Showing 318001 words to 321000 words out of 388021 words

Chapter 107 - Tarko Book Complete Book by Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

8273

Murmushi na kakaro a fuskan ina dan hade wasu yawu masu kauri da suka tsaya min a baki,,
Kafin na kai ga magana, mu kaji muryan mijin Fattu Lawal a kofan shigowa part dina ,
A take aka fara dan kimtsawa kowa tana jawo hijab don ta saka ta rufe jikin ta,
Sai da na tabbatar da cewa sun kimtsa jikin su nai mai iso da ya shigo,
Yashigo bakin shi dauke da sallama yana mai kallin yaron dake goye a bayan Mama Sa,adatu, kishiyar Mama Ladi mahaifiyar Yaya Abubakar,
Bayan mun gaisa dashine yake mai fuskanta su Mama yana cewa maigida ya umurce ni da nazo da wani don ya duba yaron,
Shine nai sammakon zuwa Suleja nazo da mutumin yanzu haka yana falon gidan yana jiran a futo da yaron,
A tare da su, Dije ya fito falon inda mama Sa,a ta sauke yaron ta mikawa Lawal shi,
Mutumin ya karbi yaron ya dan duduba shi tare da juya shi ta ko ina yana mai duban shi sai kace, wanda ke son ganin wani abu a jikin yaron,
Sai yadan sake murmushi ya dago kai yana duban Lawal a cikin jijiga kai yana cewa, Allah ya kyauta, amma wallahi sherin sihiri ne wanan,
Ya juyo inda muke yana cewa ku kadaine a gidan ko ?
A tare ake ce masa a,a akwai sauran mutane yace kowa yafito yazo nan,
Take Lami ta gaiyato duk wanda ke cikin gidan muka taru a falo kowa na kallon mutumin dake ta faman hade, hade a cikin wani bakin leda,
Saida ya gama abin da yake yi sarai ya dago kai yana cewa to kowa na gidan yana nan ko,
Nace Baba Wadda da Baba Hamza badu a gurin nan Lawal yace suna daga waje bari na kira su, ,
Wani hayakine mutumin yazuba a cikin wani dan kasko tare da bin hayakin da kallo cikin daga idon shi,
Mikewa yayi ya fara bin inda hayakin ya nufa mudai sai ido muke bin shi dashi kawai,
A can kusurwa tsakanin tagan bathroom din Sadiya dana Fatima wanan mutumin yakai wani lokaci a tsaye gurin,
Ya juyo ya fara bin duk wani kusurwa musan man na bath room yana yarfa wani abu har zuwa cikin falon gidan,
Yace a cikin hausan mutanen suleja ai wanan yaron Allah ya tsare abinsa da gaskiya sai buzun shi,
Kuma yadda abin ya so yai mai karaf guda don da jinin mahaifin shi a jikin shi sa yanzu an manta da shi,
Salawatu ce ke tambayan Lawal a cikin gadara to wanan abin da akeyi mu ya shafe mune wai,
Kafin Lawal ya bada ansa mutumin yai murmushi ya ce ya shafe ku mana tunda matar maigida kike,
Kai duk ma wanda ke tare da shi abin zai iya barazanar cutar da mutum badon komai ba don anyi sihirin ne da sunan duk wanda ke tare da mai wanan gidan,
Amma yanzu sai ku saurara mu gani daga yau zuwa kwana uku insha Allahu duk wanda ke da hannu a cikin wanan abin gaskiya zai baiyyana,
Nan ya ba mu dan sharhin cewa anyi asirine da mahaifan magida,
Sai salati aka kama sakawa wasu kuma suna kallon dan jaririn dake barci a hannun Mama Dije,
Ya nuna yaron da yatsan shi yana mai nunawa da kai yace kunga wanan yaron to rabon ne mai karfi ya kawo shi nan,
Don da ba,don Allah ba gaskiya al,amarin dake nan da wuya asamu haihuwa agidan nan,
Wanan dalilin yasa da aka shigo dashi ake kokarin bashi wahala aga har yakai ga salwanta,
Subbahanallahi inji Mama Dije tana cewa ta Allah bata mutum ba wallahi duk wani mai sheri Allah ya mayar mai da aniyar ta,
Sadiya tun zaman mu batace kalla ba saboda duk a kunyace take a gurin don tasan cewa zance bazai wuce guda ba,
Mutum yace ai yanzu insha Allah komai yazo karshe ke nan , daga yau,
Fatima tana daga gefe guda zaune da yaranta a saman kujera guda duk sun man,newa junan su sai addu,a takeyi a zuciyar ta akan Allah ya kare ta, da yaran ta,
Lami ko yar aiki ta riga da ta yanke shawaran cewa zuwa gobe zata bar gidan,
Sai muryan mutumin sukaji yana cewa, daga yanzu don Allah kada wata mace ta fita ko shigowa har nan da kwana biyu,

****** ********** ******
Mutanen uguwar, yau sun tashi a cikin wani bakon Al,amari saboda kukan halittan da ya zagaye uguwar su kamar tashin hankali, a cikin daren jiya,
Tun fitowa Sallah asubahi a massalaci jama,a suka kawo zancen wanan abin tashin hankalin da ya cika uguwar a daren jiya,
Zance ya kai zance a gurin kowa na fadan albarkacin bakin shi akan yadda zasu bullowa wanan al,amarin,
Karshe sun yake shawaran zuwa gurin mai uguwar shiyan akan zancen,
Karfe bakwai na safe duk magidan ta uguwan da matasa suna kofan gidan mai Uguwar shiyan,
Mai Uguwa yaga tashin hankali don haka daga karshe ya ba da umurnin cewa a kai, wa gidan Hajja samamay kawai abincika aga may ke saka wanan abu kuka kuma wani irin abune wanan, abin,
Hajja tana ciki duk abin duniya ya sakata gaba saboda yadda taga Dodon ta ya samu illa adaren jiya,
Sai nishi da fuci ya keyi don azaban da yake ji a jikin shi, tun daren jiya da yasha da ktat daga gidan Abubakar inda yake samun abincin shi,
Saboda ba karamin karuwa suke samu a gidan ba kasancewan hakan da suke samu a gurin shi,,
Sai gashi adaren jiya ya shiga gidan kamar yadda ya saba biyu iska yazo ya samu abincin sa ,
Yaci karo da wani irin masifan da aka saka daga ko ina nagidan,,
Hakan ne yasa shi dawowa gida a gigice maimakon yai mata aman kudi yau sai aman jini yake shega mata a wahalce,
Tun tana masa yan dabaru har takai yanzu ta saka mai ido tana kallon ikon Allah hankali a tashe,

Duk hayaniyar jama,an da ya cika Uguwar ta ko ina, fargaban halin da Dodon ta ke ciki bai barta taji motsin mutanen dake nufo gidan na ta ba ba,
Yara kanani mata maza tsofi sai matasa dake dauke da makami irin su adda, sanda gatari duk dauke a hannayen su,
A kofan gidan sukaja tunga an rasa wanda zaifara shiga,
Sai kallon kallo akeyi tsakanin manya da yara,dake tsaye a kofan, gidan nata,
Daya daga cikin matasan ne ya buga kofan da karfin Allah haka ya a sauran daman fara dukan kofan suna cewa ke kifito muna da ko ma may ye tau a gidan nan,
Sai yanzu ta farga da irin hayaniyan dake tashi a kofan gidan ta tun dazun,
Wani dan wiwi ne ya ce don Allah Baba ku jaye kawai na afka ciki yau koma maye sai mun fisgo shege a waje,,
Daga haka ya shige cikin gidan kai tsaye a daidai lokacin da take kokarin jawo kofan dakin da dodon yake a ciki ke nan,
Direct dakin ya nufa ya bangaje kofan dakin duk da a cikin maye yake bai hana shi kaduwa ba inda ya juya da gudu yana cewa,
Ayyatukursiya ka kareni kakareni daga wanan abun, da gudu ya wuce mutane yana cewa yau kan tamu ta samay mu,
Ganin shi haka a guje yasaka mutane artawa da gudu guri ya dauki ihu cikin tashin hankali, mata makwabtan Hajja sai fitowa suke da yaran su suna artawa,
Da kyat aka samu aka tsayar da wanan guy yen mashayin ana son aji may yagani,
Yace Alkur,an, tunda nake duniya ban taba ganin maciji maigirma ba irin haka don yafi wanan iccen na kofan gidan mai uguwa kauri da tsaye,
Take guri ya rue da sabon surutu kowa na fadin albarkacin bakinsa,
Wasu suce kawai dai idon sane yai mai wanan gizon yaga kaman hakana,
Wasu gungun matasa ustazai sukace su zasu shiga gidan su ganewa idon su komay ke nan,
Innalillahi wa,inna,alaihim rajjiun,
Da sauri suka gito daga cikin gidan suna kaduwa abinda idon su ya gane masu,,
Nan suka labartawa mutane cewa gaskiyane abinda wanan mutumin ya gani ya fada,
Magana da zance ya fara yaduwa acikin gari kowa da irin zancen da yake fadi akai,
Almajirin malam ne yazo masu da zance inda malam sai jijiga kai yake yana dan lumshe ido,
Dan sakon Sarki ne, yazo, da sakon ana neman malam a gidan sarki,
Malaman shiyan dama wasu malaman wani gurin aka hada zuwa gidan Hajja,
A lokacin Hajja ta koma tankar mahaukaciya sai wani abu takeyi ta na sambatu kamar yar bori,
Malam bai tsaya shakan komai ba ya fada gidan kai tsaye, tare da, addu,oi a bakin shi,,
Abinda ya gani ya tayar mai da hankali sosai, don haka, ya daga wa sauran hannu alaman su dakata,,
Ya umurci wanidaya tafigida yazo mai da wwasu abubuwan amfanin shi,
Aikuwa cikin yan mintina kadan sai ga dan sako ya dawo inda ya bawa malam sakon,
Wani irin kuka Dodo ya fara wanda ya ruda mutanen dake gurin gaba daya suka fara watse dan nesa kadan, da filin,
Dodo yana kukan kaji kukan akuya kukan, jaki dana shanu, harda na agwagi,.
Mutane sai ihu da addua sukeyi suna watsewa don tsoro,
Kuka yanzu ya keyi tankar na mutane, yana cewa Hajja ta cuce su ta bari za,a wullakanta su bayan ta samu moriya mai yawa daga gare su,
Ya karshe yana kuka tankar mutum yana cewa wayyo sun kashe mu shikenan yau kwana na yakare,
Ita ko hajja ta yanka wani irin ihu tare da faduwa kasa tana birgima tana cewa yau asirinta ya tonu yau anja mata bala,i,
Labari duk ya zagaye gari ko ina sai zancen akeyi wasu har da kari,akai don zancen yai dadin fada,
An bugo wa Baba Wadda waya ana sheda mai abinda ya faru kamar almara labarin,
Bamu fadawa kowa ba saboda kawai cin a gurin Sadiya don ko ba komai ai ana tare ko a gida,
Amma dai a can daki munyi ta surutu a tsakanin mu muna zagin Hajja akan irin sherin da ta dade tana yiwa diyan cikin ta da ta haifa, da cikin ta,
Kuma saboda son kai da rudin shedan ta aikata masu sheri da kyata wai don kawai ta tara abin duniya,
Fatima wace ana gama fada mata abinda yafaru a gida tana kashe waya tafito dalo cikin daga murya tana cewa,
Yau kan dubu ya cika don Allah ya tona asirin azzaluma, kowa ya gama ganin gaskiya a fili,
Mutum saboda da sheri ya rasa wanda zai cuta wai sai diyan cikin shi zai zalunta,
Mu kan wallahi maye ko yana tafiya yana ballin wutane bai taba cin mu don kurwan mu kur wallahi,,
Babu wanda ya tanka mata har ta karashi tsiyanta ta kwasa zuwa dakin ta, tana bambami,
Sadiya tana daga dakinta tana jin duk irin tsiya,takun da, Fatima take fada a kan ta,
Babu yadda za,tayi dole ta ja bakin ta tai shiru saboda uwar su ce ta jawo masu wanan abin faden har jikoki,
Irin yadda take ji a zuciyan ta sai take ganin kawai ta koma gida don wanan abin kunyan da may yai kama

Bayan komai ta lafa Anty Amarya tai shirin komawa gida inda muka shiga kasuwa tare mukayo sayayya,
Mahaifana tare da yan uwana, na kashe masu kudi masu yawa don, duk kudin dake a hannu na a su ya kare,
Ana gobe zata tafi mun kai wani lokaci zaune ni da ita muna kara tataunawa yadda zan bullowa al,amarin zaman gidan mu domin duk sungirmay min za,a ma ce sun haife ni kila,
Karfin gwiwar da Anty ta saka min azuciyata cewa nima fa mace ce mai yancin kanta kamar yadda suke yi zan iya har na fisu idan naso shi ya kara min kwarin gwiwa wajan kokarin ganin nafara aiwatar da nawa shirin zaman auren a cikin su,
Kamar yadda na fahinci irin ra,ayin kowacen su da irin nata halin rayuwan,
Nasan cewa nina ina kshin su wani lokaci a raina to amma ba wai irin can din nan ba da suka dauka su da zafi a kaina,
Don gaba dayan su a zuciyar su suna jin haushina da takaicina ganin irin yadda karama dani amma na dan fi su samu power a gurin miji,
Nikuma a nawa gani su sun fini samu power sosai gare shi don sai inga suna abinda suka ga dama amma saboda hakkuri ne ko so irin na yaya bai iya daukan wani mataki akan su,

****** ********** ******
Wanan tafiyan da Yaya yayi yayi ta a cikin sa,a sosai don ba karamin alheri yajawo mai ba,
Saboda hazakan, shi da ya gwada acan ya samu kyaututuka masu amfani daga hannun manyan yan kasuwan kasashen duniya, da suka ji dadin yadda ya warware matsalan da ke addaban su shekaru da dama,,
Ya siyu muna abubuwan bukata masu muhinmanci a rayuwan mu tare da sarkokin gold masu tsada,
Abubuwa dai masu muhinmanci ya siya muna daga can duk a cikin riban da yasamu can din,
Ko da yaushe muna makale da waya muna mashi ya gajiya ya aiki, da sauran abubuwa,
Ko wacen mu tana kokarin nuna nata bajintan don kawai ace ita ce star a gurin miji tafi sauran samun guri,
Yau ma hakane kamar kullum ina zaune a kusa da Dije wace hankalin ta gaba daya yana ga program din da akeyi a tv na girke girken gargajiya,
Sai kawai naji ina bukatan jin muryan dan uwana masoyina mijina uban dana,
A hankalina ke neman layin shi don inji lafiyan shi saboda munyi waya da safe yake ce min zasu shiga wani urgent meeting ne a lokacin,
Kira daya a na biyu naji ya daga wayan inda yake magana a kasalance,
Yana cewa Meenatu, yaya kuke ina big man, yana lafiya ko ya bakin ki,
Ina mai lumshe ido tare da jin dadin muryan shi da naji, har a cikin raina,
Hakan ya sani sakin ajiyan zuciya, wanda shi kan shi yaya Abubakar din sai da yaji tankar yana a kusa dani ya jawoni zuwa jikin shi,
Cikin dan lumshe Ido nake Yayana kana lafiya ya aiki da jama,a yace Alhamdullahi kaunata,
Murmushi na karayi tare da dan yin shiru na wani lokaci sai yake ce min Meenat nikuma a lokacin nake cewa yaushe ne zaka dawo Yayana, ?
Masha Allah Meenat yau kece mai tambayan yaushe zan dawo ashe yanzu andamu da yayan ke nan, kodai Big man ne ke tambayan Baban shi,
Murmushi irin maija din nan nayi ina cewa haba dai Yayana ai kaima ai kasan ko adacan andamu da kai,
Yace to Alhamdullahi tunda yanzu har anfara fitowa fili ana gwada min so irin haka,
Yace insha Allah kwanan nan zan dawo Meenat ina nan ina shiri yanzu haka ina gurin sayen motane,
Da sauri cikin mamaki nake cewa mota kuma Yayana ga mota har uku a kofan gida ba ai komai da su zaka kara wani kuma,
Murmushi naji yayi yana cewa wanan din tana da kyaune sai dai na kasa zaben kalla mai kyau,
Ga Fari, Baki Green, Assh, Yellow, Brown, Red har Pink, akwai,
Sai cewa nayi ni sai naga kamar Baka zata fi daukan idon jama,a ko Yayana yace alright ina ga kawai na dauki baki zaifi na amsa da cewa gaskiya kam,
Mun kai wani lokaci muna hira dashi inda yake dan min bayani akan irin yanayin kasar nasu,
Amir ne ya farka daga barci ya fara kuka shine yasa muka tsayar da wayan ni dashi,
Ashe kamar yadda ya tambaye ni cewa wace kallan mota nake son ya zaba hakane ya tambayi sauran abokan zamana ,
Cikin ikon Allah kowa da irin kalar da ta zaba don haka kowa kalar da take ra,ayi ya saya mata,
Gaba dayan mu in person sai muna ji ai wanda duk ya tambaya to itace star tunda har ya na tambayan, ra,ayin mutum,, kowa ta hau iska ta jiji da kai cewa ita fa ta kai, don da ita miji ke harka, yanzu,
Lawal miji Fattu nai wa maga idan zai kai yaran Fatima school don Allah ya hada da Aisha diyan Anty Safiya wace take tare dani yanzu,
Hakan akayi kuwa don tare aka kai su school din yana da dan nisa sosai da uguwar mu,
Fatima bata da labarin cewa da Aisha za,a dinga zuwa school din sai wani fankama takewa mutane a cikin gida,
Sai ranan da Yaran zasu fara zuwa school Lawal yazo daukan su ta ga Ausha ta fito cikin nata shirin ,
A take ta nuna bacin ran ta a fili,,har ta kasa boye sai tafara yadda magana cew an gwada mata bakin ciki a fili, don za,a kai yaranta makaranta shine za,a dauko wata yarinya cen a hada su tare,
Babu wanda ya tanka mata badon tsoro ba ko fin karfi kawai sai don bin umurnin maigidan da yace baya son fitina har yaje ya dawo,
Yarinyar tayi kyau sosai a cikin Uniform din inda na sa Baba Wadda suka sayo mata duk wani abinda za,a bukata na rayuwan school din,

****** *********** ******
Alhamdullahi don kowan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login