushe ni dai naga kin haihu lafiya mun rika jariri ko jaririya mun koma gida, a,cikin farin ciki,
Haihuwan Fatima yasa maigidan shigowa gari, ida zo gani yar shi yarinyar tana kama da mahaifiyar ta sosai,
Ya nuna matukar farin cikin shi ga wanan haihuwan da akai mai inda ya sai duk, wani abin bukata, ,
Hakan ne yadan haddasa hasumi a tsakanin shi da Salawatu duk da suma din yayi kokarin saya madu abubuwan yadda ya dace,
Mutanen Birnin Kebbi sun zo suna inda yan fannin Fatima da na aka dinga kai ruwa rana a tsakani saida Anty Safiya ta fito masu ta bayan gida tai masu tas,
Duk wanan shagalin dake wakana muna asibiti nida Maman Biu da Gwagona sai labarin abinda ya faru a gidane kawai ke zo muna,
Yan uwan Fatima sunyi kane kane da komai sun hana mutane walawa, yadda ya kamata gashi kuma Yaya Abubakar yace a sa masu ido shine, anty Safiya ta sa duk komai a raba a tsakanin su, ,
Gudun fitina yasa ranan suna nacewa su Ramatu su rufe part dina suzo asibiti gurina,
Acan mukayini dasu Ramatu , Aisha da mama Dije sai Amir,
Wanan abin ya bata wa Yaya Abubakar rai don ya nuna min baiji dadin hakan ba
Amma sai nace nayi hakane don a kaucewa fitina saboda zaman su a gida zai iya jawo fitina kuma,
Duk da ya dago kan zancen amma sai kawai ya kyaleni bai ce uffan ba,
Ashe Mama Dije taji fadan da yake min sai take ce mai, maisunan malam zaman mu a nan shi yafi don kaga irin yadda Fatima takewa mutane ko diyar fa tunda aka haife ta ko Gwagon ka Habbi gatanan an hanata daukan ta,
Da mamaki yake kallon Mama Dije yace an hana maku daukan bay ya nuna ta da yatsa yace ku ne za a hana dauka yata ta cikina kuma ?
Tun wanan lokacin Fatima basu gane kan shi ba again saboda ya daure masu fuska tamau,,
Fatima ganin canji a gare shi ya sa ta shiga gurin shi, tana cewa don Allah idan tayi mai wani abune yayi hakkuri don Allah,
A gurin da yake daga zaune tankar ba dashi take, magana ba,
Kowacen mu ya saba da irin rayuwan shi don haka ta san cewa yana sane da ita,
Takara cewa da kai nake magana fa don Allah kayi hakkuri,
A raunane yadago jajayen idanuwan shi da suka rine don bacin rai yana cewa a har zuke,
Fatima bazan lamunci wulakanci ga yan uwana ba duk abinda kukeyi keda yan uwan ki a gidan nan ina a sane ,
Ban son fitinane naiwa yan uwa na magana akan azauna lafiya su fita zancen ku, don dai kawai a watse lafiya da ku,
Amma wai ke shine har zaki hanawa yan uwana daukan yar ki,
Kafin ki haihu diya nawa kika samu a gidan mu kuma ba cinye su ba,
Sai yarkice kike ganin cewa zasu ci don basu kaunar ki ke da ita,
Shiru Fatima tayi don tasan cewa idan ta tanka mai zai jawo masu babban fitina a tsakanin su,
Hakan ne yasata jan bakinta tai shiru don kauce wa fitina a tsakanin su don yazu taka tsan tsan take da al,amarin su,
Da kuka tafita daga dakin saboda maganganun da ya zuba mata
Inda yace tabari tagani idan har sone ta sai wa yar ta acikin yan uwan shi,
Wanan maganan ya tsaya mata a rai don ita a nata ganin bata komai ba da za ai mata fada haka,,
Kawai da kiyayyane don ba,a kaunar ta shine za,a hadata da mijin ta don kawai su sami baraka da mijin ta, yan adawa su ji dadin, a ran su,,
Tace ni da kaina zan shiga na fita na sai wa ya ta soyayya ga kowa a gidan, nan baki daya sai na mayar da kowa bakowa ba,

****** ********** ******
Sati uku a tsakani, haihuwan Fatima ina kwance a cikin dare bayan nurse tabani maganin na, na dare na sha,
Ina jin su Gwago suna hira akan yadda mata ke ta samun olin haihuwa yanzu sabanin irin yadda a can baya duk babu wanan matsalolin ga mata,
Ina aon in basu amsa amma na kasa saboda wani irin dan ciwon mara dana fara ji tun misalin karfe hudu rana,
A hankali na lumshe idanuwana saboda na dan tuna kaman na taba jin irin wanan ciwon a baya can,
A hankali na fara lumshe idanuwa don wani irin barci nake ji mai dadi yana zo min a lokacin,
A hankali barci ya kwasheni tun ina jin hiran su sama,sama, har ban san ina nake ba,
Ashe acikin barcin da baifi minti ashirin ba nafara dan yin wani nishi sama, sama, har ta kai ankira min likita, inda yaba da umurnin akaini dakin tiyata da gagawa,
Umurnin likita su kabi don sun aje ni, kamar yadda ya basu umurni suyi ,
Ina dan iya gane mutum a lokacin sama sama da kuma jin muryoyin mutane a kaina,
An dan dauki lokaci dani a ciki yayin da yan uwa da abokan arziki suke a tsatsaye kofan shiga dakin theater, a cikin tashin hankali,
Da farko Lawal ya hana a fadawa Yaya halinda ake ciki don kada ya tayar da hankalin shi ,
Amma sai Salawatu ta buga mai waya tana tambayan shi cewa wai anfito da Meenatu din ne,
Wani irin dam yaji a lokaci guda yake tambayan ta cewa daga ina fa,,
Turus tayi ta rasa may zata ce mai don ta fahinci bai san komai ba akai,
Kashe layin ta yayi don ya fahinci cewa bazata bashi amsa ba,,
Hannun shi na rawa yana kokarin kiran layin Meenatu wayan a kashe take Mama biu ce ta kashe wayan tun da zan kwanta,
Ya kira nomban Baba Wadda wayan na ringing amma ba ai picking ba abin da ya tayar mai da hankali ke nan don ringing daya biyu Baba Wadda ke daukan wayan shi amma yau har ta katse bai dauka, ba,
Har layin baba Hamza ya kira amma ba,a daga wayan ba, saida dabara ta fado mai ya kira Sadiya,
Ita,ce ke fayace mai yadda al,amarin ya faru a tsanake tambayan ta yayi, ita tana ina yanzu,
Taba shi amsa da cewa ina gida mana mu duka kowa na gida,
Yace cikin masifa amma Sadiya baki da hankali baki da wayyo yau na tabbatar da baki san ciwon kan ki ba,
Mamakin masifan shi Sadiya keyi don saboda kishiya ce zai dinga wanan masifan haka,
Nomban Lawal ya ke nema don ya kirashi yaji amma sai layin yaki zuwa
Inda yakara kiran layin don yaji ko zai shiga, acikin sa,a yaji wayan tana ringing,
Pick, pick please lawal pick mana yake cewa acikin rudewa,
A hankali murya dassasa lawal ke karba wayan da sallama,
Lawal may ake ciki ne may ke faruwa ne wai, fada min ina Meenatu take, ne wai,
Lawal ya rasa amsa da zai karba daga cikin tambayayoyin da ya jero mai,
Lawal, yace don Allah maigida ka kwantar da hankalinka zan kiraka inmaka bayani anjima daga haka ya kashe wayan shi,
Gaba daya sai yaji duk kafofin jikin shi suna fitar da wani irin zafi a lokaci guda,
Wani iri yakeji kan shi da ilahirin jikin shi yana juya mai ,
Allah ya taimake shi ya bashi ikon shiga bathroom nan ya dauro alawala yazo ya shiga sallah yana rokon Allah sauki,
Yakai wani lokaci a zaune ya rasa wanda zai kira a lokacin daga cikin yan uwa,
Mutanen hida suka fado mai arai inda yai tunanen cewa gara ya kirasu yafada masu,
A rude ya fara kiran layin malam tsoho inda wayan ya shiga,
Malam ma tambayan shi yake da cewa Meenatu ta farfado daga suman ko,
Kara rudewa yayi yana cewa, malam don Allah atayamu addu,a please
Addua kan ai tun da dare mu keyin shi inji malam din ya amsa ma acikin sanyin jiki,
A hankali tsohon ya kira sunan jikan nashi yana cewa Abubakar ka kwantar da hankalin ka insha Allahu Allah zai bata lafiya,
Sai a lokacin ya kara samun natsuwa sosai inda yaci gaba da yin lazimi kamar yadda ya dace,
Tun shigan mu sai yanxu wata nurse tafara fitowa da sauri ta wce su ba tare da tace masu uffan ba,
Har ta dan fara tafiya ta juyo acikin hausanta da bai nuna batace abata zannuwa zata shiga dashi,
Da sauri maman Biu tamika mata zannuwa acikin leda ta ce a bari ta dawo
Keken daukan yara ta garo zuwa dakin theater din cikin sauri,
Kamar minti ashirin sai ga nurses din ta kara bude kofa tafito dauke da jarirai suna ta kuka,
Yan uku na haifa mace daya maza biyu duk kuma kuka suke don sun wahala suma,
Nurse din ta dakata dayaran a daidai inda yan uwa na suke take guri ya rude da murna,
Gwago Habbi ce tace to ina ita diyana din kuma take,
Nurse din ta dan bata rai abinda yasa kowa yintsit a gurin ke nan tace suna ciki da ita don tana jin jiki sosai,
A take hankalin kowa ya tashi don sai suka koma kuma jigunjigum ba mai cewa uffan,
Nurse din tace ina son mutum daya ko biyu su biyoni muje inda zan aje yara,
Da sauri mama biu da gwagona suka bi bayan nurse suna kallon yaran,
Baba Wadda yace Lawal yakira Yaya Abubakar yafara fada mai abinda aka samu,
Wani iri dadine ya ziyarce shi inda yake cewa to ita kuma Meenatun lafiya, take ko,
Yace cikin dan inda ind? ai tana ciki ana dan gyaran ta kafin ta fito
Murna farin ciki duk sun cika shi a lokaci guda saidai duk babu halin ya nuna saboda bukatan shi kawai yaji irin halin da yar uwar shi matar shi uwar yayan shi ke ciki,


ZEEE MAKAWA YELWA
[12/4, 10:11 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
1? 0? 2?

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH AL MUGHNI


Suna tsaye cirko,cirko a kofan dakin theater aka bude kofan da karfi gaba dayan su hankalin su ya koma a kofan, dakin,
Gadon dakin theater ne ake garoni a cikin sa a hankali zuwa ward
Gaba daya hankalin su duk ya tashi irin yadda su ka ganni a kwance tankar bani numfashi,,
An isa dakin dani inda aka taimaka azani zuwa saman gado,
Gaba daya suna tsaye a kaina hankalin,su a tashe babu wanda ke iya cewa komai daga cikin su,
Cikin girgiza kai, Lawal mijin Fattu ya fita, daga dakin a hankali
Wayan shi yake kokarin cirowa daga aljihun rigar shi a cikin dan rudewa yake kokarin kiran layin Abubakar,
Yana dauka yafara cewa Lawal ya akayi anfito da ita dai ko daga dark n,
Jiki ba karfi yace a cikin kasalalan murya anfito da ita yanzun nan sai dai gaskiya, tana bukatan addu,a sosai wallahi,
Subbahanallahi yace yayin da zufa ke tartso mashi daga ko ina na jikin shi,
Hankali a tashe, yake cewa kagane ne Lawal, yanzun haka ina nan nazo sayen ticket zan shigo insha Allahu,
Sunyi sallama batare da ya samu wani karfin gwiwa ba a wurin Lawal din wanda zai saka shi, jin dan sanyi, sanyi,

****** ********** ******
Afanin su Sadiya kuwa can gida labari ya samay su ne a lokacin da akazo daukan kayan da za,a sakawa yaran,
Fattu ce tashigo gidan ita da Antyn saloon suna kokarin shiga part dina a lokacin Salawatu ta shiga store don dauko abu,
Ita kumq Fatima tana daga cikin side din ta tana kallon hausa film,
Sadiya tana daga kitchen tana girki a cikin main kitchen tana girki, ta hango shigowan su tare da jin sallaman su,
A,a Fattu kune daga asibitin kuke ne tace eh munzo daukan rigan babies ne don ana bukatan saka masu,
An haihu ne Sadiya ce take tambaya tana kokarin gyara cooler dake hannun ta da kyau,
Da mamaki Anty Saloon ke kallon su tace tun dazun ku baku samu labari bane, ?
Ai an samu diya uku manya manya dasu shima mukazo mu dauki rigar su, wanda za, saka masu,
Da karfi salawtu tace haba Bintu uku fa kikace ai zolayar ki ma bataci ba,
Fattu ta juya tana kokarin bude daki tana cewa wallahi kuwa an haihu diya uku aka ciro mata maza biyu mace guda masu kyau da su wallahi,
Uku fa suke kokarin hada bakin su gurin mamakin jin abinda ake fada masu kamar mafarki wai Meenatu ta haifi diya uku lokaci guda,
Jin hayaniya acikin gida yasaka fatima dake daki fitowa da yar ta a kafadan ta a cikin showel,
Taga su Fattu daga kofan part dina suna cewa kuma yaran bazaki gan su kice haihuwan diya uku bane wallahi don manyane fa sosai da su,
Inda Salawatu take tsaye take duba tana son jin kmarin bayani har ta kara karasowa kus Rca tana cewa wa ya haihu ne wai
Salawtu ta dan juyi ta cewa cikin sanyin murya Meenat ce ta haifi yara uku wai,
Fatima tace kai wani ciki za,a haifi dita uku dashi wanan cikin ai baiko kai girman na, Amin ba, cewa wai yar ta,
Haba dai inji Anty n saloon tace ai kin san abin na Allah ne ai,
Tau fa inji Fatima tace to Allah ya raya a fili, sai dai a can cikin zuciyar ta har kafanta tana jin suna harde mata yayin da take kokarin komawa dark n ta,
Salawatu dake tsaye ta rungumay hannu sai cewa ta ke yi three kinds at once haba how Lucky is she haka ?,
Abin daga ubangijine amma ai ita Meenat ma batai tsan manin cewa ko biyu bane balle ace har uku,
Suka kwaso kayan da zasu dauka daga cikin troler din suka rufe dakin dama Hamza yana waje tana jiran su har yana batun shigowa sai gasu sun fito,
Sadiya bata iya cewa uffan ba sai a hankali take tafiya zuwa dakinta wani irin abune take ji ya tokare mata makoshin ta,
Abinda da ta girka don ta ci duk yafita mata arai bata ko da sha,awan shi sai zaune take tayi ta gumi,
Salawatu ba yarda ba don haka ta suri keys dinta tare da yafa gyalen ta zuwa asibitin don ta tabbatar,

****** ********** ******
Tana faka motar ta ta saka kafa guda zata fito taji wani miji da mata da yakawo matar shi awo yana cewa ,
Da za,a ce ki haifamin yan uku haka wallahi da na fikowani namiji sa,a aduniya,
Dubi fa yaran kamar mutum ya sace su gwanin ban sha,awa da su, kai yaran sun min kyau wallahi shikan mahaifin su ai ya godewa wa Allah wanan ai wani baiwane daga Allah,,
Tun wanan hiran miji da mata da Salawatu taji sai ta daskare don tasan cewa da gaske diya uku ke nan Meenatu ta haifa,
A hankali ta karaso zuwa dakin da muke saida ta samu a lokacin ba,a shiga sai mutum biyu ne a kaina sun rike min hannaye na, dake daure da drip,,
Haka yasa ta tsayawa daga waje tana mai kara tabbata da zancen daga wurin wa yan da ke tsaye daga waje suna kallon yaran gwanin sha,awa
Ita ko sai wani haba haba take dasu kamar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login