Showing 72001 words to 75000 words out of 388021 words

Chapter 25 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8194

ya kira wani abokin shi mai suna, Nasir yake sheda mai mun iso kuma gamu wuri kaza,
Nasir din ne ya iso cikin yan mintoci yai muna jagora zuwa gidan shi,
Gidane mai kyau don da ya,ke nasan gidan yaya Abubakar sai nake ganin wanan ya fishi kyau sosai, a,gaskiya,,
Agidan mun samu karramawa, da mutuntawa so,sai daga, gurin matar shi mai suna, Zulahat,
Nasir din Abokin Uncle ne, shi,ne ya yi kokarin gano muna gidan yaya Abubakar din,
A tare da su mu,ka nufi gidan yaya Abubakar dashi da iyalin shi don suga wuri,
Matar ta bani nobar wayan ta don in dinga kiran ta in har akwai wani, matsala,
A kofan wani katon gida mai get, muka tsaya,
A hankali nadan kware idona sai naga ai ba gidan bane,
Wasu kungiyar matasan uguwar da alama suna hira ne, daga can gefe guda zaune suna hiran su,,
Sai dai hankalin su na a kan mu tun lokacin da muka tsaya kofan gidan
Mamakine ya kamani acikin rai na don na ga da gaske a gidan suke nufin tsayawa,
Har a lokacin fuskana arufe, yake bisa umurnin da gwago Habbi, ta bani cewa in gyara rufe kai na,
Amma ai sai nake gani mai kwatancen bai san gidan ba dai, ko ?
Nace a rai na,
Uncle Nasir ne ya fita daga motar shi, gurin Samarin nan ya nufa suka gaisai da shi a cikin hausa,hakan yasa shi gane cewa hausawa ne, su,
Tambayan su ya yi da cewa don Allah ko mai gidan nan yana nan,?
Wanan ya kali wanan can haka suka dinga yi a tsakanin su,
Sai guda ne daga cikin su ya,ce to a gaskiya bamu sani ba don dai, mu na gurin nan tun bayan salla la,asar, zaune,
Amma bamu ga fitowar shi ba daga ciki ko shigan shi,
Sai daya daga cikin su ne ya ke cewa, barin duba maku in gani ko yana nan, ciki,
Guda daga cikin su kuma ya dakatar da shi da cewa "kai, kafa san halin guy din nan bai ko kallon kowa da mutunci fa,. Kar kaje mai gida pls
To baka ganin su baki ne bari kawai a duba masu shi ko yana ciki,
Daga gaban mota naji muryan Anty amarya tana cewa ikon,Allah,,
Get din gidan matashin ya nufa inda yafara dan lekawa ta kafa, dake akwai, sai ya kada kan shi alamar maigidan na nan, ciki,
Gabana da ga bayan mota in,da nake zaune tsakiyan su gwago da mama, Sa,a naji yaba da dammmm, duk da nasan cewa dai ba gidan yaya Abubakar bane wanan irin katon gida mai hade da, gidan sama, a ciki,
Kara bugawa saurayin, ya,yi, a lokaci guda da karfi yana kuma hadawa da,sallama, atare,
Dariya sauran suka fara yi mai suna nuna shi da hannun su, cewa ai mun fada ma baida mutunci fa,
"Yau ko ga diyan banza inji gwago Habbi daga bayan mota inda muke zaune,
Tace, zasu hana shi yai muna abin arziki,
Bugu uku ba motsin komai yasa saurayin juyowa yana fuskan tar mu cikin daga hannu alamar ba,a bude kofan ba,,
Daya daga cikin samarin dake daga zaune ,
Wani baki wanda tun zuwan mu bai ce tak ba ga zancen da a,keyi, yamike yanufi get din da karfin Allah ya dinga dukan get, din,gidan,
Murya yaji ana cewa kai wai waye hakane pls ? lafiya dai ko may ya faru, ne wai ?
Ajiyan zuciya Uncle yayi yana cewa akwai mutum ashe aciki don naji anyi magana, daga ciki,
A,lokacin ne kuma su samarin kofan gidan ke cewa bakin ne fa ke Sallama,
Daga haka suka juyo abin su suna cewa maigidan yana tafe,,
Kusan yan dakikoki mukaji karan bude kofan cikin gidan har zuwa budan get din, waje
Yaya Abubakar ne wanda ke a saye cikin wasu fararen shedda masu design din wuta,
Kanshi saye da fula mai suna minister, kayan sun matukar karban jikin shi sosai,
Ya kara,wani irin fari da kuma dan jiki, sai dai still tsayin shi mai kama da na malam tsoho yana nan,
Lekowa yayi yana kokarin magana da Samarin nan, daga cikin get din gidan
Amma sai su ke nuna mashi motocin mu da hannun su
Alamar ga masu neman ka can ?
Nobar motar yafara kallo sai dai nobar ta Sokoto ce don haka yake dan kallon motan da mamaki,,

Nasir ne ya fito daga cikin motan shi ya nufi gurin shi acikin sallama,
Gaba daya ya fito wajen gidan nashi cikin mamaki yake kallon motocin da Nasir din
Don bai san shi ba gaskiya,
Hannu suka mika wa junan su suna musabi,a kamar yadda aka sani,ga addini,
Nasiru din ne ya kauwar mai da mamakin shi yana fadin baki ne daga kebbi,,
Daga kebbi ?
Yaya Abubakar ya dan mai,maita maganan ya,kallon motocin a cikin mamaki,
Motar Uncle yake kokarin nuna mai, Sai a lokacin ne Uncle ya balle marfin motar ya fito adaidai lokacin da gaba dayan su sun kawo bakin motar mu, shi da Nasir din
Hannu sukayi da Uncle wanda kowa bai san fuskan kowa ba,
Sai dai akwai kama sosai a fuskan Uncle Nafi,u wanda yai matukar kama da mama Saratu,matar baba Samaila,
A cikin motar yaji muryan mama Sa,a tana cewa kai,Abubakar kai, muna hwa,
Lekawa yayi su kai ido biyu da,
Mama Sa,a da Gwago Habbi wace ba zai iya cewa ga tsawon lokacin da ya dauka bai ganta ba,
Sannun ku da zuwa yake cewa acikin sakin fuska da ganin su,
Kaina yana duke ina rufeda farin gyale mai duwatsu, (stones)
Daga duken da nake naji muryan shi sai da cikina ya motsa,don tsoro da fargaba,
Da guda guda muke kokarin fitowa daga cikin motocin da,ke tsaye akofan gidan, nashi
Hakalin samarin nan gaba daya ya na akan mu suna son fahintar abin da ke faruwa,
Kofan shiga cikin gidan ne yake kokarin nuna muna ,
Rike nake gam a hannun Gwago na Habbi da ke dan jana a hankali, zuwa cikin gidan
Gurin da yake tsaye ne muka dan gitta a hankali hanci ya shako kamashi turaren humra yar Sudan, da kuma na Ar,Rahab da Anty ta mulke min jiki dasu,
A hankali ya dan dago kai cikin mamakin jin wanan kamshin mai dadin shaka,
Da sauri Anty Amarya ta samay mu take cewa Gwago mu tsaya tukun,
Daidai saitin kunne na tazo, take cemin a hankali, cikin kashe murya, take ce min ki karan ta Bissimillahi, kafa, 21,
Sai kulhuwallahu kafa uku,
Falaki da Nas uku,uku, da A,uzubikalamatillahi tamat, min sherin minhalaq, sau uku,
Sai, ki rufe da Hassbunal,lahu wani,iman wakeel, kafa bakwai,
Anan muka tsaya tsaye tare da su har izuwa lokacin da na gama muka shafa a tare da su,
Mazan kuma na daga bayan mota suna ko,karin sauke muna kayan mu daga cikin buth din motan,
Still dai wanan saurayin na farko ya fara mikewa ya nufo gurin da aka,sauke kayan, ya karba daga hannun Uncle dina, zuwa ciki,
Mama sa,a dake kallon su ke ce muna alokacin da muka fara tafiya
Yaron ga dai dan Albarka ne, gashi kuma ya kwaso muna kayan,mu daga mota,
Daidai saitin kunuwa na Anty Amarya tazo tace ki,ta fadan Subbahanallahi Walhamdullahi Allahu,Akbar, abakin kin, ki, har mu shiga, ciki
Kai, kawai na gyada mata alamar to,
Daidai zamu shiga cikin gidan mai,kama da wani palace, muke jin muryan nan nashi mai kama da ta rowa yana cewa,
Sadiya ki fito ga wanan yarinyar su mama,sun kawo ta,
Shigar mu yai daidai da fitowa ta cikin wani yadin material baki mai dot, dot fari dinki dogon riga mai shara shara, kanta da hula kawai,,
Tana cewa cikin muryan nan nata mara marmari ,
Wace yarinya ce suka kawo ?
Salllamar mu yasa ta dakatar da tambayar da take mai,a lokacin,
Gani mu da ta yi yanayin ta ya dan canza sai cewa ta yi,
A,a su mama ne tafe ?
Sannun ku da zuwa
Yauwa sannu Sadiya, inji Gwago da Mama Sa,a,
Kallon gidan Anty Amarya tafara yi tana bin ko ina da ido,
Yayin da ta sauke idon ta a kan Anty Sadiya wace ke tsaye kim,kyam da ita cikin wani irin murde fuska,
Ji nayi Anty na cewa to Allah ya kyau ta kawai, mata daure miji daure,
Wani daki dake kasa a wata yar siririyar corridor, hannun dama shi shine yaya Abubakar ke cewa anty,
Rukaiyya zo ki duba dakin ki gani ko ?
?nty Amarya kusan a tare suka mike da Rukaiyya zuwa dakin da ake cewa nawa wai,,
Daki ne babba mai kyau da wani jan gadon katako mai katifa,6 by 7,
Bandakin (bathroom) Anty ta bude , baida laifi amma sam ba tsab ta a cikin sa sam,
Ta rufo kofan bayin da sauri tayo waje, kallon gidan tayi tan,gamaymay, mai kyau da sha,awa, har zuwa matakalar benen gidan,
Sai dai ba tsabta sam duk yana bukatan gyara,saboda yadda yake a har gitse,,ko ina,
Rukayya aje yarinyar nan ki taso muje, mu fara gyaran waje, inji Anty Amarya
Matar Uncle Nasir ma ta biyo bayan su,
Inda yaran ta ke ko,karin biyo bayan ta,
Juyawa tayi inda su gwago tana cewa ku zauna har inzo,
Sadiya tashigo falon da ruwan goruna a wani ture mai fadi,
Zaunawa tayi suka fara gaisawa dasu Gwago da Mama Sa,a cikin dan mutunci,
Mun samay ku lafiya Sadiya ya jama,a ya gida ?
Waya anty keyi alokacin tafito zuwa waje, inda su Uncle suke da yaya,a tsaye suke suna magana ta iso, wajen,
Ganin fitowan ta yasa Uncle ya dan zo gurin ta don jin may zata ce,
Gadon dakin fa sai an sai mata sabo don ba wani mai kyau bane, gaskiya,
Juyawa yayi inda su ke tsaye ya ke cewa Nasir, akwai wurin furniture's a kusa ne ?
Ko sai mun shiga gari ?
Wanan gadon ba zai yi ba ko ?
Uncle Nasir ya tambaya, don yaji may Anty tacewa Uncle, din,
Sai Uncle yace No, kasan ai halin mutanen mu mata,
Saratu da mijin ta sun bada kudi idan munzo asai mata duk abin da ya dace,
Murmushi yaya Abubakar wanda ke sauraren su, yayi don sani halin Baba Samaila da yayi,
Uncle Nasir ne yace akwai wani gurin furniture da zamu zasu zo su hada muna shi in,time,
Tare da Anty na da matan uncle Nasir akatafi,
Kaya masu kyau suka zabo min dai dai kudin dake hannun su,

****** ******** ******
Daga daki na har kitchen angyara shi tsune,dashi ansa mai gadaje mai launin fari da purple,aciki
Labulayya purple, da zannuwan gado na masu kyau da tun sokoto Uncle ya ba Anty ta saya mun su, inda
Abincin take away yaya yake siyowa bakin har zuwa lokacin da su ka kai,
?nty amarya tace shin wai ita matar gidan bata girki, ne da za,ai,ta sayo muna take away,
Rukaiyya ta ce a cikin shake murya, ance fa bata iya girki ba
Wai shi ke girki da kan shi in yana so,
What, inji Anty cikin gigicewa, tace ashe diya ta, ta shige su kuwa,
Dama ni wallahi banga mace ba wurin nan mace kamar kato haka ?
Kulolin da Anty Amarya suka siya min nai masu, matukar kyau ,nayi mamakin sosai, don duk masu tsada ne,gaba dayan su,
Wai da ita da yan uwan ta har da su bedsheets masu kyau da tsada,
Anty ta daga kai takarewa dakin kallo da kyau sai naji tayi ajiyan zuciya tana cewa,
Masha Allah komai yayi daidai, Meena yanzu sai hakkuri kinji,
Don Allah kada ki bi halin rayuwa irin na wanan matar gidan da ki ka sama,
Sai kin yi da gaske wajen shawo hankalin wanan miskilin mijin naki don gaskiya irin su akwai wahala kafin ki san kan su,
Kada ki ta zakewa kema kibi abin a hankali irin yadda halin shi yake,
Don in kin faye nuna zakewan ki za kiyi saurin fita a rayuwan shi,
Komai a sannu ake bin shi har zuwa lokacin da zaki shawo kan shi insha Allah,
Kuka nasa a lokacin inda sauran su gwago suka sa muna baki da cewa ai yanzu kuka ba naki bane Meena,
Tashi zakiyi ki zage damtse kamar ko wace mace,
Bawai ki zauna ki biyewa irin halin wanan matar ba,
Don Allah Anty kar ku wuce kubar ni gurin yaya Abubakar mugune ne,
Murmushi mai kama da yake Anty tayi tana jin wani iri a zuciyar ta,
Cewa tayi Meena in kina kuka ashe baki son nan da sati biyu inzo dubaki kamar yadda Uncle din ki yace,
Gwago Habbi tace Amina ki ta hakkuri keji,
Mu kan insha Allahu gobe muna komawa, gida,
Da sauri na dago kaina na kalli gurin da gwago da mama Sa,a su ke zaune,
Na ce Gwago wuce wa zakuyi ki barni a nan ?
Gwago baki ganin diyan mama Ladi ko mama ladin zasu iya biyoni suyi min cin mutunci,
Mama Sa,a ce ta haba ai ba su isa ba wallahi don malam naci musu mutunci gaba dayan su,
Ajiyan zuciya na sauke da naji abin da tace ,,,,

A Babban falon gidan suke zaune su uku, suna hira shigowan mi dasu gwago habi da mama sa,a sai Anty Amarya, wace ke tafe dani a hankali,
Gefe na samu kasan kujera daidai kafan Anty Amarya na zauna,
Uncle ya bude taron da addu,a inya juya gurin yaya Abubakar wanda zuwa yanzu sun saba sosai da junan su,
Abubakar Uncle yakira sunan yaya din ya dan daga kai tare da ansa yace to dakai da matakar Sadiya ga amanan diya na nan na danka maku,
Kafin Uncle yaci gaba da zance sai murya Sadiya ne take cewa,
Ku dai ba dan uwan ta kuma mijin ta nikan ai yanzu kishiya tace,
Anty Amarya tai caraf tace gaskiya yanzu kishiyar ki ce don zama zakuyi na abu daya,
Ashe kin gani ke nan tunda har hadama yasa ankasa barin na waje su wala sai an hada da na gida don kar wani ya ci shi kadai,
?nty Amarya ta bude baki za tai magana Uncle Nafi,u yace Short up my dear,
Dole tai shi muryan yaya Abubakar ne alokacin shi ma yake cewa Sadiya ban son rainin hankali fa,
Shiru su kayi gaba dayan su a lokacin inda Uncle yaci gaba da cewa,
Ai ta hakkuri don Allah Aminatu tana da sauran kurciya atare da ita,
Sai an kwana biyu zamu zagoyo ku don muga yaya kuke,
Ga Nasir nan in,a,kwai wani matsala sai a fada mashi don Allah,
Mukan zamu wuce don rana ya riga yayi muna sosai wallahi,
Wani iri naji daidai lokacin ne naga kowa yana kokarin mikewa don tafiya
Nima mikewa nayi alokacin cikin dan sheshekan kuka,
Hannu na Anty amarya takama zuwa daki na tana kara yi min nasiha da bani kwarin gwiwar irin abin da ya dace in yi,
Tace wanan matat muguwa ce sai kin gwada mata cewa kema A ce,,
Ina kallon ta ta wuce duk daurewan ta saida hawaye yazo mata tasa habar gyalen ta tana sharewa,
Kai na daga na kalli dakin wanda aka kira wai da sunan nice mai shi a yanzu,



ZEEE MAKAWA YELWA
[7/21, 9:28 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
3? 1?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-A'LEEM,,,,

Zaune suke a gaban malam tsoho tare da,irin abin arzikin da suka samo a ,Abuja, gurin Abubakar,,
Hankalin malam yafi karkata ga labarun da suke bashi akan zuwan su,
Sai ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da Rukaiyya ta gama zai,yana mashi tas yace
Dan nema bashi bane aida sai ya turo min ita kamar yadda na ce mai,
Ita kuma matar tashi, tayi hankali in har tana son zama a tare da shi,
Don yanzu nafi dana TARKO akan shi sai ta koma ta fadawa uwar ta don ta canza sabon TARKO don wanda ta dana ya tashi
Sukan ba su gane may yake nufi ba don haka kawai suka mike don shiga cikin gida
Malam sai faman murmushi ya keyi daga gurin da ya ke kwance,

****** ********* ******
Dawowan su mama Sa,a yayi daidai da zuwan sakon Hajja agare ta,
Hakan yasa ta gane cewa su mama Sa,a daga Abuja suke kenan gurin kai amaryan da aka boye mata ita da diyan ta dama sauran mutanen gidan,
Lalai Sa,a kin kai bakar kishiya gare ni munafuka yar cin amana,
Ba yau ba dama nasan baki kaunar farin cikkina aduniya ko kadan,
Wanan na dade da sanin shi duk alheri na kina bakin ciki da shi haka bakin cikina kina farin ciki dashi,
A cikin daga murya take wanan zancen wanda ya jawo da hankalin mutanen gidan zuwa gare ta,
In ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login