Showing 210001 words to 213000 words out of 388021 words

Chapter 71 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8187

tasan dai wanan karon an tsallake ko,

****** ********** ******
Ban farka ba sai gab da Sallah azahar ko shi yunwa ya tashe ni don wata kila da na makara da salla din,
Ido ya kai ga agogon bango naga biyu saura ga kuma yunwa na damuna,
Na sauko daga saman gadon da nake a kwance na, fara zuru kafana na akasa,
Sai naji wani abu yadan tokare ni kamar masokiya,
Dole na dan kai kwance saman filon dake daga gefe na,
Har zuwa lokacin da naji yanayin ya lafa min kafin na daure na tashi,
Bayan na dauro alwala na fara gabatar da sallah amma a dadafe na idar,
Shigowan Ramatu dakin nawa yasa na dan daga ido ina kallon ta,
Kafin ma inyi magana Ramatu ta gabatar min da abincin da ta girka min a gabana,
Tambayan ta nayi cewa Anty Sadiya fa kin kai mata ko adafa wani na gida ne,
Sai cewa tayi gaskiya batasani ba ko an girka amma dai bata kai mata abincin da tagirka ba ita,
Sai da naci na koshi sosai nazuba a plate na rufe na nufi dakin Sadiya dashi,
Na samay zaune kasa saman ties a kusa da kujeran da ke cikin daki tayi shiru tana tunane,
Sallama na ya sata dago ri nanun idanun ta da suka nuna cewa tayi kuka da su,
Nace mata ina wuni takarba min a ciki ciki kamar bata da niyan ansawa,
Nakai mata plate din abincin har gaban ta ina cewa wallahi tunda na karya da safe barci ya daike sai yanzu na farka,
Tambayan da ta jefo min shine Meenatu yau kun gaisa da Yayan ki a gidan nan,
Dago kai nayi ina mamakin tambayan ta sai dai nace mata eh,
Amma a dining na gan shi lokacin yana karyawa ni kuma zan shiga kitchen, don hada ruwa, zafi,
Ajiyan zuciya mai kama da ta bacin rai naji ta sauke tare da cewa lalai,
Yau yakai yafita gidan nan Abubakar bai koda leko dakin nan nawa ba, har ya kai ga fita gidan nan,
Takare da cewa yayi babu laifi ai duk abinda yayi Allah yana ganin sa,
Duk da yadda take magan ta bani tausayi amma sai kuma banji dadin yadda tacewa Yayan ba,
Saboda ai nasan cewa bayin kansa bane don ko ni da nazo gidan bada wani dadewa ba banji dadin hakan ba balle ita da suke tare tun farko,
Kuma gata ba lafiya ne ya ishi jikin taba duk da dai nasan Yaya yai kokari sosai akan al,amarin jikin na ta,
Zan juya na tafine nake cewa, nima da naga bai sallamay ni ba yau sai nake ganin kamar sauri ne yasa bai samu yin sallama ba,
Tace au har dake ma bakuyi sallama ba ke nan kike nufi,
Nace shi nake nufin ai nima ba muyi sallama ba dashi yau din ,
Amma ai Anty watakila a uzurce yake shi yasa ya tafi babu sallama,
Uhmm zaki ce haka ai don bazaki so a ce yai wani abuba ke ,
Murmushi nayi nac anty ki ci abinci kiyi wa Yaya afuwan don Allah dai,
Baki ta tabe tare da dan watsa min harara,
Nikan nasa kai na fita daga dakin don wani bashi bashi ke tashi a dakin,
Na samu Ramatu ta gyara muna part din tsab sai kamahi ke tashi,
Nazauna ina mai gashe ta da aiki tare da tambayan ta tako ci abinci kuwa ,
Sai na dan gyara gurin da zan zauna ina cewa yau gidan sabon al,amari ya faru,?
Don gaskiya Yaya Abubakar bai taba irin wanan fitan ba sai yau da wanan makiran ta dawo gidan nan,
Muna cikin zancen wayana yai kara Ramatu ta mike tadauko min tana mika min da sauri,
Sai dai kafin indauka kiran ya katse ko ban samu dagawa ba
Na tsura ma wayan ido ina kallon sunan Yaya Abubakar din, da ya zama missed call,
Ya Abubakar yakara kirana a karo na biyu ban daga ba ma wanan karon har kiran ya katse again,
A karo na uku da ya kara kirana na tabbatar da cewa zai gane lalai naga kiran kin dauka nayi,
Don haka dole na nadaga wayan tare da yin sallama a sanyaye
Ina jin yadda ya sauke ajiyan zuciya yana cewa kuna lafiya dai ko Meenatu,
A hankali na ansa mashi da cewa lafiya kalau,
Yace please kuyi hakkuri dazun wallahi I am sorry,
Sai da nayi nisa na tuna cewa ban tsaya mun yi sallama da ku ba,
Na katse shi da sauri da cewa haba dai a ba komai tunda lafiya ka fita,
Ai, ni agurina babu komai fatana dai Allah ya tsare muna kai lafiya,
Gaba daya na daure shi da jijiyoyin jikinsa har ya kasa cewa komai kuma ,
Naji yana cewa Sadiya na kira layin ta tun dazun taki daukan wayan,
Na katse shi da cewa amma Yaya ai kasan bata da lafiya watakila tana a cikin yanayi ne shi yasa ta kasa daukan wayan,
Subbahanallahi naji yace, tare da fadin don Allah Meenat daure ki duba min ita ki gani,
Nace na tabbatar ma lafiya take don ban dade da kai mata abinci ba dakin ta,
Yace to yaya kika samay tane da kika shiga nace tana zaune tayi wanka,
Amma dai Yaya yau bakai mata adalci ba da har kafita baka duba lafiyan ta ba,
Subbahanallahi naji ya kara cewa, yace wallahi Meenatu yau sat na rasa may yasani yin wanan babban mantuwan haka,?
Murmushi mai sa zuciya tsumaye nayi daga ban garena,
Nace Yaya yau dai na tabbatar da wani babban dalili mai kwarine za sa haka
Don kai na san ka mutum ne mai kokarin kare hakkin iyalin sa,
Don haka yaya kada ka bari shedan da shedanu su rude ka a banza,
Don a yanzu wanda keda mata har uku a gida bai kamata ace har sherin mace yai raja,a akan ka ba,
Saboda gudun zubewan girman ka da kimar ka ga re mu,
Wani itin tsawa naji ya buga min tankar a fili yake har sai da na kadu,
Yana cewa ke ya isa haka yace halan ni sa,an ki ne da zaki fada min haka,
Na dan kwantar da murya nace ba hakana bane Yaya wai naga ne ai
Maganace kawai da ya kamata a fade shi idan ya kama,
Yace wai Meenatu ni sa,an ki ne ?
Nai shiru ban ce komai ba, yakara cewa kin dade da sanin halina kin sani sarai bana son rai ni ko kadan a rayuwa na,
Nace a karo na biyu kayi hakkuri Yaya, kawai dai don naga cewa abinda akayi bai yi daidai bane,
Yayi tsuki ya kashe wayan a hasale batare da ya bari na karasa ba,
Ramatu dake sauraren mu ta nisa take ce min daga yau idan yai abinda ba daidai ba ki sa masa ido kawai,
Sai nace amma kuma ni Anty Amarya tace min mutum mai mata biyu da zaran kaga yafara kaucewa ka tunatar da shi don idan har ka kyale baka fadakar da mai shi to kuwa zai ci gaba da abin ne ba fashi,
Amma da an sashi a hanya sai yai saurin gane cewa ya saki hanya da farko,
Ramatu tace wanan kuma fa gaskiyane don wallahi, mazan da matan yanzu sai a slow,

****** ********** ******
Tun bayan kare wayan mu dashi sai ya dinga jin zuciyar shi na mai suya da zafi,
Don maganan gaskiya yasan bai kyauta ba tun dai wa Sadiya wace ba lafiya ne da ita ba,
Gahi har yar karamar kaunar shi ta bay,baya tana fada mai magana a cikin hitsara,
Wanda kuma gaskiyane ta fada sai dai irin wanan abin yana daya dafa cikin abubuwan da tun farko yake kin auren zumunta don gudun raini ga yarinya karama,
Don haka sai yaji zaman office din ya fita ran shi don haka ya dauki rigar shi ya rataya tare da hadda wayoyin shi,
Ya bar office din cikin bacin rai don ba abinda ke mai yawa a kai sai cewan da nai masa
Kada ka bari sherin shedan da shedanu yayi tasiri a kan ka mutum mai mata uku, har zai bari guda tayi galaba akan sa,
Wanu irin duka ya kaiwa sitiyarin motar shi tare da jan dogon tsuki,
Don gaskiya sai yanzu ya gane cewa Salawatu ta hillance shi da yaudara da takawar mai da tunanen shi a cikin dan lokaci guda,
Innalillahi wa,ina alaihim raj,un,,
Ya fada tare da runtse idanuwan shi a cikin bacin rai,
Tabbas sherin ta ne hakan don idan har bai manta ba tun da tabashi cup din juice din da tace yasha ,
Tun a lokacin yaji gaban shi yai mumunan faduwa sosai sai dai ya daure yasha da bissimillah,
Duka ya kara kaiwa sitiyarin motar yace why Salawatu why ban son al,amari da shirka a rayuwa na,
Kada ki ruguje min farin cikin rayuwa na please ban son zama da cin amana
Da ire, iren wanan tunane har ya kawo gida bai sani ba,
Yana shiga gidan kai tsaye ya wuce zuwa dakin Sadiya,
Tana zaune a kasa plate din da taci abinci yana gefe guda ajiye,
Ta kurawa kasan ties ido dagani tunane takeyi a hakan irin yadda yanayin ta ya nuna,
Duk da kamshin jikin shi ya sanar mata da zuwan shi, a lokacin,
Amma hakan bai sa ta dago idon ta ba ta kalle shi,
A hankali ya tako zuwa gare ta gab da ita yadan rage tsawon shi ya tsugun na agaban ta,
Yai dan gyaran murya yace, Meenatu tace min ban kyauta maku ba yau,
Sai a lokacin ta dago ido ta kalle shi tace sai dace ma san nan kasan baka kyauta muna ba ko ?
Yai murmushin karfin hali tare da dan mikewa tsaye don haka ita ma tabishi da ido,
Yace kawai yan matsalolin rayuwane wallahi har suka sa na shafa ban zo mun gaisa ba na tafi,
Yanzu Abubakar har yakai ka fara guduna haka daga cikin iyalin ka,
Look Sadiya bana son ki aza min laifin da bashi ba don kin fi kowa sanin halaiyana
So ki yi hakkuri don akasi akasamu har hakan ya faru,
Ko dai don wanan shedaniyar matar taka ta dawo ne har zaka fara wulakan ta mu, ?
Wanan maganan ta kona mashi rai sosai amma sai ya daure don kada suci gaba da sa,in sa da ita,,
Daga dakin Anty Sadiya daki na ya nufa, tun kafin ya karaso muka san da zuwan shi na fito daga wanka na gama saka wata doguwae riga mai stones a gaban shi,har kasa
Ya bude labulen dakin ya shigo yana mai kallo na a cikin daure fuskan shi,
Ina ganin yanayin sa nagane cewa yana acikin fushine sosai,
Sai dai nasan cewa shi ba mutum bane mai aurin fushi haka da yawa,
Kafin ya karaso dakin nace mai sannu da dawowa Yaya
Yace still a cikin daure fuska yauwa,
Kin sha maganin ki kuwa na bashi ansa da cewa saura na dare ya rage min yanzu,
Yace Meenatu ni kike fadawa magana haka acikin waya ?
Hannaye na nasaka daya cikin daya ina wasa dasu idon ya na kallon kasan dakin,
Yaya zaki mai dani karamin mutum haka kna ganin cewa zan aje ku agida har wata tasa in manta da ku, ne,?
Azuciya na nace yaushe kuma Yaya saidai kada akara kawai,
Yi hakkuri Yaya ya furta a hankali ban fadin don rashin kunya ba ko raini,
Ido ya dan tsura min tare da dan kada kai ya juta yabar dakin nashi,
Nabi bayan shi da kallon murmushi na san cewa fada kawai ya keyi amma ya gane gaskiya,

Daidai fitan shi daga dakina su ka hade da Salawatu
Wani irin kallon mamaki tabishi da shi tana mamakin ganin dawowan shi gida acikin irin wana lokacin haka,?
Don dai time din dawowan shi bai yi ba amma kuma gashi gida a yanzu,
Dakin ta da taga ya nufa tai saurin son ta tare shi kada ya shiga amma sai ya tura kai kawai ya shiga,
Warin hayaki ne yaji ya tukake dakin nata ba dadin sha ka,
Da sauri ya juyo zuwa falo ta biyo bayan shi tana cewa lafiya kadawo yanzu,
Bai yi magana ba sai hayewa sama da yayi abin shi zuciyar shi cunkushe da bakin ciki,
Tabbas hasashrlen shi ya zama gaskiya ke nan don idan ba wani sheri takeyi ba may ye ma,a an wanan abin da tasa, haka,
Ita ce tashigo dakin dauki da jug da goran ruwa asaman ture,
Tun kafin takaraso dakin ya daga mata hannuwan shi alaman ta dakata daga can,
Ta ja ta tsaya tana kallon shi a cikin mamaki,
Yace ki koma da wanan sherin dake a hannun ki don dk wani abinda kike nufi ba zai yi tasiri akaina ba Salawa,
Ya dago rinanun idanun shi da suka kade sukayi jajir,
Yace nayi hating din wanan halin naki ki tuba ga Allah Salawatu basai kin yi shirka zaki samay ni ba,
Cikin jin nauyi da kunyan wanan hatsabibin mijin nata tace,
Ban fahince kaba fa Oga yace please get out with this nose's,
Sim,sim ta juya zuwa kasa da jug din da ruwa zuciyar ta da jikin ta sai rawa sukeyi,
Takai wani lokaci zaune tana tunanen yadda akayi har yagane wanan abin da ta ke shiryawa da sauri haka,
Yanzu ita yaya zata yi da wanan abin kunyan da tayi aka gane ta,
Dole ta tafi tabashi hakkuri akan kuskuren ta don dai iyanzu tasan cewa wanan mutanen sai Allah,
Yau gidan namu ya koma shiru kowa na dakin shi har maigidan falon yai shiru kama bamu gidan,
Cikin daure Salawatu ta fito daga dakin ta, ta nufi dakin Yaya Abubakar,
Jin an shigo dakin yasashi daga idon shi sukayi ido hudu da ita,
Yana kallon kofan yaga itace ya kawas da kan shi da sauri yaci gaba da abinda yake yi a system din shi,
Ta nemi guri dan nisa kadan dashi ta zauna duk jikin ta a sanyaye saboda nauyi da kun yw,
Yaya bai biyo ta kanta ba yaci gaba da aiyukan shi tankar bata agurin zaune,
Murya kasa,kasa tace Oga gurin ka nazo baidago kai ba still yana mai cigaba da ai,yukan shi,
Batai magana ba shima baibi ta kanta ba har yanzu,
Sai can ta daure ta fara magana ganin bazai kulata ba dai, tace,
Nazo gurin ka Oga in nemi afuwanka akan abinda ya faru, da zu,
Don girman Allah kayi hakkuri hakan ba halina bane wallahi sherin shedan ne da abokai,
Sai a lokacin ya daina abinda yakeyi ya fuskance ta,
Look Salawatu, ki sani ni bazaki iya komai dani ba Insha Allahu,
Kanki duk abinda ki keyi zai koma idan kin matsa don nafi karfin sherin ki,
Ina kuma kin tafi hargidan mu kinga irin yadda muke rike da addini acan,
To idan har kince shirka zakiyi da surkule akaina kan ki zai koma,
Salawatu ta sun kuyar da kan ta kasa don kunya da nauyi sai hawaye ke tsiyayowa aga idon ta,
Takara ce wa don girman Allah kai min afuwan insha Allah hakan bazai kara faruwa ba agidan nan,
Yaya Abubakar ya dago ido ya dubeta yace kin fara bani tsoro sosai ga ala,amarin ki
Don zaki iya kashe mutum saboda kina da karancin imani atare da ke,
Kinga zama damu dake hatsarine babba don wanan abin rashin imani da Allah ke kawo shi,
Cikin kuka take cewa insha Allah bazan sake ba don hakan ma da ya faru dani zai sa na gyara sosai,
Katseta Yaya Abubakar yayi cikin daka mata tsawa yace,
Ke i min shiru nagaji da jin karyan yan ki bansan ma abinda yasa kika dawo min ida ba ,
Jahila kawai wace bata tsoron haduwar ta da Allah,
Yadda idon shi ya kade yai jawur yaba ta tsoro sosai don bata taba ganin shi cikin irin wanan yanan fushin ba haka,
Ya daka mata tsawa yace get out from my room,,
Sim, sim tafita yayin da yaya Abubakar ya dafe kan shi ciki wani yanayi,,,,



ZEEE MAKAWA YELW@
[9/9, 9:43 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
6? 9?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL - MUHSIN,,,


So sai na samu bed rest yadda ya kamata batare da wani tsangwama ba ko tashin hankali,
Zuwa yanzu cikina ya zaunu a jikina don na dai wanan yawan alolayin da nake yawan yi akoda yaushe,
Yau zaune muke ni da Fattu a daki na ta kawo min ziyara, yini ,
Kayan lefen da Yaya Abubakar ya saiya min su ne, tai ta cirewa guda guda tana kallo,,
Ta gama kallon su a wahalce tana mai rike baki don mamaki,
Yanzu duk wanan kayan hakka Meenatu yanzu na yarda da zancen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login