Showing 261001 words to 264000 words out of 388021 words

Chapter 88 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8275

fili ba kowa na jina sai ji nayi anty tana karba min da cewa Ameen ya Allah,
Tace cikin lumshe idanuwan ta gaskiya Meenatu mu godewa Allah mu godewa malam tsoho wanda ya hada auren ki da wanan bawan Allah,
Don kin san may na girgiza kai a hankali alamar a,a tace,
Da yanzu duk wanan abin a can waje wa mutanen duniya zai kai su,
Kinga a gare ki kuma zai shafi har wanda bai tsan mani ba daga cikin yan uwan ki,
Zaki dinga bada alheri da kika samu daga gare shi ga yan uwan ku suna ci su ma,
Amma da za,ace duk wanan auren da yakeyi a bare yake yin su zalla to babu mai samun irin wanan alherin ka a zurian ku,
A hankali nace hakane anty don ko Baba MUSA abinda naji ya fada ke nan lokacin da nai mashi wani alheri,
Tace gaskiya Meenatu mutanen da irin hikimar su ke nan ta kokarin hada auren zumunci a tsakani ya, yayen su ,
Amma mu yanzu kin sai muce ai kai ya waye bazamu yarda da irin wanan hadin ba sam,
Daga ke har shi, duk an samu masu tarbiya da biyayyan iyayye ne idan bashi, ba aida baza a kai ga hakan ba ma,
Murmushi kawai nayi ba tare da na ce mata komai ba akan zancen da take yi,
Inda take cewa har yanzu ita mahaukaciyar uwar shi bata gane nufin wanan bawan Allah ba gare su, baki daya,a,
Don haka Meenatu ki daure kici gaba da tallafawa yan uwa da abokan arzkin ku,
Don idan bake ba ce a gidan babu wanda zai fada mashi halin rayuwan da yan uwa suke a ciki har ya tallafa masu,
Domin kiga musali duk sauran mata kowa kokarin taimakawa yan uwar ta zata yi ba ruwan su da zancen yan uwan miji,
Saboda Samira ta fada min duk yadda kukayi a waya da ita da kuma mahaifiyarta,
Anty taci gaba da cewa wallahi Meenatu ke alheri ce gare su domin ke wata hasken lantarki ne a gaban su mai hasko masu alheri agurin da ya kamata,
Karan wayana dake agefena ya sata katse zancen da takeyi a lokacin,
A hankali na mika hannuwa na dauko wayan tare da dan gyara zamana da kyau,
Kafafuna na zubo su daga saman gadon da nake a kai, tare da dan tokare hannaye na a gefe guda,
Muryan shi ne ya daki kunnuwa na da zuciyana a lokaci guda,
A cikin dan lumshe idanu na karba mashi sallaman a hankali,
Meenat kuna lafiya ya zafi ya sokoto, da karatu abinda ya tambaya ke nan a gagauce a lokaci guda,
Shiru na danyi na dan lokaci guda batare da na bashi amsa ba don ban san wani zan fara amsawa ba daga cikin tambayan,
Wani murmushi mai sauti ne naji ya sake daga bangaren shi
Yace ko baki ji may na ce bane ,?
Na amsa a takaice da cewa, Alhamdullahi komai lafiya,
Sigar da yake magana yasa na fahinci cewa tana da wani manufa yin hakan,
Shiru nayi ina sauraren mai zai fada min don nagane da manufa a tare da shi,
A hankali naji ya kara kiran sunana akaro na biyu
Na ams??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a mai kamar farko da cewa, na,am, Sadauki sunan da idan na kira yake sa shi lumshe ido
Don sunane dai sai yan uwa na jiki suka san da wanan sunan ake kiran shi,
Kamar a fili nake yana kallon na yadan sakar min harara ta wayan yana cewa,
Baki da kunya ko bazaki daina kirana da wanan sunan da yan uwan Mama ke kirana dashi,
Murmushi mai kwantar wa da mai sauraro zuciya na sake ta wayan ina, cewa sunan yana min dadi ne sosai, a,raina,
Kamar wanda nake gani a fili ya daure fuskan shi tamau yace,
Kamar da gaske aida baki avoidin dina ba kin guji mai sunan ba ko waya kwana biyu da baki nisantani da farin ciki na ba muradina,
Wai ko kin san cewa kullun ina maijin haushin nisanta ni, da ki kayiwa baby na,,
Murmushi nayi tare da cewa ai bazamu dade ba zamu zo kwanan nan ,
No ku zauna abinku don ni ma kwanan zan danyi tafiya zan tafi UK, wani dan seminar da zamuyi a can,,
Wani iri naji yayin da yake wanan zancen yace gida kuma ana muna gyara shine a yanzu,
A sayaye na ce tafiya zakayi ne Yaya kwanan nan ya amsa da cewa insha Allah,
Take gabana ya fadi don sai kawai naji banji dadin tafiyan da zaiyi din ba
Shiru nayi kamar wace bata online a lokacin saboda dan tunanen da na shiga,
Muryan shine yake cewa, ba wai zan dade bane two weeks kawai zanyi na dawo insha Allah,
Don kin san ranan Friday mai zuwa za,a daura min aure insha, Allaha
Wani irin dam, dam zuciyana ya harba alokaci guda,
Sai wani irin zafi da ya ziyarci zuciyata gabana ya tsinke shiru nayi tankar ban saman network din a lokacin,
Hello Meenatu kina jina kuwa na amsa a hakali da gurin da nake zaune wani abu yana min yawo yarrrr a lokaci guda,,
Amma haka na daure cikin dakiyan zuciya nace Allah ya kai mu lafiya,
Idan kuma katafi Allah ya tsare hanya aje lafiya a dawo lafiya Allah ya bada sa an tafiya,
Ya amsa da cewa ameen a bangarena duk na matsu da ya kashe wayan ,
Saboda naji dadin yin nazarin halin rayuwa da na tsinci kai na a yan dakikun mintuna, da suka shude,
Can na tsinkayo muryan shi yana cewa nace Aliyu ya kawo maki sako kudi da wasu yan kayayyakin amfani kafin mu dawo,
Da sauri na katse shi da cewa indai Aliyu ne zai kawo min sako don Allah abar shi, nagode I,am OK here,
Yagane may nake nufi sai naji yace hmmm raini ya fara shiga a tsakanin mu ke nan ko,
Don har ina, fadi kina fadin naki saboda ba respect a tsakanin mu yanzu ko ?
Cikin murya kasa kasa nace ni gaskiya indai shine zai kawo min sako wallahi bazan karba ba yaje ya kai wa sister din shi nata kawai,
Sai kawai na kashe wayan batare da najira naji may zai ce ba,
Ya dade yana mamakin irin abinda nai mashi sai kuma ya murmusa a zuciyar shi yana cewa ashe ko wace mace ta iya kishi haka sosai, ke nan,,
Bayan na kashe wayan na dade zaune a gurin a cikin bacin rai, da irin rainin da yaya zai min Aliyu ne wanda sukai min kutun kutun har sai da yaga yar uwar shi agidan zan yarda dashi yanzu,
Wallahi sam bazan dauki wanan rainin ba tun yanzu don kawai ya mayar dani gakane zaice zancen siri tsakani na dashi sai Aliyu ya san komai, akai,
Duk da naso na tambaye shi ko zai samu dan yo muna sayayya a can amma sai kawai na dake ban ce mai komai ba,,

****** ********** ******
Kamar yadda aka tsara ayi daurin aure a ranan jumma,a bayan an sauko daga massalacin jumma,a din,
Inda itama Fatima yanzu tana daga cikin iyalan yaya Abubakar a cewan ta,
Ta caba kwalliya tai kitso ta zubo shi a gaban goshin ta, sai sheki takeyi yan uwanta sun taru don taya ta murnan wanan auren da ta daura da tsohon masoyin tana tun farko,

Babu wanda ya bugo min zancen auren acewa malam tsoho wanda ya gargadi yan gida mu akan cewa kada wanda ya fada min ,wai saboda ina cikin lalura ina dauke da ciki a jikina,
Abinda bai sani ba shi mai dungurun gun ya kirani ya fada min ko tun kafin a daura,
In ma mutuwa zanyi inyi shi dai a ganin sa ai ba komai bane don zai yi aure kuma ina da ciki a jikina a lokaci ba wani abinda zai faru,
Andaura, auren washe gari suka bar gari shi da Salawatu zuwa kasar United kingdom,
Can cikin dare ina ta sauraren kiran yan uwa na tun jiya amma babu wanda ya kirani,
Hakan yasani zaton cewa wata kila ba,a daura auren ba anfasa ke nan abinda nake tawa adddu,a ke nan a zuciyata,
Idona suna a lumshe ne naji kiran waya yana ahigowa na dauka don inga ko waye,
Sai dai ban sheda nomban ba don eitel ne ban san mai nomban ba sam,
Nadauka murya irin ta maijin barci naji ana cewa Meenatu har kin fara barci ne ,
Na sheda muryan Sister dinace Aisha diyar Baba Hamza,
Mun gaisai take magana acikin kashe murya kamar mai rada tana cewa,
Kina jina don Allah ki rufe ni don malam yace wai kada a fada maki tun jiya Yaya Abubakar ya auri wanan yar bazabarman,
Murmushin karfin hali nayi duk da gabana ya fadi amma sai nace Allah sarki malam aishi mai auren ya fada min ko,
Ta tambaya da karfi da cewa Yaya Abubakar ya fada maki fa Meenatu ?
Na amsa mata da cewa wallahi ko Anty Aisha ya fada min yau kwana hufu ke nan,
Sai naji tana cewa shikenan abinda malam ke cewa wai kada a fada maki ashe ma kin sani, ko,
Tace gashi kuma ango ya tafi shida waccan amarya taku ta Abuja tafiya kasan waje,
Runtse idona nayi don jin zafin zancen da take fada min amma sai na daure don kada, ta fahinci cewa na shiga rudani,
Nace Allah sarki, haka yace min zasu wuce a , sai danzu yake ce min za su tafi ,
Nai sauri canza zancen da cewa to yaya garin dai kowa lafiya a gida ko,
Tace duk lafiya muke mudai ta jin zafin wanan irin auren na yaya Abubakar har aure uku a shekara guda,


ZEEE MAKAWA YELWA,,
[10/1, 9:29 PM] MAKAWA: =?x?=?x?=?x?TARKO=?x?=?x?=?x?
=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?=?x?
8? 0?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- ASS- SAMAD,,,

Fatan Alheri gare ku duk kan masoyana tare da fatan cikawa da imanin ubangijin mu,
Don Allah muyi hakkuri ga irin yanayin da novel din yazo dashi ba wai son ra,ayi bane abin,
Muna son mu cin ma fadakarwan da novel din ke son ya isar muna ne dafatan zaku fahince ni,
Nagode da kulawan ku a gareni yan uwa, kunsan cewa novel ne babu time mai tsawo da zamu sa cewa, yaba da dan tazara aure a tsakanin su, don dole haka zamu matsa mu bada labarin don ya tafi daidai,


Ina aje wayan bayan munyi sallama da Anty Aisha, sai naji wani irin hawaye ya sulalo min a fuska na masu dumi,
Daga haka na samu na dan sake kuka abinda ya jawo min dan jin sauki a zuciyata,
Na mike na fada bathroom din mu na dauro alwala nazo na tayar da sallan nafila,,,
Hakan yasani jin sauki sosai a zuciya ta atake barci mai nauyi ya kwashe ni batare da tsayawa wani kwankwanto ba,
Da safe ko da na tashi duk yadda naso kaucewa Anty Amarya don kada ta fahinci cewa nayi kuka sai da ta gane hakan gare ni saboda tsananin kulan ta gareni,
Ina zaune muna break fast azahiri cinakeyi amma a gaskiya cusawa nakeyi kawai badon dadi ba.
A hankali cikin natsuwa Anty Amarya wace ta mika hannuwanta daukan soayyayen irish take cewa,
Meenatu na horeki da sawa zuciyar ki damuwa tun farko kasancewar ki mace mai ciki, wace ke dauke da wani nauyin halitta irin nata a jikin ki,
Shin baki san cewa damuwar ki zai iya shafuwan abinda ke a cikin cikin ki ba,
A hankali na sake kuka tace min ita ma a hankali ishiiii bana son wanan hawayen please,
Zan bude baki inyi magana sai take ce min ban son ki ce komai mu mata dama yan hakkuri ne saboda bamu da wani power, akan mazan mu sai yadda sukayi da mu,
Tace saukin shi guda shine idan Allah ya hada ki da dan mutunci wanda yasan darajan dan Adam,
Amma aishi maigidan ku Meenatu banda auren nashi gaskiya baida wani tsanani akan mace,
Murmushi nayi, nace, hmmm kawai don batasan halin irin miskilancin Yayana ba ne tace hakana,,
Haka dai tai ta kawo min musalai irin iri akan maza inda take ce duk wace tasa zancen namiji a rai zata kwana acikin wahala,
Zantutukan ta yasa nakara jin wasai sosai a rai na tankar bani bace wace ta kwana a wahalce, daren jiya,

****** ********** ******
A gurin Fatima Amaraya wace sai faman shiri takeyi don tarin angon ta don acewan shi, idan ya dawo zai wuto birnin kebbi ne direct, idan yadan huta,
Hakan,ne yabata daman yin gyara na musan mam wanda zai kara shigar da ita gurin mijin ta,
Mama Ladi wace a ranan tankar tayi hauka don yadda labari yazo mata kawai cewa andaura aure batare da ta san wani abu daga zancen auren ba,
Don haka washe gari duk yaranta suka taru gurin ta don kwantar mata da hankali,
Inda take shiga banan take fita ba akan Fatima da yan uwan ta,
Don ita so tayi wai ta tafi har gidan da kanta don ta samu tayiwa Fatima da iyayyen tas da zagi,
Sai dai jama an gidan mu da diyan ta basu yarda ba taje sunyi ta bata hakkuri a kai,
Har dai tagaji ta hakkura da zancen tace ai tashigo gidan zata gane kurenta ,
A can kuma gurin tafiya Yaya Abubakar ya samu hankalin Salawatu ya kwanta don haka ya shiga aiwatar da abubuwan da yazo yi can din,
Sai goshin zasu dawo ne yafita da ita akan cewa suje su dan sayo tsaraba, wa mutane,
Kusan duk tsaraban da aka siyo kanta taiwa tsaraban mai yawa bayan a tare yaba da kudin na mu hudu gaba dayan mu, ta sayo,
Duk da ya gane sai bai nuna ba sunyi magana da Jummai Dubai, cewa ta sayo mai kayan baby hakan ne yasa bai wani wahalas da kanshi gurin saye ba acan,
Saidai a wani shago yaga wasu set na kayayyakin baby kalakala yabashi sha,awa ya sayo tare da hado wasu yan kayayyaki a can din,
Sun dawo gida lafiya tare da takardan da yasamu na yabon aikin shi a can ,
Nidai tun tafiyan su sau guda ya kirani, a waya yana sheda min cewa sun tafi shida Salawatu inda nai masu adawo lafiya ,yake tambayana lafiyan jikina ce mai Alhamdullahi,
Still yadda ya fahinci magana na akwai wata a kasan zuciyata don haka sai ya basar tankar bai fahince ni ba,
Tun daga ranan bai bugi min ba sai bayan da suka dawo da kwana biyu ya bugo min da dare a lokacin muna falo zaune muna kallon wani program a Sokoto tv,
Zuwa lokacin cikkna yafito da kyau yai girma sosai zaka iya ganin shi tun daga nesa,
Ganin nomban shi ta nan kasar Nigeria ya,sani gane cewa sun dawo ke nan, daga tafiyan su,
Na dauka da sallama tare da gaishe shi cikin ladabi, ina tambayan shi sun dawo lafiya,
Bai amsa min ba sai dai yar murmushin da naji ya sake ta wayan yana cewa
A, murmushi yana cewa ina mamakin yadda ake kokarin haramta min jin lafiyan iyalina da karfin Allah,
Azuciya, ta na ce namiji ke nan yana nufin cewa shi baida laifin komai a cikin zancen ke nan, ko ?
Na dai amsa a fili da cewa uhumm aini ban isa in haramta maka abinda Allah ya halasta maka ba,
Wani dan dadi ne ya ziyarci zuciyar shi don jin may nace mai, yana cewa, ai ina ce ko rowa ake min haka,
Nan yake sheda, min cewa zai shigo banda gobe don yana son zuwa birnin kebbi ne,
Wani iri naji a raina amma afili sai cewa nayi Allah ya kai mu jibi lafiya,
Ya amsa da cewa Ameen ya Allah sai nazo kenen ki shafa min blood dina kafin nazo,
Murmushi kawai nayi batare da na ce komai ba, muka kashe wayan,
Wani irin kishine ya turnikeni lokaci guda tare da hadiya yawun bakin ciki,
Watau zai zo birnin Kebbi gurin amaryan shi ke nan yake nufi zuwa ko ?
Duk nisan tunanen da nayi ni kadai abinda ban sani ba shine idon uwar daki wace tun fara tunane na hankalin ta yake gare ni,
Ina sauke ajiyan zuciya yayin da nakai karshen tunane na sai karaf idona acikin nata,
Dan murmusawa nayi mai kama da yake a fili wanda na fahinci cewa ta gane may nakeyi,
Daga gurin da take zaune na tsinkayi muryan ta tana cewa ki dai kwantar da hankalinki, kawai, ki samu ki haifu lafiya,
A hankali na daga kai alaman to na ci gaba da kallon abinda akeyi a cikin tv,
Sai dai a can kasan zuciyata ni kaina, ina mamakin yadda na sa zancen auren nan na Yaya Abubakar a raina,
Sam banyi wanan damuwar ba a lokacin auren Salawatu da shi,
Kai kishi ho kishi ya hanani in fuskanci al,amuran gaba na ,to wai ma may nakewa kishi a gurin Fatima ne,?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login